ZUNUBIN UBA

TSORON DA BAI MUTU BA

by @secretwriter

💝ZUNUBIN UBA💝

Novel by secretwriter 💝

Sarki Saif yana zaune a kujerar baya ta motar da ke fita da shi daga harabar asibitin, idanunsa suna lumshe yayin da yake jin raɗadin raunukan jikinsa. Karan wayar hannun Zahir dake zaune a mazaunin direba ya ratsa shurun motar. Zahir ya duba wayar sannan ya kalli madubin tsakiya don satar kallon Saif. "Oga... Lamarin ya sauya salo. Yanzu nan saƙon ya zo min cewa Judge Luca ba ya ƙasar nan gaba ɗaya, ya fita zuwa wani taron sirri na shari'a. Kuma abin da mamaki, duk da na riga na samu appointment ɗin zama da shi, amma an soke shi."

Saif bai buɗe idanunsa ba, sai dai wani murmushi mai cike da haɗari ya gitta a fuskarsa. "Hmmm... A.A Rumfa ya fara taɓa sassan da bai kamata ba kenan. Mu koma cikin asibitin."

A can babban dandalin cin abinci na makarantar su Noor (Cafeteria), surutu da hayaniyar ɗalibai sun cika wajen. Noor ce ta shigo cikin takun isa, tana raba idanu har sai da ta hango Faris Al-Kaseem zaune a can kusurwar tebur na ƙarshe shi kaɗai. Cikin natsuwa da sanyin jiki ta taka har zuwa gabansa.

"Sannu dai... Sunana Noor," ta faɗa tana tsaye tare da gyara hular hijabinta na alfarma.

Faris ya ɗago kai ya kalle ta da idanuwansa, ya gyada kansa cikin ladabi. "Ehh... Na gane ki, ai class ɗinmu ɗaya." Noor ta kalli saman teburin, ta ga biscuit na naira hamsin da robar lemo dake gabansa. Nan da nan ta murtuke fuska, ta kalli mai sayar da abincin wajen tare da ɗaga murya cike da steeze. "Kai! Baya cikin matsayi na da aji na ace ɗalibin ajinmu yana cin wannan abun a gabana. Kawo masa dukkan mafi tsadan abinci da lemon da kuke da shi a wajen nan, yanzu ɗinnan zan biya komai!"

Faris ya zuba mata idanu cikin tsananin mamaki da rashin fahimtar irin wannan nuna isa, amma bai ce uffan ba har aka kawo haɗaɗɗen abincin, suka zauna suka ci. Bayan sun gama, Faris ya miƙe ya yi mata sallama ya tafi aji.

Kafin ma ya ɓace, ƙawayenta Aliya da Nahad suka rugo da gudu suka dawo kusa da ita, fuskokinsu cike da tsananin mamaki da son tsegumi. Nahad ta dafe ƙirji, "Yanzu Noor, don Allah kinsan nawa kika kashe a kan abincin wannan yaron yanzu nan kuwa? Wlh kuɗin sun yi yawa!"

Noor ta taɓe baki cikin shaƙwaba ta ƙwace jakarta, "Ban sani ba, kuma hakan bai dame ni ba. Amma dai na sani cewa kashe kuɗi a kan wanda kake so... ai ba laifi ba ne gaba ɗaya!"

Aliya ta turo baki, ta harare ta. "Tunda ba kuɗinki ba ne da kika samu da kanki ba, shi yasa zaki ce ba laifi ba ne! Amma ta yaya zai kasance mace ce zata rinƙa kashe wa namiji kuɗi a cikin makarantar nan? Ina ajinki ya tafi?"

Noor ta tsaya ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, ta sanya hannu a kwankwaso cikin takun isa da barkwanci. "Ehh! Naji ba kuɗina ba ne, amma kuma ina da waɗanda suke bani kuɗin, kuma a shirye suke su narkar min da dukiya a kowane lokaci! Idan har su ba su kashe min ba, wa kuke so ya kashe min? Nima kuma idan ban kashe wa Faris ba... wa kuke tunanin zai kashe masa a makarantar nan?" Ta faɗa tana musu fari da idanu, wanda ya sanya Nahad da Aliya haɗa baki wajen sakin salati saboda halin Noor na nuna iko da girman kai na ban dariya.

A can harabar asibitin kuma, Barrister Jannat ce ke takawa da sauri tana shirin fita daga asibitin bayan ta bar ofishin Nazra. Ba zato ba tsammani, tana daidai wani lungu na ɗakin jiyya, ta ji an janyo ta da ƙarfi ta baya. Kafin ta sami damar yin ihu, aka sanya mata takunkumin rufe fuska na asibiti (Face Mask) wanda ke ɗauke da wani irin magani na sanyaya jiki.

Gaba ɗaya idanunta suka fara dishi-dishi.mutanen  da ta gani da ƙyar ta cikin duhun idanunta... mutane ne daban sanye da fararen suit na alfarma, har da mata a cikinsu. Abin da ya fi tsoratar da ita shi ne, hular kowannensu tana ɗauke da zanen Zaki na zinari a jiki. Suka rinƙa tafiya da ita cikin wani irin salo na tsari da kariya, suna kare ta kaɗan-kaɗan daga kowane ɓangare kamar wata shugabar ƙasa. Duk wanda suka gani da baƙaken kaya zai zo wucewa ta layin, sai su canza mata hanya cikin dabara.

Haka aka shigar da ita ɗakin tiyata (Theater Room), aka cire mata suturarta aka saka mata kayan ɗakin tiyata na kore. Jannat tana ta fizge-fizge tana kuka da muryar raki, amma babu tausayi aka danna mata allurar bacci mai ƙarfi a gwiwar hannunta. Cikin daƙiƙoƙi kalilan, duhu ya gauraye komai, bacci ya yi awon gaba da ita.

Bayan wasu sa'o'i, Jannat ta fara buɗe idanunta a hankali. Hasken rana ya dake ta, sai ta tsinci kanta a zaune a kan kujerar guragu (Wheelchair) daidai ƙofar fita ta asibitin. Abin da ta gani ya sanya jikinta rawa da tsoro; fararen motoci na alfarma masu sulke (Bulletproof) sun zagaye su, dukkan ma'aikatan tsaron dake tsaye sanye da fararen kaya da gilashi sun bada baya suna jiran umarni.

A can gida kuwa, mahaifiyarsu Jannat Hajiya Jawahir ce ke ta kai-da-kawowa a tsakiyar falon gidan, fuskarta ɗauke da tsananin damuwa. Larai, mai taya ta aikin gida, ta leko daga ɗakin girki tana kallon mahaifiyar tasu. "Hajiya lafiya kuwa? Tun dazun na ganki kin kasa zama guri guda."

Hajiya Jawahir ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, "Larai... Har yanzu Jannat ba ta dawo ba fa! Kuma kinsan halinta, ba ta taba kaiwa wannan lokacin ba tare da ta shaida min ba. Na kira wayarta sau babu adadi amma a kashe take gaba ɗaya. Har Nazra na kira ita ma ban same ta ba. Ban san me ke faruwa ba, na san ba halinta ba ne kashe waya."

A daidai wannan lokacin a asibiti, Jannat ta yi amfani da dukkan ragowar ƙarfinta ta miƙe tsaye daga kan kujerar guragun, duk da yadda ƙafafunta ke rawa saboda tasirin allurar baccin da bai sake ta ba gaba ɗaya.

Ta jefa idanuwanta cikin mutanen, sai ta hango Sarki Saif tsaye, sanye da baƙaken kaya, yana kallonta cikin natsuwa. Jannat ta tako da ƙyar har zuwa gabansa, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta. "Meye hakan?!" Ta faɗa cikin muryar kuka mai ratsa zuciya. "Ko saboda na mare ka ɗazun ne ya sanya kake son nuna min iko ta hanyar hukunta ni da kisa? Me na yi maka?"

Saif ya matso kusa da ita kaɗan, fuskarsa babu alamar wasa. "Bani da niyyar kashe ki, Barrister Jannat. Taimakonki nake son yi a halin yanzu. Yau da a ce ban bada umarnin a baki wannan tsauraran kariyar ba... da tuni makiya sun riga sun kawo ƙarshen rayuwarki a cikin asibitin nan."

Jannat ta saki wata dariyar takaici da daci, ta girgiza kanta tana goge hawayenta. "Na mutu kuma? Ƙarya kake yi! Kai ne ma kake son kashe ni da kanka!"

Saif ya ƙara matsowa kusa da ita sosai, har tana iya juyo dumin numfashinsa mai sanya fargaba. "Nan da kwana biyu ki shirya... zamu je gaban kotu domin shigar da wannan babban ƙarar. Amma ki kwantar da hankalinki, ba shari'ar za a fara yi kai tsaye ba. Akwai wani babban aiki na sirri da zamu fara gudanarwa kafin mu taka kofofin kotun."

Jannat ta ja da baya da gudu, tana kuka sosai cikin tsananin rauni da firgici na baya. "Ba zan yi ba! Wallahi bani da wani buri ko sha'awa a kan wannan shari'ar taka! Ka tafi ka nemi wata lauyar amma ba ni ba!"

Saif ya zuba mata idanu, muryarsa ta koma ƙasa-ƙasa. "Haba Barrister Jann... Dole ne fa zaki yi min wannan aikin."

Jannat ta dakatar da shi cikin wata irin muryar tsawa mai cike da kuka da raɗadi dake fita daga can ƙasan ranta. "Koda kuwa zaka tilasta min, wallahi na tsane ka! Iya yau kaɗai... dukkan wahalar da mutanenka suka bani ba zan taba yafe maka ba! Can you imagine... har ɗakin tiyata (Theater Room) suka shigar da ni da ƙarfi! Na tsani ashibiti a rayuwata! Idan kaga na shiga asibiti, to rashin mafita ce ta ƙarshe ke kaini! Ba na son a saka min kayan ashibiti bare har na tsinci kaina a kan gadon asibiti... Amma yau saboda kai, ba ma gadon ashibiti na hau ba, a kan gadon tiyata na farka!" Ta faɗa tana durƙushewa a ƙasa, tana kuka mai ban tausayi.

Saif yana kallonta, nan da nan tunani ya ziyarce shi. Ya fahimci cewa har cikin zuciyarta take faɗar wannan maganar, akwai wani mummunan abu na baya (trauma) da ya taba faruwa da ita a asibiti ko a ɗakin tiyata da ya sanya take tsanar kowane tsarin asibiti a rayuwarta.

Wani sanyayyan murmushi ya sake yi, ya matso kusa da ita sosai har tana iya jin bugun zuciyarsa. "Barrister Jann... Tun kafin ma mu fara ainihin aikin namu na gaskiya, har kin riga kin tsane ni haka? Ba kiyi gaggawa da yawa ba kuwa?"

Jannat ta ɗago da sauri, ta tura ƙirjinsa da dukkan ƙarfinta. "Ka fita daga rayuwata, ɗan iska kawai!" Ta fizge jakar hannunta dake riƙe a hannun Rayyan, ta juya da sauri ta shiga motarta ta bar harabar wajen da gudu.

Saif ya bi bayanta da kallo na wasu daƙiƙoƙi, sannan ya juyo ya kalli Rayyan, ransa a haɗe. "A tsara mata kariya mafi inganci da ta dace da rayuwarta... amma kar a kuskura a bari ta gane hakan."

💝ZUNUBIN UBA 💝

Novel by secretwriter 💝