KAIFI ƊAYA

03

by @ummishatu1111




3



***Mamaki, fargaba da kuma zulumi duk shinfide kan fuskar Afeef yake kallon Aliyu zuciyarshi na lugude kamar zata faso kirjinsa ta fito, wai wannan wanne irin kwaɗo ne? Da wanne suna zai iya kiran wannan kwamacalar wacce Aliyu yazo da ita,

"ka fahimceni Afeef? Wani abun fa dole sai naka ne zai iya yi maka..... Nasan zaka yimin wannan alfarmar ko ban baka ko sisi ba..... Ka fadi duk abinda kake son inyi maka a duniyar nan, wallahi zanyi maka idan har zaka amshi wannan bukatar tawa...."

"wai dan Allah kai waye ya baka wannan shawarar Aliyu? Me yasa sai wannan ɗan jaririn? Afeef nawa yake da za ayi wannan abin dashi...."

Juyawa yayi ya kalli anty Mimi wacce ke magana cikin zafin rai, tunda aka fara maganar dama bata saka baki ba sai yanzu,

" Anty Mimi ina ganin girman ki amma kar ki sake kirana da jariri..... " shima ya fada cikin zafin rai, babu kalmar da tafi bakanta masa rai ta hassala shi irin jaririn da ta kira shi da shi a iya saninshi ai shi yanzu yafi karfin a kirashi da jariri tunda jariri na can bayan tsohuwar sa,kamar dama jira take ya tanka ta rufe shi da faɗa ta fara balbala masa masifa kamar zata doke shi, 

"kai wanene idan ba jariri ba awurina, kana da wani girman ne wanda yafi wannan? Yaushe ma kazo duniyar da har ka girma? Tatsitsi da kai....." 

Murmushi yayi mai cike da takaici da kuma baƙin ciki, 

"yaya haidar ba zan iya wannan abun da kake son inyi maka ba..... Sai anjima" daga haka ya tashi ya fice ransa a ɓace zuciyarsa na faman tafarfasa wallahi ba dan yana ganin darajar anty Mimi ba idan wata ce ba ita ba bata isa ta faɗa masa haka ya ƙyaleta ba da sai ya dauki matakin da gaba daya baza su ji dadinsa ba, ransa a mutukar ɓace ya shiga motar sa ya fita daga cikin harabar asibitin ya nufi wurin Irfan. 

Bayan fitar Afeef Aliyu kallon Mimi yayi cikin damuwa da fuskar lallashi yace, 

"My love..... Fushi yanzu da zafin rai duk ba naki bane, dole sai kinyi hakuri kin dauke kai sannan zamu samu abinda muke so daga wurin yaron nan, idan muka ce zamu bishi ta zafin kai to bukatar mu ba zata taɓa biya ba...." 

Dafe kanta tayi cike da damuwa idanuwan ta a lumshe tace, 

" ni dai haka kawai banji hankalina ya kwanta da Afeef ba cikin wannan batun, me yasa ka dage lallai sai shi? Why? "

" Afeef cousin dinmu ne daga ni har ke dan haka na san zai yi wahala yaci amanarmu gaba daya, sannan na san yana ganin girman ki dan haka da wuya yace zai cimin amana ta hanyar raɓarki sabanin idan wani ne a waje na san zai yi wahala bai yi yunƙura aikata hakan ba ni kuma hakanne bana so, bana fatan wani namiji ya shigar min gona ta.... Wannan shine reason dina na son ayi sabgar nan da Afeef... Ki daure kiyi hakuri har mu shawo kansa ya amince, idan bukatar mu ta biya shikenan... "

" it's fine.... " shine kawai abinda tace ta kifa kanta kan teburin dake gabanta dan ta rasa me yake yi mata daɗi kuma, sallama Aliyu yayi mata ya fita kuma yana zuwa motar shi ya fara kiran Afeef bayan ya tura masa sako, 

Afeef na cike da damuwa ya ƙarasa gidan Hajiya inda Irfan ke can yana jiransa, gashi yana dauke da damuwa amma kuma babu halin faɗa ko sanar da wani, duk yadda yake biye hajiya suyi ta haurawa amma yau bai kula ta ba kuma yana zuwa ta fara caccakeshi da masifa,

"sarkin zurfin ciki.... Na jima banga mugun mutum irinka ba lele, kowa yana bude baki yayi sallama amma kai sai dai kawai in ganka ka faɗo min cikin ɗaki sai kace kaine ka gina min dakin..... Wannan isar taka da ikon nan da kake yi a gidan nan ya isa haka, ko iyayen ku idan sun zo shigowa sai sun yi sallama da budaddiyar murya amma kai da yake isasshe ne sai ka gadama..... "

" wallahi nayi sallama kawai dai baki ji bane tunda yanzu ba wani ji kike yi ba sosai.... " ya fada cikin nuna alamun ƙosawa da maganar,

" to yanzu da naka kunnen nake ji da zaka ce bana ji..... Nace naka kunnen ka bani aro nake ji yanzu da kake ikirarin bana ji? "

" ohh Allah..... Ni dai yau na shiga uku, dan Allah hajiya Allah ya baki hakuri naji banyi sallama ba shikenan...." ya fada yana dafe kansa wanda yaji yana shirin fara yi masa ciwo, shigowar Irfan ta sa hajiya mayar da kallonta kansa shima ta fara balbale shi da fada,

" kai ba tun jiya nace akira min kai ba shine ka ki zuwa sai yanzu da wannan marar kunyar yazo sannan zaku haɗo kai kuzo...."

Zama Irfan yayi kusa da Afeef ya kyale hajiya bai tanka ba hakan ya sake tunzura ta tace,

"marassa kunya.... Ku tashi ku fice min daga cikin ɗaki ko inci muku mutunci yanzun nan...."

Afeef zamewa yayi ya kwanta kan kujera yana harararta batare da yayi magana ba dan ransa dama a ɓace yake kuma yana cikin damuwar wannan matsalar da yaya Aliyu ke kokarin lallai sai ya saka shi aciki shima ta shafe shi,

Yana kwance yana jinsu sai fafatawa suke yi ita da Irfan ahaka wayar shi ta fara kara ganin yaya Aliyu ne sai yaki dauka shikuma cigaba yayi da kiransa babu kakkautawa, ɗan kallonsa Irfan ya juya yayi sannan yace,

"your phone is ringing fa..... Afeef..... Are you sleeping?"

"wallahi bana jin dadi ne Irfan.... Kaina ma ciwo yake yi"

"sannu.. Allah ya sawwake"

Ita kuwa hajiya karkace kai tayi tana kallonsa zuwa can kuma tace,

"yi hakuri lele ai ban san baka da lafiya ba..... Na zata iya shegen naka ne ya tashi"

Lumshe idanuwansa kawai yayi bai ce komai ba, kwata kwata ya rasa me yake yi masa daɗi shi dai kawai yana jinsa gashi nan gashi nan dai shi ba mai lafiya ba shi ba marar lafiya ba, bayan hajiya ta fita Irfan ya dafa shi yace,

"Afeef wai me yake damunka ne? Naga kamar fa kana cikin damuwa, ko kai da mommy ne?"

Girgiza kai yayi dan baya jin zai iya sanar da wani wannan damuwar tashi,

"kaina ke ciwo Irfan..."

"bari na duba bedroom din anty Mimi na san is hardly a rasa paracetamol.."

"ok"

Ganin Irfan ya tashi itama hajiyan ta tashi yasa shi daukar wayar yaya Aliyu da har yanzu bai hakura ba wurin miss calls 10  yayi masa,

"Afeef.... Haba ƙanina... Nine fa yaya Aliyu yayanka, why are you like this? Yarda ce fa tasa nake son baka  amanar Mimi.....  Na san kai kadai ne zaka iya cika min alkawari"

"yaya Aliyu am very sorry...... Gaskiya bazan iya karbar wannan amanar ba, beside ma ni ban ko fara tunanin yin aure ba a yanzu"

"A'a Afeef..... Ka dai yi tunani dan yanzu daga ni har Mimi da kai muka dogara kaine kadai gatanmu a yanzu dan kaine zaka fitar damu daga cikin halin da muke ciki na damuwa da tashin hankali..... Dukanmu muna bukatar taimakonka dan Allah.... Please"

"Yaya haidar gaskiya bazan iya yi muku wannan taimakon ba..."

"kafi son muje mu samo bare wanda zai tona mana asiri Afeef? Kaifa dan uwanmu ne...."

"dan Allah yaya Aliyu kayi hakuri mu bar maganar nan dan wallahi kaina ba zai iya dauka ba tayi masa girma"

"ka dai zauna kayi tunani Afeef..."

Ganin Irfan na tahowa yasa Afeef katse wayar ya ajiyeta kan kirjinsa tare da lumshe idanuwansa, zama Irfan yayi yana mika masa paracetamol din sannan cikin son jin karin bayani yace,

"naji kamar kana waya, kai da waye?"

"babu kowa... Ba waya nake yiba"

Shuru Irfan yayi amma shi dai ya san kunnen sa ya jiyo masa kamar Afeef din yana yin waya sai dai amma tunda yace ba haka bane dole ya barshi a haka din.

Bayan azahar yabar family house kamar yadda suke kiran gidan ya nufi gidansu zuciyarsa cike da tunani iri iri kuma daban daban, part dinshi kawai ya shiga ya kwanta bai ko leka side din mommy ba sai ita mommy dince ta shiga wurinshi, kwance ta iskeshi harda su lulluba kamar wani mai yin bacci,

"Afeef baka da lafiya ne?"

"mommy am fine kawai ina hutawa ne...."

"ok to shikenan dama nace bari inzo in duba ka..." daga haka mommy din ta juya ta fita taja masa ƙofa, kashe wayar sa yayi saboda damunsa da yaya Aliyu keta faman yi da kira, bai kunna wayar tashi ba sai bayan magrib nan ya kula da sakon da Aliyun ya turo masa tun da safe bayan ya baro office din anty Mimi, kudine har 5m, dafe kansa yayi wanda yaji ya sara masa,

"shi kuma wannan kudin duk na menene?" ya tambayi kansa hankalinsa na sake dugunzuma, gaskiya Aliyu ya takurawa rayuwarsa haka kuma ya na neman hana shi sukuni, yayin da shi kuma Aliyun ke can yana ji acikin ransa da kuma jikinsa cewa Afeef din shine kadai zai iya yi masa abinda ya dace dan Mimi bata wasa dashi shima kuma baida lokacinta dan haka ya san baza asamu matsala ba komai zai tafi yadda ya dace kuma ya shirya ba tare da wata tangarda ba.

Tsawon kwanaki biyu shi dai Afeef ya kasa gane kansa ma dan ya rasa yaya zai yi da matsalar yaya Aliyu da anty Mimi, kullum cikin takura masa da kira Aliyun yake har hakan yasa yaki zuwa family house dan bama ya son su hadu acan, kwana yake yana sake sake cikin ransa dan ya rasa a inda mafita take. Yau ya jima yana bacci kamar yadda ya saba dan kwana biyu baya samun bacci sosai, sai after 1 sannan ya tashi, wayar shi ya dauka ya kunna yana kunnawa massages din Aliyu suka yi ta shigowa duk na roko ne da magiyar ya taimaka musu ya ceto rayuwar su shi da Mimi saboda idan bai taimake su ba komai zai iya faruwa, bai kai ga karanta massages dinba gaba daya kiran Aliyu ya shigo, dauka yayi a hankali yace,

"hello yaya haidar.....nima yanzu nake cewa zan kiraka fa sai gashi ka kirani"

"A'a Afeef wannan ba gaskiya bane.... Kwana nawa wayarka a kashe"

Murmushi yayi tare da cewa "ehh wallahi yaya..... Dama zan kira ne in fada maka na amince sannan dan Allah wannan kudin da ka turo min zan dawo maka dashi ai ba sai ka biyani ba akan wannan..... We are one family...."

"No Afeef ka barshi ka dauka kawai wata yar karamar kyauta ce daga yaya zuwa kaninsa...."

"A'a yaya wallahi ba zan karɓa ba indai har kana son inyi maka abinda kake bukata.... Bana son inji araina kudi ka biyani dan yi maka wani abu wanda zan iya yi maka koda baka biyani ba saboda karfin zumuncin dake tsakaninmu...."

"to shikenan Afeef na gode Allah ya bar zumunci, yanzu ya za ayi?"

"babu matsala yaya komai zai tafi daidai insha Allah..... But ka jawa anty Mimi kunne Allah karta yarda ta sake ce min jariri...." dariya Aliyu yayi yace,

"insha Allah, gata nan ma tana jinka ai ina office dinta...."

Katse wayar yayi sannan ya tashi ya fita zuwa part din mommy.

Kallon Mimi Aliyu yayi bayan sun gama waya da Afeef, ajiyar zuciya ya sauke jin Afeef din ya amince da kyar,

"ban tsammaci yaron nan zai amince ba.... Kawai na yi tunanin sai dai mu nemi wani..."

Shuru yaji tayi bata amsa ba saboda bata san me zata ce ba ko me zata kira wannan abun ba, ance dai auren kisan wuta to amma a rasa da wa zasu yi auren kisan wuta sai da Afeef?

" My love baki ce komai ba.... You didn't say anything.... "


" to wai me zance Aliyu? Yanzu a rasa da wanda zamuyi auren kisan wuta sai da Afeef?"

"calm down my love.... Shifa RUWAN KASHE GOBARA ba sai mai kyau ba.... Bukatar mu in dai zata biya bamu da damuwar koma waye shi.... Kiyi hakuri..... Kar wannan ya dameki...."

"Ai duk Kaine ka janyo...... Ka rinka abu kamar wani mai shaye shaye ko tabin hankali yanzu ga abinda ka janyo mana nan.... Zaka sa inyi auren kisan wuta da kanin bayana...." daga haka ta dauki wasu files ta fita ta barshi cikin office din, babu abinda yake bata mata rai irin yanda idan ta tuna cewa Afeef ne zai zame mata mijin auren kisan wuta wannan wacce irin lalacewa ce, sai dai amma idan kuma ta tuna da cewa auren na ɗan wucin gadi ne zasu koma su hade da yaya Aliyu sai ta ɗan ji sanyi cikin ranta dan tana mutukar sonsa da kaunarsa haka kuma tana ta faman missing dinshi kamar yadda kullum shima yake yi mata korafin cikin missing dinta yake, to da su cigaba da wannan zaman lalurar wanda shaidan zai iya cin nasara a kansu gara asamu a ganganɗa da Afeef din har bukata ta biya.......





_*Ummi Shatu*_👌🏻