MAƘOFTAKA DA ALJANU

Chapter 10

by @deejasmah

MAƘOFTAKA DA ALJANU 

Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma 

Last free page
CHAPTER 10
 ...Caraf ta ji an damƙi hannunta da karfin gaske. Bata bata lokaci ba wajen ɗago da kanta domin idan masifa ta kai masifa wani tsoron fita ya ke daga idonka. Gawar nan ce wadda ta gani dazu za a kusa da ita zaune a gabanta ta yi ma hannunta kyakkyawan riko. " Ki saurareni" ta fada muryarta na amsa kuwwa.
"Wace ce ke? Ku rabu da Ni me na tare maku?" Nana ta fada cikin murya mai kunshe da firgici.
"Na sani Nana ina da abin da zan sanar miki ne ki nutsu ki saurareni lokacin mu ƙalilan ne" gawar ta karasa maganar tare da kallon gawawwakin da ke kokarin saukowa daga saman gadonsu.
"Ki tabbatar a gidanki...." Maganar gawar ce ta sarƙale sakamakon shaƙeta da sauran gawawwakin suka yi. 
Janta suke da karfin gaske suna babbaka mahaukaciyar dariya. Firgigit! Nana ta farka daga mummunan mafarkin da tayi.
Ilahirin jikinta yayi sanyi sosai tamkar wadda aka samo daga cikin randar ruwa. Abin da ke bata mamaki shi ne, ga Inna Yabi dake kwance a kasa amma bacci take yi cikin nutsuwa da salama. Ita kam matsanancin sanyi take ji. "Ko dai da gaske ne naje wurin can?" Nana ta fada a bayyane.
Me gawar can ke kokarin sanar da ita, ko dai da gaske ta fara haukacewa? Saboda ko a tarihi bata taba jin wanda ya fuskanci makamancin abinda ta fuskanta ba. Cikinta ta shafa tana sauke ajiyar zuciya. 
"kamar In je macuware In duba ne?" 
"Kul! Kika sake kika fita. Muddin kika yi kuskuren tafiya tamkar kura ce ta kai kanta a fadar zakuna" wata zuciyar ta yi saurin tunasar da ita.
Ta kasa motsin kirki zaune ta takure can a karshen gado. A hankali ta ji an bude tagar dakin, duk da tsorom da ke dawainiya da ita bata gajiya ba ta kalli wurin. Garam! Tagar ta kulle kanta da karfin gaske. 
A yanzu kam Nana ta san wannan karar ta isa ta tayar da Inna Yabi, sai dai ko da ta kalli kasa bacci take yi cikin kwanciyar hankali kamar babu abinda ya faru.
Shi ya saka ta kara takurewa can karshen gado tana numfashi da kyar. Ji da tayi komai ya lafa ya saka ta zuro kafarta daya daga saman gado, cikin sanɗa take tafiya don kada ta tayar da Inna Yabi. Har ta karasa gaban tagar bata ji wani motsi ko kuma alamun akwai wani abu a wurin ba, hannuwanta biyu ta saka ta dafa tagar tare da zura kanta waje domin ganin ko akwai wani abu daya buya a wurin. Ba zato ba tsammani hannuwa ba tare da ta ga mai su ba suka shaƙe mata wuya. 

Duk iyakar kokarinta ganin ta kwace  kanta abun ya ci tura. Tsabar azaba shure-shure take da ƙafafuwan ta ko Allah zai saka Inna Yabi ta farka amma shuru, malam ya ci shurwa. 
Tun tana ganin bibbiyu har ta koma ganin duhu din ɗim! "Nana! Nana!! " Ta tsinkayi Muryar Inna Yabi sama-sama. Da kyar ta bude idanunta da suka yi mata nauyi sosai ta sauke akan Inna da ke tsaye. "Nana! Wannan ne irin abu ne? Yanzu duk gadon nan da kike kwana ke daya, sannan in ma  kasa kike son kwana ba sai kiyi min magana in matsa miki ki kwanta kusa da ni ba. Amma Nana ki rasa inda zaki kwana sai saman sanyi tayis gaki a saitin taga. Kin kuwa san illar wannan sanyin ga mace mai ciki?"
Abin da ta ji ta fada shi ya sakata saurin kallon inda take. Da gaske kwance take a ƙasa, hakan na nufin jiya suma ta yi ko kuma hankalinta ya gushe har sai da asuba ta yi.

Da kyar ta mike zaune tare da shafa wuyanta da ta ji ya na yi mata zafi. "Inna dubamin wuyana zafi ya ke mini"
"Ba dole wuyanki ya yi zafi ba kin tashi kin kwanta kasa. Wa ma ya sani ko wani abu ne ya cije ki" ta karasa mitar tana duba wuyan ta. "Subhanallahi! Nana sawayen hannun mutum ne. Me ye haka ko shaƙe kanki kika yi ba tare da kin sani ba?"
Shuru Nana tayi tana kara gasgata abin da ya faru da ita jiya, ta ma rasa me zata ce ma Inna. In ta fada mata gaskiya tabbas ta kara gaskata cewar Nana da na wani na'u'in ciwo na jinnu. 
"Nana!" Ta tsinkayi Muryar Inna na kiranta. "ko dai akwai abin da ya ke faruwa Wanda kike boye mana. Ki sani irin wannan matsalar ba a boye ta, na fahimci a dan zaman da muka yi da ke tabbas kina da damuwa amma sam baki son fada"
"Inna babu komai. Ba abin da ke damuna, kawai dai wannan rashin lafiyar ce" ta karasa maganar ta na mai sunkuyar da kanta a kasa.
"Inna Bari in yo alwallah." Mikewa ta yi ta shige kewayen da ke cikin dakin.

Bayan ta fito sallah ta tayar ita ma Inna Yabi ta Shiga daga ciki ta yi alwallah. 
Shuru ta gifta na wani lokaci daga bisani sai ga nurse ta shigo. Allurar karshe aka yi mata ta sanar da su wajen tara idan likita ya zo yin round zai ba su sallama.
Nana tafi Inna farin cikin wannan sallama da za a yi masu, domin ta gaji da zaman asibitin nan fatanta ɗaya Allah ya iyakance mata wannan masifa.

Sallamar Khaleed da kayan kalaci ita ta katse mata tunanin da take yi. Bayan sun gaisa ya ke tambayarta jiki. "Da sauki, doctor ma zai sallame mu In an Jima."
"Ma shaa Allah! Shi ya sa na sanarwar shugaban makarantar mu yau bazan samu damar zuwa ba, tare da ni za a karasa jinyar matata." ya karasa maganar ya na ɗaya mata gira.
Murmushi ta yi tana kallonsa. "Janna!" Ya kira sunanta cikin sanyi murya. Kallonsa ta yi saboda Indai ya kira wannan sunan abu mai muhimmanci zai fada. "Ke rayuwata ce na rasa gane wace irin kauna nake miki, don Allah kada kiyi abin da zai saka cikin nan samu matsala. Kaf burikana na duniya a yanzu suna bayan wannan cikin, a yanzu zan iya ce miki shi ne fatana inga kin haifa muni Magaji ko kuma magajiya" ya karasa zance suna kallon juna ido cikin ido.
"Ehen!"
Iyami da ta jima da shigowa dakin ce ta yi gyaran murya.
"To Romeo da Juliet, Kai gaskiya wurin nan ana zuba kauna. A asibitin ma, ina ga in mun koma gida? " Ta karasa maganar tana dariya.
"To shugabar 'yan saka ido ta kaf africa. Anya yarinyar nan zamu tafi dake gida kamar ma takurawa mutane za kiyi" cewar Khaleed.
"Binku ai ya zama farilla, can zamu je in kara kwass"
Ɗaya ma Nana gira tayi suna dariya.
Likita ne ya shigo bayan sun gaisa ya ce ma Khaleed ya bishi office ya amshi sallamarsu. 
Yaya Adama ce ta karaso ita ma su duka a tare suka ranka ya zuwa gidan Nana. 
Saka kafarta cikin gidan ta saki ajiyar zuciya. Alhamdulillah! Ta fada a cikin zuciyarta. Iyami da Yaya Adama su suka gyara gidan suka share ko ina. Lokaci daya gida ya dauki sauti, ganin azahar ta kusa Iyami ta dafa masu abinci zuwa la'asar Inna Yabi da Yaya Adama suka fara maganar tafiya. "To Nana! Wannan jinkanya dai ko jika sun wahalar da kakanninsu. Ki ma fada masu suna zuwa duniya ni ce ta farko da zan fara ja masu hanci, In ɗan tsunkulesu ladar jinyar da nasha.
Dariya mutanen falon suka dauka. "Ke dai Inna kina jiran kyakkyawan ango ko kuma kishiya shi ya sa kike ta yi masu hidima."
Nana dai sunkuyar da kanta tayi ƙasa ta na murmushi, nepar da aka maido ta saka Nana shiga ƙurya don ta saka chaji.
Kasancewar socket din kusa da Mirror ya ke, a saman shi ta ajiye wayarta. Har zata juya kamar ance ta kalli Mirror abin da ta gani ya sakata fiddo ido gabanta na dukan uku-uku.
Cikin da ke jikinta ne take hange ƙuru-ƙuru ba tare da shamakin komai ba a cikin mirrorn. Jariri kwance yana ɗaya hannu alamar a daukesa. 
Ja da baya Nana ta yi saboda ta tantace  da gaske cikinta ne kuwa. 
Tabbas kuwa shi ɗin dai ne take ganin ba tare da na'urar likita ta haska mata ba. 
Gumi ne ya shiga wanke ilahirin jikinta.
"Nana!" Ta tsinkayi Muryar Yaya Adama na faɗa. 
Da sauri ta fita fakon tana kokarin boye damuwarta. Bankwana suka yi masu har bakin Get Nana ta rakasu.
Iyami Kuwa tana falo ta samu kallo. Inda Nana ta lula duniyar tunanin abin da ya faru. Ƙarar bugun gidan da ake yi ce ta saka Iyami mikewa zata fita.
"Ci gaba da kallo ki bari duba" cewar Nana. Har ta karasa bakin Get din ba a daina dukan kofar ba.
"Waye?"
Nana ta fada.
"Makoftanki ne" ɗaya bangaren aka fada.
Rass! Gaban Nana ya yanke ya daɗi. Wani irin juyi abin da ke cikinta yayi ba shiri ta duƙa ƙasa, tana dafe bayanta da cikinta cikin tsananin ciwo...

Meenat A. 'Yandoma