Page 28
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
*_Wannan shafin sadaukarwa ne ga mabiya wannan labarin._🥰*
Page 28
__________🖌️Bata sake magana ba har sai da Mommy ta ƙaraso gurin. "Yaya kai ne ka koma haka?" Ta faɗa tana ƙare mashi kallo. "Muhasin" Mommy ta faɗa da raunanniyar murya tare da rungumeshi.
*Bayan wasu mintuna*
Fa'iza na zaune a gefen gadon, Mommy kuma na daga tsaye, an sakawa Muhasin drip har ma ya samu barci. Ajiyar zuciya ta sauje tare da faɗin "Fa'iza muje parlour" Kallon shi Fa'iza ta sake yi sannan ta juya ta miƙe ta bi bayan Mommy. Suna zama a parlour Mommy ta kalleta ta ce "Fa'iza bana so ki faɗawa Muhasin komai game da Aziza, ko ya tambaya kice masa ta tafi Dubai saro kaya"
"Amma ko nan gaba ai zai sani Mommy"
"Eh na san zai sani, amma ba yanzu ba, a barshi ya ɗan huta na kwana biyu tukun"
"To shikenan, ba matsala"
****** ****** ******
"Ban amince ki koma gidanta ba" Ya faɗa yana driving, ita kuma Janan tana bayan motar a zaune. Ɗan ɓata rai tayi bata sake cewa komai ba.
"Wato har kin ji haushi dan nace karki koma gidan Aziza da zama"
"Ni ba haushi naji ba" Ta faɗa kanta yana kallon titi.
Ya ɗan juya ya kalli Janan sannan ya ce "Ƙanwata kina jin rigimar yarinyar nan, taya zan bari taje inda na san za ayi min snatching"
"Ban ga laifinka ba Yaya Habib nima na faɗa mata taƙi ji, matar da bata santa ba har tayi saurin yarda da ita har haka"
"Ki rabu da ita tayi fushinta ta gama amma ba zan yarda taje ba"
Ita dai Sadiya bata ƙra magana ba har suka ƙarasa gidan su Habib, shi ya sauka ya buɗe gate, sannan ya dawo ya shigar da mota, sai daya koma rufe gate ita kuma ta fito, Janan ma ta fito.
"Nifa gabana faɗuwa yake"
"Ki nutsu babu abinda zai faru sai alkhairi"
"Amma amma me kike tunani da ta ce tana son ganina, ni wallahi tun jiyan nake tunani amma na kasa samun tsayayyar amsa"
Janan bata samu yin magana ba saboda ganin Habib ɗin ya taho.
"Ku mu shiga ciki" Shi ya yi gaba su kuma suna biye dashi.
Tunda suka shiga Sadiya ke bin ɗakin da kallo tamkar na amarya, ga daddaɗan turaren wuta da ƙamshinsa ke tashi. Ɓangare guda kuma faɗuwar gaba yana ƙara yawaita a ƙirjinta. Ya shiga kiran Maman tashi amma a cikinsu babu wanda ya iya magana.
Tana fitowa Sadiya tayi ƙasa da sauri, ganin hakane ya saka Janan itama ta sauka ƙasan. Har sai da Mama ta zauna sannan suka gaisheta, Sadiya sam ta kasa kallok fuskarta, Janan ce ma take ɗan satar
kallonta.
"Ku koma kan kujera ku zauna" Mama ta faɗa tana nuna masu kujerar da hannu.
A kunyace suka zauna, Sadiya ta fara wasa da ytsun hannunta.
"Wacece Sadiyar a cikinku" Ji tayi gabanta ya faɗi, Janan ta nunata tare da cewa "Gata nan"
"Kece matar auren kenan, amma ba kama"
"Mam..." "Rufa min baki Habib ko in saɓa maka, da kayi tunanin na kirata ne dan in ji daɗi, to na kirata ne dan in mata gargaɗi" Sadiya ji tayi ƙwalla ta zo mata, amma tayi ƙoƙarin hanata zubowa, Janan kanta ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi bare shi Habib da ya fara dana sanin kawota gidan tun a yanzu.
"Dama a ƙauye aka san asirin, dan na fara tunanin sun asirce min kai" "Mama ni babu wanda ya yi min asiri, kawai ina sonta ne, kuma har cikin raina" "Habib ni zaka yiwa rashin kunya akan mace?" Shiru ya yi yana huci, ransa a matuƙar ɓace yake. Ita kuma ta kalli Sadiya ta ce "To duba kiga abinda kika aikata, kin dai gani ɗana yana son guduna a kanki. Wai ma me kika masa? Ya baki ƙoda? Ya kula dake lokacin kina gurguwa sannan kuma a yanzu da yaji da aure a kanki ya kasa haƙura jira yake wancan ya dawo ya sakeki shi ya aura, wannan aikin hankaline? Kin bi kin juya kan ɗana ya susuce a kanki, wallahi ji nake na tsaneki sosai, ni ban ga abin so ake ba" Ta ɗan yi shiru sai kuma ta cigaba da cewa "Akwai zaratan mata a family ɗinmu wanda babu abinda zaki nuna masu amma ya dage sai ke. Dama cewa nayi a kiraki na ganki naga uwar mene a tattare dake da har ya so ki? Ashe dai babu komai, sai tsagwaron talauci da idanu kamar na mayu" Jin haka ne ya saka Sadiya ɗago manyan idanun nata wanda suka zama jajir ta kalli Mama. Sai kuma ta ɗauke ido ta miƙe. "Janan...mu..tafi" Ta furta muryarta a sarƙe. "Umma ta gaida Assha amma ki sani zamanki surukata abu ne da zai baƙanta miki, kamar yadda ba zan taɓa ƙaunarki ba, saboda ba da son raina za a auro ki ba" Bata ce komai ba, ta fuzgi hannun Janan a fusace ta fita.
Da sauri ya tashi "Zauna, magana zan yi da kai" Mama ta dakatar dashi. "Mama kiyi haƙuri nayi miki biyayya ne dan ban son ko na auri Sadiya ta rainaki, amma dole zan je na bata haƙuri a bisa abinda ya faru" Da sauri ya fita, tana masa magana amma sam yaƙi saurara.
A ƙofar gidan ya ci karo dasu. "Sadiya please dan Allah kiyi haƙuri" Ya faɗa lokacin daya tare gabanta. Ta matuƙar daurewa saboda bata yi hawaye ba amma dai idanunta cike suke, ƙiris ya rage su fito.
"Janan ki saka baki dan Allah, ku bari na fito da motar na mayar daku kamar yadda na ɗauko ku"
"Wallahi ba zan shiga motarka ba" Sai lokacin hawaye suka samu damar zubo maka.
Cikin shashsheƙa ta kalleshi "Mahaifiyarka ce, bani da yadda na iya, amma....am...ba.....bazan..iya jurewa ba, mayya, mai asiri...." Ta girgiza kai "Ban taɓa kawowa kaina irin wannan jarabawar rayuwar ba, kawai ka tafi" Tana gama faɗa ta wuce, har zai bita Janan ta dakatar dashi. "Yaya Habib a yanzu Sady ba zata saurareka ba, kayi haƙuri ka san idan mutum yana cikin fushi babu abinda ba zai faɗa ba, amma ka bari ta sauko na san zata sauko da wuri"
"Amma nina ɗauko ku daga school ni ya kamata na mayar daku"
"Ka san ba zata shiga motarka ba, ka bari zan lallaɓata, ka koma kawai zamu hau Napep"
"Okay to bari na baku kuɗi..." "No ka barshi, da kuɗi a hannunmu" Tana gama faɗa ta wuce shi kuma ya kasa motsawa a gurin.
Kafin ma su kai bakin titi ta fara jin jiri yana ɗibarta. "Janan ji nake kamar zan faɗi" Janan riƙeta tayi tare da faɗin "Ki daure mu samu napep" Suna tsayuwa kuwa wata mota tazo dai-dai inda suke ta tsaya. Mamallakin motar ya zage glass ya kallesu "Sannunku 'yan mata" "Yauwa" Janan ta furta a taƙaice. "Idan ba damuwa kuzo muje na rage muku hanya" "A'a mungode" Janan ta faɗa a taƙaice.
Ba yanda bai yi ba amma sam taƙi yarda ta shiga motar, har sai da suka samu napep suka tara shi kuma yana biye dasu a baya har cikin makaranta, sai da suka sauka a hostel sannan ya tambayi wasu 'yammatan sunansu aka faɗa masa, ya nemi a bashi number aka kuma bashi ta Sadiya sannan ya juya.
******* *******
Tana kwance kan three seater da laptop akan cikinta tana kallo. Zama ya yi sannan ya kalleta "Yammata kallo ake" Ɗagowa tayi ta kalleshi tayi murmushi sannan ta saka pause.
"Yaya ka fito" "Eh ya gidan, ina Mommy" "Mommy bata nan taje gidan Uncle Bala, ka san bikin Yaya Muhammad ake yi" "Bikin har yazo kenan" "Eh"
Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin ya ce "Yau sati na guda da dawowa amma Aziza batayi waya ba, to wai ya akai baku da number ɗinta?" Ɗan sosa kai Fa'iza tayi sannan ta fara kamo ƙarya "Am..da..dama..kasan ta kira..so..so bamu saving ba" Baki ya buɗe yana kallo Fa'iza yadda take kama magana da ƙyar haka ya tabbatar mata da ƙarya take.
"Ya naga kana min wani kallo?" Ta faɗa cikin mazewa.
"Fa'iza" "Na'am"
"Ina Aziza tsakanin ki da Allah"
Shiru tayi ta kuma ɗan ɓata fuska.
"Karki ɓoye min gaskiya, ni dama tunda na dawo jikina ya bani akwai matsala" "Babu komai" "Ɓoye min za kiyi"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kawar da kai. Tashi ya yi ya koma kujerar da take, yayi facing ɗinta "Faɗa min gaskiya" "Mommy ta ce kar na faɗa" Ta furta tana sauke kai ƙasa.
"Ba zata san kin faɗa min ba"
"Ka tabbata?"
"Eh na tabbata"
Sai da ta ɗan ji jim, sannan ta bashi labarin duk abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa. Hankalinsa ya matuƙar tashi dan kasa zama ya yi ya miƙe tsaye. "Mommy ta ce bata son ka san komai a yanzu"
"To ina Aziza ta tafi?"
"Bani da masaniya Yaya, amma nayi niyyar hanata Mommy ta ce in barta"
"Wallahi har Abuja sai naje na ciwa Hafeez mutunci"
"Ya cuci Aziza ya lalata rayuwarta, ni babban tashin hankalina da har yanzu ban san inda take ba, babu ta yadda za ai mu sameta, amma jikina yana bani Aziza bata ƙasar nan, saboda abokan aikinta haka suka faɗa min"
"Ya Salam" Ya furta tare da kwantar da bayansa a jikin kujera, sai kuma ya ɗago "Kina nufin wannan 'yar aikin aka aura min?"
"Ƙwarai da gaske, itama ashe bata sani ba, sai da ta fara soyayya da wani sannan ta sani lokacin har an saka rana sai Kawu Yakubu ya faɗa masu abinda ke faruwa shi ne suka zo nan ka saketa baka nan" Gabansa ya yi mummunan faɗuwa.
_Idan ka tabbatar kana da aure karka yarda ka saki matarka, ita zata zame maka garkuwa._ Tuno da furucin Zaliha ya saka shi ƙara faɗin "To yanzu tana ina?"
"Gaya, an dai ce idan ka dawo zaka saketa sannan ta auri wancan ɗin. Ita Mommy na kasa gane kanta Yaya, taya zata aura maka wannan kucakar yarinyar kuma gurguwa"
"Gurguwa ce?"
"Ba anan gidan ta samu wannan ciwon ba, Yaya wai baka tuna ta ba? Ita ce wadda muka taho da ita daga Gaya"
"Na manta" Ya furta a sanyaye. Jin horn ya saka Fa'iza saurin tashi, ta window ta leƙa taga shigowar motar Mommy dan haka ta kalleshi "Yaya Mommy ta dawo, kuma naga mood ɗinka ya canza, kar ta gane na faɗa maka"
Miƙewa ya yi tare da faɗin "Zan shiga room ɗina" Kai kawai ta gyaɗa tana kallinshi.
Mommy taƙi ta faɗa masa, haka yake kwana ya yini da tunani, ko fita ta hana shi bare ya samu yaje gurin Hafeez a Abuja, rabonshi da waje tun washe garin dawowarsa da suka kaishi aka masa gyaran kai da fuska. Ko shaguɓe ya yi sai ta canza maganar, sam ya rasa yadda zai yi.
****** ****** ******
Kan katifar ta ƙarasa ta zauna tre da miƙa mata waya "Waye?" Ta furta a sanyaye. "Habib ne" Janan ta faɗa tana ƙoƙarin manna mata wayar ta goce. "Ba zan ɗaga ba" Shi ne abinda Habib yaji ta faɗa cikin faɗa.
"Janan ki faɗa mata ni mahaifin Habib nake son nayi magana da ita" Ɗan zaro ido Janan tayi, a ranta ta ce ashe yana tare da Daddynsa "Sady ki karɓa Daddyn Habib ne ke son magana dake" Ta saka mata wayar a kunne.
"Sadiyar ce?" Taji muryar dattijon. "Eh ina wuni" Ta furta a sanyaye. "Lafiya lau ya kike ya karatun" "Alhamdulillahi" "Sadiya kiyi haƙuri kan abinda ya faru, nayi magana da Habib akan zuwan naku, sam ban san ta ce kizo ba, ki sani ita kaɗaice bata son auren saboda wani banzan ƙudiri nata, kuma hakan ba zai hana aurenku ba, zan ɗauki mataki akai dan Allah kiyi haƙuri kin kwantar da hankalinki" Bata ce komai ba, sai hannu da ta saka ta goge hawayen da yake neman zubo mata. "Kiyi haƙuri dan Allah ki sanyaya ranki, ya ce min kin daina ko ɗaga wayar tashi, to ayi masa afuwa, ita kuma zan zauna da ita zan mata faɗa akan abinda tayi"
"Babu komai Abba" Ta furta a sanyaye. "Allah ya muku albarka" "Amin ya rabbi"
Tana katsewa ta kalli Janan sannan ta ce "Ni a tsorace nake Janan"
"Sady kin ƙi faɗa min komai game da rayuwarki, wane aurene a kanki?" "Ina son zuwa Gaya gobe, Baffa ya ce yana nemana, idan na dawo zan nutsu in baki labarin komai, amma yanzu ban cikin nutsuwa Janan" "Shikenan Allah ya dawo dake lafiya"
"Amin"
Da yamma Habib yazo, ta fita ta sameshi a cikin wata dalleliyar Mercedes sabuwa fil. Ko da ta shiga motar ma ƙare mata kallo take yi "Wannan motar fa?"
"Jiya aka kawota" "Tayi kyau, kyautarta aka baka?"
"Me kika ɗauki sana'ar waƙa? Ba zata iya kawo min wannan kuɗaɗen ba?"
"A'a ni ban ce ba, kawai fa tambaya nayi"
"To motarki ce" "Mota ta?" Tayi tambayar tare da yin dariya "Baki yarda ba? Da gaske kena siyawa, dan har takardun motar ma da sunanki aka yi, kawai dai na san ba zata zo hannunki ba sai bayan biki, yanzu na kawo ne dan ki gani"
"Yayana" Ta faɗa da farin ciki tana zaro ido cike da mamaki.
"Na zama speechless wallahi, kai gaskiya na gode sosai"
"Babu godiya tsakaninmu. Gobe sai Gaya ko?"
"Ya akai ka sani?"
"Mun yi waya da Baffa ya ce jibi zamuje Kaduna, shi wannan Muhasin yake ko waye ya dawo"
Dafe ƙirji tayi, tana neman fita daga nutsuwarta, da ƙyar ta iya tattaro nutsuwarta "Dama shi ne kiran?" "Eh bai faɗa miki ba kenan?" "Eh kawai ya ce yana son ganina" Ta furta a sanyaye.
Kallon shi ta ƙara yi "Bana son na rabu da kai Yayana, bana son abinda zai rabamu, shiyasa hankalina ya tashi da Mama tayi min wannan msganganuɓ, to gashi Abba ya kwantar min da hankali kuma wani matsalar na ƙara kunno kai."
"Karki damu, shima ai bai san anyi auren ba kin ga kuwa dole zai sake ki" Kai kawai ta gyaɗa jikinta gaba ɗaya a sanyaye, shi ne ya yi ta ƙoƙari har ya kwantar mata da hankalinta.
Tana komawa hostel ta kira Aziza. "Sady ya kike" "Lafiya lau, ya Junior"
"Junior gashi yana ta rigima, ni kuma Sady bani da lafiya ina yawan jin jiri"
"Sannu Aunty Allah ya baki lafiya"
"Amin nagode, yaushe zaki shigo?"
"Dama kiranki nayi na sanar miki Muhasin ya dawo, jibi ma zamu je Kaduna, gobe nake son zuwa Gaya"
Aziza da rake zune sai da ta miƙe, farin ciki sosai ta tsinci kanta a ciki. "Aikuwa insha Allah nima jibi zan je Kaduna" "Na san ai burinki kenan, shiyasa nace bari na faɗa miki"
"Nagode Sady"
*Bayan Kwana Biyu*
Tunda suka zauna kuma da yanayin tarbar da aka masu har tafi ta farko muni ya saka jikinta ya fara rawa, dama gata matsoraciya. Tun shigowarsu Kaduna take kiran Aziza ta ce tana hanya amma gashi har suna cikin gidan bata ƙaraso ba.
Mommy na kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, Muhasin kuma da Fa'iza a zaune suke a kujera daya. Tunda ya kalli Sadiya sau ɗaya ya kauda kai gefe. Shi kansa gabansa yana faɗuwa bare ita Sadiya da take jin kamar zai faɗo.
"Muhasin...!" Momny ta kira sunan nashi da kakkausr murya.
Kallonta ya yi, ya amsa a sanyaye. "Nayi maka aure a bisa rashin saninka, da kuma tunanin wannan aure zai kawo ƙarshen matsalarka, sai dai kuma sai wata matsalar daya kunna" Shiru ba wanda ya ce komai.
Umma ji take kamar ta shaƙo Mommy tayi ta suka, Habib kuma idonshi akan Muhasin, yayinda Baffa da Malam Yakubu ke kallon Mommy Sadiya kuwa kanta yana ƙasa.
"Gata nan, wai ta samu miji za tayi aure, shiyasa suke neman a sawwaƙe mata, ni da na san aure ba zai amfanar damu ba da ba zan haɗa ba, amma ba yadda muka iya, kayi haƙuri a bisa karan tsaye da nayi maka. Gata nan dai ka sakar masu kayansu ko ma huta da zarya."
Shiru ya yi kamar ba dashi ake ba. Sai da ta ƙara kallonshi ta ce "Magana nake maka Muhasin"
"Mommy am sorry to say ni bazan iya sakinta ba, zan zauna da ita. Dan haka zan gyara mata side ɗin da zata zauna, kuma a haɗo mata lefe, idan sun buƙata ayi shagalin biki kamar yadda ake yiwa ko wace mace"
"Wallahi baka isa ba...!" Ta miƙe a kiɗime hawaye tuni ya ɓalle a idanunta.
Shigowar Aziza ya yi dai-dai da tsala kuka da ɗanta ya yi, dan haka gaba ɗaya suka mayarda kallonsu gareta, tuni Mommy ta miƙe tsaye.