Chapter 2
KUKAN ZUCI.....🥲*
*2026*
nanamaryama
*Free book*
*Page 3&4*
Ya ce "mama nayi maki alƙawari zata warke in sha Allah"!
Ohh Allah ya taimake mu dai abinda muke fata ya kasance É—in ÆŠan nan' mungode Allah ya saka da alheri...
Kidaina godemin saboda kin zama tamkar uwa a gareni ina jikin kamar "Ummi na ne shine dalili kinga ko ai ba zaki gode ma ÆŠan ki ba sai dai ki bashi umarni ko Mama?''
Haka ne kam "Muhammad Allah ya maka albarka ta faɗa tare da goge ƙwallar dake idonta "....
Magungunan aka ɗaura ta saboda cutar batai tsanani a jikinta' Alhamdulilah tana samun sauƙi ba laifi tunda yanzu zata ji alamar tana jin fitsarin sakamakon a baya bata ji sai dai taga tana yin sa!
Zaune take hannun ta ɗauke da kofi sai maganin dake hannun hagu ta riƙe taki sha......a karo na uku Mama ta ce" Humaira ya kamata ki maida hankali ki sha fa haba kinfi minti 30 riƙe da abu ko sai na ɗura maki ne?''
Uhmm "Mama wallahi maganin ÆŠaci ne dashi Allah nagaji da sha ta idasa faÉ—a tare da zuba maganin cikin bakin ta tana ya mutsa fuskar ta''
Minti uku da gama shan maganin Dr ya shigo hannun sa É—auke da kular abinci sallama É—auke a bakinsa yana zama kusa da Mama.....da murmushi ta amsa mashi tare da faÉ—in ina su Hajiya?
Alhamdulilah tana gaida ku' tace gashi ya faɗa tare da miƙa mata kular da ya shigo da ita....... A'a wannan daɗi haka Muhammad ina zamu kai shi hidimar zatai yawa fa Allah, ga ɗawainiyar asibiti ga ta abinci da yawa abin ai...
Ai kaganta nan yanzu muka gama diramar shan magani da ita!
Kallon ta yai tare da faÉ—in tunda baki san magani duk zan mai da makisu allura kawai....
A'a yaya don Allah 🥲zan ci-gaba da sha daga yau abani wani ma nasha yanzu ' zan sha dagaske nake maka yaya tana maganar tana kuka kamar wadda aka ce an mata mutuwa!
Daga shi har Mama dariya suka mata tare da mata woning idan har bata san allura dole ta rinƙa shan magani kam..
★★
★
★★
Agogon da ke manne a bangon ne ya buga ƙarfe biyu na dare tana zaune kan dadduma ta gama sallah, tare da addu'ar Allah ka shirya "Yusuf shi da mahaifinsa a kan abinda suke su gane ba dai-dai bane" fatan dai su gane gaskiya gaskiya ce karya karya ce, lazimi take Kofar Palo ɗin aka turo tana zaune tana kallo dai Yusuf ne shi da abokin sa ya sha yai makas abin shi har ya kasa gane gida shi ne ya shigo dashi' da sauri ta tashi ta kamo hannunsa tare da faɗin innalilahi wa'inna ilaihir raji'u Allah ka kawo mana mafita a cikin rayuwar Yusuf Allah!
Cikin magagin giya ya ce" Dalla malama ki mana shiru da wannan mugun bakin naki haba".
Kwantar dashi tai kan kujerar Palo ɗin, shi kuma abokin nasa ya miƙa mata mukullin motar shi ya mata sallama, zama tai kusa dashi tana mai share ƙwallar bakin cikin da take kwasa na wannan yaron, da mahaifiyar sa na raye hakan dai tasan dai bazai faru ba a fili ta furta Mahaifin ka ya lalata maka rayuwa wallahi Yusuf ta idasa faɗa tare da komawa sama daman shi take jira ya shigo ta kwanta!
*Washe Gari*
Ƙarfe 9:30 ya farka daga a sararan barcin da ya yi babu addu'ar tashi daga barci a bakin sa haka ya miƙe wayar sa ya fara laluba ya gani miss call din sama da goma ya gani a wayar, dubawa yai tare da yin tsaki ya maida ya aje tashi yai da niyar ya hau sama zuwa ɗakin sa.......... Hajiya da take sanye cikin farin hijabi a jikinta ta ce" Yusuf har ka tashi ga break fast ɗin ka can kaje kayi ni zan fita anguwa sai na dawo"
Kallon ta kawai yai tare da faÉ—in naji ya ya idasa hawa benen, É—akin shi ya shiga kai tsaye wanka ya shiga kan shi ya sakar ma ruwa sannan ya fito ba tare da ya yi alwala jallabiya yasa tare da sakkowa dealing table É—in ya fara break fast É—in hankali kwance...
Minti 40 ya É—auka sannan ya gama ya dawo palon ya kunna TV Bollywood ya kai ya ci-gaba da kallo, Yusuf mutum ne mai san sharholiyar duniya ba ruwan sa da Sallah ma sai lokacin da yaga dama yake yinta!
Kamar kullum da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana ya fito cikin shirin shi na fita daman yau suna da birthday ɗin wani abokin sa, sanye yake cikin amless fara da gajeren wando baƙi ita ma hular kan shi baƙa takalmi fari agogon hannun sa fari' idanun sa sanye suke cikin farin glass ya haɗu iya haɗuwa motar shi ya shiga a kan hanya ne ya haɗu da wata yarinya bazata wuce 16 to 18 ba, yai maganar duniyar nan amma tai banza dashi a Cikin zuciyar sa ya furta tun da dai ina san nasan zumar ki tabbas sai naji ko da yardar ki ko akasin haka ya kada motar yai gaba saboda yaga gidan da ta shiga irin na ya mu bayin nan, da isar sa wajen gu ya canza da Wakar saboda wasa shi za'ai domin ya saki kuɗi.....
Bayan kwana biyu' ta samu sauƙi sosai ba laifi ba kamar yadda aka kawo ta ba ta ce"Mama yaushe zamu tafi gida ne wai?''.
Humaira ba yanzu sai kin kuma samuwa ko da zamu tafi dai...
Lah "Mama na warke fa da gaske' kalli kiga fa yadda na koma ba kamar da ba Allah Mama nidai nagaji da zaman asibitin"
Tunda take maganar"Mama" ta saki baki lokacin da aka kawo ta asibitin bata san Inda kanta yake ba shine yanzu take maganar nan' ta ce a'a lalle ƴar nan kin samu Allah ya ƙara sauƙi..
★
Sai wasa Yusuf ake{Suf} yana ta zubar da Naira yake ga Æ´an mata kowacce ribibin shi ' Saboda kuÉ—in shi suke san shi.....ya amshi speaker É—in ya ce" da yawan ku saboda kuÉ—i na kuke so na' na sani don haka ni bana amfani da maccen da tasan maza da yawa, nine zan fara amfani da ke sannan wani ya sanki gaskiyar labari kenan idan kinsan ke second hand ce' to please ja please ki rungumi sorry madam!
Wata daga cikin su da bazata wuce shekara sha tara ba' sanye take cikin doguwar riga pink sai baƙin gyale da tasa da takalmin ta Pink tai matuƙar kyau da wayar ta a hannu ta fito cikin filin tare da shewa irin tasu ta ƴan duniya ta ce" kenan dai suf na jawahir mahi ne ƴan mata sai kubada hanya!
Kallon ta yake sama da ƙasa tai bala'in ƙyau kamar me a cikin zuciyar sa ya ce" come my baby girl ya faɗa tare da idasa wa kusa da ita''........ duk ƴan matan gun suka kama jin haushin tambayoyi ya mata ta amsa daga nan ne ya ce daga yau Jawahir mahi ta zama tashi...
Sai a kasa buÉ—a mata tare da canza sauti zuwa na masoya!
Ta ce.........
Contuie
Please idan kin karanta don Allah ki share fisabidillahi Æ´ar uwa littafin KUKAN ZUCI paid book ne 500 special group 1k ne amma a arewapen Free ne idan kin fallow É—ina ba