Page 29
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 29
__________🖌️"Aziza..!" Fa'iza ta furta da matuƙar mamaki. Ita kuma Aziza kai tsaye inda Sadiya take ta nufa saboda ganin ta durƙushe a ƙasa ta fara rera kuka. "Aunty ki saka baki dan Allah Aunty" Sadiya ta furta cikin kuka. "Ki share hawayenki komai zai daidaita" Aziza ta faɗa tana ɗagota.
Habib so yake ya yi magana amma ganin su Baffa sun ƙi saka baki ya saka shi danne zuciyarshi.
"Wallahi kaji na rantse ko? Ba zamu taɓa iya haɗa iri daku ba, dama bamu san an ɗaura ba, kuma dole a kunce" Umma tayi maganar rai a ɓace. "Kiyi min shiru Lami" Baffa ya faɗa a fusace. Mommy dai ta kasa cewa komai sai ƙurawa Aziza ido da tayi.
"Yaya dan Allah ka sawwaƙe mata, saboda tana da wanda take so" Kallon Aziza ɗin ya yi dama tunda ta shigo idanunsa a kanta. "Ba zan saketa ba Aziza,idan har kin ga mun rabu to sai dai idan ni ne na mutu ko ita, amma ni dai ba zan iya rabuwa da ita ba"
"To sai ka saketa, kuma yanzu anan, me zakayi da 'yar talakawa matsiyata" Sai lokacin Mommy tayi maganar, ya juya ya kalleta "Mommy kin san ita ɗin 'yar talaka ce kuma kika aura min? Mommy ke fa baki da wata magana sai akan talaka wai su takawa ba mut...." "Ka rufa min baki ko in sharara maka mari, kuma ka saketa ko in tsine maka"
Lumshe ido ya yi sannan ya buɗe "Ba zan iya ba, ina son zama da ita, dan haka zaki iya tsine Mommy indai farin cikinki kenan" Juyawa ya yi zai yi side ɗinsa Sadiya ta fuzge daga hannun Aziza, tasha gabansa da sauri. Kallonta ya tsaya yana yi, fuskarta har ta fara ja, gata nan kuma sharkaf da hawaye. "Kenan so kake ka tsayar da rayuwata? So kake na mutu shiyasa kaƙi sakina, ko kuma so kake na kuma komawa gurguwa" Ta ƙarasa maganar cikin shouting. "Babu ko ɗaya, so nake dai mu rayu tare, mu haifi 'ya'ya amma taya zan so matata ta mutu, ni rayuwar aure nake so muyi, saboda nima ina son ganin 'ya'ya, ni ba aljani bane, taya za a hanani aure, sannan ni ba jahili bane da zan samu dama kuma in bari ta kubce min. Ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru"
"Ba zan zauna da kai ba, ba kuma zan taɓa ƙaunarka ba, ka sakeni kawai" "Kina ɓata lokacinki, ba zan iya sakinki ba"
Sai kuma ya juya gurin su Baffa, har gaban Baffa ya tsugunna tare da faɗin "Baba ka sani duk da saki halastaccen abu ne amma Allah baya so, ni ban ga aibu a gareta ba, Baba ƙiyayya take jawo saki ni kuma babu ita akan Sadiya, ina sonta dan Allah ka saka baki a wannan lamarin"
Habib runtse idanu ya yi, yaji zuciyarsa na wani irin tafasa. Ya buɗe ido yana kallon Baffa yana jiran amsar da zai bashi.
"Da ace Sadiya tayi na'am da kai, to babu yadda zamuyi zamu barku tare, amma ta ce bata so, tana tsoro domin ita ta san abinda ta gani, yaro ka taimaka ka sauwaƙe mata"
Miƙewa ya yi tsaye, yadda ya miƙe kamar an saukar masa da mutuwa "Kowa kenan baya bayana, kowa kawai so yake na saketa, to ni kuma koda babu mai bin bayana ni ina nan akan bakana" Ya kalli Baffa "Nan da sati guda zata tare, za a kawo lefe kafin lokacin"
Gaf da Sadiya ya kawo ya tsaya suna facing juna, fuskarta kaca-kaca da hawaye "Ban ma san kamanninki ba sai yau, amma kuma a hakan ni kin min, kiyi haƙuri ba zan sakeki ba, zaki kuma tare a gidan nan, koda zaki riƙa yankar naman jikina a ko wace rana" Yana gama faɗa ya wuce. Ji tayi jiri yana ɗibarta, ta riƙe goshinta tare da sulalewa ƙasa ta suma. Umma, Aziza da Habib suka ƙarasa gurinta a kiɗime.
*1 Hour Later*
Mommy nata yawo a tsakar parlour, Aziza na zaune a ƙasa rungume da ɗanta, yayinda Fa'iza take zaune kan kujera tayi shiru. Jin takun tahowarsa ya saka duk suka ɗaga ido suna kallonsa, har ya ƙaraso cikin parlourn ya ƙarasa gaban Mommy ya tsaya "Mommy kiy..." Mari ta wanka masa wanda shi ne ya hana shi ƙarasa maganar. Sai kuma ta fashe da kuka tare da zama kan kujera. Dukkansu kallon mamaki suke mata "Shikenan ni bani da say akan 'ya'yana. Aziza ta kwaso abin kunya, kai ka tafi ba da sanina ba, sannan ka dawo na umarceka daka saki waccan yarinyar kaƙi, Fa'iza ta gudu ta bar ƙasar sai da taga babu yadda zatayi sannan ta dawo, kai ma gaka ka dawo sannan itama Aziza ta dawo" Jin haka ya saka Aziza miƙewa "Ni ba dawowa nayi ba, kamar yadda kika koreni na tafi ba zan zauna ba Mommy, yanzun ma zuwan Yaya ne ya saka nazo" Ta furta tana goge hawayen daya zubo mata.
"Babu inda zaki koma Aziza, kina nan tare damu" Muhasin ya faɗa tare da saka hannu ya ɗauki Babyn" Kallon Mommy ya yi sannan ya ce "Mu 'ya'yanki ne, baki da kmarmu, Mommy meyasa kika canza?" Zaunawa ya yi kusa da ita da hannu ɗaya ya dafa cinyarta "Muna buƙatar kulawarki Mommy, ƙaddara ce ta faɗa mana dan Allah kar wannan ya sa ki guje mu" Janyo Muhasin tayi a jikinta tare da ɗaukar Junior.
Fa'iza itama da sauri ta taso ta rungume Mommy, sai dai ita Aziza tana zaune anan ƙasa tana cigaba da kuka. Mommy da kanta ta tashi ta ƙarasa gabanta tare da janyota, ɗago rinannun idanunta tayi ta kalleta, ta saka hannu ta goge mata hawaye "Ki share hawayenki Aziza" Rungume Mommy tayi tare da ƙara fashewa da kuka.
******* ****** ********
A hankali ta buɗe idanunta da suka mata nauyi. Dishi-dishi ta fara gani kafin kuma ta ga Umma, abubuwan da suka faru take gani kamar a mafarki kafin ta ware idanunta gaba ɗaya. Sai kuma ta miƙe zaune, Umma ta riƙeta, rungumeta tayi tare da fashewa da kuka, ita kanta Umma kukan take.
"Umma ba zan zauna dashi ba, dan Allah"
Baffa dake tsaye shi ya riƙa rarrashinta, haka dai suka samu suka nufi Gaya. Ko a mota Sadiya ban da kuka babu abinda takeyi, idanunta sun yi jajur sun ƙanƙance, kanta kuwa ji take tamkar zai faɗo saboda ciwo. A haka suka ƙarasa gida, ai suna shiga tsakar gidan ta fasa kuka a fili tamkar an mata mutuwa ta ƙarasa ta rungumi Inna da kuma Ladi dake tsakar gidan. "Da alama dai ba a dace ba" Shi ne abinda Inna ke nanatawa har su Baffa suka shigo. Ladi ce ta ɗauko wata tabarmar ta shimfiɗa musu.
"Malam wai mene yake faruwa?" Inna tayi tambayar. Bai ɓoye komai ba ya faɗa mata yadda sukayi.
"Ai wallahi basu isa ba, bayan mun san manufarsu a farko kuma suce zasu saka yarinya a masifa, bayan auren ma ba bisa gaskiya aka yi shi ba"
"Inna wallahi ba dan Baffa ya kwaɓeni ba, da sun ga rashin mutuncin da basu taɓa tsammani ba" "To taya ya zan bari haka ta faru? Gida su fa muka je, kuma sakin nan a hannun yaron nan yake, dole mu bi abubuwan a hankali"
"Dan fa sun ga ana yi masu a hankalin shiyasa suke abinda suka ga dama. Yanzu Baffa mene mafita?"
"To ni dai a nawa ganin a cigaba da lallaɓasu har ya samu ya saketa"
"Baffa wannan a hankalin fa ba zai yuwu ba, kana ganin yaron yadda yake magana da gadara, ni dai gara kawai akai kotu""
Kotu haba Lami ina muka ga kuɗin da zamu maka su kotu?"
Sai lokacin Habib ya ce "Baffa nima ina ganin hakan shi yafi, in dai ba kotu ba to babu wanda zai raba wannan auren"
"A'a a dai bari mu gani nan da kwana biyu, amma batun akai kotu tun yanzu an yi gaggawa"
Haka dai suka yi ta tattaunawa har zuwa lokacin da Habib zai tafi, Baffa dai ya ce abar Sadiya zuwa monday sai ta koma kafin nan ta ɗan wartsake.
******* *******
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin "Wannan shi ne asalin labarina, kuma tun bayan dana haifi Muhasin naje suka wulaƙantani ban sake komawa ba, ku san shekaru talatin kenan" Ta saka hannu ta share hawaye. Dukkansu kowa ya kasa magana, kallon Aziza tayi sannan ta ce "Na shiga tashin hankali a lokacin da naji kina da ciki, kuma na tabbatar abinda muka aikata da mahaifinku shi ne ya bibiyemu ya faɗa kanki"
Kai Aziza ta sauke ƙasa har lokacin hawaye take. "Nayi dana sani matuƙa shiyasa nake ganin kamar kema zaki yi hakan, wannan dalilin ne ya saka nake ta ƙoƙarin ganin an zubar dashi, amma bamu san mene ya haɗiyo ba, wataƙila zai zama wani a rayuwa shiyasa Allah bai bani ikon cin galaba a kanki ba"
"Mommy...!" Muhasin ya faɗa a sanyaye. Ɗagowa tayi idanunta cike da hawaye tana kallonshi. "Ina ganin laifi da haƙƙin iyayene ya saka muka shiga wannan matsin rayuwar. Kiyi haƙuri Mommy, amma yana da kyau muje Yola domin ki nemi gafar iyaye da kuma shi wanda kika..." Ya kasa ƙarasawa.
"Shikenan, yaushe kuke tunanin zamuje? Dan ina so muje gaba ɗaya"
"Da wuri Mommy, idan son samu ne zuwa next week"
"To shikenan, zan fitar da rana sai muje"
Kwana biyu dai haka Aziza tayi shi sam babu wani kwanciyar hankali a tattare da ita. Damuwa ce mai tarin yawa a tattare da ita, haka shima Muhasin.
Yana kwance kan ƙafiyayyen gadonsa, idanuwansa na kallon POP ɗin ɗakin.
_Sadiya._ Kawai yaji zuciyarshi ta ambaci sunan. "Ta ya ya zan yi rayuwa da ita?" Miƙewa ya yi zaune, tare da dafe kanshi ya ɗan shafa sumarshi, a cikin zuciyarshi yana hango hoton fuskar Sadiya lokacin da take hawaye tana faɗin ya saketa" Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "Naga tsana ƙarara a fuskarta" Miƙewa ya yi kai tsaye ya.
Tana jin knocking sai da gabanta ya faɗi, dan a tunaninta Mommy ce, shiru ta ɗanyi kafin ta bada iznin shigowa. Idanunta akan ƙofar har ya shigo sannan ta ce "Oh Yaya Muhasin kaine"
"Eh, Junior barci yake" Kallon Babyn tayi sannan ta kalleshi "Ya gama rigima ya yi bacci" Akan sofa ya zauna.
"Aziza na san kin san komai game da ita Sadiyan"
"Eh na san ta, ai a Kano take karatu anan Maitama Sule"
"Okay kenan ma tana karatu"
"Eh 100 level take"
"Wow" Kallonshi tayi da mamaki kafin ta ce "Yaya wai me kake nufi da hakan?"
"Aziza ba zan iya sakinta ba"
"Saboda me?"
"Itace garkuwarmu"
"Shi ne kawai dalilin?"
"Wannan ba hujja bace babba a ganinki?"
"Eh saboda kar mu cuci yarinya, kar ta rasa rayuwarta a kan abinda bata sani ba, Yaya wannan ba hujja bace, yarinyar nan tana da wanda take so, Yaya karka tauye mata haƙƙi"
"Ni kuma ina buƙatar kariya a gareni daku, sannan ina so nima naga jinina, Aziza ba zan iya sakinta ba"
"Idan ta mutu fa?"
"Haka kike fata?"
"Yaya wai wane irin abu kake haka, kar ka zama mai son kanka a rayuwa"
"Na zama" Ya faɗa rai a ɓace sannan ya miƙa mata waya.
"Saka min number ɗinta"
Zama ta gyara tana kallonshi kafin ta ce "Ni bani da number ɗinta" Wayarta ya kalla a gefe, da sauri ya ɗauka.
"Yaya dan Allah kar kayi haka"
"Nayi ma, dole ne na karɓi numberta saboda ina son zuwa gurinta. Yana gama kwashe number ya ajje mata wayar a gabanta, sannan ya tashi ya fita.
Ajiyar zuciya ta sauke, tare da dafe kai.
******* ******* *******
Sai da ta gama faɗanta tas, sannan Abba ya kalleta ya ce "To kin gama faɗan naki?" "Haba Malam ai gaskuya ce dole ne a faɗa, shikenan mu an mayar damu sakarkaru, a jira Habib zai ƙare, sai kace ita kaɗaice mace"
"To wai ke baki san ƙaddara bane? Idan fa Allah ya yi yarinyar nan matar Habib ce babu yadda kika iya sai kika ga rabo ya rabaki da duniya" "Oh so kake in mutu kenan?"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Mutuwa ai tana kan kowa, ina dai so na sanar dake ne, shi rabo in ya rantse ba yadda kika iya" "To ai shikenan, idan ana aure kan aure sai ayi mu gani" Tana gama faɗa ta tashi ta bar parlourn. "Ke kullum ba zaki tausasa kalaminki akan ɗanki ƙwaya ɗaya tilo" Ya dawo da kallonsa ga Habib "Tunda iyayenta sun yi na'am da kotun sai akai amma nima dai nafi son a ɗan ɗaga ƙafa a gani"
"To shikenan Allah ya shige mana gaba, ya kuma saka su ƙwatowa yarinya 'yanci tunda dai bata so dole ake neman yi mata" "Abba zuwa gobe nake son shigar da ƙarar ma" "Idan zakaje zan baka number wani abokina anan kotun musuluncin yake aiki" "To Abba, nagode"
***** ****** ******
"Ke wato sam baki iya damuwa ba, in kina cikin damuwa kisan kanku ne kawai bakiyi, amma kin ta azabtar da kanki da yunwa da kuma kuka" Inna ta faɗa tana buɗe jug ɗin koko har ya huce bata sha ba.
"Ga abincin rana har na kusa gamawa amma baki taɓa na safe ba, Sadiya wai baki san ƙaddara bane?"
Sai lokacin ta kalleta idanunta kaca-kaca da hawaye.
"Ni na ƙoshi Inna"
"Aikuwa dole kici, wallahi ko ɗure ne sai na miki, bari na dubo wuta na dawo.
Inna na fita Sadiya ta kai dubanta ga zoben hannunta "Allah ya isa, ban yafe ba" Ta furta cikin kuka. Sannan ta cigaba da faɗin "Kai ne ka fara ruguza rayuwata me nayi maka da kayi min fyaɗe? Abinda kayi min shi ne farko kuma silar faruwar duk wannan bala'in da nake ta fuskanta" Ta saka hannu ta rufe fuska tana shashsheƙa.
Wayarta data fara ringing ta kalla, ganin number ce ya saka bata ɗaga ba, har kira uku amma bata picking.
Muhasin ganin bata ɗaga ba, ya saka shi miƙewa ya koma ɗakin Aziza. Bata nan amma yaji ƙarar ruwa da alama wanka take, wayarta dake kan mirrow ya ɗauka tara da shiga contact ya yi dialing number Sadiya.
Ita kuma tana nan tana aikin kuka taji kira ya sake shigowa, ganin daga Aziza ne ya saka ta ɗauka da sauri dan tayi tunanin zata ce mata Muhasin ya saketa, amma sai kawai taji tattausar muryarshi tayi mata sallama. Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa. "Sadiya da fatan kina lafiya?"
"Dawa nake magana?" Ta faɗa da dasasshiyar muryarta. "Muhasin ne, dama ina so nace miki ina son zuwa na ganki sannan ina so ki faɗi kalar fur" "Dakata Malam? Wallahi ka fita a idona na rufe, ba zan taɓa ƙunarka ba impact na tsaneka kuma ba zan taɓa sonka ba, a 'yar aiki kuka fara ɗaukata kuna mini wani gani-gani"
Cije laɓɓansa ya yi dan yaji zafin furucinta.
"To karki soni mana, dan kin ga ina lallaɓaki, ni ɗinma ba sonki nake ba, maleji kawai zanyi, kuma ko ki soni ko karki soni dole kizo ki zauna a gidana domin igiyarki ukuce a hannuna, kuma ko kin zo gidan nawa a 'yar aikin zaki cigaba da zama"
"To ba sai nazo ɗin ba, ai da inzo gidanka gara a kaini kabari, kuma ka jira sammaci kotu ce zata raba aurenmu in kai baka saki da daɗin rai ba, zaka sakeni dan dole mtswww" Taja don tsaki ta kashe wayar.
Kallon wayar yake yana jin ƙunar rai. Ajjeta ya yi kan mirrow yana juyowa ya ga Mommy tsaye ta harɗe hannayenta a ƙirji.
SaNaz🌸🤘