KAIFI ƊAYA

04

by @ummishatu1111

KAIFI ƊAYA....


NA
UMMI A'ISHA


4


***Cike da kasala da damuwar da yake ta boyewa cikin ranshi ya shiga part din mommy, babu kowa cikin part din kamar yadda gidan ya saba kasancewa dan ita Manal ta tafi makaranta ita kuma mommy ta fita aikinta kamar yadda ta saba, table a shirye shiyasa kawai zama yayi ya fara zuba breakfast din da yaga mommy ta ajiye masa, yana cin abincin yana tunani cikin ransa yanzu ta ina ya dace ya fara sannan wa ya kamata ya tunkara da wannan maganar ta yana son a daura musu aure da anty Mimi?

Har ya gama breakfast din bai tsayar da magana guda daya a cikin ransa ba kawai ya san ayau dole sai ya magantu ko ayi ko a ƙi yi, fata yaji yana yi acikin ransa ma Allah yasa iyayen nasu suki amincewa inyaso shikenan kowa ma ya huta sannan shi yaya haidar din ba zai zarge shi da yaƙi yi masa taimakonba kamar yadda yake ta fadar taimako taimako,

Part dinsa ya koma ya samu wuri ya zauna bakin gadonsa yana bin dukkan cikin bedroom din nasa da kallo, katafaren gado ne babba kirar Turkiyya fari tas komai tsaf tsaf kuma fes fes babu wasu tarukuce masu yawa aciki dan daga gadon sai wardrobe da mirror sai bedside drawers  sai shoe rack shikenan komai a kammale kuma a tsare, kowanne lungu da saƙo na cikin ɗakin ƙamshi ne mai daɗi ke tashi na turaren oad,

Gani yayi zaman shurun ba zai kai shi ba shiyasa kawai ya tashi ya nufi cikin toilet ya sakarwa kanshi shower, bai wani jima cikin bathroom dinba ya fito daure da towel, cikin kankanin lokaci ya shirya sannan yayi salatul duha raka'a biyu kafin ya dauki key din motar shi ya fita, yana driving yana tunanin ta inda ya dace ya bullowa wannan lamari da haka har ya isa family house, bai shiga ko ina ba sai wurin Hajiya tana zaune cikin bedroom dinta tana gurza goro jikin wata yar karamar greater ta roba, zama yayi kusa da ita,

"Hajiya kaka wai dama har yanzu baki hakura da cin wannan goron bane....."

"to sarkin iyayi da sa ido..... Ban daina ba sai kuma yaya?"

Dariya yayi ya girgiza kansa yace 'babu komai..... Allah ya baki hakuri.... "

" amin..... Ɗan neman sababi "

" to ai maganar ta wuce nace kiyi hakuri...... Ashe hajiya auren anty Mimi ya mutu?"

Tamkar ya sosa mata inda yake yi mata ciwo yaji tayi kwafa kafin cikin takaici tace,

" Aurenta ya mutu mana Mai sunan malam, ai wannan shashashan yayan naku baida ta ido sam..... Ya kasa riketa kullum cikin saki har sai da igiyar auren ta kare kowa ma ya huta...... Yar uwarka cikin ku ɗaya amma ka gagara riketa..... Wallahi takaicin mutuwar auren nan da nake ji mai sunan malam takaicin ya isa.... Tsakanina da Aliyu sai dai ince Allah ya isa... "

" subhanallahi Haba hajiya menene kuma abin yi masa Allah ya isa? Dan Allah kiyi hakuri ki cire bacin ran daga cikin zuciyarki.... Ai shi aure rai gareshi fa, ki dauka kawai dama zaman auren nasu ya kare Kinga dole a rabu idan ma saki bai raba ba sai ki ga wani aciki ya mutu... To Kinga da mutuwar ai gara ace auren ne ya mutu ko..... "

" Hakane lele..... Ai sakarai ne wannan yayan naku... "

" a dai yi hakuri Hajjaju..... Ni yanzu wata magana na zo muyi dake ta sirri idan har kin amince... "

" ina jinka ɗan lele na... "

Tankwashe kafafuwansa yayi ya sake gyara zamansa a gabanta kamar mai shirin daukar karatu,


" cewa nayi tunda auren anty Mimi ya mutu Hajiya.... Ni ina son zan aure ta "

Fasa hambada goron da yake hannunta zuwa bakin ta tayi ta tsaya tana kallonsa bayan ta gyara zaman gilashin ta sosai,

"mai sunan malam..... Kai ma ka fara irin wannan shaye shayen na zamani ko?"

Girgiza kai yayi yana kokarin danne dariyar sa,

"me kuma ya kawo maganar shaye shaye Hajjaju na?"

"to idan ba shaye shaye kake yiba Afeef ina kai ina auren Mimi?"

"saboda me kika ce haka? Ke ya dace ince ko kin fara gigine?"

"Mimi sa'ar ka ce? Shekaru nawa ta baka? Dan raini ko me?"

"Hajiya waye yace dole sai wadda kafi a shekaru zaka aura? Sunnah ce fa mai karfi auren wadda ta fika kuma wadda ta taɓa aure, annabi ma ai haka yayi shiyasa nima nake son yin koyi da shi, so nake in yi sunnah kan sunnah.... Sai dai ko idan bakin ciki zaki yimin kawai "

Shuru Hajiya kaka tayi kamar me yin tunani yayinda shi kuma ya zuba mata ido yana kallonta,

" Allah mai iko..... Ka tabbata abinda ka fada haka ne mai sunan malam? Bafa na so sai daga baya kazo ka mayar dani sakarkara... "

" wallahi Allah da gaske nake indai za a aura min anty Mimi ko yau ɗinnan a daura min auren am ready......"

"wallahi idan daga baya ka sake dawowa kace zaka canja zance bazan saurareka ba Afeef..."

"na yarda wallahi....."

"shikenan...... Naji kuma na gamsu sannan ka kawo kukanka inda za a share maka hawaye...... Kana da ni ai sai wadda kake so zaka aura koda ace akwai wani bare ma babu wani din duk taki bazawaran korarsu take ashe rabon sha lele na ce...."

Dariya shi dai yayi ya karbi goron nata yaci gaba da gurza mata, sallamar Irfan tasa gaba daya suka mayar da hankalinsu kanshi shigowa yayi yana murmushi kafin yace,

" soyayya ake sha ne hajiya kaka da mai gidanta.... "

Dariya Afeef yayi ya kalleshi  yace,

"ka san dai fada yafi yawa cikin wannan soyayyar...."

"ai tsohuwar nan tana abinda take so wallahi..... Haka kawai sassafe ina bacci tasa Abba yaje ya taso ni wai sai naje har gidan anty Batool dake karshen gari na kai mata abu....."

Dariya Afeef ya fara yi sannan ya kalli hajiya yace "gaskiya ki daina tashin sa idan yana bacci..... Kaima ka dawo gidan daddy kawai bacci a gidan daddy har azahar ake kaiwa"

"kuma fa ka kawo shawara mutumina..." Irfan ya fada yana harararta, 

Ita dai tana jinsu bata kara bi ta kan maganar tasu ba tayi iska dasu kamar bata ji,. Afeef yana so ya fadawa Irfan abinda suka tattauna da kaka amma kuma sai bai san ta ina zai fara fada masa ba dan kamar cin fuska ne ko kuma reni yace yana son zai auri yayarsa tunda ba wai zai fito fili ne ya fada masa yaya Aliyu ne ya matsa masa ba,

Tare suka wuni har magriba amma koda wasa bai fada masa ba. Suna farfajiyar gidan da misalin ƙarfe uku da rabi na yamma motar anty Mimi ta shigo gidan, gaba ɗayansu mayar da hankulansu wurin suka yi har zuwa lokacin da ta kammala parking ta fara kokarin fitowa, tashi Irfan yayi ya nufi wurinta yana yi mata sannu da zuwa shi kuma Afeef na zaune yana kallon su kuma daidai lokacin Janan ta fito daga part din hajiya ganin motar anty Mimi sai itama ta nufeta cike da farin ciki dan anty Mimi na da mutukar kirki da kulawa shiyasa kowa na familyn ke kaunarta,

"Anty Mimi barka da zuwa..."

"yawwa Janan... Ya gida?"

"Alhamdulillah" ta fada tana bude mata kofa, fitowa tayi Irfan ya karbi handbag dinta ta dan kalleshi tace,

"part din Ammi zanje, ka kai min handbag din part din Hajiya kaka...."

Tare da Janan suka nufi part din Ammi kuma sai lokacin ta dan saci kallon Afeef dake gaishe ta daidai lokacin da zasu gifta ta kusa dashi wani musulmin ƙamshi yaji lokacin da suka zo dab dashi, ita kam tun shigowar ta gidan idanuwan ta suka sauka kan ɗan tatsitsin yaron da Aliyu ya zabar musu dan zama tsanin kaiwa ga nasararsu,

"Anty mimi sannu da zuwa.... Ina yini"

"lafiya.... Afeef ya kake.." ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan tana tafiya suna gaisawa nan ya bita da kallo atamfa ce a jikinta dinkin straight gown golden color ta yafa mayafi ƙarami golden color shima ƙafarta ta saka baƙin sneaker mai kyau da tsada, shuru yayi yana tunani gami da mamaki to idan har shi yaya Aliyu yana yi mata irin wannan soyayyar da ta kai kololuwa me yasa ya kasa hakuri ya kasa jure duk wani bacin rai dan su cigaba da zaman su cikin kwanciyar hankali har sai da ya haramta zaman su, dawowar Irfan yasa shi watsi da tunanin da yake yi suka cigaba da hirarsu.

Bayan sallar magriba kamar yadda iyayensu suka saba hallara da kuma haɗuwa a falon hajiya yau ma hakance ta faru, suna tsaka da hirarsu suka ji hajiya ta ɗan yi gyaran murya sannan ta dube su gaba ɗaya tace,

"Gobe idan Allah ya kaimu bayan an idar da sallar juma'a ina so za a daurawa Mimi aure.... Ga sadaki nan nice nan zan bada gudunmawar shi...."

Baki bude cike da mamaki kowannensu dake cikin falon yake kallonta banda Afeef duk da shi dinma hukuncin hajiyan yazo mishi a bazata, daga yin maganar dazu dazun nan shine har za a daura aure a gobe gobe?,

" Hajiya aure? Ita mimi dince ta kawo mijin kenan? Yaushe suka hadu har suka daidaita? Waye shi?" duka wadannan tambayoyin Abban Aliyu ke jerowa hajiya wanda kamar ya shiga cikin zuciyoyin Abban Mimi da daddyn Afeef da faruk da kuma Aliyu dan shima Aliyun so yake yaji da wa za a daura auren dan ta yuyu wani ne daban,

" Abun ai duk na gida ne.... Mai sunan malam yace yana son Mimi zai aureta, tunda duk daga tsatso guda ɗaya suka fito shiyasa naga babu dalilin ɓata lokaci gara kawai a daura musu aure......."

Shuru dukkansu suka yi kowa da abinda yake ayyanawa cikin ransa zuwa can Daddyn Afeef ya nisa yace,

" amma Hajiya ita Mimi din an tambayeta anji ta bakinta tana son shi ko kuma akasin haka? Saboda ita yanzu ba karamar yarinya bace da har za ayi mata dole ko kuma a tirsasa ta a aura mata wanda bata so...."

"Ai ko tana so ko bata so tunda shi ya gani yana so to magana a wurina ta kare, gobe insha Allah za a daura musu aure wannan umarni na ne ba shawara ba....."

"to shikenan hajiya Allah ya nuna mana goben kuma Allah yasa albarka aciki, Allah yasa yin Allah ne, mutuwa zata raba...."

Mikewa yaya Aliyu yayi ya fita batare da ya yiwa kowa magana ba bayan ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya, kowa dake falon binsa yayi da kallo cikin zuciyoyinsu suna tunanin ta yuyu wannan hukuncin da hajiya ta yanke ne baiyi masa dadi ba sai dai shi sam ba haka bane a gareshi, wani sanyi da farin ciki yaji yana ratsa zuciyarsa dan ya san shikenan plan dinsa ya tafi yadda yake so kuma burinsa zai cika cikin kankanin lokaci,

Yana fita daga cikin part din hajiya cikin motar sa ya shiga ya zauna ya dauki wayar shi ya soma kiran layin Mimi, fitowarta daga wanka kenan daure da towel a jikinta ta dauki wayar tashi ranta a cunkushe babu dadi kuma tamkar zata saka kuka dan bacin rai,

"My love..... Albishirinki..... Hajiya ta amince da maganar auren nan, to cut the long story short gobe za a daura muku aure da Afeef...."

Wani haushi taji ya sake turnuke ta a maimakon murna ko farin ciki, sai da ta ja tsaki ciki ciki kafin yaji tace,

"soo why are you excited??"

"Love, you will come back to me soon....... That's it"

"it's fine"

"Dan Allah koda su Abba zasu tambayeki ko hajiya akan kina son shi zaki aure shi just say yes...... Please"

"ok"

Daga haka ta katse wayar tana jin ranta yana cigaba da ɓaci haka kawai ba tare da wani dalili ba.

Bayan fitar Aliyu babu wanda ya iya magana sai hajiya da ta rakashi da harara sannan cikin mita tace,

"kafi ruwa gudu shashasha kawai, da kana son nata amma shine kayi mata saki ɗai ɗai har uku.... Aure babu fashi baza a fasa dan kai ba...."

Shi dai Afeef tunda aka fara maganar ya sunkuyar da kai kirjinsa na dukan uku uku haka kawai yaji yana fargaba wacce bai san ko ta mecece ba........