GADAR TSAUTSAYI 32
by @nusybee143
Page 32
Tafiya ta cigaba da yi a hankali, lokaci lokaci tana share hawayenta,kafin ta koma gefe ta zauna ta yi shiru tana kallon masu wucewa da komawa
Tana nan a tsugunne har dare ya soma yi sosai,ga bacci,ga gajiya,ga yunwa, abubuwa sun yi mata yawa sosai, lokaci lokaci take share hawaye
Bata san inda zata dosa ba, ballantana ta san me zata yi, tana nan a zaune ta ji magana kamar daga sama
"Baiwar Allah lafiya?me kike yi a nan wajen?"
A firgice ta ɗaga kai tana kallon mutumin da zai iya kai wa shekaru arba'in ko ma fiye,amma sai ta kasa ba shi amsa,ya sake tambayarta "baiwar Allah na ce lafiya?
Me kike yi a nan da wannan tsohon daren?"
Goge hawayenta ta yi ta ce "ni baƙuwa ce,ban san inda zan je bane,garinmu ana tashin hankali ne,an kashe mijina gashi bani da kowa"ta samu kanta da yin wannan ƙaryar
Duk da cewa ba shi da tabbas na maganarta amma ya tausaya mata sosai,ya ce "to Allah ya kawo mana ɗauki,tashi ki shiga a daidaita sahuna gata nan,sai na kai ki gidana, zamanki a wajen nan a matsayinki na mace hatsari ne"Shaheeda ta rissina tana godiya,ta shiga a daidaita sahun tashi,ya tayar suka bar wajen
Wata ƴar ƙaramar unguwa ta masu ƙaramin ƙarfi ya nufa da ita,a ƙofar wani tsohon gida suka yi parking, Shaheeda ta fara bin gidan da kallo,a ranta tana tsarkake Ubangiji,dama akwai irin waɗannan mutanen masu rayuwa a irin wannan gidan a duniya?
Bata sake tsinkewa da lamarin Ubangiji ba sai da ta shiga gidan,ɗakuna ne a jere,kusan guda shida,amma da alamu wannan mutumin ba shi kaɗai bane a gidan,don ta ga wasu maza guda biyu, ɗaya ma suna tare da matarsa,da alamu su ma mazauna gidan ne
Wasu ɗakuna ya nufa a cikin ɗakunan gidan,ya shiga wani da sallama
Matar da take zaune tana gyarawa wasu yara shimfiɗa ta ɗago tana kallonsu tana faɗin"sannu da zuwa!
Ka daw....."maganar ta maƙale a bakinta ganin Shaheeda a bayansa, wadda ta yi tsuru-tsuru kamar a ce mata 'kyat'ta zura da gudu
Mutumin bai tankawa matar ba,ya dubi Shaheeda da kulawa ya ce mata "ƴan mata shigo,ga waje ki zauna "babu musu Shaheeda ta shigo cikin ɗakin, sannan ta zube a gaban matar tana gaishe ta
A yatsine matar take kallonta da cikin jikinta, kafin ta amsa da" lafiya "Sannan ta miƙe ba tare da ta sake kallon sashen da suke ita da mijin ba ta fice daga ɗakin,shima kuma babu ɓata lokaci ya bi ta, Shaheeda da take zaune ta bi su da kallo duk jikinta a sanyaye
Su kuwa suna shiga ɗaya ɗakin da ya zama na kwanansu ta dubi mijinta da ya shigo ta ce"baban faruku wacece wannan yarinyar da kuka zo tare?a ina take?"
Baban faruku ya samu waje ya zauna,ya dube ta ya ce"haba Rabi, menene abin ɗaga hankali ne? zauna sai na gaya miki ko?"babu musu rabi ta zauna,baban faruku ya gaya mata komai da Shaheeda ta gaya masa
Shiru ta yi na ɗan lokaci tana kallonsa, kafin ta ce"to yanzu da ka kawo ta ya kake ganin za'a yi da ita?
Ka san dai ɗakunan da ka kama mana guda biyu ne,kuma ɗaya nawa ɗaya na yarana,don haka a bayyane yake bata da wajen kwanciya a gidan nan,sai kuma maganar matsayi,a matsayin wa ka kawo ta gidan nan?"
Shiru baban faruku ya yi na wasu mintuna kafin ya ce"ai ba zama zata yi mai tsawo ba,na ga tana buƙatar neman taimako ne,ga dare, na san za ki taimaka kasancewarta mace shiyasa na kawo ta,kuma ba a matsayin kowa ba sai na baiwar Allah musulma mai buƙatar neman taimako, shine za mu taimaka mata kawai"
Rabi ta haɗe rai ta ce "to ta zauna,amma ba daɗewa zata yi ba, sannan kuma ban yarda da mu'amala tsakaninku ba,kuma na ɗan lokaci ne zata tafi,ni ba don cikin jikinta ba ma da sati guda zan ɗebar mata ko ta tafi ko na kore ta wallahi "
Murmushi ya yi ya ce"to babu matsala in sha Allah,amma yanzu ki ba ta abinci idan akwai"Rabi bata kalle shi ba ta ce"babu,sai dai ko naka"kai tsaye ya ce"a ba ta nawa babu matsala,kin ga ta fi ni buƙata saboda abin da take ɗauke da shi"rabi ta kalle shi tana taɓe baki sannan ta miƙe tsaye ta ɗauki kwanon dambun da ta yi ta fice don kai wa Shaheeda
Shaheeda tana zaune ta takure kamar mai jin sanyi, zuciyarta cike da fargaba,sam bata ga laifin matar nan ba idan ma korarta ta yi ko ta hantare ta,ita da mahaifinta ma ya kore ta,ya nuna baya buƙatarta?
Ta goge hawayenta tana gyara ƙafarta da ta yi tsami, kafin ta yi wani yunƙuri sai ga Rabi ta shigo tana sallama ciki-ciki
Shaheeda ta amsa murya a sanyaye, rabi ta kalle ta a fizge,sai da gabanta ya faɗi,don kyan yarinyar ya ba ta tsoro, a ranta ta ji dole ma ta saita mata hanya nan ba da jumawa ba,kar mijinta ya sauya tunani akanta
A sanyaye Shaheeda ta sake gaisheta,ta amsa da "lafiya,ga abinci nan ki ci,idan kin gama ci ga buta can sai ki yi alwala ki yi sallah,ya sunanki ne ma?"
Shaheeda ta yi shiru na ƴan seconds, kafin ta ce "sunana Fatima"
"To ya yi kyau Fatima"ta jefa mata wani tsohon labule duk ya yi ƙura,ta ce"kyau shimfiɗa a can wajen,daga bakin ƙofa, saboda kin ga babu waje"Shaheeda ta ɗauka tana faɗin "to na gode aunty"rabi ta kalle ta ta taɓe baki sannan ta fice daga ɗakin
Alwala Shaheeda ta ɗauro,ta zo ta tayar da sallah,ta rama magriba da isha'i da bata yi ba, sannan ta zauna ta fara cusa abincin,su da daɗin da dambun ya yi mata,abinka da mai ciki,amma ta kasa cin shi sosai, ragowar sai rufe shi ta yi ta koma ta kwanta a takure,bayan ta shimfiɗa labulen da aka ba ta, saboda tsananin gajiya da nauyin jiki irin na mai ciki cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita
A ɓangaren Ummeey kuwa,da ƙyar ta danne kukan da take yi ya shiga sashenta,kanta har wani jiri yake yi ta lalubo wayarta,babu ɓata lokaci ta dokawa Hajiya Jamila kira
Bugu biyu ta ɗaga da sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana faɗin"Hajiya Jamila kina nan?"
Hajiya Jamila ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazartar muryar Hajiya Zainab, kafin ta ce"me yake faruwa ne Hajiya Zainab?
Ko dai wannan matsalar ce?"
Kuka ya ƙwacewa Hajiya Zainab, cikin karayar zuciya ta ce"ta faru ta ƙare ma Jamila, Alhaji ya kori Shaheeda,ya ce ya cire ta daga cikin ƴaƴansa"
Hajiya Jamila ta ji dukan maganar,ta san dole abin zai yi wa Hajiya Zainab ciwo, ƴarta ɗaya, Allah ya jarabce su akanta,amma mahaifinta maimakon ya zaɓi ya gyara ya gwammace ya nunawa duniya cewa shi yana da wasu yaran ko da ace bata tare da shi,ya manta komai daren daɗewa matsayinta na ƴa a wajensa ba zai taɓa canjawa ba
Amma sai ta dake ta ce "to Hajiya Zainab ki kwantar da hankalinki,ki turo ta nan,ko da babu driver,baban nata yana cikin ɓacin rai ne,amma yana hucewa shikenan in sha Allah,komai zai daidaita ki kwantar da hankalinki "
Hajiya Zainab ta girgiza kai ta ce"ba za ki gane bane Hajiya, tunda ya nuna ba zai amshe ta ba to ta zauna, Alhaji yana da kafiya musamman akan ra'ayinsa
Kuma Allah ya gani tun sanda aka ce za'a kai ta makaranta ban so ba, saboda Shaheeda yarinya ce ƙarama,amma mahaifinta ya dage,ya ce ya ji ya gani,a ƙarshe gashi nan ni nake girbar shukar, ƴata ce ta lalace shi babu abinda ya yi masa zafi tunda yana da wasu yaran,Ni gani an bar ni a cikin tashin hankali da baƙin ciki,ko da wannan cikin ai ni nake ganin damuwa"
Hajiya Jamila ta girgiza kai ta ce"Hajiya bawa bai isa ya kauce ƙaddarar da Allah ya rubuta masa ba,ko ta wanne hali,da ni da ke da kowa ma mun san wacece Shaheeda mun san abin da zata iya da wanda ba zata iya ba,mun yi mata kyakykyawan zato, abin da ya faru ƙaddara ne da jarrabawa,mu san Shaheeda ba maza ta bi ba, aure ta yi, duk da cewa bata yi auren akan yadda ya dace ba,amma dai ba zina ta yi ba,ɗanta ɗan Sunnah ne,yaudarar da aka yi mata bata isa ta saka ɗanta ya zama shege ba, ki kwantar da hankalinki hajiya
Yanzu dai ki turo ta,ko da ma a ce Alhajin naku bai yarda ta koma gidansa ba ni zan riƙe ta ni da nawa Alhajin,kar ki damu Hajiya "Hajiya Zainab ta yi murmushi tana faɗin"na gode, sai,in sha Allah yanzu zan turo ta, sai kin ji ni Hajiya "suka yi sallama ran kowa a cikinsu babu daɗi
Tana sauke wayar Muyassar ya yi sallama, Ummeey ta ɗaga kai tana kallonshi ta amsa da murmushi a fuskarta,ya ƙaraso cikin falon yana kalle-kallen ta inda zai gano Shaheeda
Cikin girmamawa yadda ya saba ya gaida Ummeey, Ummeey ta amsa cikin fara'a tana faɗin"ango ya shirye-shirye?"Muyassar ya ce"alhamdulillah Ummeey
Ina Shaheedan?na ji abin da ya faru da ita,ban ji daɗin abin da ya faru ba,amma babu komai, za'a san yadda za'a yi kafin a samu Abban ya huce in sha Allah
Ki yi haƙuri Ummeey "
Ummeey ta sauke numfashi ta ce"babu komai Allah ya kyauta kawai
Shaheeda ai na bar ta a falon Alhaji,ban sani ba ko ta taho "
"Wai falon Abba?"ya faɗa yana kallonta da yanayin mamaki akan fuskarsa
Bata damu ba ta ce"eh can na baro ta, wataƙila ta shigo yanzu
Na yi magana da ƙawata ma,zan tura ta can gidanta kafin abubuwa su lafa a san yadda za'a yi"
Muyassar yana kallonta da yanayin mamaki da damuwa ya ce"amma kuma yanzu na baro wajen Abba,amma kamar bata can"
"Ba ta can?"ta faɗa a ɗan tsorace,bata jira amsarshi ba ta miƙe da sauri ta fice daga sashen ta nufi sashen Abba
Sai da ta je ta samu tabbacin cewa tun da ta fita Shaheeda ta fita, a lokacin kasa nuna kararta ta yi,a gigice ta dubi driver tana faɗin"don Allah kai ni na duba ƴata,kar ta faɗa wani halin,don Allah mu bi hanya yanzu......."
"Zainab!"ta ji muryar Abba a fusace
Juyawa ta yi a gigice tana kallonsa,sam bata kula da jama'ar gidan da suka taru suna kallonta ba, Abba ya dube ta fuska a ɗaure ya ce"ban hana ki nemo ƴarki ba ki riƙe abarki,amma ki zaɓa ko aurenki ko ƴarki,daga sanda kika fita daga gidan nan da niyyar kin tafi neman ƴarki daga lokacin ki saka a ranki kin datse igiyar aurenki da kanki,zaɓi ya rage naki "yana kai wa nan ya kewaye ta ya bar wajen
Hajiya Ruƙayya da abin yake yi mata daɗi ta dubi Ummeey da take daskare a wajen ta ce"Allah ya kyauta dai!
Dama bahaushe yana cewa rana dubu ta ɓarawo ɗaya ta mai kaya,banda haka da ta yaya za mu san masu zuga yara suna lalacewa a gidan nan?
Allah ya kyauta"Hajiya Atika ta taɓe baki tana faɗin "Ameen dai"suka fara watsewa daga wajen suna kama gabansu
Da ƙyar Ummeey ta ja ƙafarta ta koma ɗakinta,tana zuwa ta zube a tsakar dakin tana mayar da numfashi, ƙasa-ƙasa ta samu zarafin ambaton"Inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!!!"
Shikenan ta sani a yanzu,ta rasa ƴarta,komai ya ƙare mata, Allah ya kawo mata dauki
Tana jin wayarta tana ringing amma ta kasa ɗagawa, saboda tashin hankalib da take ciki,duk da cewa ta san Hajiya Jamila ce ya kira akan batun Shaheeda
💫
Shaheeda kuwa saboda tsabar gajiya tunda ta kwanta bacci bata iya tashi ba sai da washegari Rabi ta shiga ɗakin tana tayar da yaranta don su yi Sallah,ta tashi da ƙyar,ta ɗauki buta don ta je ta yi fitsarin da ya matse ta a mara
Bayan ta yi Sallah tana zaune ta yi zuru,yaran da ɗaiɗai da ɗaiɗai suke zuwa suna gaishe ta,ta amsa tana murmushin yaƙe
Ɗaya daga cikin yaran, wanda ta ji ana kira da faruku,da alamu shine babban shine ya kawo mata abincin karyawa,kunun gero ne da yar tsala,shima wannan abincin ya shiga ranta sosai,don haka ta ci da yawa,dama gashi da yunwa ta tashi, kamar ba ta ci abinci ba
Wajen ƙarfe bakwai da rabi yaran suka fice zuwa makaranta, Shaheeda ta kwanta ta lumshe idanu kawai tana tunanin yadda rayuwa take wujijjiga ta
Baban faruku ne ya yi sallama ya shigo ɗakin,ta tashi zaune tana amsawa,ya shigo sosai ya samu waje ya zauna, Shaheeda ta rissina ta gaishe shi
Ya amsa da sakin fuska, sannan ya dube ta da kulawa ya ce "Ni zan fita aiki,ga wannan"ya miƙa mata ɗari biyar,ya ce"na san ba za ki rasa abin da kike sha'awa ba,sai ki siya ki ci ko?"Shaheeda ta karɓa tana rissinawa, cikin sanyin murya ta ce"na gode Allah ya saka da alkhairi"baban faruku ya amsa da Ameen sannan ya fice daga ɗakin
Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana,a lokacin bacci ya fizge ta, cikin baccin ta rinƙa jiyo hirar matan gidan
"Umman faruku wai wacece wannan matar da na ga sun zo tare da baban faruku jiya?baƙuwa kika yi ne?"umman faruku ta taɓe baki ta ce "wacece ni?
Mai gidan dai,nima tare na gansu ai"
"Mai gida kuma umman faruku?
Ƙanwarshi ko yar ɗan'uwanshi?"
"Mhm!ke ma dai kya faɗa maman jidda, wallahi babu ɗaya,a hanya ya ce ya tsinto ta"
"Kan uban can!sannu umman faruku!
Wallahi kaf duniya babu wanda ya isa ya yi min haka, tabɗijam!"a cewar ɗaya matar
Maman jidda ta ce "maman Ahmad ni ba wannan nake tunani ba, wallahi na fi zargin ƙarya take yi,karuwa ce kawai,ko wadda idanun ba su gama buɗe idanu a yawon dandi ba,mu je mu tuhume ta ta rantse abin da ta faɗa gaskiya ne,idan bata rantse ba wallahi mu fatattake ta, saboda tsaf sai ta lalata mana mazaje wallahi,ba zai yiwu muna zaman lafiya da mazanmu ba daga taimako a ɗauko mana masifa
Ni bari ma ku gani, wallahi ba zan yi sanya ba"ta miƙe ta nufi ɗakin da Shaheeda take ciki da Adams, don har wani zafi take ji a ƙirjinta,ji take yi ma kamar ta ga mijinta tare da wata macen,ko ma ya ce zai aure ta, dama ta fi sauran matan gidan zafin kishi
#Nusy_bee