...BASHI!

Page 27

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 27

__________🖌️Kallonta Sadiya take, ta kasa cewa komai, ita kuma tayi murmushi tare da faɗin "Ina so kamar yadda kika bawa yarona dabino da zam-zam to ko bayan raina ki zame masa uwa, na san Muhasin zai zame masa uba koda bana raye, ko ina raye ma dan Allah" Shiru Sadiya tayi, ita kuma ta cigaba da cewa ba wai ina nufin ki rayu da Muhasin ba, ɗana ne kawai bana so a goranta mishi"
Sai lokacin Sadiya taji sanyi a ranta. "Karki damu, zan riƙeahi tamkar nina haifeshi" "Nagode, ni kuma na yarda zan koma gidanmu, ara min waya na kira Mommy"
Fito da waya tayi ta bawa Aziza, ita kuma a take ta kira number.

Tana É—agawa ta sauke ajiyar zuciya. "Mommy ina yini"

Mommy dake kwance sai da ta miƙe zaune jin muryar Aziza.
"Aziza" "Na'am Mommy ina yini" "Lafiya lau ya kike?"
"Lafiya lau, kin gama fushin kenan?"
"Mommy ni bana fushi dake, kawai hukunci da kika yanke ne na ɗauki zaɓi"
"Zaɓin naki bai ɓulle ba shiyasa a yanzu kika kirani?"
"Mommy naga kamar bakiyi kewa ta ba"
"Naga kin zaɓi duniya ne a kaina shiyasa"
Ajiyar zuciya Aziza ta sauke, da ƙyar ta iya faɗin "Dama na kiraki ne in faɗa miki na haihu an samu namiji"

Mommy miƙewa tayi tsaye ta fara yawo a ɗakin kafin ta ce "To kira kika yi na tayaki farin ciki ko kuma kin kira ne ki bƙanta min?"
"A'a, na kira na faÉ—a miki na haihu kuma ina so na dawo gida"
"Amma dai ba da shege ba" Taji zafin furucin dan har sai da ta É—an lumshe ido najin radaÉ—in furucin Mommy.

"Mommy dashi zan zo, ina zan barshi in ban zo dashi ba"
"Ba zan taɓa yarda ki dawo min gida da shege ba, wallahi naso kin haifeshi ba a raye ko kin yi ɓarinsa, Aziza kin cuceni"
Kuka ta fashe dashi tare da kashe wayar, tana ganin Mommy na kira amma taƙi ɗagawa.
"Kiyi haƙuri, ban san abin zai ɓata ranki har haka ba, da ban ce ki kira ba.
"Ba zan koma ba Sadiya, anan zan ƙare rayuwata" Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka, Sadiya ta rungumeta tana rarrashi.

*Bayan Wata Biyu*

Tana fitowa daga hall taji gabanta ya yanke ya faÉ—i "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta a sanyaye. "Lafiya kuwa?" Janan ta tambaya.

Kallonta Sadiya tayi sannan ta ce "Kawai ji nayi gabana ya faÉ—i" Ta faÉ—a tana kallon Janan. "Ba komai insha Allah alkhairi ne" "Allah yasa"

Wayarta da ta fara ringing ta kalla taga sunan Aziza na yawo. Da sauri ta É—aga tare da faÉ—in "Auntyna barkanmu da rana" "Yauwa Sadiya ya karatu"
"Lafiya lau, Ya Junior fatan yana lafiya"
"Eh Alhamdulillah, ina so yau idan babu damuwa ki shigo please, akwai maganar da zamuyi"
"Okay to babu damuwa insha Allah zan zo da mun kammala lectures"
"To Allah ya kawoki lafiya"
"Amin ya rabbi, sai nazo" Tana katsewa ta kalli Janan "Muje wallahi yunwa nake ji kin san ban samu naci abinci ba muka fito" "Okay muje ko" Sun fara tafiya suka wuce wasu 'yammata a zaune, sai kuma Sadiya tayo baya da sauri.

Kallon budurwar take, cikin tashin hankali tana ƙara ƙarewa zoben hannunta kallo, sak irin zoben da ta tsinceta a hannunta a ranar da aka mata fyaɗe. "Kaiii!..." "Lafiya kuwa?" Janan ta tambaya. "Ba lafiya ba Janan" Sadiya ta faɗa tare da ƙarasawa gaban budurwa ta riƙo hannun da yake ɗauke da zoben. Fuzgewa tayi tana kallonta kafin ta ce "Lafiya? Meya haka?"
"A ina kika samu wannan?" Sadiya ta furta tana pointing É—in yarinyar.
"Ji wani rainin hankaƙi ina ruwanki da inda na samu?"

Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo mata a fuska, ta kalleta ta ce "Dan Allah ki faÉ—a min" 

"Anisa kin santa ne?" Ɗaya daga cikin ƙawayen tayi tambayar.
"A'a, amma da alama itama ta san sani abu" Sai kuma ta kalli Sadiya "Ina so ki zo mu koma inda babu mutane sai muyi magana" Kai ta gyaÉ—a, tare da kallon Janan "Ina zuwa" Janan da ido kawai ta bita dan ta kasa fahimtar komai.

Bayan hall ɗin suka nufa, suka samu wasu kujeru suka zauna. "Tun dana ga kin riƙo hannuna na san tabbas kema kin san wani abu daga zoben nan" Anisa ta faɗa tana share hawayen da suka zubo mata.
"Naga kema irin zoben ce a hannunki hakan ya tabbatar min da wataƙila kema abinda ya faru dani shi ne ya faru dake, amma kafin nan ina son miki tambaya"
"Wace tambaya?" Sadiya ta faÉ—a jikinta a sanyaye."
"Wata nawa zoben tayi a hannunki?"

Shiru Sadiya tayi na wani lokaci kafin ta ce "Ba zan iya tunawa ba, amma kusan shekara"
Kai Anisa ta gyaÉ—a tare da faÉ—in nima haka ne, akwai wata Ć´ar BsC Biology itama hakane, idan na kintata dai-dai rana É—aya aka mana fyaÉ—e"

Zaro ido Sadiya tayi kafin ta ce "Taya haka zata faru? Bayan ba garinmu É—aya ba, ko kema 'yar Gaya ce?"
"A'a ni anan Kano nake"
"Ni ranar da aka min fyaɗe na fita ne bayan magriba sayen icce, sai naji naci karo da mutum kasancewar garin ya yi duhu da hadari sosai, daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba, sai tashi nayi na ganni a ɗakin hotel"

"Nima haka fa, tashi kawai nayi na ganni a É—akin hotel, a Gaya, haka Maryam ma, ya kamata muje gurinta muyi magana."

Sadiya jikinta gaba ɗaya rawa yake, ta miƙe a kiɗime. Haka suka je ta faɗawa Janan tayi haƙuri zata je ta dawo "Wai mene yake faruwa ki faɗa min"
"Janan zan faÉ—a miki amma bari in gama sanin abinda ban sani ba" Tana gama faÉ—a ta wuce 

Basu sha wuya ba domin Anisa ta san inda zata sameta, sai dai suna lectures, Anisa ta mata text a waya sai gata ta fito. 

"Anisa kece, sannunku"
"Yawwa Maryam ya lectures"
"Alhamdulillah! Lafiya kuwa?"
"Wannan" Ta nuna Sadiya "Matsalarmu iri É—aya ce"
"What...?" Ta furta tana ƙarewa Sadiya kallo kafin tayi saurin riƙo hannunta ta kalli zoben "Kema?" Kai Sadiya ta gyaɗa.

Sai da suka samu kujeru a plantation É—in sannan Maryam ta kalleta "Ya sunanki?"
"Sadiya"
"Ni kuma Maryam, ita kuma Anisa"
Anisa ta ƙara da faɗin "Shekaruna 17, Maryam kuma 18, ke kuma fa?"
"17 zan shiga amma ban ƙarasa ba"

Shiru ne ya biyo baya kafin Maryam ta ce "Mutum ɗaya ne, kuma dole akwai manufarsa ta yin haka, ina son na sani amma kuma kusan shekara guda a garin da ban taɓa zuwa ba aka rugurguza rayuwata, ni ina zargin duk wanda ya mana abin nan ɗan Gaya ne"

Anisa ta ce "Za ta iya yuwuwa ba É—an garin bane, acan dai plan É—in sa yake"

"Sadiya ke me kike tunani?" Cewar Maryam.

"Na fara tunanin wannan zoben ta tsafi ce" Dukkansu a tsorace suka miĆ™e tsaye. Kallonsu tayi sannan itama ta miĆ™e tare da cire zoben hannunta. "Rana É—aya aka mana fyaÉ—e kuma aka saka mana zobe a hannu, dole ne akwai tsafi a lamarin, ya kamata mu haÉ—u dan mu gano matsalar, mu zufafa tunani, kuma a wasu lokutan mu riĆ™a cire zoben dan tabbatar da abinda muke zargi, lokacin dana ga zoben a hannuna nayi tunanin wanda ya yi min fyaÉ—e ya saka min dan wata rana ya gane ni, amma kuma a lokacin da na ga Anisa da ita na fara tunani da ban, sai kuma ganin ki da nayi da ita hankalina ya Ć™ara tashi, kar mu bari mu cutu, akwai amfanin zoben a tare damu akwai abinda yasa aka saka mana ta yuwu ma lokacin É—aya aka yi amfani damu" Runtse odo Maryam tayi, ta buÉ—e tare da kallonsu. "Hakan ya kamata muyi" 

A take sukayi exchanging numbers sannan suka watse ko wanne da jimami a ransa.

             ****** ****** ******

Kallon shi take lokacin daya fito parlourn "Kamar shirin fita kake yi?" "Eh Mama" "Ka zauna muyi magana kafin ka fita" "Okay" Ya furta gami da samun guri ya zaun yana kallon Mama.
"Sadiya sunanta ko?" Jin ta ambaci Sadiya saka shi É—agowa yana kallonta. "Eh Mama" Ya furta a sanyaye.
"Okay so ina so ka kawo ta na ganta"
Shiru ya yi kafin daga bisani ya amsa mata da "To" 
"Zuwa gobe da yamma ka kawo ta"
"Insha Allah zan kawota."

Tashi ya yi ya fita, ita kuma bata ƙara ce masa komai ba.

Yana fita ya kira Sadiya a waya, sai dai har ya mata three missed calls bata É—aga ba, kai tsaye ya nufi school É—insu.

Ta ɓangaren Sadiya kuwa tana gidan Aziza, bata san meyasa ba sam bata son idan tana gaban Aziza ta riƙa ɗaga wayar Habib.

"Naga kamar kiranki ake yi" Aziza ta faɗa tana kallonta. "Ai ba wani serious kira bane shiyasa ban ɗaga ba" "Dama na kiraki ne in sanar dake wani abu da yake damuna, a matsayin ki na macen da nake gani a matsayin 'yar uwa naga ya dace na faɗa miki" "Ina jinki, Allah yasa dai lafiya" Shiru Aziza tayi kafin ta ce "To da sauƙi dai. Sadiya bana iya bacci da dare, kullum sai inji kamar ana sukar min ƙirji, sam bani da nutsuwa a tsorace nake, shi ne nake neman alfarma ki ɗan zauna dani anan, saboda har yanzu ban ƙarasa warware ba saboda kar ciwo ya danne ni da dare na rasa mai taimako. Idn har ba zan takuraki ba" Shiru Sadiya tayi kafin ta ce "Muna tare da Janan na san ba zata ji daɗi na barta ita kaɗai ba, amma dai zan yi shawara na gani"
"To shikenan ba matsala, kiyi shawarar"


Habib kuwa ko daya je school ya kirata bata ɗagawa still ya yi mata text babu reply, kawai ya kira number Janan, ita ta fito ta sanar dashi ai ta tafi gidan Aziza, ji ya yi ransa ta ɓaci sosau, wato dan tana gidan Aziza shi ne taƙi ɗaga kiranshi. "Dan Allah ko zaki kira ta a wayarki, ni na kira ban sameta ba" "Okay bara na kirata" Ta ɗaga eayar ta kira ringing biyu sai gashi ta ɗaga. "Hakan ya nuna kina ganin kirana kika ƙi ɗagawa"

Ji tayi ta daskare a zaune, ta kasa cewa komai saboda kunya, bata taÉ“a sanin yana sa number Janan ba. 
"Yanzu naga kiranka ina so na biyo sai naga kitan Janan ya shigo" Kar kiyi min ƙarya Sadiya saboda iya sarƙewar muryar nan kaɗai ta isa ta saka na gane ba gaskiya bane abinda kike faɗa."

Wani yawu ta haÉ—iya kafin ta ce "Ai gani nan yanzu zan dawo school É—in" "Kar ki damu kiyi zamanki a gidan Aziza, dama ina so dai na faÉ—a miki Mommy na son ganinki gobe, so ki shirya waluraren 5 na yamma zan zo na É—auke ki" "Yan..." Ji tayi ya kashe, dan haka ta sauke wayar ta kalla dan ta tabbatar sannan ta sauke 'yar ajiyar zuciya, sam bataji daÉ—in haka ba.

"Wanda zai aureki ne ko?" Kawai taji Aziza tayi maganar. Bata iya cewa komai ba, kawai dai ta sauke kanta ƙasa, tana jin zugi da raɗaɗi a ranta, sam bata so Habib yana fushi da ita, ita kanta ta san tana matuƙr ƙaunar Habib, bata san meyasa take irin haka ba. Dana sanin ƙin ɗaukar wayar ta fara.
"Karki damu Sadiya, ki daina ƙin ɗaukar wayarki saboda ni. Ai dashi kike soyayya ba yadda za ai na hanaki domin kuwa ko Muhasin ya dawo dole ya sakeki ki aure zaɓinki"
Murmushin yaƙe tayi tare da faɗin "Karki damu Aunty, kawai dama mun ɗan samu matsala dashi shiyasa ban ɗaga ba tun farko."

              ****** *******

Yana durƙushe gaban Arɗo, yana ƙra masa godiya a bisa kyautatawar da ya yi masa. "Babu komai, ai an zama ɗaya. Ni dai ina fatan idan ka tafi, in har ka samu lafiya zaka dawo ka auri Zaliha saboda tana matuƙar Sonka"
"Insha Allahu na maka alƙawari" Fatan alkhairi ya yi nasa sannan ya tashi ya ƙarasa inda Zaliha take.

Kallonshi take tana murmushi kafin ta ce " Yanzu gobe ya war haka kana garinku"
Ɗago manyan idanunsa ya yi wanda yanzu duk sun jame saboda rayuwar ruga, eayuwar da bai saba ba, ya saba kullum cikin AC, ga uwa uba damuwa. Fuskarshi sam babu gyara gemu ya yi tsaye, ga sajensa ma duk ya ƙaru ya yi buzu-buzu, gaba ɗsya dai Muhasin ya zama kamar ba shi ba. "Zan dawo insha Allahu"

"Ina fatan ace ka samu lafiya, ba dan aurena ba, kawai ina da burin hakan"
"Zan samu, ko ma ince na samu insha Allah"
"A tsawon watannin da nayi maka magani inda da tabbacin ka samu lafiya a yanzu"
"Nima haka nake fata, nagode sosai Zaliha ina matuƙar ƙaunarki, da Arɗo zai yarda, aurenmu za a ɗaura in tafi dake" Murmushi tayi wanda har ya bayyanar da haƙoranta kafin ta ce "Ai sai yaje da kanshi ya gani kuma ya tabbatar da maganin ya yi sannan zai yarda."
"Shiyasa nace maka ka zauna da matarka ina mai tabbatar maka ta haka ne zaka gane maganin ya yi."
"Kin dage dai ina da mata, bayan ni na san bani dasu"
"To ai zaka je kuma zaka tabbatar"
Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ƙara cewa komai ba.

Washe gari kuwa tunda farar safiya gaba ɗaya suka rakashi can cikin gari inda daga nan ya ƙarasa titin da zai samu motar da zata kaishi Mani. Sun yi tafiya mai nisan gaske, sannan kuma sun daɗe a titi kafin Allah ya kawo mota irin wannan 'yar ƙurƙurar da ake ɗibar kaya, anan shima ya shiga baya, yana riƙe da 'yar jskarshi.

Zaliha kuwa sai da hawaye ya zubo mata, da ta ga dagaske dai tafiya zaiyi. Kallon shi take shima yana kallonta har lokacin da motarsu ta É—aga har suka yi nisa yana É—aga masu hannu suma suna É—aga masa.

Ko daga Mani ma motar Katsina ya shiga, yana ɗaukin zuwa gida, gefe guda kuma yana kewar su Zaliha musamman ma ita daya shaƙu da ita sosai.

Daga Katsina kuwa direct motar Kaduna ya shiga sai dai har a lokacin bai ci komai ba, kuma har aka isa Kaduna bai saka komai a bakinsa ba, a Katsina dai ya tsaya ya yi azahar sannan ya shiga mota, wuraren ƙarfe biyar suka isa Kaduna.

Tana riƙe da hannun Mommy tana mata yankan farce. "Wallshi Mommy kina haƙuri da Daddy, ai na rantse da Allah Daddy ko hmm"
"Fa'iza kenan, haka rayuwar aure take, gaba ɗaya haƙuri ne a cikinta" "Mommy ba irin wannan ba"
"Zaki yi auren kema amma ban fatar miki auren irin mahaifinki"
"Ai wallahi kamar akan ƙaya nake, wallahi ban san zamana a Nigeria yafi daɗi ba sai dana je Mommy wata 'yar ficiciyar yarinya yake aure, sai zuba rashin mutunci take" "Tayi lokacinta ne"
"Mommy wannan da tazo its kuma shiru bata sake dawowa ba"
"Tunda kika ji bai magana ba ai ya san inda take"
"Lallai..." Jin Knockimg ne ya saka su yin shiru.

Fa'iza ta miƙe tare da buɗewa. Wani mahaukaci ƙara ta saki tare da rungumeshi "Mommy Yay..." Sai kuma ta tsaya ya kasa ƙarasa maganar.