Page 30
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 30
__________🖌️Ɗan sosa kai ya yi, yana shirin yin magana Aziza ta fito daga toilet. Kallon Muhasin tayi sannan ta kalli Mommy. "Lafiya kuwa?" Ta faɗa idanunta akan Muhasin. "Muhasin...!" Mommy ta kira sunanshi, dukkansu suka kalleta "Sadiya ce?" Shiru ya yi baice komai ba, sai lokacin Aziza ta ƙarasa kan bed ta ɗauki hijab sannan ta koma jikin mirrow ta ɗauki wayarta ta duba.
Kallonshi tayi ta ce "Yaya amma sai tayi tunanin nice na baka wayar ka kirata" "To sai me tayi duk tunanin da zatayi ita ta sani" Aziza kallonshi tayi da mamaki. Mommy kuma ta ƙarasa ciki tare da zama kan sofa. "Wai mene matsalarka? Tunda har basu so ka saketa mana? Ni kaina ba son haɗinka da ita nake ba" "Mommy an tabbatar min da itace garkuwata, ni ɗinma ba sonta nake ba, kawai babu yadda zan yi ne" "Waye ya faɗa maka itace garkuwarka" "A inda naje, dan su suka fara faɗa min ina da aure amma ni da ban ma yarda ba"
Gava ɗaya labarin ya basu na zaman shi a rugar su Zaliha. Yana gama basu Mommy ta ce "Na amince ta zauna mu gani idan ko mai ya zama normal sai ka sallameta" Da mamaki Aziza ta kalleta, ita bata taɓa ganin mace mai son kanta kamar Mommy ba, babu yadda ta iya ne saboda mahaifiyarta ce. "Za a tauyewa Sadiya 'yancinta Mommy, tana da wanda take so kuma har an saka rana sannan ta gane tana da aure, kuma zuwan su na farko gidan nan kin wulaƙantasu tare da jaddada musu zaki saka Muhasin ya saketa yana dawowa, kuma yanzu kina faɗar wai ta zauna, haba Mommy"
Kallon Aziza tayi kafin ta ce "Aziza wai nice na haifeki ko kuma ke kika haifeni?" Shiru Aziza tayi, tana jin ranta babu daɗi. "Ko kece babu wanda zakiyi dan ɗanki ya samu lafiya, amma na lura ke kina da kafiya. Karki manta yaron nan" Ta nuna yaron da yake kwance yana bacci "Tun yana ciki kike ƙaunarsa, to nima haka nake sonka kuma zan iya yin duk wani abu da zaku samu sauƙi" "Kamar hakane mahaifiyar Sadiya take ƙaunar 'yarta" Tana gama faɗa kawai ta bar ɗakin.
Kai tsaye ɗakin Fa'iza ta nufa, tana shiga kuma taga Fa'iza ta miƙe a firgice daga durƙusun da tayi a ƙasan gadon, ɗan leƙawa tayi bata ga komai ba, Fa'izar ta fara mata wani kallo. "Mene haka? Za ki shigo babu sallama" Kamar fa baki da gaskiya?" "Eh bani da ita kuma ba zaki sani ba." Murmushi Aziza tayi sannan ta ce "Kin san idan tayi wari dole ma gani" "Oho dai" Juyawa Aziza tayi ta fita, sai dai bata koma ɗakinta ba parlour ta nufa, ita kuma Fa'iza tana biye da ita.
"Aziza wai meke faruwa nayi? Naga yanayinki ya canza" "Ai ko na faɗa miki kema ba bayana kike ba" Za tayi magana kenan sai ga Muhasin ya taho da Junior a kafaɗarsa. "Wato fushin ya saka kin manta da yro ko" Murmushin ƙarfin hali tayi, zata karɓa ya zauna tare da faɗin "Ai kuma yanzu yazo hannun Daddynsa"
"Ni fa kun saka ni a duhu wai mene ke faruwa?" "Akan fa Sadiya ne" "Mtsww wallahi na ɗauka abin kirki ne, ni wallahi Yaya da ka sawwaƙe mata, wata kucaka da ita" "A'a ke kuma ya ida ban da cin fuska" Cewar Aziza. Dariya Fa'iza tayi sannan ta ce "To nayi shiru mai sabuwar ƙanwa" "Eh naji dai."
****** *******
Tana ajje wayar Inna ta shigo "Wallahi kisha ko kuma nayi miki ɗure" "Ni ba zan sha abu ya huce ba" Cewar Sadiya tana ta zuɓurar baki. "To bari ki gani" Ganin Inna tana neman danneta ta ɗura mata ya saka ta ce "Tsaya Inna ba sai kin min ɗure ba" "To ɗauki kisha, in har baki so nayi miki" Ɗaukar jug ɗin tayi ta tsiyaya kaɗan tasha da ƙyar sannan ta kalleta "Na ƙoshi" Sai kuma ta saka hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Inna ta gyara zama ta kalli Sadiya sosai ta ce "Ita rayuwa tana zuwar maka ba yadda ka tsarata ba, kiyi haƙuri ki krɓi rayuwa a yadda tazo miki sai ki ga Allah ya dube ki" "Inna wallahi gara na mutu dana zauna a wancan gidan" "Ki daina faɗar haka Sadiya, sai haƙuri babu yadda kika iya da ƙaddara" Hannu ta saka ta sake goge wani hawayen.
Inna haka ta riƙa yi mata nasiha har zuwa lokacin da ta samu sanyi a ranta.
*Bayan kwana biyu*
Suna zaune tsakar gida gaba ɗaya suna hira sai jin sallama tayi, ɗaga kan da zatayi taga Janan, aikuwa da gudu ta miƙe taje ta rungumeta tare da faɗin "Ya akai kika san gidanmu" "Ta hanyar Yaya Habib mana, tunda kin ƙi sanar min kuma kin ƙi dawowa school" Kan tabarmar suka ƙarasa ta gaida Umma da Inna. "Ita ce Janan, ɗakinmu ɗaya kuma course mate ɗina ce "Okay sannunki ya karatu?" "Alhamdulillah" "Sadiya kije a nema mata ruwa da lemo mai sanyi ko?" "To Umma" Ta faɗa tana jan hannun Janan suka shiga ciki. Suna shiga ɗakinta Janan ta zauna kan katifa "Ke Sady wai kin ga yadda kika faɗa kuwa? Wallahi kin rame" "Hmm! Ba dole ba, Janan ba zaki gane ba, wallahi ina cikin matsala sosai" "Wai mene yake faruwa?" "Kedai huta na baki labari" "Wane hutu ni da zan koma yau, ke dai ki bani labari ni ɗinma da labari na taho" "To ina zuwa" Ta faɗa sannan ta fita.
Sai da taje ta sayo mata lemo da ruwa sannan ta dawo ta zuba abinci a food plask tare da plate da spoon ta kawo ta dire gaban Janan. "Kai Sady sai kace wata baƙuwa" "Eh mana koda ba baƙuwa bace ai na san kin kwaso yunwa da ƙishi tun daga Kano fa" Lemon ta zuba a cup tasha sannan ta kalli Sadiya "Sady ina saurarenki" Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke sannan ta bata labarin duk abubuwan har haɗuwarta da Maryam da kuma Anisa. Kasancewar ƙasa-ƙasa suke maganar shiyasa Umma sam basu jinsu.
"Gaskiya kin ga jarabawa ko ma ince kina ganinta "Yanzu mene abinyi?" "Ni fa ba zan je gidanshi ba, Janan wannan bala'in dana gani kaɗai ya isa, kuma ma rashin mutunci da raina talaka da suke yi ya yi yawa, wai kin ji maganar daya ke faɗa min a waya, babu kwantar da murya" "Gaskiya ni kaina nafi so ki kasance tare da Yaya Habib saboda ya sadaukar da rayuwarsa a kanki, dan haka nima na bayar da goyon bayan ki zauna dashi ki rayu dashi ba wannan da bai san darajarki ba" "Wallahi kuwa, shi kan shi Yaya Habib ɗin a damuwa yake, ɗazu dai mun yi waya ya ce har an tura masu sammaci jibi za a zauna a kotu. Da yake kotun musulunci ce to tsakaninmu ne za ayi mana shari'a"
"Gaskiya dai a tilasta masa ya yi sakin nan, dan ba za kiyi daraja a idanunsu ba, kuma Yaya Habib ma tausyinsa nake, duk da Mamansa nada matsala amma kin ga mahaifinsa ma na ƙaunarki" "Hakane" Ta furta a sanyaye.
"Yauwa akwai wani guy da yake nemanki fa, yana ta zarya school da ya karɓi number ki to ya ce idan ya kira baki picking" "Bana son ya zamana Muhasin ɗin nan ne ya kira shiyasa kawai nake ƙin ɗaga waya"
"Aikuwa ya kamata ku haɗu ya ce in kin dawo yana so ku haɗu" "Haɗuwa kuma akan wane dalili?" "Ya san komai akan wannan zoben" Ta faɗa tana nuna zoben hannun Sadiya" "What...? Dagaske kike ko da wasa?" "Kin dai san ban miki irin wannan wasan ko?" Ajiyar zuciya ta sauke, Janan ta sake faɗin "Maganar gaskiya shi ne ma ya kwatanta min gidanku ba Habib ba, hakan ce ta saka na gane lallai ya miki kyakykyawan sani" "Amma da mamaki Janan" "Ni kaina abin ya ɗaure min kai, amma dai ina tunanin yana da masaniya sosai akan wanda ya miki fyaɗe" "Gaskiya nima zargin da nake, amma kin san me, ba zan yi ƙasa a gwiwa ba, yanzu zan shirya muje Kano, in yaso jibi su Umma sai su iskeni can, zan masu ƙryar test ne damu" Tana gama faɗa ta tashi ta fita.
Sai da ta gama tsarsu har suka yarda, suna ta shiwa Janan albarka data taso tazo har Gaya tun daga Kano dan ta sanar da ita wannan test ɗin. Uwa uba tunda Janan tazo suka ga Sadiya ta ɗan sake. Tare suka tafi Kano ji take kamar ma tayi tsuntsuwa amma dai ba yadda ta iya.
Ko bayan sun sauka Janan ta kirashi amma sai ya ce yana wani ɗan aiki zuwa ƙarfe 5 na yamma su haɗu a Green Park, saboda nan babu mutane sosai. Dan haka school suka wuce, Sadiya tayi wanka ta kwanta a katifarsu tayi lamo gani take sam lokaci baya tafiya. Miƙewa tayi tana kallon Janan kafin ta ce "Anya Janan ba zan sanarwa su Anisa ba?" "A'a ki dai bari ki fara jin ta bakinsa tukun" "Naga ai matsalar tamu ce gaba ɗaya" "Duk da haka ki dai bari ki fara jin dame yazo, karki damu ai tare zamuje kuma a gabana za a yi komai" "To shikenan" Ta faɗa a sanyaye.
*Yamma*
Tunda suka zauna a park ɗin duk wanda ya shigo sai ta ɗaga kai ta kalleshi sai taga kmar mutumin ne zai zo amma sai taga ya wuce su.
*05:40pm*
"Ni fa Janan na sare, gani nake kamar ba zai zo ba, gashi har 6 ta kusa, yanzu zakiji anyi magriba" "Mu dai ɗan ƙara jir..." Shiru tayi tare da faɗin "Kin ganshi ma ya shigo" Jin haka ya saka Sadiya juyawa ta kalleshi, kallon sani tke masa sai dai ka kasa gane a ina ta sanshi.
"Sannunku, am sorry na ajjeku ban zo da wuri ba" "Karka damu" Cewar Janan "Me kuke bukata a kawo muku" Har Janan zata sake magana Sadiya tayi saurin cewa "Babu! Buƙatarmu kawai ka faɗa min wanda ya ruguza rayuwata" Murmushi ya yi sannan ya ce "Kamar a hasale kike Sadiya" "Wannan ba maganar wasa bace, kasan irin illar da aka min?" Hawaye tuni ya cika kurmin idanunta, Janan ta dafata "Calm down" Hannu ta saka ta dafe goshi sannan ta kalleshi "Ka faɗa min gaskiya" "Kin san da ba zan faɗa miki gaskiya ba da bama zan nemeki tun farko ba, amma ki sani zan faɗa ne saboda naga ana neman ayi miki illa a rayuwa, kuma ina so na tabbatar miki da abinda ke faruwa dake ne saboda naga ke yarinya ce, kuma tun ranar da abin ya faru nake bibiyarki, na kuma tausayawa talaucin da kike ciki Sadiya" Kallon shi tayi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta kuma ƙagu taji wanda ya yi mata wannan illar. "Ka faɗa min dan Allah" Tayi maganar very calm.
*Bayan kwana biyu*
Duk da zazzaɓin daya rufeta sosai, amma a haka a daddafe tayi wanka ta shirya. Janan ma tuni ta gama shirin dan ita zata taimaka mata suje gurin. Wayarta data fara ringing ya saka ta lumshe idnunta, dam ƙaran wayar jin shi take kamar zai fasa kwanyarta. "Sady Habib ne" Janan ta furta a sanyaye. Karɓa tayi ta kara a kunne "Hello!"
"Sadiya ya jikin naki" Ɗan cije laɓɓnta tayi kafin ta ce "Da sauƙi"
"Idan ba zaki iya ba ki bari nazo na ɗaukeki, saboda already na ɗauko Baffa yanzu haka muna cikin Kano"
"Karka damu muma muna hanya, mu haɗu acan ɗin."
Banzan kallo taga Muhasin ɗin yana watsa mata, tare da Mommy kaɗai suka zo, Sai Habib da Mahaifinsa sai kuma Baffa da Malam Yakubu.
Guri ya yi shiru lokacin da aka gabatar da ƙarar tasu, alƙali ya ɗago yana shirin yin magana ta yi saurin cewa "Ina da magana ya mai shari'a" Dukkansu kallonta suke, hawaye cike a idonta ta ce "Na janye ƙarar zan zauna da mijina" Kallon mamaki suke mata, Muhasin ya yi wata dariya ta samun nasara. Alƙalin ya tambayeta ko mene dalili ta ce ita bata da wani dalili na sawa a raba auren dan haka ta janye. Habib ya yi iya yinsa dan ta gane illar abinda take shirin aikatawa amma tayi kunnen uwar shegu, a ƙarshe dai aka sallami ƙarar tare da cin ta tara na ɓata lokacin shari'a.
Suna fitowa Janan na riƙe da ita, Habib ya ƙaraso gurin tare da mahifinsa da kuma Baffa.
"Sadiya ko kin haukace ne?"
Sai lokacin hawaye suka fara bin ƙuncinta ɗaya bayan ɗaya "Da hankalina Habib, yau duhun da nake ciki an yaye shi naga haske, Habib na san kaine ka sato ni sannan a gabanka aka ci mutuncina aka min fyaɗe, na tsaneka, da ace na faɗawa sauran kaine da ba zasu barka ba, amma ba....ba..." Sai kuma kukan ya kubce mata, Muhasin da Mommy suka juyo suna kallon ikon Allah.
"Sadiya wace magana kike faɗa haka mara daɗin ji?" Cewar Baffa. Ɗagowa tayi ta riƙe gefen zuciyarta "Baffa....Shi ne ya...rab...rabani da farin cikina, wane laifin na aikata maka? Meyasa sai ni? Gara naje gidan Muhasin na mutu daa zauna da mai mummunar ɗabi'a irin taka, duk son da kake min na ƙarya ne, har ƙoda da ka bani duk yaudara ce, ko kuma alhakine oho.." Kuka ta ske saki gwanin ban tausayi. Cikin faɗa Habib ya ce "Wace magana ce haka kamar kin sha wani abu" Hannu ta saka ta goge hawaye duk da cewar wasu basu bar zuba ba "Ni ma da aka faɗa min da baki ban yarda ba Habib, sai dana ga hotuna da video sannan na gaskata, ko kana buƙatar na nuna masu? Ban taɓa tunani ko a mafarki zan ga fuskarka a aikata irin wannan zunubin ba, suma nayi na awanni kafin na farfaɗo, kuma har yau bani da lafiya zazzaɓi ne a jikina, ji nake kamar mutuwa zan yi, amma na danne zuciyata naƙi nuna maka, dan so nake azo nan na ganka ido da ido a gaban Baffa na sanar da kai" Sadiya wannan ƙarya n...." "Dakata, ba wani abu da zaka kare kanka dashi" Tana kuka ta sake faɗin "Ka bar iya wannan dan Allah, kuma kaje ka binne uwa ta Aunty Aziza in har wani abu ya sameta?..." Ji tayi jiri na ɗibarta. "Ba...zan...yafe...ma.." Bata ƙarasa ba a take ta zube a gurin.
*Alhamdulillah*
_Wannan shi ne ƙarshen ZINA BASHI CE Book 1._
*Zai yi wuya ku gane inda labarin nan ya dosa, ba zaku iya gano ni ko ku gane abinda ke gaba ba, na ƙalubalanceku😃😂*
A book 2 akwai cakwakiya mu kasance tare dan jin.
*Hafeez da ɗanshi*
*Ya labarin Zaliha, shin Muhasin zai aureta?*
*Ya rayuwar Sadiya zata kasance a gaba?*
*Shin ya zata kaya da Habib, shi ne dagaske suka sato Sadiya ko kuwa? Idan shi ne meye dalili? Waye yake masu fyaɗe? Mene dalilin aikata haka, bayan a labarin Habib babu wannan ɓoyayyen lamari, waye wanda ya fallasa abin?*
*Mene maƙasudin kisan da ake idan muhasin na son mace ko tana son shi?*
*Sadiya zata mutu ko kuwa? Shin zata je ta zauna da muhasin ko kuwa?*
_Akwai abubuwa da yawa da kuke buƙatar amsoshinsu, dama wasu da zasu zo a gaba, mu kasance daku_