ZUNUBIN UBA

Farkawar Hadari

by @secretwriter

## CHAPTER TWO  
**đź’ťZUNUBIN UBAđź’ť**  
**Novel by secretwriter đź’ť**  
Hasken rana mai dumi na karfe goma na safe ya riga ya gauraye garin Abuja , yana mai haskaka wani daki na musamman da ke cikin wani katoton bene. Dakin ya kayatu da hadaddun kujeru na fatar damisa, bangon dakin kuma an jera hotunan manyan mutane da lambobin yabo na kasashen waje. Mutane uku  ne zaune a ciki, dukansu dattawa ne wadanda furfura ta fara fito musu, sanye da fararen manyan riguna na alfarma da hulan zanna-bukar. Kana ganinsu kasan cewa manyan masu kudin kasar ne, kuma jiga-jigan 'yan siyasa ne masu fada a ji.  
Daya daga cikinsu, Alhaji Harris, ya gyara zamansa tare da buga hannunsa a kan teburin dake gabansa, fuskarsa murtuke cikin bacin rai. "A.A Rumfa!" Ya kira sunan mutumin dake zaune a babban kujera na tsakiyar dakin. "Akan me zamu ji wannan tsinannen labarin da sassafe haka? Wai daga tashi daga bacci, sai labarin da zamu ji shi ne har yanzu tsoron wannan yaron kake yi? Yaron da kowa ya sani cewa ya riga ya mutu ya bar duniya?"  
A.A Rumfa ya sauke gilashin idonsa na karatu a hankali, ya kalli Alhaji Harris da wasu idanuwansa na tsohon makiya karshe, sannan ya girgiza kansa cikin takun natsuwa. "Haba Alhaji Harris, ka fiya gaggawa da yawa a rayuwarka. To bari na fada muku gaskiyar lamari; da ace jiya ban bada umarnin a kyale su sun karbi kayan Sarki ba, to da yau ba wannan labarin muke tattaunawa ba. Da a ce yau mun nuna musu turjiya, da duk kujerun ikon nan da kuke takama da su yanzu haka, yau dinnan zaku wayi gari an kwace su gaba daya, kuma da hakan zaku fara cin karo maimakon wannan zancen na yanzu. Don haka ku fada min, tsakanin asarar kujerunku da abin da na yi jiya, wanne ne mafi alkhairi a gare ku?"  
Alhaji Rabi’u, wanda ke zaune a gefe yana juyawa tare da wasa da carbi a hannunsa, ya yi gyaran murya sannan ya gyada kansa. "Ehh... Gaskiya ne, mun fi son wannan zabin naka na kare kujerunmu. Amma fa kai kanka Ranka ya dade, me yasa ka ki yadda da cewa Sarki ya riga ya mutu? Lokaci fa sai tafiya yake yi, kusan shekaru sun shiga tsakani. Da a ce yana raye a cikin duniyar nan, ai da tuni ya bayyana kansa ga mutane."  
Alhaji Harris ya karbe maganar da sauri, "Ehh, nima abin da nake gani kenan. Kuma ma gaba daya saboda me zaka rinka damun kanka a kan mutumin da ko da yana raye, mun Riga mun San ,muna da masaniyar abin da muka yi masa, abin da zai sanya ko yana da sauran numfashi ba zai taba iya yawo a cikin mutane kamar sauran talakawa ba?"  
Wani kallo mai cike da taraddadi da fargaba A.A Rumfa ya sakar musu, sannan ya jingina bayansa da kujera, yana tuno mugun  hatsarin da mutumin nan ke iya haddasa musu. "Kar ku manta fa... wannan abun da kuke magana a kansa, shi ne babban tsarinmu na biyu (*Plan B*) idan har bai mutu ba. Don haka dole ne hankalina ya ki kwanciya, domin kuwa jiki na yana ba ni cewa Sarki bai mutu ba! Kuma ina son na tabbatar da hakan ne da idona kafin mu san mataki na gaba da zamu dauka. Yanzu haka ma bincike ake yi na sirri akansa,kuma Ana samun cigaba sosai kuma Abinda ya faru jiya ya kara karfafa shakku na."  
Harris ya jinjina kai, fuskarsa cike da daci. "Amma dai kar ku manta da kalmar karshe da ya fada mana tun kafin ya bace; ya ce ko da yana da rai ko ya mutu, babu wani dan adam da ya isa ya hana shi shigo da fitar da kayansa cikin kasar nan!"  
"Kuma shi ne abin takaicin..." A.A Rumfa ya fada cikin takaicin murya, yana matse damtsen hannunsa. "Gashi baya nan a halin yanzu, amma duk da haka jiya mun kasa yin abin da ya dace saboda tsoron sunansa kawai."  
Alhaji Rabi’u ya ja tsaki mai karfi, ya jefar da carbin hannunsa. "Kaii! Wannan tsinannen yaron ya takura mana da yawa a rayuwa wallahi! Ko yana raye ko yana mace, yana ci gaba da girgiza daular mu."  
A daidai wannan lokacin, wata hadaddiyar farar mota ce mai kirar **BMW** ta shigo cikin harabar makarantar sakandare ta manyan masu kudi  Noor ta faka motar a hankali a gaban rukunin azuzuwan daliban *Senior Secondary*.  
Ta fito Sanya da kayan makaranta na Alfarma Kofa ta baya ta bude. Ta mika hannu ta dauki hadaddiyar jakar makarantarta (*school bag*) daga kujerar baya, sannan ta rufe kofar motar da karfi, ta nufi ajinsu (*SS2*) tana takawa cike da natsuwa da sanyin jiki.  
Tana shiga cikin ajin, yawancin daliban da ke zaune suka fara gaishe ta cikin girmamawa da neman alfarma, saboda kowa ya san yadda take fantama wa a makarantar . Noor kuwa ba ta cika bi ta kansu ba, sai kawai ta dinga gyada kai tana neman inda ta saba zama. Tana samun wuri ta zauna,Aminiyanta  na kusa da ita guda biyu, Nahad da Aliya, suka taso da sauri suka dawo kusa da ita suka zauna domin su sha hira.  
Ba a dade ba, kofar ajin ta bude sai ga malamin dake koya musu darasi, Malam Umar, ya shigo rike da littattafai a hannunsa. Gaba daya ajin suka mike tsaye don girmamawa tare da hada baki wajen yi masa sallama da gaisuwa. Malam Umar ya amsa cikin fara'a, sannan ya nuna musu hannu alamar su zauna.  
Sai dai a wannan karon, kowa ya lura akwai wani boyayyen bako dake tsaye a gefen malamin. Malam Umar ya kalli ajin, sannan ya kalli Noor da sauran daliban dake kusa da ita. "Wannan sabon dalibi ne da aka kawo ajinku yanzu (New Comer), kuma ina fatan zaku zauna da shi lafiya, Insha Allah har ku gama karatunku na makarantar nan gaba daya."  
Malamin ya juyo ya kalli yaron, wanda idan ka duba tsawonsa da siffarsa, kusan sa'an Noor ne ko ma ya girme ta da shekara guda. Yaron yana da kyan fuska, sanye da kayan makarantar da suka zauna a jikinsa dumm, gashin kansa kuwa an Aske  shi daidai yadda tsarin makarantar ya nuna. "Bismillah, yi musu bayanin kanka," Malam Umar ya fada masa.  
Yaron ya matso gaba kadan, ya gyara tsaiwarsa ba tare da nuna fargaba ba, sannan ya saki wani sanyayyan murmushi wanda ya bayyana kyan fuskarsa. "Sannunku da yau... Sunana **Faris Al-Kaseem**. Ina fatan zaku karbe ni hannu biyu, kuma zaku iya taimaka min da duk wasu abubuwan da ban sani ba game da tsarin makarantar nan."  
Kafin ma kowa ya ce uffan a cikin ajin, Noor ta gyara zamanta da sauri, fuskarta dauke da wani irin  farin ciki da ba a saba gani ba. "Sosai ma kuwa Faris! Me zai hana? Zamu taimake ka da komai," ta fada da babbar murya cikin  farin ciki da sanyayyen murmushi.  
Gaba daya ajin suka dauki shuru dif  kamar an musu mutuwa! Kowa ya zuba wa Noor idanu cike da tsananin mamaki. Daliban ajin sun yi dumu-dumu da mamakin abin da Noor ta yi, domin kuwa kowa a makarantar ya sani cewa Noor mace ce mai girman kai da aji (*Steeze & Class*), ba ta taba kula maza na ajin ko magana da su ba, bare har ta nuna murnar karbar sabon dalibi.  Faris ya kalle ta yayi murmushi ya nufi inda aka tanadar masa domin ya zauna. Malam Umar ya gyada kai sannan ya fita don basu lokaci.  
A daya bangaren kuma na gari, Jannat ce zaune a cikin babban ofishinta na lauyoyi (*Chamber*), tana sanye da kyakkyawan  suit dinta na aiki baki wanda ya fito da kyan ta da kuma matsayinta na Babban Lauya. Ta dade tana tattaunawa da wasu manyan abokan huldarta (Clients) akan wata shari’a  ta kasuwanci. Bayan sun kammala komai cikin nasara, suka yi musu sallama sannan suka tafi.  
Tana shirin gyara takardun dake kan teburinta, sai ga wayarta ta fara ruri da karfi tare da girgiza. Ta duba fuskar wayar, ganin sunan 'Nazra' ya sanya ta danna amsa da sauri tare da sanya wayar a kunne.  
"Hello Nazra..." Jannat ta fada cikin muryar gajiya amma cike da kauna.  
Daga daya bangaren, muryar Nazra ta fito cike da wani irin zazzafan farin ciki da doki. "Anty Jannat! Dan Allah ki taya ni murna! Wlh abin farin ciki ne... wannan mara lafiyan nawa na dakin asibiti (Patient) ya farfado yanzu haka! Ya tashi daga coma!"  
Jannat ta saki wata gajeruwar ajiyar numfashi ta jin dadi, ta tashi tsaye tana murmushi. "Kaii! Masha Allah, Alhamdulillah Nazra! Gaskiya na ji dadi sosai da wannan daddadan labarin. Domin kuwa bawan Allah nan, yadda kike ba ni labarinsa kullum, ya sha wuya da yawa a rayuwarsa. Allah ya kara masa lafiya."  
"Eh wallahi Anty Jannat, nima abin da nake gani..."  
Kafin Nazra ta karasa maganar, sai ga kofar ofishinta na asibiti ta bude da karfi da gaggawa. Wata nas (*Nurse*) ce ta shigo da gudu, fuskarta cike da tsananin razana da firgici, numfashinta yana sarkewa. "Dr. Nazra! Dan Allah ki zo yanzu ki gani... Abin ya baci fa!"  
Nazra ta razana, ta katse wayar da sauri ba tare da ta yi wa Jannat sallama ba, ta  yadda  wayar a kan tebur ta bi bayan nas din da gudu zuwa dakin jiyya na mutumin.  
Tana shiga cikin dakin, wani mummunan gani ne ya sanya ta tsayawa durus, gabanta ya fadi da karfi. Mara  lafiyan nan (Sarki), wanda yanzu ya farka, ya samu almakashi ta dressing (*dressing scissors*) dake kusa da shi. Cikin wani irin yanayi na hauka da firgici, ya rinka amfani da almakashin  nan yana yanka kansa guri guda biyu daban-daban, jini yana kwarara a kan fuskarsa yana haduwa da sauran jikinsa, duk da hannu guda daya yake yin wannan abun saboda dayan hannun yana daure.  
"Sarki! Dakata dan Allah!" Nazra ta fada ta nufi  inda yake  cikin fargaba.  
Mutumin yana ta nishi sama-sama, idanunsa sun yi jawur kamar garwashi, yana nuna alamun baya cikin hayyacinsa gaba daya. Da kyar, da taimakon sauran ma'aikatan asibitin da suka rugo dakin, suka samu nasarar kwace almakashin daga hannunsa tare da danne shi a kan gadon. Nan da nan Nazra ta umarci a masa allurar bacci mai karfi (*sedative*). Cikin daĆ™iĆ™oĆ™i kalilan, allurar ta kama shi, sannan ya koma ya lumshe idanunsa ya fada cikin bacci na dole, nishinsa yana fita a hankali.  
Nazra tana tsaye a gefensa, tana duba jinin da yake jikin sa , gaba daya jikinta yana rawa saboda firgici da tausayinsa. Ta juya da sauri ta dauko takardunsa na bincike (*Files*), ta dauki alkalami ta fara rubuta wasu takardun gaggawa.  
Ta kalli nas din dake kusa da ita, muryarta na rawa. "A dauki takardun nan maza, a je a yi masa gwajin jini na gaggawa (Test), sannan a wuce da shi dakin hoton bargo da kwakwalwa (*X-ray & Brain CT Scan*) yanzu dinnan ina son na ga sakamakon!"  
Ta dafe goshinta tana kallon Sarki dake barci, tana mamakin wane irin mugun abu ne ke damun kwakwalwar wannan bawan Allah.  
đź’ťZUNUBIN UBAđź’ť  
Novel by secretwriter đź’ť