KAIFI ƊAYA

01

by @ummishatu1111

KAIFI ƊAYA.... 
_A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._


NA

UMMI A'ISHA

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI



1



****Room 204 (A'isha specialist Hospital), a saman ƙofar ɗakin akwai nameplate wanda aka rubuta shi da kalar ruwan zaiba rangadaɗaɗau Dr. Mimi B. Muhammad MBBS, FMCOG, a cikin office din teburi ne guda ɗaya dake dauke da stethoscope yashe kamar mataccen miciji,patients file a gefen dama sai medical journals a ɓarin hagu kusa dasu wani framed ne dake dauke da hoto yana kallon ƙasa gefen shi littafi mai tsarki izu sittin ne ƙanana gwanin burgewa cikin gidansu,kujeru guda biyu gaban teburin, kujerar zaman ta lanƙaye da white coat dinta yayinda wani taftekeken window yake bayan kujerar wanda kana iya hango ƙaton lambun cikin asibitin da ko yaushe ke kaɗo iska mai daɗi mai kunshe da ƙamshin tsirrai da ciyayi yana kawowa cikin office din amma hakan baya hana ƙamshin antiseptic da mint gum bayyanuwa kowanne lokaci she told patients "fresh air helps healing" but she never opened it for herself,a jikin bango medical certificates dinta ne kakkafe tare da wani babban frame a jiki an rubuta "sometimes the doctor needs healing too". A hankali ta yunƙura ta tashi daga kan kujerar da take zaune wacce ke dauke da tarin tulin takardu da files na marassa lafiya bisa kan teburinta, wani ɗan ƙaramin katako ajiye akai sannan sunanta maƙale jikin katakon inda aka rubuta Dr Mimi Basheer Anda, ji take kamar ta ɗora hannu a kai saboda tsananin damuwa da baƙin cikin da take ciki, bata san ta fara zagaye cikin office din nata ba saboda tana cikin duniyar tunani, fargaba da kuma alhini ga tarin takaici da ya cika kwanyarta da kuma zuciyar ta baki ɗaya. Jikin teburinta taje ta tsaya ta dafa shi kanta na kallon sama, sanye take cikin bakar doguwar riga abaya wadda ta dace da jikinta, kanta ta saka dan ƙaramin farin hijabi amma duk da haka bai ɓoye tulin gashin da ya lullube goshinta ba baki sidik dashi, fara ce amma amma ɗau ba saboda wani irin kala fatar ta take dashi kamar gyadar da ta soyu (roasted groudnut), her eyes deep brown, tired but sharp like a surgeon's scalpel, she didn't wear makeup to hide she wore it like armor, madaidaiciya ce wurin tsayi da yanayin jikinta matsakaiciya dan bata cikin sahun masu kiba haka kuma bata cikin sahun sirara sai dai ta kirar jikinta tana da kiba ta kirjinta da kuma hips dinta dan tamkar tayi ciko sai dai kallo daya zaka yi mata ka gane natural halitta dinta ce haka a ƙalla zata kai shekaru 32 to 33 but her beauty didn't shout it whispered,she wasn't "pretty" she was presence, the type of woman who walks into a room and the air adjusts, Mimi's beauty was the kind that heals others, even when she was breaking. 

Tana jin lokacin da aka bude kofar office din nata aka shigo amma hakan bai sa ta iya sauke kanta ba daga kallon saman da take yi bare har ta juya taga wanda ya shigo,

"Dr..... What's going on? Ga patients awaje da yawa suna jiran ki......."

Cikin damuwa ta sauke kanta ta ja wata doguwar ajiyar zuciya kafin ta juya ta kalli Dr jalila,

"Dr am not fine..... These days am not myself...... Am tired of everything....."

Kallonta Dr jalila tayi na yan mintunan da basu wuce biyu ba zuwa uku tace da ita,

"Dr why are you like this? You are a doctor and you are saying you no fine? Kina duba wasu ma bare kuma ke kanki? Idan kina ganin kina bukatar hutu you have to take a leave and rest.... But karki takura kanki, kina nemawa wasu lafiya ke kuma kina kokarin cutar da taki lafiyar we don't want this.... "

" Okey Dr thank you.... Insha Allah i will think about it.... "

" ok Dr, don't mention it "

Bata ƙara magana ba wayarta dake ajiye kan tebur dinta ta fara ƙara hakan ya bawa Dr jalila damar juyawa dan fita daga cikin office din ita kuma ta kai idonta kan wayar tata ta tsura mata ido tana kallonta tare da kai hannunta ta ɗauka amma ta kasa ɗaga kiran sai kallon kan screen din wayar take _Hayatie_ shine sunan da tayi wa mai kiran nata saving dashi wanda harda heart guda biyu da padlock duk maƙale jikin sunan, tana ji kuma tana gani har wayar tayi ta katse wani kiran ya sake shigowa wanda shima bata ɗauka ba shi kuma mai kiran tamkar baida niyyar haƙura har sai ta ɗaga,

Kan kujerarta ta koma ta zauna cikin damuwa ta ɗaga kiran ta kai wayar kunnenta sai dai bata yi magana ba,

"Mimi..... My love can you hear me?"

"ina jinka..."

"My love.... I have been missing you, i have been missing you every day......."

Numfashi ta ja da kyar kuma ta fesar dashi da kyar saboda sarkewar da kirjinta ke yi time to time, cikin damuwa tace,

"Wannan shine abinda na jima ina nuna maka amma taurin kanka da zafin fushin ka da kuma fusatacciyar zuciyarka ta hanaka gani da kuma fahimta..... Yanzu gashi muna ji muna gani ka haramta mana rayuwa da juna...... And you know what? The most painful part of it is that ban taɓa jin ina mugun sonka ba sai yanzu da hakan ta kasance yaya Aliyu.... Wallahi yanzu son da nake maka ya ƙaru da irin yawan da ni kaina ban san ta yanda zanyi explaining ba..... Ka sakani cikin damuwa, am always thinking about you..... Kullum dama acikin zaman mu ina fada maka mu ba yara bane idan matsala ta faru kamata yayi mu zauna muyi discussing da juna ba wai muyi ta fada ba, munyi girman da ya wuce muyi irin wannan since we are not a child......"

Daga can inda yake zaune taji shima ya ja ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka ya ƙoshi, babu abinda yake hangowa sai irin kyakkyawar surarta da dirin da Allah yayi mata,

" Mimi i know that I mess up...... Yanzu dai duk wannan maganar bata da muhalli kawai mu nemi mafita kamar yadda na fada miki daren jiya a waya, kema kin san ba zan iya rayuwa batare da ke ba.... Kema kuma na san ba zaki iya rayuwa ba tare da ni ba, dan Allah mimi kar ki haramta mana cigaba da zama da juna, wannan shawarar da na fada miki ita kadai ce mafitar mu, kinyi tunanin?? "

" Yaya Aliyu har yanzu ban gama yanke hukunci ko tunani akan wannan maganar ma ba wallahi, asalima tun bayan da muka gama waya da kai na kasa komawa bacci gashi har yanzu da na fita office bana cikin hayyacina kawai ina ta tunani kamar wata tababbiya..... Ka sake bani lokaci"

"Mimi bamu da lokaci fa, kin san iyayen mu, komai na iya faruwa..... Dan Allah ki amince da wannan shawarar tawa dan wannan hanyar ce kadai mafita a gare mu, we have no option... Ni ban yarda da kowa ba sai shi"

"ka bani time zuwa lokacin da zan koma gida..... Duk abinda na yanke zan fada maka.... Insha Allah I will let you know"

"to shikenan mimi na, I love you"

"I love you more yaya haidar..."

Katse wayar tayi ta ajiye ta zuba mata ido bayan tayi tagumi, ita kanta ta san a yanzu dai bata da nutsuwar da zata iya duba patients yanda ya kamata har ta yi musu abinda ya dace shiyasa ta tattara nata yanata kawai ta nufi gida ba wai dan lokacin tashinta yayi ba.

*
Kyakkyawan saurayi ne matashi fari dogo siriri mai manyan idanuwa da dogon hanci ɗan kimanin shekaru 27 zuwa 28.Tashinsa daga bacci kenan yaji wayar shi na ƙara, mika hannu yayi ya dauka fuskarshi dauke da murmushi sakamakon ganin sunan wanda ke kiran nashi,

"Irfan yane? ya ake ciki?"

"gani nan zan zo gidan na dauke ka yanzu...."

"ok to sai ka shigo, bari nayi wanka before ka karaso...."

Daga haka ya ajiye wayar ya sauka daga kan tafkeken gadonshi ya shiga toilet wanka yayi bayan yayi brush ya fito yana kallon time yaga 1 saura wasu mintuna cikin kasala mai hade da gajiya ya soma shiryawa, yana saka kayanshi ya jiyo shigowar Irfan cikin gidan take kuma ya fara damunsa da wani irin mahaukacin horn, wayar shi kadai ya dauka ya fesa turare a jikinsa sosai ya fita, babu kowa a gidan sai iya masu aiki kadai shiyasa batare da ya saurari kowa ba ya fice yaje ya samu Irfan cikin mota yana yin waya, bude gaban motar yayi ya zauna yana kallon Irfan din dake waya,

"Yanzu ina gidansu Daddy ne naje dauko Afeef zamu karasa gidan yanzu insha Allah kafin ki dawo.... Zan fada mata..... Ok to adawo lafiya" 

Kallon Afeef din Irfan yayi bayan ya gama wayar ya ajiye ta, 

"Anty Mimi ce.... Saƙo ta fada min wai in fadawa hajiya saboda tana ta kiran wayarta bata shiga" 

"Oh Allah sarki ni tunda na dawo ma har yau ban hadu da anty Mimi ba fa...." 

"Hmmmmm ai akwai matsala ne.... Anty Mimi na cikin damuwa sosai" 

Cike da mamaki Afeef ya kalleshi saboda jin abinda ya fito daga bakin sa, 

"me ya faru? Ko damuwar rashin haihuwa dinne?" 

"harda wannan dinma amma yanzun dai ka san sun rabu da yaya Aliyu....." 

Bude baki Afeef yayi yana kallon Irfan cike da mamaki, 

"yaya Haidar ya saki anty Mimi?" 

"wallahi kuma har saki uku Afeef.... Ashe ba muyi maganar da kai ba.... Har fa ta gama idda ko yanzu ta samu miji aure zata yi"

"innalillahi wa inna ilaihir rajiun..... Ban taɓa sani ba wallahi sai yanzu.... To shi kuwa yaya Haidar me ya sameshi haka? Me yayi zafi shi da ba shaye shaye yake yi ba, saki har uku...... This is bad.... Soo sad"

"very very sad Afeef....."

"gaskiya banji dadin jin wannan labarin ba, Allah ya rufa asiri yasa haka shine yafi zama alkhairi"

"amin ya Allah..... Anty Mimi na cikin damuwa tun bayan da abin ya faru wallahi"

"to ai mutuwar aure babu dadi ne Irfan, gashi kwata kwata auren nasu kamar bazai fi 6 years ba ko?" ina iya tuna time din da akayi bikin nasu"

"ehh 6 years yanzu...... Idan ma bai  karasa ba to kadanne fa..."

"kai amma yaya Aliyu bai kyauta ba"

"babu komai ai, suma su Abba duk basu wani damu sosai ba, tunda abune na family, duk gida ne to babu ma amfanin fushin..... Hajiya ce dai kawai ta damu"

"wannan dama ai sai tafi kowa bala'i ni shiyasa zaka ga bana son abu ya hadoni da ita..... Ta fiya masifa wallahi"

Dariya Irfan yayi ya juya ya kalleshi sannan ya mayar da idanuwanshi kan titi yaci gaba da driving dinsa kafin yace,

"wallahi bari su daddy dai su ji ka, hajiyan tasu kake kira da masifaffiya ko?"

"to karya nayi, mace kin tsufa ma ba zaki hakura da faɗa da masifa ba"

"zaku gauraya ne.... Kai ai ɗan lelenta ne ma na manta, duk cikin jikoki tafi ji da kai"

"na sani ai" ya fada yana dariya, har suka je unguwar GRA maganar da suke yi kenan, gidane babban gaske mai dauke da gate guda uku, biyu suna kallon juna yayin da suka saka ɗaya a tsakiya gaba ɗaya gidajen upstairs ne na alfarma wanda ya ƙawatu kuma ya wadatu da shuke shuken flowers da manyan bishiyoyi kala kala a tsakiyar wawaken filin gidan akwai round about wanda ke zagaye da fitilu masu kyau da tsari dan ƙarawa gidan ado da ƙawa, ko ina manyan motoci ne lafiyayyu a faffake suna numfash, wanda yake tsakiyar suka shiga gidane madaidaici dan sauran sun fishi girma, masu aikin gidan suka fara cin karo dasu suna ta aikace aikacensu na abincin rana, ciki suka shiga inda wani babban falo yake sai bedrooms guda uku, biyu a ƙasa guda ɗaya a sama, wata farar dattijuwa na zaune kan kujera da farin glass a fuskar ta, a shekaru zata kusa shekara casa'in koma ta ɗora,

Da sallama suka shiga ta amsa tana kallon su ɗaya bayan ɗaya har suka samu wuri suka zauna,

"Afeef..... Sai yau ka gadamar zuwa ka gaishe ne lele?"

"hajiya ni tunda na dawo babu inda naje ga Irfan nan ki tambaye shi kiji"

"to Allah ya sawwake..." ta fada tana mayar da kallonta ga Irfan,

"Hajiya anty Mimi tace in fada miki yau da wuri zata dawo kisa ayi mata lunch kafin ta dawo wai faten dankalin turawa take so asa mata wake kadan da ganye aciki..."

Kai ta gyaɗa sannan tace "Allah ya dawo da ita lafiya... Bari in fada musu" yunkurawa tayi ta tashi ta fita, bayan ta fita Irfan ya kalli Afeef yace,

"zo mu shiga gida muci abinci dan ni yunwa nake ji"

"nima yau banyi ko breakfast ba ina ta bacci amma mu bari wannan tsohuwar ta dawo kafin tayi mana sharri tace mun ɗaukar mata wani abu ka san halin ta....."

"kuma tsaf zata fada ba..."

Shuru dukkan su suka yi saboda shigowar hajiya kaka kamar yadda suke kiran ta, zama tayi tace,

"kuma din da ban gayyatoku ba gashi nan nasa a kawo muku abincin ba dan halinku ba...."

"ai mu dama kin bar kayanki dan bama son gori..." Afeef ya faɗa yana ciccin magani, muficin dake kusa da ita ta ɗauka ta jefa masa tana cewa,

"ai kuma ka dawo lele..... Zaka yimin shuru ko sai na fasa bakinka"

"hajiya kaka wallahi gaskiya fa ya faɗa, ke ba abin ki bawa mutum abuba gori ya biyo baya..." Irfan ya fada yana dariya, 

"ku dai kuka sani... Kwa kai shi in kayane" 

Ahaka masu aiki suka shigo suka same su suka kawo musu abinci, jallop din shinkafa da salad sai farfesun kaji a wani mazubin na daban sai kuma waina da miyar taushe, ƙasa suka sauka suka zauna kan carpet suka zuba abincin suna ci suna tsokanar hajiya kaka, shigowar Mimi yasa gaba ɗaya suka mayar da kallonsu da kuma hankulansu gareta wanda kallo ɗaya zaka yi mata ka gane dunbin gajiyar da take tattare da ita wadda ta bayyana ta kasa ɓoyeta......... This is where it all starts, where the pain begins, where the love refuses to break............! The question is would you have stayed if love stopped looking like it used to?? Please don't scroll fast....


#Kaifi ɗaya#
#EmotionalRomance#
#Haidar#
#MimiAndAfeef#

Ummi Shatu 👌🏻