05
KAIFI ƊAYA.....
NA
UMMI A'ISHA
5
***Da mamaki akan fuskar Irfan yake kallon Afeef cike da son jin ƙarin bayani saboda wannan lamari ya bashi mamaki haka kuma ya ɗaure masa kai, to duk tayaya wannan maganar ta faro ko kuma ta samo asali,
"Afeef wai me yake faruwa ne? Anty Mimi fa naji ance zaka aura, ko dai Suhana kake so wannan tsohuwar ta rikirkita maka magana?"
Ɗan murmushi Afeef yayi ya juya ya kalli Irfan da idanuwansa gaba daya ke kansa yana kallon sa baya ko kiftawa sannan yabada gaba daya attention dinsa kansa alamar yana son yaji amsar da zata fito daga bakin sa,
" Wallahi ba rikirkita magana Hajiya kaka tayi ba Irfan.... Ni na fada mata ina son in auri anty Mimi...."
Shuru yaga Irfan yayi yana ta faman kallon sa kamar wanda ke son gano wani abu akan fuskarshi,
"look Irfan.... Na san baza kaji dadi ba sannan zaka dauka kamar reni ne ya sani auren anty mimi..... Allah ba raini bane ko kuma wani abu mai kama da haka...."
"Amma dagaske kana son anty Mimi ko dai kawai tausayinta kake ji saboda aurenta ya mutu?"
Wani ɗan kyataccen murmushi Afeef yayi ya shafa kansa yace da Afeef,
"to kai ka taba ganin inda mutum ya auri mace idan baya son ta? Ina son ta mana kuma ina tsananin tausayinta wallahi....."
"Allah yasa albarka.... But ka shirya karɓar wuju wuju daga wurin anty Mimi dan wallahi na san definitely she will reject you...."
"shine abinda nake tsoro Irfan..... Amma dai zamu gwada mu gani"
Sallama suka yi Irfan ya shiga gida shi kuma Afeef ya nufi gidansu. Daga Afeef har daddy babu wanda ya sanarwa da mommy abinda yake faruwa kuma kamar abin hadin baki suma su Abba babu wanda ya fadawa iyalin sa shiyasa gaba daya matan basu sani ba sai iya mazan ne suka sani, Afeef baccinshi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bayan gari ya waye da ya tashi baima fita da wuri ba har sai da yaya Aliyu ya kira shi sannan ya shirya ya fita, farar shadda ya saka harda babbar riga kamar wani angon gaske,
Anty mimi kam tun 9 ta fita saboda tana da theater da zata shiga har guda biyu, kallonta Hajiya tayi lokacin da zata fita tace,
"Yau dai insha Allah addu'ata da na jima ina yi miki zata tabbata Mimi, yanzu zaki san kinyi aure insha Allah....."
Bata kula ta ba ta fita abinta, sai dai kuma cikin ranta tana ta sake sake da haka har ta isa hospital tunani dai yaki kare mata sannan duk yadda taso ta manta da lamarin ko ta cire shi daga cikin ranta ya gagara.
Bayan an idar da sallar juma'a aka daure auren Anty mimi da Afeef kuma hajiya kaka ce ta bada sadaki kamar yadda ta alkawarta naira dubu ɗari sabbi filfil, wata hamdala da ajiyar zuciya yaya Aliyu yayi bayan yaga an kammala ɗaurin auren, kowa dai cikin iyayen nasu da yan uwa sai murna suke yi duk da ba wani shagali za ayi ko kuma ake shirya yi ba dan abune da yazo musu babu shiri kuma babu tsammani,
Bayan su Abba sun dawo daga daurin auren Abba fari ya shiga part dinsa inda ya iske Ammi tana zaune cikin kitchen ita da Suhana suna hada dambu, cikin kitchen din Abba ya shiga fuskarshi cike da fara'a,
"Yau dambu ake dafa mana Ranki ya dade..."
"Abba sannu da zuwa..." Suhana ta fada tana dariya,
"sannu auta..... Sannu da aiki"
"sannu da zuwa...." ammi ta fada kafin ta fara yunƙurin mikewa, murmushi Abba yayi yace,
"yi zamanki ba sai kin tashi ba kici gaba da aikin ki.... Nima wurin hajiya zan shiga..... Ungo karbi wannan kudin...."
Hannu ammi tasa ta karba tana jiran karin bayani dan bata san ko kudin menene ba,
"sadakin mimi ne..... Yau aka daura mata aure"
Cike da mamaki Ammi da Suhana suke kallon Abba kafin ammi tayi ta maza wurin tambayar sa,
"aure kuma Abba? Da wa aka daura musu aure?"
"ehh aure fa, da Afeef aka daura..."
"Afeef kuma? Wanne Afeef din?"
"Afeef nawa muke dashi? Wanda dai kika sani"
Daga haka Abba ya fita yabar ammi da Suhana daskare awurin dan tsananin mamakin da suke ciki,
"Wai ammi yaya Afeef dai da na sani abokin yaya Irfan? Na gidan daddy?"
"Suhana shine nima abinda nake ta mamakinsa, taya mimi zata auri Afeef, Anya kuwa Afeef din da muka sani ne?"
Shigowar Irfan yasa gaba daya suka mayar da kallonsu gareshi da kuma hankalinsu gaba daya,
"Irfan wai me yake faruwa ne? Yanzun nan abbanku ya fita bayan yazo min da wata magana mai rikirkita kwakwalwa....... Wai waye ya auri yayar ku?"
"Ammi Abba bai fada miki Afeef ne ya aure ta ba?"
Shuru ammi tayi wanda ita kadai ta san abinda take tunani,
"yaya Irfan kuma antyn ta sani?" Suhana ta bukata cikin al'ajabi,
"ta sani...."
"kuma tana son shi?"
"wallahi shine ban sani ba amma dai shi yana son ta dan shine ma ya samu hajiya kaka da maganar jiya shine kawai ita kuma hajiya tace yau a daura musu aure...."
Babu wanda ya sake magana a cikin su har Irfan ya gama basu labarin abinda ya faru ya fita, ita dai ammi ta rasa wanne irin tunani zata yi dan sai take jin abun wani gwangwaragwan amma kuma ba a san me Allah ya shirya ko kuma ya ɓoye ba.
Afeef bayan sun dawo daga daurin auren da yake jinsa kamar wasa dan shi har yanzu ma ya kasa gaskata cewa wai shine yayi auri ya auri anty mimi, wurin hajiya kaka ya shiga tana zaune ita kadai,
"Yawwa lele na yanzu nake son insa a kira min kai dama inji...."
"to gani ai, ya aka yi?"
"cewa nayi yaushe kake son amaryar taka ta tare?"
"A'a ba yanzu ba hajiya...."
"sai yaushe kenan?"
"ba yanzu ba dai, za ta tare a hankali.... Sai na gama wasu shirye shirye"
"to ai shikenan Allah ya kaimu, tunda dai an daura muku auren ai anyi mai wuyar"
Daga haka ya wuce cikin bedroom dinta ya kwanta, yana jin lokacin dasu abba suka shigo wurin hajiyan harda daddynshi, cike da farin ciki da jin dadi hajiya tace,
"nagode, sannunku da kokari, yanda kuke yimin biyayya ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi yayi muku albarka, Allah yasa yayanku suyi muku fiye da haka, Allah yayi muku albarka ya faranta muku...."
Yana jinsu sai tattauna maganar suke yi da maganar inda ya dace su zauna shi da anty mimi amma sai ya jiyo hajiya tana cewa ta tambayi mai sunan malam yace ba yanzu ba tarewa sai nan gaba, ita dai duk wani abu da yace shi ake yi, tun dai yana jiyo su har ma ya daina jiyowa gaba daya, yaga daga hajiya har su Abba sun dauki wannan auren nashi serious basu san na dan wani lokaci bane.
Anty Mimi tana fitowa daga theater ta iske yaya Aliyu yana cikin office dinta yana jiranta, jikinta babu wani kwari fuskar ta babu fara'a ta shiga cikin office din tana rike da files din patients din da ta yiwa theater, zama tayi ba tare da ta kalleshi ba ta fara rubutu cikin files din yana zaune yana kallonta cike da soyayyarta cikin ransa,
"my love..... An daura aurenku da Afeef....."
Yi tayi kamar bata ji shi ba taci gaba da rubutun ta har zuwa lokacin da ta kammala, cike da wani yanayi mai wuyar fassarawa ta ɗago ta kalleshi jin ya kira sunan ta,
"mimi kamar ba kya farin ciki da wannan plan din nawa?"
"Wai dan Allah yaya Aliyu what's your problem? Ba dai abinda kake so ba kenan kuma gashi ya tabbata? What do you want again? Kana dai gani ina aiki ne...... Don't distract me please......"
Numfashi taji ya sauke kafin ya kamo hannunta ya riƙe cikin nashi,
" am very sorry my love, kiyi hakuri da wannan halin da na saka ki, Insha Allah idan muka sake komawa ma'aurata I will do better i promise you..... "
Zuba masa ido tayi tana kallon sa bata ko kiftawa kamar yadda shima yake kallonta ba tare da kiftawa ba, a hankali ta janye nata idon ta fara kokarin janye hannunta daga cikin nasa, sakin hannun nata yayi cikin kalar ban tausayi yace,
" insha Allah 3 weeks kadai wannan auren naku zai yi daga nan zan saka shi ya sake ki......"
Kai ta ɗaga masa hakan ya bashi damar tashi yayi mata sallama ya fita.
La'asar sakaliya ta tashi daga office ta nufi gida, tunda ta doshi gidan taji gabanta yana faman faduwa ras ras amma ahaka ta daure ta karasa tayi parking tana kokarin fitowa ta hango suhana na fitowa daga part din Ammi zata shiga part din umma wato part din su janan, itama suhana ta hangota shiyasa ta nufo wurinta fuskarta dauke da murmushi,
"Anty mimi sannu da zuwa.....kamar kuwa kin san yanzu nake tunaninki cikin raina....."
"Suhana akan maganar auren da aka daura yau ne ko?"
Cike da mamaki suhana ta kalleta tace,
"anty mimi kin samu labari ashe? Soo you know? I thought ma ko baki san da maganar ba"
"na sani...."
"to amma anty mimi da yardar ki?"
Bata amsa mata ba ta fito rike da handbag dinta ta rufe motarta ta shiga wurin Ammi suhana na biye da ita, Ammi na zaune cikin sitting room suka shigo,
Kallon Anty mimi Ammi tayi da kyau kamar wadda take nazarinta kafin tace da ita,
" Mimi wai me yake faruwa ne? Dazu abbanku ya kawo min sadakinki wai an daura muku aure da Afeef...... Taya akayi akai haka?"
"Ammi wallahi nima ban sani ba kawai yau da safe before in fita naji hajiya tana yimin maganar....."
"ikon Allah..... To ko hukuncin hajiya ne? Dan idan ba ita ba babu wanda ya isa ya zartar da wannan hukuncin...."
"amma dai hajiya gaskiya bata kyauta ba dan wallahi janan idan ta samu wannan labarin zata shiga damuwa dan tana tsananin son yaya Afeef sosai.... Sannan shi kansa yaya Aliyu ba zai ji dadin wannan abun ba...." suhana ta fada tana turo baki kamar itace aka daurawa auren,
" ni duk ma ba wannan ba, ya za ayi ace ciki ɗaya tushe daya tsatso ɗaya amma ayi irin wannan kwamacalar? Abinda yayi Aliyu shi yayi Afeef amma kuma a rasa da wanda za a daurawa Mimi aure sai da Afeef? Saboda dai kawai babu wanda ya isa yayi turjiya?" Ammi ta fada cikin bacin rai,
" wallahi Ammi Allah dai ya kyauta kawai "
Ita dai Anty Mimi tashi tayi ta bar sitting room din dan ta san bata da abinda zata ce.