Chapter 6
Wata danƙareriyar baƙar mota ce mai kyau da ɗaukar hankali ta yi parking a harabar ABS Orphanage Home, wani babban mutum ne mai cike da natsuwa da kamala, tare da wata mata dake cikin shiga ta alfarma suka fito a hankali daga cikin motar. Ganin babbar mota ta tsaya a harabar wurin, ya sa wasu daga cikin ma'aikatan gidan da suke kai kawo a harabar suka zo su na yi musu sannu da zuwa, amsa musu suka yi cikin fara'a da sakin fuska. Mutumin ya buƙaci da su yi masa jagora zuwa ofishin shugaban gidan. Duba da yanayin shigarsa, da kuma alamu da suka nuna cewar babban mutum ne, ya sa babu ɓata lokaci, ɗaya daga cikin ma'aikatan ya yi musu jagora zuwa ofishin. A bakin ƙofa suka tsaya ya shiga ya nema musu iznin shiga kafin suka shiga. Cikin sakin fuska Director ya tarbe su yana nuna musu kujeru biyu da suke gaban teburinsa. Zama suka yi, mutumin ya miƙa masa hannu suka gaisa, bayan sun gaisa ne Director ya ce "Da alama yau muna da manyan baƙi?". Ya yi maganar yana murmushi.
Nisa wa Alhajin ya yi, sannan ya ce "Da farko dai sunana Alhaji Ibrahim Musa, wannan kuma mai ɗakina ce Hajiya Maryam, ni haifaffen garin nan ne, ina zaune a gidana dake Maitama, ni babban ɗan kasuwa ne. Na yi aure kusan shekaru goma sha bakwai da suka wuce, sai dai har yanzu Allah bai azzurtamu da samun ƙaruwa ba, Allah ya jarrabi mai ɗakina da son yara, ta kan ɗakko yaran dangi ta riƙe a wurinta, sai dai tafiyar ba ta yin nisa ake fara yi mata habaici da gori a kan yaran. Hakan ya sa ta haƙura da ɗaukar ɗan kowa, to shi ne daga baya muka yanke shawarar zuwa nan mu karɓi yaron da zamu riƙe shi tamkar ɗan da muka haifa. Idan ba damuwa muna son sanin yadda tsarin karɓar yara yake da ƙa'idoji".
Director ya jinjina kai yana faɗin "Ma sha Allah, Alhaji na ji bayaninka, duk wasu tambayoyi da zamu yi maka ka bayar da amsarsu tun kafin mu tambaya. Yadda tsarin yake, idan mutum yana son karɓar yara, akwai matakai da dama da muke bi domin ganin mun ba da yaro a hannun mutane na gari. Da farko dai zamu gudanar da komai ne a rubuce bayan mun gama tantance mutanen da za su karɓi yaran tare da tabbatar da in da suke rayuwa babu wata matsala, abu na biyu muna saka hukuma a ciki domin ƙara tabbatar da tsaro. Zamu sake yin duk wani binciken da ya kamata kafin mu baku yaran".
Alhaji Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Shikenan ba damuwa, yanzu zamu iya duba yaran? Sannan idan da hali ina son duk wani binciken da za ku yi ku yi shi yanzu domin mu tafi da yaran, saboda muna cikin zumuɗi ne da son ganin yara a kusa da mu".
Director ya ce "Ok ba matsala Alhaji, sai dai ba za ku samu karɓar yaran a yau ba, ku ɗan bamu lokaci saboda binciken da zamu gudanar, da kuma cike-ciken da ya kamata a yi, in sha Allah muna kammala bincikenmu za mu sanar da ku, amma Alhaji yaran guda nawa ne kuke buƙata?".
Alhaji ya ce "To shikenan ba damuwa. Muna godiya sosai da sosai, da yaro ɗaya na so mu ɗauka, to sai matata ta nuna tana son ɗaukar ƴa mace budurwa. Domin ta maye wa yarinyar gurbin uwa da ta rasa".
"To shikenan Alhaji. Yanzu za ku iya tashi mu je ku duba yaran kafin a gama gudanar da bincike sai ku karɓi yaran, ku yi haƙuri fa muna bin komai ne cikin tsari, da kuma yadda doka ta tanada". Director ya yi maganar yana miƙewa tsaye. Alhaji ya ce "A'a babu komai, ai hakan yana da kyau, gara a dinga yin komai cikin tsari, saboda wasu mutane basu da kyau".
Daga haka suka fita domin su duba yaran, bayan sun gama duba yaran ne suka nuna wani ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu, da wata matashiyar budurwa ƴar shekaru goma sha bakwai. Director ya ce "Ma sha Allah, idan komai ya kammala za ku ji mu" godiya suka yi masa sosai, kafin suka bar gidan zuciyarsu cike da farin ciki da annashuwa.
****
Bayan kwana biyu, Ilham na zaune a falo Momy ta zo, zama ta yi kusa da ita tana ƙare mata kallo, sannan kira sunanta
"Ilham"
Ɗago da kanta ta yi ta ce "Na'am Momy"
"Jiya Daddynki ya sake yi mini zancen ɗan abokinsa Bashar, ya ce in sake yi miki maganar in ji ra'ayinki".
Shiru Ilham ta yi ba ta ce komai ba. Momy ta ce "Kin yi shiru ba ki ce komai ba?".
"Momy me kike so na ce? Ni fa na faɗa tun farko bana son sa, don haka ya yi haƙuri kawai, ina da wanda nake so".
Zuba mata ido Momy ta yi tana kallonta, cikin takaici ta ce "Amma dai Ilham ki na bani kunya wallahi, kai Allah wadaran naka ya lalace, wai ke wace irin yarinya ce mai kafiyar tsiya? Shi wanda ki ke so ɗin an ce miki yana ƙaunarki ne? Ko kuma ya damu dake ne? Amma saboda lalaci da mutuwar zuciya shi ne za ki ƙwallafa rai akansa, kina bibiyarsa yana wulaƙanta ki, kin san irin takaicin da nake kwasa akan wannan abin? Wallahi da ina da iko ko gidansu da ki ke zuwa ba za ki je ba, na san kina zuwa ne saboda shi, to bari ki ji, a wannan karon kin yi kaɗan, dole ne ki cire Sudais a ranki, tunda ba shi kaɗai ne namiji a duniya ba, ki dubi irin mazan da suke sintirin zuwa wurinki, amma ke gabaɗaya hankalinki baya kansu, kina can kin tare a wurin wanda ba ki da wani muhimmanci a wurinsa, yaron da bai dubin kowa da mutunci".
"Haba Momy, wallahi Yaya Sudais yana da kirki sosai, ke ce kawai kike ganin rashin mutuncinsa, kuma yana sona f...." "Rufe mini baki ko na make ki a wurin nan". Momy ta katse ta, kafin ta ci gaba da faɗin "Gidan uban wa yake son naki? Wannan yaron bana tunanin ko so na ƴan uwantaka yana yi miki balanta son aure. Ilham ki saurare ni da kyau, dole ki kula Saddik ɗan Alhaji Bashir, saboda shi ne wanda yake sonki, sannan zan sanar da mahaifinki kin amince da shi, wallahi Allah kika ƙaryata ni ko kika ce masa ba kya sonsa sai dai ki nemi wata uwar ba ni ba". Shiru Ilham ta yi tana magana ƙasa-ƙasa tana tura baki. Momy ta shiga masifa da kumfar baki, tana aibata Sudais.
*****
Tun da suka baro asibiti ita da Halima, tsawon kwanakin nan, ba da son ranta take zuwa makaranta ba, sai dan gudun kar Yaya Aliyu ya tarar da ita a gidan ya sa take shiryawa ta tafi tana tunzura baki.
Tana zaune a cikin aji tare da ƙawarta Jamila, Ma'u ta ce "Jamila kin san Abida ba ta da lafiya?".
"Subhanallah! Abidan? Me yake damunta?". Jamila ta tambaya.
Cikin damuwa Ma'u ta ce "Daga yin zazzaɓi jikinta ya rikice, kin san da ma ba isashiyar lafiya ce da ita ba, shi ne da aka kaita asibiti suka ce wai sai an yi mata aiki, tana fama da wani ciwo ne a cikinta".
"Na shiga uku ni Jamila, aiki kuma?".
"Eh aiki, har ma an yi mata aikin kusan kwana huɗu kenan. Sai dai Jamila haka kawai na ji jikina ya yi sanyi akan lamarin nan". Jamila ta dafa kafaɗarta ta ce "Kar ki damu in sha Allah babu abin da zai faru. Da izinin Allah za ta samu lafiya, Allah Sarki masoyi Yaya Aliyu, ki ce jiya hankalinsa a tashe yake?". Duk da Ma'u na cikin damuwa sai da ta kwashe da dariya ta ce "Iska na wahalar da mai kayan kara, Allah Jamila ki rufawa kanki asiri ki fita harkar wannan botsararren Yayan nawa, ke yanzu nan har burge ki yake yi? Mutum kullum gashi nan kamar boss ki ce shi kike so? Sannan kina ganin yana da mata har da ƴa, a haka za ki ce kina sonsa? Ke a tunaninki zai yarda kina matsayin ƙawata? Na san ba kula ki zai yi ba" Ta ƙarasa maganar tana kallonta.
Jamila ta ce "Eh na ji ɗin, a haka nake sonsa kuma in sha Allahu shi zan aura". Kallon ba ki da hankali Ma'u ta yi mata, ta ce "Ke banza ce Jamila, to ita kuma Aunty Halima ya kike so ya yi da ita?". Ta yi maganar tana sake kwashe wa da dariya.
"Ai shi mijin mace huɗu ne, kin ga Ma'u idan ba za ki faɗi alkhairi ba sai ki yi shiru. Kuma Yaya Aliyu ne sai na aure shi ko da ta huɗu zan je matsayin matarsa ina son kayana".
"Kai amma Jamila kin ci kai, ni dai wallahi Allah ya kiyaye ni auren mai mata, ba zan taɓa iya auren mai mata ba. Kullum na yi sallah ina roƙon Allah a cikin ƙaddarata Allah ya sa babu zama da kishiya a ciki". Ta ƙarasa maganar iya gaskiyarta.
"Danƙari! Ma'u Allah ya sassauta miki wannan ɗan banzan kishin da kike da shi, to yanzu idan mai matar kuma za ki aura f...." Ba ta ƙarasa maganar ba Ma'u ta katse ta da faɗin "Haba Jamila wannan ai mugun fata kike yi mini, to bakinki ya ƙare a kanki, aniya tabi aniya, in sha Allah ba zan auri mijin wata ba". Dariya Jamila ta dinga yi har da ƙwalla, wato a duniya Ma'u ta tsani a yi mata zancen kishiya, sai da ta gama dariyar sannan ta ce "Gobe zan zo ki raka ni asibiti dubiya".
"Gidanmu za ki zo?". Ma'u ta tambaya
"Eh".
"Aunty Halima fa ta san kina son mijinta".
"Eh mana to sai me? Ba a aure ita ake aurenta?".
"Hmmm, Allah ya sa ta naɗa miki shegen dukan tsiya". Jamila ta yi dariya ta ce "Ai babu komai, ko ta dake ni daɗi zan ji, ko ba komai zan yi farin ciki hannun da ya taɓa jikin Yaya Aliyu ya taɓa nawa".
Da sauri Ma'u ta kalle ta tana riƙe baki, sannan ta ce "Kuma aka ce miki hannun nata ya taɓa shi ɗin? Jamila ke dai ƴar iska ce wallahi".
Dariya Jamila take yi sosai, ta ce "Abin da yafi taɓawa ma ta yi".
"Ƴar iska ni Yayana ba haka yake ba". Kasancewar babu malami a cikin ajin ya sa Jamila ta riƙa yi wa Ma'u shegantaka tana dariyarta, a haka dai har aka tashi daga makaranta. Ko da Ma'u ta isa gida yamma ta yi sosai, a lokacin har Halima ta gama girkin dare, Yaya Aliyu na gida, taga ya ɗauki abincin zai tafi asibiti, ta so ta bishi, sai dai ganin fuskar nan tasa a ɗaure ya sa ta yi shiru abinta.
*****
Zaune suke a takure cikin wani ƙaramin ɗakin da babu wadataccen haske a ciki, tunda aka ɗakko su daga gidan marayu, aka ajiye su a cikin ɗakin ba a sake bi ta kansu ba. Kallon ƙaramin yaron ta yi da yake kwance yana bacci, daga yanayin yadda yake sauke ajiyar zuciya zai sa a gane sai da ya yi kuka sosai kafin ya yi baccin. Wajen ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare aka turo ƙofar ɗakin, wani basamuden mutum ne ya shigo fuskarsa babu annuri, cikin wata irin ƙatuwar murya ya ce "Ke, ɗakko yaron nan ku fito". Tashi ta yi da ƙyar saboda yunwar da take ji, cikin ƙarfin hali ta saɓa yaron a kafaɗarta ta bi bayan mutumin, wani madaidaicin falo suka shiga, nan ta tarar da wasu manyan mutane su biyu a zaune cikin shiga ta manyan kaya. Tunda suka shigo falon ɗaya daga cikin yake bin ta da wani irin kallo, ita kuma ɗayan mutumin dake zaune kusa da shi take kallo ko ƙiftawa ba ta yi, ganin irin kallon da wannan yake yi mata ne ya sa ta sunkuyar da kai, ta zauna a ƙasa tare da kwantar da yaron a wurin. Gyaran murya ɗayan ya yi ya fara magana "Alhaji Sango ka gansu nan, ina fatan dai sun yi maka?".
Cikin jin daɗin Sango ya ce "Sun yi mini yadda nake buƙatar su, musamman ma macen, gata nan ƴar duma-duma, zan kwashi romo a wajenta".
Dariya ɗayan mutumin ya yi ya ce "Shikenan ciniki ya faɗa, yanzu sun zama mallakinka, za ka iya tafiya da su". Ya yi maganar yana ɗakko wayarsa ya kira wata lamba ana ɗauka ya ce "Allah ya ƙarawa malam lafiya da nisan kwana, ko yanzu dai kamar kodayaushe ne, aikin da aka saba yi ne za a yi, domin wannan karon har biyu aka karɓo". Shiru ya yi yana sauraron na cikin wayar kafin ya ce "Yawwa Malam, a mayar da kowa kurma akan zancen yaran". Dariya ya yi, sannan ya ajiye wayar.
Sango ya ce "Shegen kaya, baka da dama Alhaji, ka zama Musa a fuska Fir'auna a zuci". Ya yi maganar yana duban ƙaton da ya shiga ɗaki ya fito da su, ya ce "Ka ɗauki ƙaramin yaron ka kai shi mota, a tabbatar an yi masa abin da aka saba yi. Ku jira ni a waje nan da awa ɗaya zan fito".
Ɗaukar yaron aka yi aka fita da shi, wanda har yanzu bacci yake yi bai san abin da ake yi ba.
Ita kuma tana nan zaune a wurin ta yi mutuwar zaune, ƙwaƙwaran motsi ma ta kasa yi, tana son ɗagowa ta sake kallon fuskarsa domin tabbatar da cewar shi ɗin ne ko kuma dai mai kama da shi ne.
"To ita wannan ya ka bar ta a nan? Ko ba da ita za ka tafi ba?" Ta ji muryarsa yana tambayar ɗayan
"A'a da ita zan je, kawai ina son in fara mayar da ƙwalamata ne, tun a nan, saboda ba zan iya haƙura har in je can ba".
Dariya ya yi, ya ce "Wannan gaskiya ne, to ga ɗaki nan, sai ka shiga da ita" ɗago da kai ta yi ta kalle shi, muryarta na rawa ta ce "Dama ashe hak...." "Ke" ya daka mata tsawa, kafin ya ce "Waya baki izinin yin magana a nan wurin?". Shiru ta yi ba ta sake cewa ƙala ba, hawaye masu zafi da raɗaɗi suka fara zubo mata. Sai kuma ya yi ƙasa da murya ya ce "Ƴammata ki yi haƙuri, domin wannan kukan ba zai hana a yi miki abin da aka yi niyya ba, a rayuwar nan da kika gani mafi yawan jama'a duk abin da kika ga suna yi mafitarsu ce suke nema, in ma na alkhairi ne ko akasin haka".
Sango ya yi murmushi yana faɗin "Rabu da ita, ai ba za ta sake yin magana ba, balle ta yi gardama akan abin za a umarce ta da yi" daga haka ya ja hannunta ba tare da musun komai ba tabi bayansa ya shiga wani ɗakin da ita. Kafin ya shiga ɗakin ɗayan mutumin ya ce masa
"Ni zan wuce gida saboda dare ya yi, sai mun yi waya, ina yi maka fatan sauka lafiya". Jinjina kai Sango ya yi ya shiga ciki da ita, shi kuma ya tattara kayansa ya bar gidan.
Sai wajen ƙarfe ɗaya Alhaji Sango ya fito shima ya bar gidan tare da wannan ƙaton na ɗazu, wanda shi ne ya shiga cikin gidan ya fito da yarinyar da take a sume ba ta san inda kanta yake ba.
Amanarcool
***