27
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.
Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***
*Page 27*
Sunaima batasan Matar Saifullahi ta haihu ba har sai da akayi kwanaki uku da Haihuwar tasani Shima Hajiya ta kira awaya su gaisa sai take Fadamata suna Hanya zasu karaye su yi barkan Haihuwan matar Saifullahi Sunaima mamaki ya kamata Cikin Karfin Hali tace"Matar Saifullahi ta Haihu ne Hajiya..?
Hajiya batayi mamakin Tambayan Sunaima sai tace"Hala tun bayan tafiyarsa baku waya bane..?Don nima Rabona dashi tun ranar daya isa Lagos din..!?
Da farko Sunaima bata gane Mganar Hajiya ba sai da ta karishe mganarta sai ta gane inda ta dosa data kwafsa da tana shirin cewa Shi wane..?sai tayi Saurin gyara bakinta Cikin Sanyin Murya da mamakin Sulaiman tace"Eh gaskiya Hajiya...Inaga shiyasa bai Fadamin ba..!
Tafada tana kara mamakin Sulaiman ashe baya ma agidan bata sani ba yana Lagos lalle ashe shi da gaske yake yi Fushin dayake yi da ita abayana tana Dauka wasa ne sai yanzu tasan da gaske yake yi ita har ga Allah bata Dauka bayanan ba Da kwana Biyu tadaina jin motsinsa ta zata yana kai Dare ne kafin ya dawo tayi barci.
Hajiya ce ta cigaba da fadin"Dayake kisan Taron yan kasuwa ne Abbansu bazai samu zuwa ba sai ya Turasa Kafin ma Matar saifullahin ta Haihu tare suka Tsara tafiyar washegari sai ga Haihuwar yasa ya tafi shi kadai..Shiyasa ma ban kiraki ba nasan in ya dawo zai kawoki..!
Sunaima tace"Insha Allahu Hajiya..Allah ya kaiku lafiya ki gaishemin da Hajiya karama in kun isa Zan kira Hajiya ina so nayi ma Mejego barka..!
Hajiya ta amsa mata Daganan suka yanke kiran Sunaima ta koma ta kwanta Duk kuma sai jikinta yayi sanyi Ta fara kokarin Tattara abunda ta Faru waje daya tsakani ga Allah in tana son gaskiya itace bata da gaskiya itace take kasan sa shi shugabane gareta bai kamata ba sam sai alokacin Taji bata kyauta ba sai alokacin ta san cewa tana cikin Fushin Ubangiji sai alokacin ta gane kuskuranta zamanta da Sulaiman bai taba bata mata da gangan ba Kokarinsa ya ganta Cikin Farimciki ya faranta mata ya Mutumtata ita da iyayenta Shin Sulaiman ya Chanchanci wannan Hukunci a wajenta..?
Bai kamata ba bai kuma Chanchanta ba Sulaiman ya wuce wannan awajenta ya kamata ta nemeshi ta bashi Hakuri ya yafe mata.
Gida gashi ita kadai daga ita sai yan aiki ita tana Daki nan take wuni sai in Zataje wajen aiki tana Dawowa kuma tana Daki bata fitowa falo ko abinci Daki Magajiya ke biyota dashi,Abunda ta samu shine karatun Novels Aneesa ta koya mata sai dai bata bari ya taba Ibadarta ba.
Yanke hukunci kiransa tayi sai dai kira biyu tayimai bai Dauka ba sai kuma Jikinta yayi sanyi sai ta yanke Shawaran Turamai sako.
"Sorry...Sorry....Sorry.....!
Sai dai har sai da ta cire rai Ta sake kiransa bai Dauka ba Duk sai ta Damu ta koma tayi Tagumi sai yanzu nadaman abubuwan data aikata Sai yanzu taji bata kyauta ba kuma Daga gani yayi Fushi mai Tsananin Dayasa ya kyaleta sai dai tayi mai uzurin kila bai gani ba tunda taro sukace kila bai da Lokaci ne ko bai ga kiran ba.
Lokacin dataji Ringing din wayarta tana rawan jiki ta zata Sulaiman ne sai taga ashe Hajiya ce take kiranta ta Dauka suka gaisa nan Hajiya ke sanar da ita sun iso suna Asibitin Dayake ba"a sallami Khadijan Daga asibitin ba Ga Mejegon su gaisa.
Hajiya ta bama Khadija matar Saifullahi karo na Farko suka gaisa da Sunaima cikin Sakewa Sunaima tace"Ashe an samu karuwa..?Allah ya raya ya baki lafiyar shayarwa..ashe C.S akayi miki..?
Khadija tace"Eh wlh..Ameen Nagode..!
Sunaima tace"Masha Allah..Allah raya me aka samu ne..?
Cikin Jin kunya tace"An samu mace..!
Sunaima tace"Allah ya rayata..Sai ya dawo zamu zo suna in Allah ya yarda..!
Khadija tace"Ameen sai kunzo Bby na nan tana jira..!
Sunaima tace"Kada ta Damu muna nan zuwa..Agaida Megidan..!
Khadija tace"Zai ji yama dan Fita ne wajen asibitin..!
Daganan sukayi sallama ta mika ma Hajiya wayar ita kuma sai ta bama Hajiya karama suka gaisa daganan ta bama Mahaifiyar Saifullahi suka gaisa tayi mata barka da Allah ya raya Daganan sukayi sallama.
Sunaima sai ta yanke shawaran Kiran Saifullahi tamai barka data kirasa yaji Dadi sosai,shi yake fadama ta ma Zuwa Jibi za"a sallamesu su koma gida suka Rabu kowa na jin dadi har yana Tsokanarta ta zama gauruwa Saraki bayanan Dariyan yake tayi mai Domin sai da taji wani iri sanin yadda Sarakin ke Fushi da ita.
Sunaima abun ya fara Damunta sosai har washegari Sulaiman bai nemeta ba yanzu kam ta sani Sulaiman yana Fushi da ita kuma Fushi mai Tsanani sai ta fara Tunanin hanyar da zata basa Hakuri tunda itace bata da gaskiya kuma itace akasa.
Ranar aikin Rana gareta Bataso ta kara Hawa adaidaita Laifi kan laifi bata da Lambar sani ballatana ta Kirasa kanta ya kulle sai ta samu Dubara Fita tayi ta samu magajiya ta Tambayesu ko suna da Lambar sani Magajiya tace Samira nada shi Allah ya Taimaketa samira ta saka ta kira mata Sani tace yazo yanzu tana nemansa aikuwa bai bata Lokaci ba sai gashi yazo Sunaima ta Umarcesa da ya kaita wajen aiki Daman key din Motar tana Hannunsa Motar ne ke gida Cikin Rawan jiki ya amsa mata ya kuma Dauketa zuwa wajen aiki kafin su rabu sai da ta karbi Lambarsa Da cewar in tatashi Zata kirasa abun ya basa mamaki Ranar Dayakai yallabai Filin Jirgi dayace ya maida Mota gida shima yaje ya Huta Har sai ya dawo sai yace mai kai Hajiya wajen aiki fa..?
Sai yayi banza dashi bai ce komai sai dai ya kara nanatamai ya maida Motar gida har sai ya dawo da haka suka Rabu kwana Biyu ba wanda ya nemesa sai yau shiyasa abun ya dan basa mamaki sai dai bai maida kai ba Tunda ba abunda ya shafesa bane
Har a wajen aiki Cikin Damuwa take Saboda ta kara kiran Sulaiman wannan karon ma bai Daga ba sai ta Sare Rauninta ya bayyana Hankalinta ya tashi sosai idanuwanta suka cika da kwallah,Sai alokacin tasan Saraki ya wuce Mijin kanwarta awajenta ya koma wani mahadin Rayuwarta da bazata iya Rayuwa babu shi ba ita kadai ta kebe kanta tasha kukanta bata da wanda zata Fadamawa ya bata Shawara,Sai Inna kuma ita Inna bazata gane abubuwa ba Sai ta gama Rufe Mutun da Fada Mitarta na Fama wannan mtsalan ita ta Faroshi Saboda haka ita zata gyarashi da yardan Allaah.
Sulaiman bai dawo ba sai da ya kwana Biyar a lagos Ya dawo Ranar Jumma"a da yammah Sunaima bata gida tana Wajen aiki,Ranar Duty yammah gareta,Sani yaje ya Daukosa Daga Filin Jirgi.
Tunda ya iso bai nemi Sunaima ba,Saboda yaga alamun yawan Sake matan dayake yi ne ta rainasa tana ganun kamar shi da ita Dayane sannan Taurin kanta sai ya nuna mata Shi Mijinta ne sannan zata gane kuskuranta
Yana ganin kiranta da Sakonta yayi kamar bai gani ba bai Dauka zata Saduda haka da wuri ba Sun yi mgana da Saifullahi ya fadamai Sunaima ta Kirasa yayi ta mamakin a ina taji Haihuwar Shidai bai fadamata ba sai da sukayi mgana da Hajiya take fadamai sun yi waya da sunaima ita ta ke Fadamata Haihuwan har ta bata suka gaisa da Mejego da maman Saifullahi sai alokacin ya gano inda taji Labarin Haihuwan.
Yana dawowa ko Hutawa bai yi ba ya wuce kamfani ba kowa achan Saifullahi sai jiya matarsa ta koma gida daga asibiti yaso ya dawo yacemai ya zauna har ayi suna shi yana Hanya zai dawo Dalilin Dayasa yana Dawowa wanka kadai yayi ya sauka kaya ko Abinci dasu magajiya suka Shiryamai bai bi ta kansu ba Sani ya kara kwasansa zuwa kamfani
Karfe 6 da wani abu na yammah Sunaima ta kira Sani tace yazo ya Daukesa Lokacin yana kamfani yana Jiran Sulaiman su shiga Meeting,Ganin kiranta ne yasa ya tafi Daukota suna Hanya kiram Sulaiman ya shigo wayarsa Cikin Sauri ya Dauka.
Sulaiman cikin dan bacin rai yace"Kana ina ne Sani..?
Sani yace"Ina Hanya Ranka ya Dade..Hajiya naje na Dauko daga asibiti..!
Alokacin bai gane wata Hajiya yake mgana ba yasa yace"Wata Hajiyan..?
Sani yace"Antyn su Wasim mana yallabai..!
Sai alokacin ya Tuna da yacemai Daga asibiti tabe baki yayi ya Datse kiran bayan yace ma Sani yana Jiransa yayi Sauri Sunaima na bayan Mota tana jinsu da Farko hankalinta baya kansu sai dai jin yana ambatan yallabai yasa ta kasa kunnenta Domin ta Tabbatar da Sulaiman yake mgana bayan ya gama mganar tana so ta tambayeshi Saraki ya dawo ne..?Sai dai batasan wani kallo zai mata ba da kuma yadda zata Dora Tambayar nata batare da Sani yayi mata wani Fahimta ba.
Kamar Sani ya Shiga ranta ya waiwaya baya yana Fadin"Hajiya yallabai ne ke kira..Yana ta fadan yana Jira na a kamfani Dayake Dazu naje Filin Jirgi na Daukosa..!
Ajiyar Zuciya Sunaima ta Sauke batare da tace komai ba,Ranta yayi Hasken jin ya Dawo tayi kewarsa sosai bawai kewar wani abu ba sai dai tayi kewar Hallayarsa masu kyau da nasaba.
Abakin get tace ya ijiyeta Tunda ana Jiranta Daganan ya juya ita kuma ta karisa Cikin gidan,Da samira taci karo afalo ta Duka tana mata sannu da dawowa,ta amsa sama sama ta Shige Dakinta Sauri sauri ta yaye kayan Jikinta ta saka Doguwar riga baka ta Fito zuwa Kirchen ta iske magajiya na wanke wanke suka gaisa tace mata Zatayi ma Sulaiman girki ne Samira ta leka ta kira wacce ke gyaran Falon tace tazo ta Dauko Nama ta wanke ta tafasa mata ita kuma sai ta Dora tuwon,Shinkafa take so yimai Miyar Kubewa Bushashiya.
Kama kama sukayi ma aikin ganin mangariba tayi Sunaima na neman Shiri ta kuma san Sulaiman na son Tuwo zata fara ban Hakuri dashi Sai ta Daure Tuwon shinkafar Ta barma Magajiya ta Saka mata Cikin Leda ita kuma taje tayi sallah bayan ta barma Samira miyar ta Kada mata Tunda ta gama komai.
Daki ta koma tayi wanka tayi Sallah Sauri Sauri Saboda bataso ya Dawo bata Shirya ba Cikin Doguwar Shadda ta Fito,Mai ruwan gold tayi kyau sosai tayi Daurin Ture kaga Tsiya,Sai gashi ta bata Lokaci Tana kwalliya bata Fesa Turare ba saboda yanzu batason warin Turare sai taji Duk ranta baya Dadi Zuciyarta na tashi Shiyasa ta Daina amfani da Turare kwata kwata sai Spray daya zama Dole.
Tana Cikin kara gyara Daurin Dankwalinta taji mganarsa Sama Sama afalo yana amsa gaisuwan magajiya bata tsaya wani jan aji ba tayi Fit ta fito daga Dakin tana gyara Takunta Duk da yadda gabanta ke Faduwa na rashin Sanin yadda Saraki zai karbeta.
Har ya wuce yana kokarin fara Haura Steps yaji Muryanta Cikin Sanyi tana Fadin"Sannu da zuwa..!
Cak ya tsaya kafin ya Juyo yana kallonta Ido Hudu suka Hada Sai da Dukkansu zuciyansu ya amsa Sunaima taga Saraki yayi mata kyau da kwarjinin da bata taba gani ba,Yana Sanye da yadi mai ruwan Sararin samaniya Shara shara ne mai kyau yana yarari harta Farar Vest dinsa ana iya ganu sai Hular Daya Saka asaman kansa Zanna Bukar yana Rike da karamar Jakar Briefcase dinsa wata leda Dake Dauke da Tambarin Kamfaninsa na madara Kamar yadda ta kafesa da ido haka shima ya Kalleta sai dai shi yayi Saurin Dauke kansa Duk tayi kyau ta karamai Kiba da Haske cigaba da Tafiya yayi Lokaci Daya yana Fadin"Lafiya..!
Daganan bai ko kara juyowa ba har Sulaiman ya haye sama ya bar ta nan Tsaye sai jikinta kuma yayi Sanyi Da takasa koda Motsi Allah ya taimaketa ita kadai ne afalon su Samira na Barayinsu sai ta kwashi Siraran kafafunta ta koma Daki tana jin kamar ta Dora hannu Tayi ta kuka Gefen gado ta zauna Tana Tunanin Sulaiman ya ki bata Fuska tayaya zata Tunkareshi ta bashi Hakuri..Tasani Laifinta mai yawa ne Ammh har ga Allah ba da gangane ne take gudunsa ba Haka take jin yanayinta Har kuma yanzu hakan bata sauya ba Ganinsa Daga nesa bata ko kaunar ya matso kusa da ita.
Tana nan zaune tana saka tana warwara har aka kira Isha"i ta mike ta Saka Hijabi ta Tada sallah Ta idar kenan taji ana mata Knooking ta Mike tana bada izinin Shigowa sai ga Samira ta shigo sai da ta Duka kana tace"Ranki ya dade yallabai ne yace a kaimai abinci sama..Shine Magajiya tace nazo na Sanar dake Tuwon zamu kaimasa ko whiterice din da muka Dafa..?
Sunaima na Kokarin Ninke Hijabinta tace"Ina shi Sarakin yake..?
Samira tace"Ya tafi masallaci..!
Sunaima tace"Ok..bari nazo..!
Daga haka Samira ta fice ita kuma sai da ta kara gyara fuskarta ta Kara Daura Dankwalinta dakyau sannan ta Fita,Kitchen ta shiga ta iske sun Saka Tuwo cikin wata Cooler babba sai ta samu karamar Cooler ta zuba Tuwon da Miyan ta samu Faranti ta jera ta Dauko mai ruwa da Filet yau batayi wani Drinks ba lokaci ya kure.
Dauka Tayi ta nufi shashen Sulaiman gabanta na Dukan Tara tara saboda batasan yadda zai karbeta ba aranta Tana Harhada Kalaman da zatayi amfani dasu wajen fara bashi Hakuri.
Sallama tayi bayan tayi knnoking din kofar taji Shuru jinta abude yasa ta Tura ta shiga ba kowa afalon Allah yasa Jiya ta shigo ta gyara ko"ina kamar tasan yana Hanya.
Kan Center table din Dake Falon ta Ijiye Tuwon Tibi shi kadai ke ta Hayaniya shi kadai ba kowa afalon,Zama tayi tana jiransa sai dai Shuru ba motsinsa Kila yana cikin Bedroom dinsa ne gajiya tayi da Jiransa ta Mike ta Bisa Ciki Tana Shiga ta iskesa tsakar Dakin Dagashi sai Gajeron wando ba riga ajikinsa Dayake maikon Ruwa Daga gani bai Dade da Fitowa wanka ba,wayace a kunnensa yana mgana.
Sallama tayi akaron Farko sau Daya ya kalleta bai kara ba ya maida kansa yana Cigaba da wayar da yake,Ganin haka yasa ta Tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya har ta yanke shawaran komawa sai kuma wata zuciya tace"Sunaima baki da gaskiya fa..Kuma kece a kasa ke zaki fara kwantar dakai kada ki manta Saraki fa..!
Tuna haka yasa ta fara takawa garesa Yana ganin haka sai ya juyo yana kallonta Itama kallonsa take hannayenta ta Dora a kunnuwanta Duka Biyu ta Duka Ta Dago irin kamar Tana Jumb din bakinta na Motsi tace"Sorry...!
Yadda tayi sai da jikinsa ya amsa ammh sai ya barsa yayi kokarin Rabata ya fita daga falon yana Fadin"Saifullahi muyi mgana gobe da Safe..nagaji yau din nan..!
Sunaima taga wannan ne Dama ta karshe a wajenta Duk da yadda Zuciyarta ke tashi Tana shakan kamshin Turarensa haka ta Daure yana Shirin fita ta Ruga ta Bisa ta Rungumesa ta baya lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin"Kayi hakuri..Am so sorry na tuba..!
Take fada tana Shesshekan kuka,kukanta da Biyu take yi na Farko na Rauninta na Biyu kuma na yadda Kamshin Turaran Saraki ke hawa kanta ta rasa madafa ba abun tayi mgana ba Laifi ya dawo sabo.
Yadda ta rikesa tana kuka yasa ya kasa Tafiya ya barta tsayawa yayi Cak batare daya waigo ba Hannunwanta ya rike duka Biyu cikin Fitar hayyaci yace"Why Sunaima.?kin rainani har haka bansani ba da zan saka miki Doka ki hauta ki zauna..?Saboda ni mijin kanwarki ne har yanzu ban kai matsayin mij..!
Bata bari ya karisa ba tayi saurin Juyowa gabansa Tana kallonsa Lokaci Daya tana Rufe mai baki da hannunta sai Hawaye Cikin Raunin murya tace"A"a kada kace haka..ba haka bane..Am sorry bansan me zan ce ba..Ammh ina so ka sani Miji na na Dauke ka ba Mijin kanwata ba kaine Duniyata yanzu..!
Tafada tana kallonsa ido cikin ido Da Sauri ya Jimke hannunta yana Fadin"Really..?kina SONA Sunaima..?A mtsayin Mijinki ba Mijin Sunaira ba..!
Bazata iya bashi amsa ba Sai kawai ta Fada Jikinsa ta kamkameshi tana Fadin"Basai na fada ba..adan zamana Dakai ya kamata ka fahimci na Karbi Kaddaranta na yarda kaine Duniyata..!
Bai Rumgumeta back ba illah cewa da yayi"No ba haka nake son ji ba...Ina son jin Sulaiman ina sonka..!
Tana Cikin jikinsa kanta na Kan kirjinsa tana kokarin yaki da abunda take ji tace"I LOVE U...SARAKI NA..!
Kamar a mafarki haka yaji Da Sauri ya kamkameta yana Fadin"Love u much Sunaimata..Kin hukuntani da Fushinka..Daurewa kawai nakeyi..!
Sunaima tace"Nima haka..Ammh abu Daya ya rage..?
Yadagota yana kallomta yace"Menene..?
Sunaima tace"Ka janye barina da kayi da Allah akan Abunda ya faru ranar..Da kuma hawa adaidaita kayafemin..!
Tafada cikin Rauni kara Jawota yayi ya Rumgumeta yana Fadin"Na janye na janye mganata Nima ki yafemim..!
Kara kamkame juna sukayi ya fara Shinshinarta yana fadin"I miss u...!
Muryan Sunaima kasa kasa tace"Me too..!
Cikin wani yanayi gabadaya ji tayi kamar Zuciyaeta zata fito saboda yadda take ji Kamshin Saraki hawa kanta yake kamar ta Turesa ammh ba Dama hakanan ta bashi Halin kai ganin yadda yake Sarrafata da Zafi Zafi Dole ta Daure ta bashi halin kai suka Fada kan gado kankame da juna sai da suka samu natsuwa tare sukayi wanka Rigarsa ta saka suka fita Falo Ganin Tuwo tayimai ya Dinga saka mata albarka bayan sun gama cin Tuwon ne suka kara komawa Ruwa Sunaima kamar ta Saka kuka haka ta Dinga ji sai da Saaraki yaja ta gaji Lilis kana ya kyaleta bayan ya Fadamasa kwanakinsa ya fanshe.
Da asuba daya dawo sallar asuba ya nemeta bata isa tayi mai gaddama ba sai dai suna tsakar sha"anin Zuciyarta ta fara tashi kafin tayi wani motsi Aman ya kawo haka ta amayeshi Shida zanin gado sai ya kuma Rude ya koma ya riketa yana Fadin"Sannu Sunaimata..Daman baki da lafiya ne..?
Sannu meke damunki..?
haka yake ta fada yana rawan jiki ko kyamar aman ba yayi sai kuma yabata Tsausayi shi ya kaita Tiolet yayi mata wanka ya Daukota bayan ya yaye zanin gado da kayan da ta bata da amai ya wurga Roban wanki.
Ya sauya Zanin gado ya koma ya kwantar da ita yana ta jera mata sannu.
Gari na wayewa yace suje asibiti tace ta warke lafiyanta kalau to ganin tatashi garau yasa ya kyaleta aranar yake Fadamata gobe sunan Matar Saifullahi ta marairace tace don Allah ya kaita Sai da ta nemi yin kuka yace gobe ita da su Wasim zasu tafi Gabadaya su kwana Daya su dawo Ranar Litini da Safe sunaima ta Fara Murna Da Farinciki da yammah suka tafi suka saima Maijege da Bby kaya Masu kyau sannan suka biya gida Sunaima ta fadama inna Da yaran suka taho Sunaima nata Murna yau Sulaiman bazai dameta ba Tunda ya yarda ta Dauko yaran shi kuma ganin Kulafacinta kan yaran yasa yace su taho dasu gata bata jin Dadi yana Tsausayinta yasa ya Daga mata kafa ranar ta kwana da yaranta Washegari Lahadi Karfe 10am na Safe suka Dauki Hanyar Karaye Sulaiman shi da kansa ke Tukin Sani na gida Sunaima na gaban Mota Wasim na baya Wafiyya kuma na jikin Sunaima suna Hira da Saraki sama sama itama tafiya batayi nisa ba Sunaima ta Fara barci wanda baya isarta a kwanakin Sulaiman ya samu daman kare mata kallo yana lkara ganin Farin data kara da kuma yadda tayi kumatu bai kawo komai aransa ba yana Tunanin Hutu ne da Chan jin yanayin Waje yasa ta koma haka.
Karfe 12:30pm na rana suna karaye Gidan Saifullahi inda ya gina Gadon Mahaifinsa ginin zamani mai kyau,Ba nan suka fara zuwa ba sai da suka biya gidansu Saifullahin suka gaisa da Mama Dayake basu da wanni nisa sosai taji Dadi sosai ta rasa ina zata sakasu nan sukayi azahar suka sha Fura da Danwake itama tayi taronta Ita da yan"uwan khadija Tunda Duka abun na gidane.
Sai azahar suka isa gidan Suna Sunaima da yaran suka shiga Cikin Gida Saifullahi da Sulaiman kuma suka koma Chan gidansu Sulaimam din inda ba yalwar jama"a sosai.
Khadija ta rasa ina zata saka da Sunaima sai nunata take tana matar Sulaiman ce ana mata maraba da Far"a tana ji ana fadin itace yayar matar tasa daya aura Khadija tace eh,Tanaji ana cewa Allah Sarki gashi ta Rike ya"yan yar"uwanta ita dai batace komai ba
Ta bama khadija abunda tazo mata dashi nata dana Sulaiman sai godiya take tana ta nuna ma Mutane Turaman zani hudu da rigunan yara sai Su sabulai da omo,Su wasim sun ga yara suna tsakar gida suna ta wasa bayan sun ci abinci ita kuma Sunaima suna Uwar Daka kan gadon mejego taci abinci alalan taci sosai da kunin Zagin da akayi,Shi tayi ta sha yayi mata Dadi.
*Janafty*