GAMO DA KADDARA
## CHAPTER THREE
**đź’ťZUNUBIN UBA đź’ť**
**Novel by secretwriter đź’ť**
A cikin falon katoton gidansa da ke cike da kayan alfarman da aka kwaso daga kasashen turai, A.A Rumfa yana tsaye sanye da wata tsadaddiyar riga ta siliki. Fuskar sa babu alamar digon annuri, sannan idanunsa suna lumshe yayin da ya kara wayar a kunne, muryarsa tana fita kasa-kasa amma cike da wata irin barazana.
"Malik..." Ya kira sunan mutumin da ke daya bangaren cikin wani irin takun isa. "Ina son ka tabbatar da cewa ka gano dukkan sirrin da ke cikin asibitin nan kafin ka bar harabar wajen. Tunda har kace ka hango kafafun Rayyan suna shiga cikin babban asibitin, to akwai babban shakku. Ka gano min ko Sarki yana nan a raye. Idan kuwa har ka tabbatar da yana dakin asibitin nan... to ka tabbatar da ka shigar da shi barzahu kafin ka bar cikin asibitin nan. Ba na son kuskure!"
Daga daya bangaren, muryar Malik ta amsa cikin sanyin jiki amma cike da kwarin gwiwa na marasa imani. "An gama oga. Ka kwantar da hankalinka, ba zai sake ganin hasken gobe ba."
A daidai wannan lokacin, a can cikin babban ofishin Dr. Nazra na asibitin, shiru ne ya gauraye tsakaninta da Rayyan. Nazra tana zaune a kan kujerarta ta aiki, yayin da Rayyan ke zaune a gabanta, hannayensa biyu dafe da kansa, yana jiran jin sakamakon binciken kwakwalwa (*Brain CT Scan*) da aka gudanar a kan Sarki.
Nazra ta sauke numfashi, ta ajiye hoton hoton bargo da kwakwalwa (*X-ray*) a kan teburin, sannan ta kalli Rayyan cikin sanyin murya da tausayawa. "Munyi duk gwaje-gwajen da suka dace Rayyan. Uhmm... A bangare guda, za mu iya cewa akwai sauki kwarai, tunda ba a sami wata matsala ta shafar sassan kwakwalwa da ke kawo mantuwa (*amnesia*) ba. Ya tuna komai na rayuwarsa, kuma zai gane kowa da komai."
Ta dakata kadan, fuskarta ta kara sauya launi zuwa damuwa. "Amma matsala mafi girma da ta same shi ita ce... ya kamu da wata cutar kwakwalwa ta musamman da muke Kira da *Severe Post-Traumatic Self-Harm Disorder*. Wannan cutar tana sanya shi dinga cutar da kansa. Zai rinka tuno mummunan abin da ya faru da shi a baya, sai wani bangare na kwakwalwarsa ya rinka raya masa cewa komai fa da ya faru... laifinsa ne! Sannan kwakwalwar za ta nuna masa cewa shi ne ya kamata ya hukunta kansa. Wannan dalilin ne zai sanya shi rinka yankan jikinsa ko tunanin kashe kansa, domin a lissafinsa , wannan raunin da yake ji wa kansa shi ne daidai gwargwadon hukuncin da ya kamata ya fuskanta."
Rayyan ya ji gabansa ya fadi dumm! Ya dafe kirjin sa , idanunsa suka ciko da kwalla. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya fada cikin muryar raki. "Wace irin jarabawa ce wannan Sarki? Wlh Dr. Da ace ya samu matsalar mantuwa, da hakan ya fi mana sauki nesa ba kusa ba a kan wannan tsinanniyar cutar."
Dr. Nazra ta girgiza kanta cikin rarrashi. "A'a Rayyan, a fannin lafiya babu maganar gwara waccan cutar. Kawai mu dage da addu'ar Allah ya ba shi lafiya. Kaima kanka ka ganshi yanzu, ya dawo hayyacinsa sosai, matsalar kawai ita ce wadancan tunanin na baya idan suka taso masa. Muna kan shirin daura shi a kan ingantattun magunguna (*Antipsychotics & Mood Stabilizers*). Sai dai kash... magani kadai ba zai iya yin abin da shi zai iya yi wa kansa ba, da kuma kulawar ku na kusa da shi."
Rayyan ya gyada kansa cikin gamsuwa, sannan ya matso kusa da teburin gwiwoyinsa duka biyu a kasa, fuskarsa cike da neman alfarma. "Ehh haka ne kam. Amma Dr... ko zaki iya yi min wata babbar alfarma dan Allah? Na taba jinki kina maganar cewa yayarki babbar lauya ce (Barrister)?"
Nazra ta dan gyara zamanta cikin mamaki. "Ehh, na fada maka hakan. Lafiya dai ko?"
Rayyan ya hada hannayensa biyu waje guda. "Wallahi muna da bukatar kwararriyar lauya wadda za ta iya bincika mana wasu takardu da tsare-tsare na doka cikin sirri. Ko zaki iya rokar min ita ta zo asibitin nan dan Allah mu tattauna? A halin da muke ciki yanzu, ba zan iya fita na nufi ofishinta ba saboda tsananin tsaro. Wannan ashibitin naku ne kadai nake jin zai iya ba mu cikakken tsaron da muke bukata a halin yanzu."
Nazra ta kalli yadda hankalinsa ya tashi, ta ji tausayinsa ya ratsa ta. "Shikenan, babu damuwa. Bari na kira ta a waya yanzu."
Bayan Rayyan ya tashi ya fita daga ofishin Dr. Nazra, ya nufi dakin jiyya na musamman da aka mayar da Sarki. Yana tura kofar dakin ne, wani irin abin mamaki ya doke shi wanda ya sanya jikinsa gaba daya yin sanyi. Wayar hannunsa ce ta subuce ta fadi a kasa, *katas!* Ba tare da ya damu da daukar wayar ba, ya jefa idanuwansa a kan abin da ke faruwa a gabansa.
Cikin sauri ya karasa kusa da gadon, muryarsa cike da tsananin razana. "Sarki Saif! Me nake gani haka?!"
A kasa, gaban gadon, Malik ne kwance matacce ko sumamme, jikinsa duka ya daku, fuskarsa ta kumbura ta fashe da jini, sanye da kayan ma'aikatan asibiti na batan maza.
Sarki Saif, wanda ke zaune a gefen gado yana goge jinin da ke hannunsa da bargo, ya dago wadancan manyan idanunsa da suka yi jawur kamar garwashi, ya kalli Rayyan cikin wani irin sanyayyan takun isa da daci. "Me ka gani? Malik ne fa a kwance a gabanka, ya sha dukan mutuwa."
Rayyan ya kasa magana, sai dube-dube yake yi. "Amma sarki... ta yaya?"
Saif ya gyara zamansa, wani murmushi mai cike da mulki da gadara ya subuce masa. "Wani karin bayani kake bukata Rayyan? Shin ni, Sarki Saif, har na kai matakin lalacewar da za a turo wannan tsinannen Malik din domin ya kashe ni? Mutumin da idan na kalle shi, ba na banbance shi da mace saboda raunin sa? Wa ye Malik da zai zo gabana da sunan kashe ni?" Ya fada cikin muryar takun mulki dake girgiza dakin. "Ko Laila sai ta Hukunta Malik ba sai na sah hannu Ba
Yana fadin sunan **'Laila'**, sai ga wani zazzafan radadi ya soke ainihin tsakiyar kwakwalwarsa. Ya dafe kansa da sauri da hannunsa guda biyu, yana nishi sama-sama, fuskarsa ta nuna zafi da dacin dake cikin zuciyarsa. Ya runtse idanunsa, sannan ya bude su a fuskar Rayyan. "Dauke min wannan danyen naman a gabana! Kuma a sanar da duniya cewa, gobe gaba daya zan dawo fada ta!"
Rayyan ya dafe kirji cikin fargaba. "Sarki Saif! Akwai babbar matsala fa! Ba za mu iya yin shelar dawowar ka a halin yanzu ba."
Saif ya doka masa wani kallo mai cike da bacin rai. "Akan me? Ka san dai na fi karfin na zauna a cikin rami ina boye kaina yayin da kananun farauta irin su A.A Rumfa suna yin abin da suka ga dama a cikin gari! Dole ne su san cewa Sarki ya dawo domin ya karbi abin da yake nasa!"
"Sarki haka ne, na sani!" Rayyan ya fada cikin rarrashi, ya dafe gwiwarsa. "Amma wani lokacin, dole ne mu barsu su yi abin da suka ga dama, domin yin hakan ba wai tsoro ba ne... taku ne na hikima. Kaine da kanka ka koya min wannan dabarar a baya! Idan muka sanar da dawowar ka yanzu, akwai babbar matsala, domin kuwa akwai wani katoton tarkon da suka dana mana. Idan har ba mu shirya ba, mu zamu fada a ciki. Akwai wasu tsare-tsare da nake yi a sirri kafin mu fito fili. Dan Allah... ka bani mintuna talatin (30 minutes) kacal, saboda jiran tashin ka kawai nake na fara Aiwatar da shirin,ka amince da ni a kan wannan takun."
Sarki Saif ya zuba masa idanu na tsawon wasu dakiku, yana auna gaskiyar maganar Rayyan, sannan ya sauke wani boyayyen numfashi. "Shikenan. Na baka mintuna talatin din."
Kafin ma a kai mintuna talatin din, Barrister Jannat ta riga ta iso asibitin cikin hanzari, sakamakon kiran gaggawa da kanwarta Nazra ta yi mata. Ta tura kofar ofishin Nazra, sanye da bakaken kayanta na lauyoyi masu nuna aji. Ta yi sallama tare da zama a kan kujera, fuskarta babu alamar wasa.
"Gaskiya Nazra..." Jannat ta fada tana ajiye jakar hannunta. "Ba don tsananin rokon da kika yi min ba, da babu abin da zai kawo ni asibitin nan a yau saboda ina da aiki da yawa."
Nazra ta taso da sauri ta dafe kafadarta tana murmushi. "Kiyi hakuri Anty na,wallahi lamarin ne ke da muhimmanci sosai. Bari na kira shi a waya yanzu."
Jannat ta harare ta kadan cikin mamaki. "Oh! Har da lambar wayarsa ce da ke a halin yanzu?"
"Haba Anty Jannat, ba zaki gane ba. Mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata kwarai," Nazra ta fada tana danna lambar Rayyan. Bayan sun yi magana, ta ajiye wayar ta kalli Jannat. "Gashi nan zuwa yanzu dinnan. Ya dan fita ne don ya duba wani abu, amma yana kokarin yin fakin (*parking*) na motarsa a harabar asibitin."
"To shikenan, ina jiran sa," Jannat ta fada cikin natsuwa.
Nazra ta kalli yayar tata, sai ta saki wani murmushi na dabara. "Daga nan kafin ya karaso, taso mu je dakin jiyyar sarki (Ward) ki gani da idonki, kiyi masa ya jiki."
Jannat ta mika mata hannu, "To shikenan, mu je."
Suna cikin takawa a dogon layin asibitin (*corridor*), Nazra ta hango Rayyan yana kokarin shiga cikin dakin Sarki Saif cikin sauri. Suka kara sauri har suka isa bakin kofar dakin.
"Assalamu Alaikum," suka yi sallama tare da tura kofar dakin suka shiga.
A lokacin, Rayyan yana tsaye jikin gadon yana gyara wa Sarki Saif bargon gadon, yayin da shi sarki Saif din ke cikin ban daki (*toilet*) yana wanke jinin da ya rage a jikinsa. Rayyan ya dago kai yana murmushi lokacin da ya ga Nazra. "Ah Dr. Nazra! Yanzu ma nake shirin tahowa ofishinki..."
Kafin ma Nazra ta ba shi amsa, Rayyan ya zubawa matar da ke kusa da ita idanu. Gaba daya lokaci guda jikinsa ya mace, idanunsa suka firfito waje cikin tsananin firgici da mamakin da bai taba zato ba. Ya bar abin da yake yi, ya nufi inda suke da gudu, idanunsa radau a kan fuskar Jannat!
A daidai wannan dakiƙar, kofar ban dakin ta bude. Sarki Saif ne ya fito, sanye da fararen kayan marasa lafiya da aka canza masa, fuskarsa da kansa daure da bandejin magani. Yana takawa da kyar saboda jikin sa da yaji ya fara mai ciwo Bayan dukan da yayi wa Malik, amma cikin sanyin jiki da sauri ya nufo inda su Nazra suke tsaye.
Yana isa gabanta, ba tare da wani bata lokaci ba, ya mika hannunsa guda biyu ya kama hannayen Jannat da karfi, yana mai matse su a cikin nasa. Wadancan idanuwansa na mulki nan da nan suka cika tabke da zafafan hawaye, suka canza launi suka yi jawur kamar garwashi saboda tsananin shauki da radadi.
"Laila...!" Ya ambaci sunan cikin wata irin murya mai ratsa kashi da rauni, wadda ta fito tun daga kasan zuciyarsa. Wasu zafafan hawaye masu dumi suka kwararo a kan fuskarsa.
Kafin ma Jannat ta sami damar fadin uffan ko fahimtar abin da ke faruwa, Saif ya jawo ta da karfi jikinsa, ya tura kansa a wuyanta tare da rungume ta tsam (*hug*) a kirjin sa, kamar wanda aka bashi kyautar rayuwarsa da ya dade yana nema. Falon ya dauki wani sabon sanyi, yayin da Nazra da Rayyan suka tsaya kallon abin al'ajabi.
đź’ťZUNUBIN UBA đź’ť
đź’ťNovel by secretwriter đź’ť