KAIFI ƊAYA

06

by @ummishatu1111

6



***Nuƙu nuƙu anty Mimi tayi ta faman yi ta gagara sakewa gaba ɗaya dan ko abinci ta kasa ci daga karshe dab da magriba ta fito daga part din Ammi ta nufi na hajiya bayan ta bar Ammin tana ta faman nanata maganar auren da aka daura musu ita da Afeef, haka kawai ta rasa me yake damunta dan jinta take yi gaba daya zuciyar ta babu dadi,

Lokacin da ta shiga part din hajiya babu kowa dan itama hajiyan tana cikin bedroom dinta ita da Irfan da Afeef, kai tsaye cikin bedroom dinta ta wuce bata ko leka hajiyan ba, zama tayi ta rafka uban tagumi ba tare da ta san abinda zata yi tunani ba har sai da taji an shiga salla a masallaci sannan ta iya tashi ta shiga tayi alwala ta fito, koda tayi sallar magriba anan wurin da tayi sallar ta cigaba da zama har lokacin sallar ishah yayi bayan ta idar ta shiga tayi wanka tana fitowa tasa sleeping gown ta kwanta duk ranta a bace,

Kiran da ya shigo cikin wayarta ya sake tunzurata amma sai ta kai zuciyar ta nesa ta dauki kiran dan ta san muddin idan bata dauka ba to haka zai cigaba da kiran ta babu ji babu gani indai Aliyu ne.

Bayan an idar da sallar ishah Afeef gida ya nufa batare da ya koma wurin hajiya ba daga nan waje suka yi sallama da Irfan ya tafi, yana zuwa gida tunda ya shiga part din mommy yake jiyo fadan da take yi kamar zata ƙone gidan,

"Afeef aka ɗaurawa aure da Mimi saboda mugunta da wulakanci? Duk family din naku a rasa da wanda za a daura mata aure sai da Afeef ? Saboda shi kadai ne namijin da ya rage a duniya ko me? Wallahi ba zan yarda da wannan zaluncin ba, wannan ai mugunta ce, yaro bai kai ya kawo ba a aura masa bazawara? Afeef din nawa yake.... "

Daidai lokacin Afeef ya shiga falon mommy wanda yake babban gaske komai yaji kuma ya dace da yanayin falon, suna zaune ita da Manal wacce ke bata hakuri, da kallo mommy ta bishi har ya samu wuri ya zauna yana kallon su,

" mommy lafiya? Me yake faruwa? "

"Dagaske ne an daura muku aure da mimi?" 

"ehh mommy dagaske ne...." 

"to uban waye ya bada izini aka yi hakan wanda yafi ni uwar da ta durkusa ta haife ka?" 

"mommy calm down..... Bafa abin tada hankali bane ko kuma abin damuwa...." 

"ni kake cewa wannan ba abin tada hankali bane Afeef? Ina matsayin mahaifiyarka har a daura maka aure kai da ubanka ku kasa fada min saboda ban isa ba? Sai yanzu Manal take gani a group dinku na family ana maganar...." 

"mommy wallahi wannan auren kawai dai kaddara ce...." 

"to ko abinda yafi kaddara zaka kirashi dashi wallahi bazan lamunta ba kuma bari daddy din yazo ai ina daidai daku daga kai din har shi..." daga haka ta tashi ta wuce cikin bedroom dinta dake sama, suka bita da kallo, Manal dawo da kallonta kanshi tayi cikin sanyin jiki tace, 

" yaya what's going on? Wai dagaske ne auren nan ko kuma prank ne?? Dan Allah ka fada min this is a prank.... "

Girgiza kai yayi yace "unfortunately this is not a Prank Manal, wallahi dagaske ne an daura mana aure da anty Mimi" 

"amma yaya Afeef meyasa? Me yasa zaka yarda a daura muku aure da ita?" 

"saboda ina son ta mana, ko an fada miki dole aka yi min?" 

"amma dai yaya ai ka san Janan kai take so shiyasa ta rinka rejecting din samari tana korarsu...." 

"ban son shirme fa..." daga haka shima ya tashi ya fita zuwa part dinshi cikin zuciyarshi yana addu'ar Allah dai ya huci ran mommy ta sauko daga wannan dokin fushin da ta hau. 

Bayan yayi shirin bacci har ya kwanta ya jiyo hayaniyar mommy da daddy tana tashi bayan daddy din ya dawo, tashi yayi ya saka silifas dinsa ya fita zuwa part din mommy din a ranshi yana cewa wannan shine kalubalenshi na farko dangane da aurensu da anty Mimi, tamkar kazar da ƙwai ya fashewa acikin ciki haka ya shiga cikin falon duk jikinsa a sanyaye,

"Daddy... Mommy..... Me yake faruwa ne? Cikin dare kuna hayaniya haka bai dace ba kowa dake cikin gidan nan yana jinku...."

"idan ka kuskura ka sake magana sai naci maka mutunci..... Bada kai aka hada kai aka munafurceni ba aka aura maka matar da ba sa'ar aurenka ba....." mommy ta faɗa cikin zafin rai,

"to ai ba auren dole aka yi masa ba ɗan naki, gashi nan ki tambaye shi kiji shine da kansa yace a aura masa ita yana son ta...."

Wani kallo mommy tabi Afeef dashi babu shiri yayi ƙasa da kansa daidai lokacin Manal ta fito daga cikin bedroom dinta sanye da sleeping dress idanuwanta cike da bacci,

" mommy dan Allah kuyi hakuri..... "

" wallahi ko sama da ƙasa zata hade ba zan taɓa yarda wannan auren ya dore ba ya zama dole kuma tilas a raba auren nan..." mommy ta fada cikin fushi kafin ta haye upstairs ta barsu tsaye nan kowannensu yana binta da kallo lokacin da take taka steps,

" Afeef jeka abinka ka kwanta.... Manal kema wuce kije ki cigaba da baccin ki.... "

" Daddy amma kamar mommy tayi fushi da yawa" Afeef ya faɗa cikin damuwa,

"babu komai zata sauko ka san halin mommynku ai... Tafi ka kwanta abinka"

Juyawa yayi ya fita itama Manal ta nufi bedroom dinta yayin da shi kuma daddy yabi mommy zuwa upstairs, tamkar mommy zata fashe dan tsabar bakin cikin da take ciki a haka Daddy ya shiga ya sameta, cikin zafin rai da jin haushi ta juya ta kalli Daddy,

"wai meke damunki? Yanzu fa mun wuce wannan lokacin da zamu zauna muna musayar yawu a gaban yaranmu, daga Afeef har Manal duk sun girma babu karamin yaro yanzu a cikin su, dan Allah ki rinka sassautawa ranki...."

"haka zaka ce? Iyakar wannan kadai zaka ce? Ohh yanzu gaba daya laifin ma ka dauka ka ɗora a kaina kenan.... Yanzu laifina kake gani kamar nice na kirkiri matsalar ko..... Taya za ace ɗana ƙwaya ɗaya tal a daura masa aure da yarinyar da ba budurwa ba wadda ta girmeshi kuma ba tare da amincewa ta a matsayina na mahaifiyarshi ba..... "

" kiyi hakuri duk wannan ba abun tada hankali bane, kiyi musu addu'a kawai ta fatan alkhairi..... "

Shuru yaji tayi bata sake tanka masa ba saboda bakin cikin da take ciki ji take kamar ta hada su gaba ɗaya ta rufe da duka. Zuciyar Afeef cike da damuwa ya koma cikin part dinsa ya zauna gefen gado, wannan shine kalubale na farko da ya fara fuskanta ya ayyana hakan cikin ransa, ya jima idonsa biyu kafin ya samu bacci ya dauke shi wanda bashi ya farka ba sai bayan asuba, wani baccin ya sake komawa har sai da rana ta fito, brush kadai ya iya yi ya fita zuwa part din mommy sakamakon yunwar da yake ji kamar me,

Mommy ce kadai cikin falon tana marking scripts kasancewar yau weekend ne tana gida bata fita ba amma sai dai fuskar ta kadai idan ka kalla zaka fahimci ranta a mugun ɓace yake, ya san mommy tana da zafi sosai kuma mace ce mafadaciya wadda bata da hakuri ko kadan,

"mommy ina kwana....."

"lafiya..." daga haka bata sake kula shi ba taci gaba da aikinta ba tare da ta ko kalleshi ba, shi dai dan gatan mommy ne kowa ya san wannan amma kuma yanzu ya san dole mommy ta canja masa saboda wannan abun da ya faru, zama yayi a ƙasa kan rug ɗan nesa da ita kaɗan kafin yace,

"mommy dan Allah kiyi hakuri...... Na san na ɓata miki rai kuma tun farko ya dace in sanar dake maganar auren mu da anty Mimi, na san nayi laifi kuma ban kyauta ba amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe min....."  shuru yaji tayi masa bata amsa ba ahaka har ya gaji da zama ya tashi ya ƙarasa kan dining ya zauna kunu da ƙosai ya zuba yaci ya tashi ya fita zuwa part dinsa yana tambayar kansa to wai ma wacce kaddara ta aike shi yaje yayi wannan auren?

" tsautsayi....." ya fada a cikin zuciyarshi, ajiyar zuciya ya sauke ya shiga cikin toilet yayi wanka ya fito, gaba daya ji yayi zaman gidan yayi masa kunci shiyasa kawai ya dauki motar sa ya fita, sanye yake cikin bakaken kananan kaya jeans da t shirt a gaban rigar tashi an rubuta Trust, can wurin da babu kowa ya tafi yaje yayi zamansa shi kadai cikin mota bayan ya saka wayar shi a flight mood da yaga lokacin salla ya yi ruwa ya dauka daga cikin boat dinshi yayi alwala ya dauki prayer mat ya shinfiida kasan bishiya yayi sallar shi yaci gaba da zama a wurin har la'asar sai lokacin ya tashi ya shiga motar sa yabar wurin ya nufi family house, yana zuwa ya samu yaya Aliyu tsaye kamar dama shi yake zaman jira, parking yayi ya fito yaya Aliyu ya mika masa hannu suka yi musabaha kafin yaji Aliyun yace,

"Afeef ina fata ka fara lissafi saboda bana son ku wuce 3 weeks zuwa 1 month....."

"babu problem yaya Haidar Allah ya nuna mana lokacin....."

"yawwa na gode Afeef.... Ban san irin godiyar da zanyi maka ba"

"Babu komai yaya, we are one family...."

Fitowar yaya Faruk da Irfan tasa suka bar maganar, kallon Afeef Irfan yayi yace,

"yau ina ka shiga ne wai wayarka bata tafiya...."

"na yi bacci ne..."

"to zo muje ciki..." binsa yayi zuwa ciki bayan sun gaisa da yaya faruk wanda yake kallon Aliyu cike da mamaki saboda a iya sanin sa Aliyu yana da masifar zafin kishi da kuma riƙo musamman akan Mimi shiyasa duk wanda yayi yunkurin zuwa wurinta da sunan yana son ta to fa masifa ce take tashi daga wurin Aliyu amma yau gashi abin mamaki Afeef ya aure ta baiyi musu wannan haukan ba, gaskiya bai taba kawowa zai ganshi haka ba ko cikin mafarki,

"Aliyu wai ni abinda yake bani mamaki sai naga kamar baka damu da auren mimi da Afeef ba, anya kuwa Haidar din da na sani ne mai zafin kishi......."

Dariya Aliyu yayi ya mikawa Faruk hannu yace,

"to ya zanyi faruk, Afeef ai kanina ne dole banida yadda na iya dashi, da dai wani ne bashi ba sai in tada bore....."

"gaskiya ka kyauta, kuma naji dadi da ka gane hakan har ka sassautawa zuciyarka ka cirewa kanka damuwa, life goes on..... Just move on....."

"yes I moved insha Allah faruk...."  runfa suka nufa wacce ke dauke da kujeru a cikinta suka zauna suna cigaba da tattaunawa kamar yadda suka saba. 

Anty Mimi tun bayan da ta shiga cikin bedroom dinta jiya bata sake fitowa ba Hajiya tayi mitar tayi mitar har ta gaji ta ja bakin ta tayi shuru,ko breakfast da lunch ma sai cikin dakin aka kai mata, lokacin da Afeef suka shiga part din hajiyan samu suka yi tana tambayar Hajjo daya daga cikin yan aikinta, 

"ita wannan gimbiyar ko sarauniya zan kira ta dashi ne ban sani ba ta ci abincin da ake kai mata??" 

"wallahi hajiya ban sani ba sai dai ko idan zuwa za ayi a duba...." 

"rabu da ita tayi ta kare ƙalau...." 

Bayan Hajjo ta fita Irfan ya kalli hajiya yace "wacece?" 

"Amarya mana, ban sani ba ko amarcin ta fara tun jiya dai da ta shiga ciki bata sake fitowa ba..." 

"kuma lafiya lau take?" Afeef ya bukata yana kallon hajiya, 

"to ni ina zan sani ne, ni da ban ganta ba" 

"ina zuwa..." ya fada kafin ya mike ya fita zuwa bedroom dinta dan jiki da jini sannan yau da gobe sai Allah, a bakin kofa ya tsaya yayi knocking tana zaune kan gadonta da laptop a gabanta tana wani research.......