KAIFI ƊAYA

07

by @ummishatu1111

KAIFI ƊAYA.....



7



***Shuru kamar ba zata amsa ba saboda haushin kowa take ji, shi kuma bai fasa ƙwankwasa kofar ba, a hankali tamkar bata so ta tashi ta sauka daga kan gadon nata ta nufi bakin kofar tana tsaki cikin ranta,

"Wai hajjo me kike bukata ne...... Bana fada miki kar ku sake kawo min komai ba....." tana budewa taga Afeef tsaye hannayenshi cikin aljihun wandon shi, kallon juna suka yi tsawon mintunan da baza su wuce ɗaya zuwa biyu ba kafin ta dauke idonta ta kalli gefe, 

"Anty Mimi fatan komai lafiya?"

"Lafiya lau......."

"Ok, dama na zo in duba ki ne ko ba ƙalau ba saboda naji Hajiya tace tun jiya bata ga kin fito ba...."

"lafiya....."

"shikenan tunda lafiya...... Amma kin ci abincin?"

"naci" ta fada a takaice kamar bata son cigaba da maganar "

" to shikenan, sai anjima" ba tare da ta amsa ba kawai yaga ta mayar da kofar ta rufe tayi komawarta ciki, shima juyawa yayi ya koma inda ya fito inda ya tarar da hajiya da Irfan suna cigaba da maganar anty Mimi dan yanzu kamar haushin kowa take ji, wuri ya samu ya zauna kusa da hajiya cikin ransa shima yana fatan lokaci yayi yayi ya zo ko ya huta da wannan tsaka mai wuyan da ya jefa kansa.

Har dare yana family house amma babu ko alamar motsin anty Mimi kai tamkar ma bata cikin gidan bayan kuma tana nan a cikin daki sai tufka take yi da warwara ita kaɗai, shi kam yana son ya koma gida amma yana tunanin halin da zai sake zuwa ya tarar da mommy dan yanzu babu fuska ko kadan daga gareta shiyasa yaji gaba daya baya son komawa gidan sai dai kuma idan har bai koma dinba nanma wata sabuwar matsalar ce dan haka ya lallaba ya nufi gida kuma tunda ya shiga part dinsa ya rufe bai sake fitowa ba har zuwa lokacin da yayi bacci. Washe gari bayan ya tashi a fusace ya hango mommy ta fito daga cikin part dinta ta wuce wurin motar ta sai faɗa take yi, yasan ita da daddy ne kuma ba zai wuce akan wannan maganar kwaya daya ba ta aurenshi da anty Mimi, sakin labulen da yake hannunshi yayi ya shiga cikin toilet, ji yake a ransa ma kawai gara ya shirya yayi tafiyar sa calabar dama a yanda ya tsara zuwa upper week zai koma amma yanzu tunda zaman nashi baida wani amfani ko alfanu ai gara ya koma bakin aikinsa saboda baya jin dadin wannan rashin jituwar da yake ganin yana faruwa kullum tsakanin mommy da daddy kuma duk a ta silarshi da sanadiyyarsa, ko breakfast bai yi ba kawai yayi wanka ya fita family house acan ya yi breakfast dan yana shiga gidan Ammi ya tarar suhana da Irfan suna kokarin karyawa suhana ta soya musu dankali tare da sos din kwai ita kuma Ammi din bata nan ta tafi raka hajiya gaisuwa,

Zama yayi yana kallon Suhana da tun bayan shigowarshi take kallon sa tana kunshe dariyarta,

"Yaya Afeef sannu da zuwa ina kwana?"

"Lafiya lau, ya aka yi ne? Dariyar me kike yi?"

"dariyar yanzu ka zama in law dina mana...."

Murmushi yayi ya zauna ya dan kalli Irfan kadan kafin ya mayar da kallonsa gareta,

"Bana son ki rinka yimin kallon in law, am your blood brother....."

"na sani ai yaya..."

"good...."

Shi dai Irfan yana jin su bai yi magana ba hankalinsa na kan breakfast dinshi da wayar shi dake hannun sa, janye flate din Afeef yayi ya kai gabanshi ya fara ci yana hararshi, girgiza kai Irfan yayi ya saki murmushi ya kalleshi yace,

"Good morning in law....."

Wata sabuwar hararar Afeef ya sake aika masa yace "bana son neman magana fa"

Dariya suhana tayi dake zaune tana jinsu sannan cikin ranta tana jin dadin yanda zumuncin ahalin nasu ke tafiya ta yadda har sun zamo tsintsiya, haka kuma kowa na kaffa kaffa da dan uwansa babu bambanci bare waraki, sallamar janan ta katse mata tunaninta kuma ta dawo cikin hayyacinta, atare duka suka amsa sallamar nan ta shiga cikin falon inda suke yin breakfast din,

"yaya Irfan ina kwana, Yaya Afeef ina kwana...." janan ta fada tana ajiyewa suhana dan karamin food flask din da ta kawo mata wainar fulawa,

"lafiya lau...." Afeef yace kadai yayin da shi kuma Irfan yaci gaba da tsokanar janan bayan ya amsa gaisuwar ta, cike da kunya kunya take amsawa Irfan kafin taja hannun suhana suka fice gaba daya daga cikin falon. Bayan fitar janan da suhana Afeef ya kalli Irfan wanda idonsa ke kan screen din wayarsa yana kallo yace,

"Irfan ina jin zuwa gobe zan koma calabar....." ajiye wayar Irfan yayi ya kalle shi yace,

"saboda me? Ba da naji kace sai zuwa upper week ba?"

Ɗan murmushin takaici Afeef yayi wanda ke kunshe da damuwa sannan ya kalli Irfan ya bashi amsa da,

"ehh but i change my mind..... Inada ayyuka da yawa.... I have alot of works soo kaga is better na koma instead of nayi ta zama a nan gida ina hutun jaki kaya aka...."

Ajiyar zuciya Irfan ya sauke yace "hakane but ya maganar ku da anty Mimi? Ko ba yanzu zaku tare ba?"

"Anty Mimi zata cigaba da zama a nan har zuwa lokacin da komai zai zama settled kamar hakan zai fi...."

"ok to hakanma yayi, in dai har kun riga da kun gama tsara komai kun fahimci juna ai shikenan ni ina ganin babu problem...."

"Yeah..." shine kawai abinda Afeef yace ɗan shuru ya ratsa falon kafin Irfan ya katse shurun da cewa,

"itama kamar bata nan taje hospital tun da sassafe.... May be an kirata emergency ne..."

"Allah ya dawo da ita lafiya" ya fada a hankali kuma daga haka bai sake cewa komai ba har suka kammala breakfast din, nan suka cigaba da zama suna kallon ball ahaka Ammi ta shigo ta same su sun dawo tare da hajiya daga ta'aziyyar da suka je,

Sauka daga kan Kujerar da yake zaune yayi ya durkusa ya gaida Ammi ta amsa cikin sakin fuska da kulawa sannan ta wuce ciki,

"wai ko har an fara yar surukuntar ne?" Irfan ya fada cike da tsokana saboda yaga har lokacin kan Afeef din na ƙasa bai ɗago ba sannan bai tashi daga tsugunnon da yayi ba,

"you are not serious..... Ammi ai uwata ce ba suruka ba"

"to ai naga kana ta faman sussunne kai ne...."

"to yanzu dai ka tashi mu tafi wurin hajiya...."

"muje... Fada ne zamu sha shi marar dalili tunda idan tsufanta ya motsa haka take yi"

Dariya Afeef yayi yace "dambun nama nake son a sammin tunda gobe zan tafi"

"zata baka ai.... Kuna shiri ai sosai"

"amma dai ai ka san hajiya ba tabbas nima wata rana tana birkice mun idan ƴar rikicin na kusa"

Da wannan hirar suka ƙarasa part ɗin hajiya wacce ke zaune tana faman lasar farfesun naman kai wanda ya dahu rigif, zama suka yi suka fara tsokanarta wani ta kula su wani ta rabu dasu, zuwa la'asar anty Mimi ta dawo gidan amma babu wanda ya san dawowarta bare har ya ganta dan bedroom dinta ta wuce ba tare da ta nemi kowa ba,

Shima Afeef yau bai nemi inda take ba yayi sallama da Hajiya ya tafi, iya hajiya da Irfan ne kadai suka san zai koma aiki gobe, da yake yawanci idan zai koma tafiyar asubanci yake yi shiyasa tun dare ya yi kokarin shirya jakar kayansa kamar yadda ya saba, bayan ya kammala haɗa komai ya fita zuwa part din mommy iya Manal ce kadai cikin falon tana kallo ya shiga ita kuma mommy din tana cikin kitchen, har cikin kitchen din ya bita cikin sanyin murya yace,

"mommy sannu da aiki......"

"yawwa"

"mommy na gama shiryawa gobe zan koma calabar..." ɗan sanyi mommy taji acikin ranta da taji cewa zai koma aiki gobe saboda bata son yaci gaba da zama auren nan da aka lankaya masa ya ɗore,

"Gara ka koma ai tunda zaman naka anan baida wani amfani..."

"insha Allah gobe zan tafi mommy...."

"Amma me yasa baka fada min da wuri ba, ai da anyi maka snacks kamar koda yaushe...."

"babu komai mommy, hajiya ta bani...."

"to shikenan"

Ganin yanda mommy din ta dan sauko har tana tarairayarsa yasa ya dan ji sanyi da dadi cikin ransa, 12 na dare ya kwanta bayan ya saita alarm dan yana son ya tashi kafin asubah tayi saboda gudun makara sai dai amma baccin yaƙi zuwar masa a maimakonshi ma tunani yaji yana ta bijiro masa cikin wannan lokaci wanda gaba ɗaya akan lamarinsu ne da ya shafi yaya Aliyu haidar, Anty Mimi da kuma shi, tun farko mema yasa ya yarda har yaji tausayinsu ya karɓi wannan tayin nasu? Juyi kawai yake ta faman yi har misalin karfe 1 da rabi na dare, da ya tabbatar baccin ba zai dauke shi a wannan lokaci ba sauka yayi daga kan gadon nasa ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito, sallar nafila yayi raka'a biyu sannan ya samu wuri ya zauna kan abin sallar tashi yana mai cigaba da yin addu'o'i har 3 saura kuma sai lokacin ya dan ji bacci a idanuwansa babu ɓata lokaci ya koma saman gadon shi ya kwanta, makara ya so yi saboda bai kwanta da wuri ba amma dai da kyar ya iya tashi ya shirya ya fita bayan yayi salla, sun yi sallama da kowa na gidan sannan ya tafi yana ji a cikin zuciyarsa wannan tafiyar tashi itace zata bawa zuciyar mommy damar hucewa cikin kankanin lokaci.

Yaya Aliyu tun ranar da aka ɗaurawa Afeef da anty Mimi aure ya fara jera lissafi wato ranar da ya dace Afeef ya saketa kamar yadda suka yi alƙawari, cikin bedroom dinta yake kwana hotunanta kafe a kowacce kusurwa ta bangon ɗakin, wani lokacin su kwana suna waya wata rana kuma su raba dare suna waya saboda irin dafin soyayyar da kowannensu ke ji cikin ransa, haka da rana da safe da yamma baya samun sukuni komai kankantarsa har sai ya kirata yaji muryar ta, sosai yanzu take jin abun yana bata tsoro dan kamar wanda Aliyun ya zautu abubuwan da yake yi a kanta sun fara wuce lissafin hankali,

Tun tana cikin bathroom tana wanka taji yana kiranta amma bata dauka ba saboda ta makara yau sosai kuma ba kowane ya makarar da ita ba face shi saboda shine ya hanata bacci suna ta faman hira har asubah, gashi yau akwai aiki shiyasa take ta sauri bata tsaya wani daukar wayar shi ba, cikin sauri ta fita ta bar gidan ta tafi asibiti kuma tana zuwa ta shiga theater, shi kuma ganin yana ta kiranta bata dauka ba yasa shi fita daga gida ya nufi asibiti dan ya san tana can tunda yau akwai aiki, daga shi sai kayan bacci ya shiga motar sa ya figeta zuwa asibiti, ta shiga theater dan haka ya zauna yana jiranta wanda ba ita ta fito ba sai 12,

"Aliyu yau baza ka fita aiki bane?" ta fada tana kallon sa bayan ta zauna kan kujerar ta,

"wallahi zan je aiki My love, in fact ma akwai wani important meeting da nake dashi but ba zan iya zuwa ba mutukar ban jiki ko kuma na ganki ba..." girgiza kai tayi cike da tausayinshi tace,

"Am fine... Dan Allah ka daina wasa da aikin ka, ina nan lafiya lau...."

"ta yaya zan iya tabbatar da hakan alhali ban sameki ba koda a waya ne?"

"Kaga ai na shiga theater ne and you know idan na fito dole zan kiraka back...."

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta cikin sanyin murya yace,

"insha Allah saura 1 week daidai Afeef ya sake ki kamar yadda muka shirya......"

"Babu problem, Allah ya kaimu...."

"yana nan ma kuwa? 2 days bana ganinsa, ko ciwon nashi ne ya tashi ko ya motsa? Bari na kirashi naji...." wayar shi ya dauka dake ajiye kan teburinta ya fara kiran layin Afeef..........