HAULA HABEEB

BABI NA TAKWAS.

by @amdeeytejjdunique587

BABI NA TAKWAS

Hibba

“Hibba, wai me yake faruwa ne, har ana batun gobe kamu, amma har yanzu ba mu ga idon ango ba balle abokansa. Gaskiya da sake! Kin ga Malama ki ba mu lambar shi mu kira shi.” Wata daga cikin ƙawayen amarya ta faɗa, don abin ya dame ta. Ta yaya za a ce tunda aka shiga satin biki suke tare, amma ko ƙyallin angwaye ba su gani ba?

Wani banzan kallo Hibba ta wurga mata. “Ke, ’Don uwarki wurina kika zo ko wurin angwayen?” Ta yi maganar tana harararta haɗi da banka mata ashar kamar yadda suka saba.

Dariya suka kwashe ita da sauran ƙawayen. Cikin haɗin baki suka ce, “Ai dukkanmu nan da kike gani tambayar da ke bakinmu kenan. Shiru kawai muka yi muna saurare.”

“Ai ko sai dai ku yi ku gaji, don wallahi sai dai ku gan shi idan kun kai ni ɗakinsa. Dama saboda irin ku na ɓoye shi.” Daga haka ta miƙe ta yi waje don Mom tana kiranta.

Ita ma a wani ɓangare abin yana damunta. Soyayyar Habeeb ce kawai ke ɗawainiya da ita, da wallahi ba ɗan iskan da isa ya sa babbar yarinya kamar ta a yi mata wannan wilaƙancin ta yarda. Amma shi ma ɗin zai shigo hannu ne, bari dai a yi auren. Wannan ai ba abu ne mai wuya ba. Tana wannan tunanin har ta iso, ba ta yi knocking ba ta tura ƙofar ta shige ɗakin.

“Wai har yanzu Habeeb ɗin bai zo ba?” Tambayar da Mom ta yi wa Hibba kenan bayan ta shiga ta zauna a bakin gado inda Mom ɗin ke zaune.

“Bai zo ba,” shi ne kawai amsar da ta ba ta.

“Taɓɗi jam! Ai ko ba zai yiwu ba, bari in kira su. Sai ka ce akuya zan ba shi, da zai ce zuwa kawai zai yiya ɗauka. To ko akuya ce sai ya zo mun yi ciniki, balle mutum sukutum. An gaya masa kwantai ki ka yi. Na tara mutane, kowa sai tambaya yake, ina ango da abokansa?”

“Hmmm, magulmata dai. Idan ba haka ba ina ruwansu? Dama idan ana aure, ango tarewa yake yi a gidan su amaryar halan, shi ya sa da ba su gan shi ba suke wannan maganar.” Miƙewa ta yi ta nufi ƙofa.

“Ni fa Mom, ki raba ni da maganar wannan ƙawayen naki.” Daga haka ta buɗe ƙofar ta fice da abunta.

Da kallo ta bi ta har ta fice, kafin ita ma ta miƙe ta fito cikin nata ƙawayen aka ci gaba da sha’ani, don ta yi gayya sosai. Tunda aka shiga satin auren take amsar baƙi har zuwa yau.

Habeeb

Aka turo ƙofar office ɗin ba tare da an nemi izini ba. Kamar yadda ya zama al’adarsa, bai ɗago ba balle ya ga wane ne. Aikin gabansa kawai yake yi, bai ko nuna alamar ya san an shigo ba.

Kuka ta fashe da shi mai ƙarfi, ta ƙaraso inda yake, a jikinsa ta yi niyyar faɗawa. Kallon da ya yi mata ya taka mata burki. A gabansa ta tsaya, kuka kawai take yi, kai ka ce saƙon mutuwar ubanta aka aiko mata.

Ƙala bai ce mata ba, sai barin aikin da ya yi ya jingina da jikin kujerar. Ya lumshe ido yana sauraron yadda kukan nata ke ƙoƙarin hargitsa masa tunani.

Sai da ta yi mai isarta don kanta ta yi shiru. A gabansa ta durƙusa, ta fara faɗin, “Habeeb, me na yi maka? Me ya sa ka tsane ni? Ka san cewa ina sonka. Ashe saboda kana da wacce kake so shi ya sa kake min wulaƙanci? Menene aibuna? Me na rasa? Ka faɗa min abin da ba ka so a tattare da ni.” Ta ƙara sautin kukan nata, tana mai ɗora kanta a kan gwiwarsa.

Dafe kansa ya yi, don duk kukan nata ya ishe shi. Can cikin wuya, kamar an tilasta masa, ya ce, “Kina damuna.”

Sassauta kukan ta yi kamar rarrashinta ya yi, ko da yake ita a wajenta ai abin farin ciki ne, don ita ji ta yi ma kamar rarrashinta ya yi. Sau nawa za ta zo wurinsa, amma har ta gama zamanta ta tafi bai ce mata kanzil ba? Shi dama ba ya tozarta mata masu cewa suna son shi. Amma da kanki idan kika ga babu fuska, za ki yi wa kanki ƙiyamul layli. Masu tsaurin ido ne ma irinta ke zuwa inda yake har su furta. Wasu kuma sai dai su yi ta rara-gefe. Indai ya ga za ki ke yi masa naci ne, securities ɗinsa ma sun ishe ki. Amma ita wannan, tsabar naci irin nata, ba wulaƙancin da bai yi mata ba, amma ta ƙi haƙura. Dole ta sa ya rabu da ita, ba don ya ji zai iya ko da abota ne da ita ba.

Sai da ta sassauta kukan kafin ta ce, “Babe! Please, me kake so? Me na yi maka da ba za ka iya aurena ba? Me na rasa da ba za ka iya aurena ba za ka zaɓi wata? Bayan ka san irin son da nake maka.” Wani sabon kukan ya sake bijiro mata.

Kau da kai ya yi gefe, don ta ba shi tausayi. Bai so a ce ta kamu da soyayyarsa har haka ba, don shi bai taɓa sonta ba. Ba ya so kuma a ce wani ya cutu saboda shi, bai ji daɗi ba. Ita ba ta san ita wannan matar ma shi bai santa ba. Da ta kwantar da hankalinta, ga shi shi ba rarrashi ya iya ba.

“Ki je gida,” kawai ya iya furtawa.

Zunbur ta miƙe. “I don’t understand, in je gida? In koma in zauna, ba ni da makoma. Haba Habeeb, me ya sa ka tsane ni?”

Bai sake ce mata komai ba, ya mayar da hankalinsa kan aikin da yake yi, ba tare da ya sake bi takanta ba.

Hawayenta ta share, kafin ta ce, “Na san abin da zan yi.” Jakar hannunta ta sauke, ta warware mayafinta ta yi wurgi da shi. Ta zage zip ɗin doguwar rigar da ke jikinta, ta sake shi ya sauka ƙasa. Sai da ta koma haihuwar uwarsa, ta nufe shi.

Hankalinsa ya yi gaba a kan abin da yake yi, shi duk ya zaci ma ta tafi. Bai yi awo ba, ya ji an shafa fuskarsa, kafin ya ɗago ya duba abin da ke shirin faruwa. Ta kai hannunta inda bai zata ba.

Cak! Ya riƙe hannunta. Kallo ɗaya ya yi mata, ganin yanayinta ya kau da kai. Bai ɓata wata-wata ba kuwa, ya bi ta da wani lafiyayyen mari da ya sa ta hantsila gefe guda. Wani irin zuciya ta ciyo shi, ya miƙe tsaye ya yi ball da ita daga inda take kwance. Da sauri da kuma ƙarfi, sanin waye shi ɗin, ya taɓa ƙarar rawar emergency da ke kan teburinsa fiye da ƙa’ida. Daga haka ya faɗa bathroom ɗin office ɗin, ya rufa ƙofar da ƙarfi.

Salim

Ya sake kiran wayar a karo na biyu, cikin sa’a ya ɗauka.

“Dude, where are you?” ya tambaya bayan an amsa daga can.

“Wa’alaikumussalam,” ya faɗi.

Ya fesar da iskar bakinsa. “Oh! Sorry, Assalamu alaikum.” Sai da ya amsa kafin su ci gaba da magana.

“Ya ake yi?” Habeeb ya faɗa daga can, a lokacin yana fitowa daga gidan marayun nasa, gidan da yake zuwa duk lokacin da ransa ya ɓaci. A wannan gida ne kawai za ka samu Habeeb cikin yara yana wasa da su. A nan kaɗai za ka ga Habeeb yana dariya har haƙoransa su fito.

“Kana ina?” Salim ya sake tambaya.

Sai da ya zauna a motarsa, ya connecting Bluetooth ɗinsa bayan ya ɗaura sit belt, ya ɗauki hanya motar ta fara tafiya, kafin ya amsa da, “I am on my way getting back from the orphanage. I went to visit them. Any problem?” Ya tambaye shi bayan ya amsa.

“Yeah, akwai matsala. Wai dama ba ka je gidan su yarinyar nan kun gaisa ba, har yanzu?” Ya yi shiru yana jiran amsarsa, amma shiru. Duba wayar ya yi, ya ga ko yana kan layi ko ya katse ne, yana nan da kiran yana tafiya.

Sake mayar da wayar kunnensa ya yi. “Kana jina?” ya tambaya don a tunanin ko network ne ya riƙe.

Kamar bai ji abin da ya ce ba, ya ce, “Yeah, ina jinka. You said there’s a problem, ina jinka ka faɗa.”

A yanzu ya fahimci yana jin shi, rainin hankalinsa ne ya motsa. “Yanzu kana nufin ka ce ba ka ji abin da na ce ba bayan nan? Dude, ka ji tsoron Allah. Don ba ka son yarinyar nan ba, shi yake nufin ka wulaƙanta ta ba? Tunda ka yarda za ka aure ta. Ina guje maka haƙƙi fa. Kar sai bayan an yi auren ka kamu, irin kamuwar...” Ɗutt! Ɗutt! Ɗutt! Ɗin da ya ji, alamar an katse wayar, ne ya sa shi bin wayar da kallo sororo cike da mamaki. Ya san ko ya kira shi, ba ɗauka zai yi ba, shi ya sa bai ba kanshi wahala ba. Shiga motar ya yi ya nufi gidan Anti Ummi.

Abokansa biyu, waɗanda tare suke shirye-shiryen bikin, ya ɗauka. Su suka wakilci ango da abokansa. Ya san Habeeb ba shi da wasu abokai da za su wakilce shi a garin, ba don ba shi da abokai ba, sai don ya yi watsi da su tun suna bibiyarsa har suka gaji. Tafiyarsa Turai ta sa ya ƙara nesanta da abokan. A yanzu idan ya kira su za su zo, don suna son abota da shi, sai dai shi ɗin ne sai a hankali. Mutanen da zai iya kira da abokan Habeeb, yawanci a yanzu ba sa ƙasar. A yanzu hukuncin da ya yanke shi ne, nemo abokansa na nan a yi komai da su.

Zuwan Salim ya yi wa Hibba daɗi, don ya fitar da ita kunya a cikin ƙawayenta. Ko ba komai, yanzu dai bakinsu zai mutu. Sannan ya ba su kuɗi da kuma haƙurin rashin zuwansu a kan lokaci. Ya kuma ce gobe za a kawo mata rigar da za ta sa a dinner ɗin da suka shirya. Ya yi mata alƙawarin zuwan kamun da za su yi anjima kuma. Ta ji daɗi sosai, ba kaɗan ba.

Kamar yadda ya yi alƙawari, ya je ya nemo abokan Habeeb, kuma sun ce za su zo a yi komai da su. Ba abin da ya ba shi mamaki sai da ya ga ashe har anko suka yi na dinner da ɗaurin aure. Ashe tun sanarwar da ya yi a social media suka gani, tun lokacin suka fara shiri. Ɗaya ma ya kira Habeeb a kan maganar ƙawayen amarya, sai ya ce wai ba a nan suke ba. Hakan ya yi wa Salim daɗi, irin karar da suka yi wa ɗan’uwansa, duk da a wani ɓangare kuma ya jinjina irin halin Habeeb. Murmushi kawai ya yi.

Kamar yadda ya yi alƙawari, da yamma ya tattara abokansa da na Habeeb ɗin ma, duka suka je wurin kamun. Sun yi kara kam ma sha Allah. Su ma an ba su tsaraba, ba su wani daɗe a wurin ba suka tafi. Ba yadda bai yi da Habeeb ya zo su je ba, ya ƙi.

Shirin biki ya kankama ta ko wani ɓangare, don HAZ Mansion kam ya marabci baƙi maza da mata. ’Yan uwa da abokan arziƙi na kusa da na nesa, duk an hallara, kowa sai murna yake yi. A wani fanni kuma, wasu zukata cike suke da waswasi da rashin sanin makoma. Wasu kuma na jiran yadda reshe zai juye da mujiya.