INUWAR BAY
## CHAPTER ONE
**đź’ťZUNUBIN UBA**
**Novel by secretwriter đź’ť**
Sararin samaniya ya yi bakikirin, hadari ya hadu ya murtuke fuska wanda ke nuna alamun saukar ruwan sama na cikin dare. A cikin dakin asibitin,shiru ne mai ratsa kashi ya yi masauki, sai kawai karan injinan da ke taimakawa rayuwar maras lafiya da ke tashi akai-akai, *beep... beep... beep...*
Rayyan yana tsaye jikin katoton gilashin dakin, hannayensa sanye cikin aljihun wandon sa, idanunsa sun yi jawur saboda tsananin gajiya da rashin bacci. Dirar karan wayarsa ta katse daddadan shurun dakin. Ya ja tsaki kadan, ya zaro wayar sannan ya duba fuskar ta, ganin sunan 'Zaid' ya sanya shi danna amsa tare da karawa a kunne, ransa a bace.
"Hello Zaid! Wai ba na fada maka a daina kirana daidai wannan lokacin ba? Kasan ina asibiti ai!" Ya fada cikin muryar rada mai cike da gargadi, yana mai satar kallon gadon asibitin
Daga daya bangaren, Zaid ya gyara zamansa cikin sanyin jiki, "Ah, ba haka bane oga. Akwai matsala ce babba ta taso yanzu. Labari ya fito dumu-dumu cewa sun ki karbar kayanmu, kuma na tabbatar da cewa akwai sa hannun A.A Rumfa a cikin maganar nan..."
Kafin Zaid ya karasa, Rayyan ya juyo da sauri, gaba daya jikinsa ya dauki zafi, idanunsa suka firfito. "Me kace?!" Ya katse shi da karfi, har sai da muryarsa ta amsa a cikin dakin. "Sun ki karbar kayanmu kuma? Dama suna da wannan ikon ne?"
"Eh wallahi oga," Zaid ya fada, muryarsa na rawa kadan. "Wlh dama na fada maka, yanzu ne za su fara daukar zafafan matakai a kanmu, musamman da suka sami labarin cewa mutum guda daya tilo da ke dakatar da su... ya mutu."
Wani sanyayyan murmushi mai cike da daci ya subuce wa Rayyan. Ya jada baya kadan, ya jingina bayansa da bango, sannan ya lumshe idanunsa yana jin radadin abubuwan da ke shirin faruwa. "Hmmm... Na san za a rina. Daman na san hakan za ta faru, amma gaskiya ban yi tsammanin za su dauki mataki cikin gaggawa haka ba." Ya bude idanunsa, wani irin karsashi da kwarin gwiwa na shugabanci ya bayyana a fuskarsa. "Anyway, ka bani mintuna biyar kacal. Da kansu, kuma da kafafunsu za su karbi kayan nan."
Zaid ya marairaice, "To oga, ko dai na shirya yanzu na tafi babban ofishin nasu (Headquarter) ne mu bincika?"
Rayyan ya gyara tsaiwarsa, ya duba agogon hannunsa sannan ya saki wata gajeruwar dariya ta gadara. "Kayi zaman ka kawai Zaid. Babu wanda zai je inda suke, babu kuma wanda zai biya musu bukatar hakan. Amma ina tabbatar maka, kafin gari ya waye za su karba. Sai anjima."
Yana gama fadin haka ya kashe wayar. Ya sauke wata boyayyar ajiyar numfashi mai nauyi, wadda ta fito tun daga kasan zuciyarsa. Cikin sanyi ya taka kafafunsa ya matsa kusa da gadon da ke tsakiyar dakin.
Wani saurayi ne ke kwance, dogo, sanye da kayan marasa lafiya. Shekarunsa ba za su wuce talatin da biyu ba (32). Duk da irin jinyar da yake ciki, da kuma uwar ramar da ya yi, hakan bai boye ainihin kyawun halittarsa ta jinin fulani ba. Fatar sa mai launin cakulan (chocolate), dogon hancinsa, da kuma kwantaccen gashinsa mai baki da sheki sun sanya shi yin kwarjini ko a hakan. Da ace mutum zai yi masa magana, za a rantse zai amsa ne yanzu, sai dai kash... yana can cikin duniyar *coma*, duniyar da babu tabbas na ranar dawowa.
Rayyan ya zauna a gefen gadon, ya sanya hannunsa ya dafe goshin abokin nasa, muryarsa ta karye, cike da shauki da tausayi. "Sarki... ban sani ba ko kana jina a halin yanzu. Amma ina so na fada maka wani abu; ba za mu taba cire tsammani a kanka ba. A kullum addu'armu ita ce Allah ya dawo mana da kai gare mu cikin koshin lafiya." Ya runtse idanunsa, hawaye guda daya ya subuce masa. "Sarki... abubuwa sun fara rikice min. Wasu abubuwan sun fi karfina, bana iya daidaita su ni kadai. Dan Allah sarki... Allah ya tashi kafadun ka."
Karan tura kofar dakin ne ya sanya shi saurin goge fuskarsa tare da mikewa tsaye da sauri don kada a gane halin da yake ciki.
Dr. Nazra ce ta shigo, sanye da farar riga ta likitoci (*lab coat*), tana rike da takardun duba marasa lafiya. Rayyan ya dage, ya tilasta wa kansa sakin murmushi. "Dr. Nazra, barka da aiki. Ya aikin?"
Ta dakata tana duba takardun, sannan ta dago kai ta dube shi da idanu masu cike da kwantar da hankali. "Lafiya lau, Alhamdulillah Rayyan. Ya mai jikin?"
Rayyan ya matso kusa da ita, fuskar sa cike da fargaba da begen jin wani labari mai dadi. "Dr. Wai har yanzu babu wani sabon cigaba ne? Shuru fa har yanzu."
Dr. Nazra ta saki wani murmushi mai sanyaya rai, ta girgiza kanta alamar lallashi. "Ah, haba Rayyan. Kar ka damu mana, ai ana samun cigaba sosai Insha Allah. Jikinsa yana karbar magani, kuma nan ba da dadewa ba zai tashi. Baka gani ba, kusan kwana biyu kenan ma ba mu mayar da shi dakin jiyya na gaggawa (ICU) ba? Yanzu haka ma na zo ne na dan duba yanayin sa kafin na tafi gida, amma babu wata matsala, komai yana tafiya daidai."
Rayyan ya ji wani sanyi ya ratsa ransa, ya gyada kansa cikin gamsuwa. "Ehh, haka ne kam. To na gode kwarai da gaske Dr. Wallahi kin taimake mu da yawa, ba mu da bakin gode miki."
"Ah haba, babu komai ai. Wannan aiki na ne, kuma nauyi ne ya rataya a kaina," ta fada tana duban agogon dake dakin. "Sai da safe."
Bayan Nazra ta fito daga asibitin , ta nufi motarta dake fake a harabar ashibitin. Ta shiga, ta tayar da ita sannan ta dauki hanyar gida kai tsaye.
Tafiyar mintuna kadan ta kaita gaban wani katoton gida na alfarma, gidan daga tsarin ginin sa kadai zai fada maka cewa masu kudi ne ke rayuwa a ciki. A jikin babban get din gidan, an rubuta da wasu baki na zinari: **JAWAHIR RESIDENT**.
Bayan mai gadi ya bude mata, ta shigar da motar ta fito. Cikin gajiya ta shiga cikin katoton falon gidan, wanda aka kawata shi da kujeru na alfarma da fitilu masu kyau . A tsakiyar falon, mahaifiyarta ce zaune ita kadai tana kallon talabijin cikin natsuwa.
Nazra na ganinta, sai ta saki jakar hannunta ta nufi wajen mahaifiyar tata da gudu, ta fada jikinta ta rungume ta tsam, kamar wata yar shekara bakwai. "Momy!" ta fada cikin muryar shagwaba.
Mahaifiyar ta shafa bayanta cikin so da kauna, "Sannu da zuwa Nazra Ya aikin ashibitin na yau?"
Nazra ta dago kai tana murmushi, "Lafiya lau Mom." Ta raba idanu tana kallon ko'ina na falon. "Mom, ina Anty Jannat da kuma Noor suke ne? Gidan shuru."
Maman ta saki dariya mai sauti, ta girgiza kanta. "Noor dai yanzu nan na kore ta ta wuce daki don ta yi aikin gida na makaranta (Assignment). Ita kuma yayar taki Jannat, tana can daki tun duni tana waya da wasu abokan huldar ta (clients)."
Nazra ta tabe baki tana dariya, "Haba Mom. Bari naje na kira su duka mu fito falo mu zauna mu sha hira mana."
Maman ta dafe kafadarta, "Ke kuwa da kika dawo yanzu, ba kya bukatar ki huta ne? Kici abinci mana kafin wata hira."
"Mom muna zuwa kawai!" Nazra ta fada tana dariya yayin da ta mike ta nufi bangaren dakin Jannat.
Tana tura kofar, ta hango Jannat zaune gaban babban kwamfutarta (system), tana ta daddanna madannai cikin natsuwa da kwarewa, sanye da farar gilashin karatu.
Nazra ta tsaya a bakin kofa, ta yi gyaran murya tare da yin sallama cikin zolaya. "Wai wannan Barrister tamu ba ta san wani abu wai shi hutu ba ne? Me kike nema ne a duniyar nan da ba ki same shi ba tukuna?"
Jannat ta juyo a hankali, ta tuge gilashin idonta ta ajiye a kan teburin, fuskarta dauke da murmushi na kauna. "Ah! Ashe har kin dawo?"
"Eh mana! Kuma Mom kadai na tarar a falo tana kallo." Nazra ta karaso cikin dakin ta zauna a gefen gado. "Fito mu koma falo mana mu yi hira, bari naje na kira Noor ma."
Jannat ta harare ta cikin wasa, "Ke kam Nazra, ba kya gajiya ne? Mutum ya dawo daga aikin asibiti amma ko hutu ba ya bukata? Allah ya raba ki da wannan surutun naki na asali."
Nazra ta tuntsire da dariya, ta mike tana takawa zuwa tsakiyar dakin cikin takun isa. "Anty Jannat, ni fa ba a karkashin wani nake aiki ba, kuma ba aikin gwamnati nake yi ba. Wannan ashibitin ai namu ne, mu muka gina shi, kuma ni nake da dukkan ma'aikatan cikinsa. Ina zuwa ne kawai saboda ina son na rinka yin amfani da abin da na karanta (practice). Ba kamar ke ba... mutum ace yana matsayin lauya (Barrister) amma ya ki yin aiki a kotu, sai harkar kasuwanci! Anty Jannat, kiyi hakuri dan Allah ki rage neman kudin nan, ke fa yanzu *Successful Entrepreneur* ce kuma gashi ke *Barrister* ce."
Jannat ta girgiza kanta tana dariya, ta tashi tsaye daga kan kujerar. "To shikenan kinyi gaskiya, Amman Dan Ina lauya da dole bane sai nayi practice ah hakan ma Ina Aiki na mu je falon. Amma dai kamata ya yi ki fara zuwa kiyi wanka ki canza kaya, sai ki same mu a can. Bari ni kuma na kira Noor din."
"Ohooo! To shikenan," Nazra ta fada tana nufi dakinta cikin farin ciki.
Bayan kamar rabin sa'a, gaba dayansu suna zaune a babban falon gidan. Nazra na zaune a kasa gaban karamin tebur tana cin abinci cikin sauri-sauri saboda yunwa, yayin da Maman ta ke zaune a babban kujera, Jannat da Noor kuma suna gefe guda.
Jannat ta gyara zamanta, ta kalli mahaifiyarta cikin girmamawa. "Yauwa Mama, gobe fa zan kawo miki takardun sabon gidan nan (*Apartment*) da na saya, kofofin sanya hannu (signature) sun shirya, sai ki saka hannu kawai."
Mahanfiyarsu ta cika da farin ciki, ta daga hannayenta sama. Tace Allah Na gode ma "To shikenan Jannat , Allah ya muku albarka, ya buÉ—e muku kofofin alkhairi."Su ka ce Aameen
Noor, wadda ke zaune tana danna wayarta cikin sanyin jiki, ta dago kai ta kalli Jannat cikin shagwaba ta turo baki. "Anty Jannat..."
"Na'am Noor, me ya faru?" Jannat ta fada tana juyo da hankalinta gare ta.
Noor ta matso kusa, muryarta a sake, "Daman kudin da ke cikin *account* dina sun kusa karewa... Ko za a tura min wani abu ne? Kinsan gobe akwai wasu 'yan abubuwa da nake son na magance a makaranta."
Nazra dake cin abinci ta tsagaita, ta ajiye cokalin hannunta da karfi a kan kwanon, ta juyo tana kallon Noor da mamaki. "Wai ke Noor, me kike yi da kudi ne haka? Can you imagine Mom! Wannan yarinyar tana aji biyu na sakandare (SS2) fa kawai, amma yadda take almubazzaranci da kudi abin yana da yawa gaskiya. Me kike nema da ba kya samu a gidan nan? Har fa direba kika ki bari ya rinka kaiki makaranta, kika ce sai ke da kanki zaki yi tuki!"
Jannat ta ta juyo ta kalli Nazra , "To meye a ciki don ta samu duka wannan, Nazra? Ko kina so ta dandana irin wahalar da mu muka sha a baya ne? Bayan mu da kanmu muka yi alkawarin cewa Insha Allah zamu samar mata da duk abin da take bukata a rayuwa?"
Nazra ta ji ranta ya baci, ta kawar da kanta gefe guda, muryarta cike da rauni da bacin rai. "Kinga Anty Jannat, dan Allah idan ana hira, ki daina tunatar da ni irin radadi da wahhalhalun (*trauma*) da muka fuskanta a shekarun baya. Abubuwan suna da zafi sosai."
Mahaifiyarsu dake saurarensu, ta sauke numfashi mai nauyi, fuskarta ta nuna damuwa kwarai. "Duk da haka dai, abin da Nazra ta fada gaskiya ne. Ya kamata ku rinka lura da tarbiyyar Noor, kunga yanzu nauyin yana kanku gaba daya, sai kun taya ni."
Jannat ta sunkuyar da kanta cikin girmamawa, "Karki damu Mom, wallahi muna lura da ita sosai."
Maman ta mike tsaye tana dafe kwankwasonta saboda ciwo da yake yi mata . "To kowa ya tashi ya je ya kwanta, dare ya yi." Ta yi musu sallama sannan ta nufi dakinta.
Suma sauran suka fara shirin mikewa don tafiya dakunansu. Noor ta gyara zama, ta kalli yayyen nata guda biyu, fuskarta cike da tambayoyin da suka dade suna cin zuciyarta. "Wai dan Allah... idan na tambaye ku, ina mahaifina yake? Kuma me ya faru a shekarun baya da kuke yawan boyewa? Sannan me yasa a duk lokacin da na tayar da wannan maganar a gaban Mom, sai ciwonta ya tashi?"
Wannan tambayar ta sauka a cikin falon kamar saukar walkiya. Dif! Falon ya yi shuru kamar babu mutane.
Nazra ta runtse idanunta da karfi, nan da nan wasu zafafan hawaye suka cika idanunta, suka fara kwarara a kan fuskarta. Ta dubi Noor cikin tsananin bacin rai da muryar kuka. "Dan Allah Noor... ba za ki iya hakura da wannan maganar ba? Uban me hakan zai amfane ki idan kika san inda yake? Shi wanda kike ta kiran babanki... me ya taba miki?" Ba tare da ta jira amsa ba, ta mike da gudu ta bar falon tana kuka sosai.
Noor ta razana da yanayin Nazra, amma hakan bai sanya ta hakura ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta kalli Anty Jannat, wadda tun sanda aka fara maganar ta yi dif, ta kasa cewa uffan.
Wani irin mamaki da fargaba suka kama Noor lokacin da ta kalli fuskar Jannat. Jannat din da take kallonta a matsayin jaruma, mace mai juriya, a halin yanzu kuka take yi na zuciya; hawaye ne masu dumi suke bin kuncinta a hankali, amma ta ki barin muryarta ta fito.
Noor ta matso kusa da ita cikin sanyin jiki, ta zauna a kasa kusa da kafafunta, hankalinta a tashe gaba daya. "Anty Jannat... kema kukan kike son kiyi? Idan kuna yin haka, ta yaya hankalina ba zai tashi ba ta ya zan samu natsuwa ? Me ke faruwa ne?"
Jannat ta saki wani rafannan murmushi mai cike da tsananin daci da rauni. Ta mika hannunta ta share hawayen Noor, sannan ta kalli cikin idanun yar uwar tata.
"Noor..." Ta fada cikin muryar da ke rawa saboda kuka dake cin makogwaronta. "Wasu labaran... ba su da dadin ji ga mai sauraro. Haka zalika, ba su da dadin fada ga mai bada labarin. Wani lokacin, shuru shi ne mafi alkhairi a rayuwa." Ta sanya hannunta ta shafa gashin kanta cikin sanyaya gwiwa. "Amma idan lokaci ya yi... watakila zaki san komai. Sai dai kawai ina fata, kuma ina addu'ar kada wannan labarin ya fito daga baki na... saboda tsananin dacin dake cikinsa."
Ta mike tsaye da kyar, ta sake dubanta cikin tausayawa. "Kije ki kwanta, gobe zaki fita makaranta." Daga nan ta juya ta bar Noor zaune ita kadai a tsakiyar falon, tana kallon bayanta cike da fargaba da dimuwa
đź’ťZUNUBIN UBAđź’ť
đź’ťNovel by secretwriter đź’ť