FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · INUWAR BAY
## CHAPTER ONE **💝ZUNUBIN UBA** **Novel by secretwriter 💝** Sararin samaniya ya yi bakikirin, hadari ya hadu ya murtuke fuska wanda ke nuna alamun saukar ruwan sama na cikin dare. A cikin dakin asibitin,shiru ne mai ratsa kashi ya yi masauki, sai kawai karan injinan da ke taimakawa rayuwar maras lafiya da ke tashi akai-akai, *beep... beep... beep...* Rayyan yana tsaye jikin katoton gilashin dakin, hannayensa sanye cikin aljihun wandon sa, idanunsa sun yi jawur saboda tsananin gajiya da rashin bacci. Dirar karan wayarsa ta katse daddadan shurun dakin. Ya ja tsaki kadan, ya zaro wayar sannan ya duba fuskar ta, ganin sunan 'Zaid' ya sanya shi danna amsa tare da karawa a kunne, ransa a bace. "Hello Zaid! Wai ba na fada maka a daina kirana daidai wannan lokacin ba? Kasan ina asibiti ai!" Ya fada cikin muryar rada mai cike da gargadi, yana mai satar kallon gadon asibitin Daga daya bangaren, Zaid ya gyara zamansa cikin sanyin jiki, "Ah, ba haka bane oga. Akwai matsala ce babba ta taso yanzu. Labari ya fito dumu-dumu cewa sun ki karbar kayanmu, kuma na tabbatar da cewa akwai sa hannun A.A Rumfa a cikin maganar nan..." Kafin Zaid ya karasa, Rayyan ya juyo da sauri, gaba daya jikinsa ya dauki zafi, idanunsa suka firfito. "Me kace?!" Ya katse shi da karfi, har sai da muryarsa ta amsa a cikin dakin. "Sun ki karbar kayanmu kuma? Dama suna da wannan ikon ne?" "Eh wallahi oga," Zaid ya fada, muryarsa na rawa kadan. "Wlh dama na fada maka, yanzu ne za su fara daukar zafafan matakai a kanmu, musamman da suka sami labarin cewa mutum guda daya tilo da ke dakatar da su... ya mutu." Wani sanyayyan murmushi mai cike da daci ya subuce wa Rayyan. Ya jada baya kadan, ya jingina bayansa da bango, sannan ya lumshe idanunsa yana jin radadin abubuwan da ke shirin faruwa. "Hmmm... Na san za a rina. Daman na san hakan za ta faru, amma gaskiya ban yi tsammanin za su dauki mataki cikin gaggawa haka ba." Ya bude idanunsa, wani irin karsashi da kwarin gwiwa na shugabanci ya bayyana a fuskarsa. "Anyway, ka bani mintuna biyar kacal. Da kansu, kuma da kafafunsu za su karbi kayan nan." Zaid ya marairaice, "To oga, ko dai na shirya yanzu na tafi babban ofishin nasu (Headquarter) ne mu bincika?" Rayyan ya gyara tsaiwarsa, ya duba agogon hannunsa sannan ya saki wata gajeruwar dariya ta gadara. "Kayi zaman ka kawai Zaid. Babu wanda zai je inda suke, babu kuma wanda zai biya musu bukatar hakan. Amma ina tabbatar maka, kafin gari ya waye za su karba. Sai anjima." Yana gama fadin haka ya kashe wayar. Ya sauke wata boyayyar ajiyar numfashi mai nauyi, wadda ta fito tun daga kasan zuciyarsa. Cikin sanyi ya taka kafafunsa ya matsa kusa da gadon da ke tsakiyar dakin. Wani saurayi ne ke kwance, dogo...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.