Rabin Raina

8. Zuciyar shi

by @inkedbynadeerah


Gurin ya ɗauki shiru na ɗan wani lokaci. Habib ya dubi Najib yana jiran amsa.

Kafin Najib yace uffan, wani a cikin su ya katse shirun da cewa, 


"Wato fa bro, naga you are serious akan wanna batun. Ka fara tsara auren mutane kenan? 


Kuma fa gaskiyar ka, Najib ya dace sosai da wannan ƙanwar taka. Da alama ka iya aikin ka.


To don Allah nima ka sakani a layi. Idan an gama da nashi project ɗin, gani a gefe. Ina so na angonce kwana kusa.”


A wannan karon, Najib yayi dariya tare da kowa, banda mutum ɗaya a cikin su da ɓacin rai ya ɗan nuna a fuskar sa duk da cewa yana iya ƙoƙarinsa kada a gane. 


Najib ne kadai ya lura da canjin yanayin.


Sadiq ya kau da kai a lokacinda ya ɗauki doguwar glass cup ɗinda ke gaban shi a kan table, ya kai baki ya kurbi ruwa mai sanyin dake ciki sannan ya ajiye, yana mai sauraron maganganun su ba tare da ya saka baki ba.


Sadiq ya daɗe yana ɗauke da wani abu a ransa game da Hauwa ba tare da ya bari ya fito fili ba. Sai dai ganin yadda Habib ke ƙoƙarin haɗata soyayya da Najib ya sanya shi jin wani irin bacin rai mai nauyi da yake ƙoƙarin kufce masa.


A karo na farkon haɗuwar Najib da Hauwa a zahiri, Najib ya lura cewa akwai wani abu ƙulalle a zuciyar Sadiq.


Sadiq yayi musu wani irin kallo a lokacin da Habib yake introducing ɗin su. Duk da suna nesa dashi hakan bai hana Najib gane abin da ke cikin idanun sa ba.


Wani abu ne mai kama da kishi, ya bayyana a fuskar sa. Haka yasa Najib ya gane lallai sadiq nada interest akan Hauwa.


Yanzu ma ya ƙara tabbatar da hakan ganin yadda mood ɗin Sadiq ya canza.


Najib yayi nazari a ransa irin sarƙaƙƙiyar da zai iya afkuwa tsakanin shi da Sadiq nan bada daɗewa ba. 


Habib ya gama nashi dariyan sannan yace, "To ai dai dai kenan mutumina. Kaga sai ayi tuwo na mai na. Ita ‘yar uwata shi kuma aboki na. Abin zaiyi kyau sosai.“


Sadiq ne ya tashi da shirin barin gurin tareda ɗaukar makullin motarsa dake ajiye kan table. Dukkansu suka dube shi, fuskokin su na ɗauke da alamar tambaya. Habib yace,


“Sadiq, ina zaka kuma?" 


Sadiq ya bashi amsa ba tare da ya ɗago kai ba. "Zan wuce gida ne." Ya fara tafiya ya nufi ƙofar fita restaurant ɗin da fuskar fushin da bai nuna ba sai daya juya musu baya. 


Suka dube shi cikin rashin fahimta. Najib shima yayi mamakin yanayin da Sadiq ya shiga. Baiyi tsammanin abin zai kai haka ba.


Habib ya ƙara da cewa, 


"Ji mana, we just got here kuma zaka tafi muna magana mai muhimmanci. Kai daya kamata kayi supporting ɗina amma kana cewa zaka wuce yanzu? Ko wani abu ne ya faru?" 


Sadiq ya waigo da kallon sa zuwa kansu da fuska babu alamar walwala. Ya mayar da kallonsa daga kan Habib zuwa kan Najib. Idanun sa suka ƙara bayyanar da ɓacin ran da Najib ne kaɗai ya gani. 


"Ba komai, na tuna akwai wani urgent issue ne da zanyi handling. Inn shaa Allah we will soon see again.”


Yana faɗin haka ya fice ya shige motarsa ya tafi.


Da tafiyar Sadiq gurin da suke ya ɗanyi shiru. Abokin su dake zaune daf da Najib yace, 


“To ya, ina fatan an sani a layin dai. Zaka samo min nawa matan ko?”


Habib ya dago da kallon sa yayi dariya. “Kar ka damu. Lokacin ka yana zuwa.”


“Ah to shikenan. Zan iya jira. Kar dai an mance dani.”


Najib ya ci karo da kallon da Habib yake masa, irin kallon zasu ƙarasa maganar wani lokaci. 


Najib ya kau da kansa kamar bai fahimci ma’anar kallon ba, amma a ransa kuwa, yaji daɗin yadda maganar ta tsaya anan, domin bai shirya amsar da zai bawa Habib ba.


*****


Hasina ta daɗe tana jiran dawowan yayan ta. Shiru ba batun sa har wajen ƙarfe goman dare. Haka nan ta haƙura ta wuce ɗakin ta domin bacci ya gama kame mata idanu.


Najib bai dawo gida ba sai kusan karfe goma da rabi na dare. Da isowarsa ya shige ɗakinsa ya shiga bathroom ya watsa ruwa sannan ya fito yayi shirin bacci. 


Yana kwanciya kan gadonsa tare da rufe idanunsa da niyyar bacci, Maryama ta fado masa a rai. Da wasa da wasa, Maryama tana ƙaƙarin mamaye wani babban gurbi cikin zuciyar shi. Tunanin ta na yawan zuwa masa ba tareda ya shirya ba. 


Ko da wani abun Maryama bai ɓata cikin motarshi ba, zai yi ƙoƙarin bin hanyar da zai sa su zama kusa da juna.  Yanzu kuma da bracelet ɗinta na gurin shi, sai ya ji kamar ƙaddara ta sake bashi wata hanya zuwa gareta. 


Sai da bacci ya sace shi sannan zuciyar shi ta samu hutu da tunanin Maryama.


****


Maryama ta tura curtain na window ɗin ɗakinta gefe guda tare da lanƙayawa jikin curtain holder. Komawa tayi ta zauna kan gadonta mai tudu, tana hangowa garden ɗinda ke wajen gidan. 


Kamar kullum, yau ma flowers ɗin sunyi kyau sosai, suna bada kaloli masu ban sha’awa ƙarshashin rana mai sanyin hasken safiya. Tana iya hangowa masu aiki da suke musu bayi. 


Tayi salati tana mai ƙara godewa Allah daya sanyata cikin bayinsa masu wadata. Kallonta ta mayar kan agogon dake manne jikin bango. Ya nuna karfe takwas na safe. 


Mikewa tayi ta shige bathroom tayi brush sannan ta wuce sashen iyayenta ta gaidasu kamar yanda ta saba. 


Bayan sunyi breakfast ta sanar dasu cewa tana neman izinin su tana so taje shopping, tana son sayan wassu abubuwan da take buƙata. Suka amince mata kamar yadda suka saba a duk sanda tazo musu da buƙatar ta. 


Kasancewar ranar juma’a ce, ta koma ɗaki don fara shirin fita da wuri kafin sallar juma’a yayi kada driver yayi mata nisa ta kasa samun shi.


Ta sake shigewa bathroom tayi wanka sannan ta kasance cikin shiri. Da fitarta harabar gidan ta samu driver ya fice da ita.  


****


Cikin raha da labarantawa juna Najib ya samu iyayensa suna breakfast. Ya gaida su cikin ladabi, suka amsa cikin sakin fuska sannan ya jawo ɗaya daga cikin kujerun dining table ya zauna.


"Yau kuma an fito da wuri ne?" Mahaifinsa ya tambaye shi


Najib yace, "Eh Abba, yau na fito da wuri. Ina Hasina? Ko bata tashi ba?" 


Hajiya Bilkisu ta bawa ɗanta amsa.


"Eh, har yanzu bata fito ba. Kasan ƙanwar taka akwai iya sana'ar bacci.


Akwai ranan da bata fito breakfast ba har sai da aka zo aka kwashe komai saboda lokacin abincin rana ya kusa.”


Najib yayi murmushi. “Ai lokacinta ne yanzu. Data shiga school zata rage bacci.”


Alhaji Bello ya gyaɗa kai. "Ai kuwa wannan maganan naka gaskiya ne. Ballantana tace likitanci take so ta karanta? Ita da irin wannan baccin zasuna kewan juna" 


Hajiya Balkisu tayi ʼyar dariya dajin abinda mijinta ya faɗa. Da gama dariyarta ta kalli Najib sannan taja guntuwar ajiyar zuciya. Najib dake cikin ɗiban fried chips da serving spoon zuwa plate ɗinsa ya ɗago kai. Kallon shi takeyi da fuskar mai son furta magana. 


Shima Alhaji Bello ya kai kallonsa gareta a lokacinda yake faman kurɓe shayinsa mai ɗumi.


Najib ya mayar da hankalinsa kan plate ɗinsa yaci gaba da ɗiban chips dai dai yadda zai isheshi sannan ya miƙa hannu kan sauce bowl ɗinda ke tsakiyar table. 


Da ganin haka a hankali Hajiya Bilkisu ta tura masa kwanon sauce ɗin yadda zai ɗauka ba tare daya wahala ba. Najib ya shiga sawa saman chips ɗinsa sauce tare da ce mata ya gode.


Har yanzu Alhaji Bello bai ɗauke kallonsa daga kanta ba. Fiskarsa ɗauke da alamar tambaya ya kira sunanta. 


"Bilkisu?" 


A hankali ta waigo kansa.


"Ɗanka yaƙi ya saurare ni akan maganar aurensa..."


Alhaji Bello ya ajiye mug ɗinda ke hannunsa sannan ya tuntsure da dariya. Bayan ya gama sheƙe dariyarsa sannan ya fara faɗin, 


"Ni wallahi na ɗauka zakice kinaso kije ziyara gida ne. You did exactly what you are doing right now dana hanaki zuwa Maiduguri wancan karon. Yanzu kuma batun auren Najib ne?"


Itama Hajiya Balkisu tuntsurewa da dariya tayi. Najib ya murmusa murmushi mai sauti yana mai cin abincinsa.


"Abban Hasina, wallahi ina kwaɗayin naga Najib yayi aure. Kaga hankalinsa zaifi kwanciya. Amma yamin biris da zancen."  


Najib yayi ajiyar zuciya tare da dakatar da cin abincinsa, ya ajiye fork ɗinda ke rike a hannunsa cikin plate.


"Ummi, kiyi haƙuri. Bana so ki sa kanki cikin damuwa akan abinda bai kai ya kawo ba." 


Damuwa ya sake bayyana a fuskar mahaifiyarshi.


"Bai kai ya kawo ba kace? Ka tuna fa kai ba mai zama guri ɗaya bane ballantana na samu isasshen lokaci nayi maganan nan dakai. Ya kamata ka rinƙa bani hankalin ka akan wannan maganar.


Ko ƙishin ƙishin na cewa kayi budurwa bana ji. Ga 'yan mata nan kala kala..." Taci gaba da magana tana kallon mijinta. 


"Ni cewa nayi ma idan bashida lokacin neman wadda zai aura zan iya zaɓar masa mata. Kaga komai ai zaizo da sauƙi.” 


Dajin haka Najib ya lumshe idanunsa tare da sauƙar da wata ajiyar zuciyar da ya tabbatar mata cewa bai goyi bayan maganar ta na ƙarshe ba. 


Idan mahaifiyarshi ta yanke hukuncin haɗashi aure da wata, yaya zaiyi da batun Maryama data fara ratsa masa zuciya?


Ai bazai ma tsaya har hakan ta faru ba. Al’amarin bazai yi kyau ba. Nan yayi nazari… 


Ya kamata ya sake haɗuwa da Maryama. 


Ya kamata ya gano meye zuciyar shi take ciki…


Meye ainihin abinda zuciyar shi take ji game da ita?


Alhaji Bello dake lura da duk abinda ke wakana ya duban matarsa cikin lallaɓa. 


“Haba Bilkisu, jiya fa kinfi kowa damuwa bai tashi da wuri yayi breakfast damu ba. Abincin rana ma haka ya fice baiyi damu ba. To yau kuma gashi ya fito da wuri ya same mu amma kin ɗago da wata magana. Let him eat in peace mana." 


Najib ya ƙoƙarta ci gaba dacin abincin ba tareda ya nuna cewa ya fita ransa ba. Don da zaran ya nuna hakan, nan kuma mahaifiyar shi zata shiga wata sabuwa na rashin cin abincinsa. 


"To shikenan Abban Hasina, zan haƙura da maganar zuwa wani ɗan lokaci. Amma ba wai na hakura bane." Hajiya Bilkisu ta faɗi haka sanda take ƙoƙarin tashi daga kujerar ta. Ta dubi Najib sannan tace masa, 


"Tun jiya Hasina take son ganinka amma baka kusa. Ina faɗa maka ne saboda nasan nan bada jimawa ba ficewa zakayi.”


Da gama maganarta ta haura sama zuwa ɗakinta ba tare da ta jira yayi magana ba.


Alhaji Bello ya ɗan dubi ɗansa na wani lokaci ƙalilan a lokacinda Najib ya ɗago da kallon sa. 


"Najib, nasan yanzu zaka ce bakada lokacin maganar aure. Zaka ce you are too busy to get married. I understand, nima da haka nake kafin na haɗu da mahaifiyar ka. 


Amma tunda ta nuna maka maganan nada muhimmanci a gurinta, kayi haƙuri ka saurare ta this time around kafin ka koma Canada. Hankalinta zai fi kwanciya. Ina fatan ka gane?"


Najib ya sake dakatawa da abincin da yake ci. "Abba na gane, zanyi ƙoƙarin naga hankalin ta ya kwanta game da wannan batun.”


Mahaifinsa ya gyaɗa kai alamun yaji daɗin hakan. Ya ɗauki mug ɗinsa daya ajiye yaci gaba da shan shayinsa daya rage sauran ƙadan.


Najib ya janyo jug ɗinda ke kusan cike da juice na fresh fruits da suka sha aikin blender, ya tul tula cikin glass cup daya kai rabi ya kafa a bikinsa ya sha.