Nadama page 12
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI🙆🏼
Fatima Isah
Edit.....2026
Love story 2015🥰
***
Page ɗin yau naki ne ƙawar arziki tun ta yarinta Tabara Muhammad Kabir haƙika komi nada lokaci ubangiji Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a Ameen.
*******
PAGE 12
Duk wani abu da ya kamata ayiwa Amarya Pendo Ummi tayiwa Fatima, irin abubuwansu na Fulani da dai sauransu ita kanta Fatima takanji sauyi a jikinta takanyi tunanin inama wannan gyara da akayi mata duk na Musaddik ne.
Bayan an gama komi da misalin ƙarfe 8:00pm Dad ya ɗauki 'yarsa da kansa zai kaita har gidanta kuma ya hana ko wace mace binsu uwa uba harda Pendo Ummi ya hana ya ce sai dai su tafi daga baya.
Fatima tanaji tana ganin yau zatayi ban kwana da 'yan uwanta za'a kaita gidan wanda tafi tsana a duniya, tana tafe tana kuka har ta isa mota Dad shida kansa yasa hannu ya buɗe mata sannan ya kamata ya zaunar da ita a kujerar baya, driver ne yazo da sauri Dad ya daga mashi hannu ya ce.
"A'a barshi Suleiman na hutar da kai yau ni zanja da kaina nakai 'yata har ɗakinta sannan na saka mata albarka."
Suleiman yana murmushi ya buɗewa Dad mota yana faɗin.
"Gaskiya ne Alhaji ai dama haka ya kamata duk uban ƙirƙi ya dinga yiwa ya'yansa duk ranar da aka ɗaurawa yarinya aure to ya ɗauketa da kansa ya kaita har ɗakinta yayi mata addu'a domin kuwa matan da za'a tara su kaita wata ko murna maybe batayi da aure balle ta samu damar yiwa ma'auratan addu'a gaskiya wannan halin naka Alhaji ya kamata duk uba na gari ya yi koyi da kai, Allah ya tsare Allah yasa wannan aure an yishi a sa'a, in shaa Allahu wannan aure anyi shi kenan har abada."
Tunda Suleiman ya fara magana Dad ya tsaya yana kallonshi cike da jin daɗi kalamansa yayi murmushi ya ce
"Suleiman nagode da wannan adduar taka sannan ina mai yi maka albishir daga yau ka tashi daga driver gidan nan zaka koma kana cikin kashin kanka na baka ƙyautar million goma da gida kaje kaja jari."
"Alhaji ne? Ko dai mafarki nake?"
"Suleiman ba mafarki kake ba da gaske ne wannan yana ɗaya daga cikin ƙyaututukan dana tana darwa wannan auran ga duk wanda ya taya ni murna cika wannan burin nawa."
Suleiman ƙasa ya faɗi yana mai cigaba dayiwa Dad godiya ita ko Fatima a zuciyarta ciwa ta yi.
'Humm Dad kenan ai kam kana dab da asarar dukiyarka danko ni wallahi banga mijin aure ba'
Check Dad ya ɗauko ya rubutawa Suleiman har naira million goma kamar yanda ya faɗa mashi tare da makullin gida.
Hannun Suleiman na rawa yasa hannu ya amsa yana godiya hawaye na fita a idonsa ya ce.
"Alhaji nagode Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya a kan yanda kake taimakon talakawa insha Allahu wannan auran ainyishi kenan mutu karaba"
"Allah yasa Suleiman dan Allah sai aje a kama sana'a."
"Insha Allahu Alhaji na gode."
"Haba is ok godiya ta isa haka."
Har Dad ya tayar da mota ya fita Suleiman ya kasa tashi daga inda yake tsugunne.
Dad na cikin mota yana driving a hankali cikin ƙwanciyar hankali yana kallo 'yar tashi ta madubin mota, yana kallon yanda hawaye ke fita a fuskarta.
A haka har suka isa makeken gidanta dayasha ado na kece raini, bayan sun isa mai gadi yayi sauri ya buɗe mashi get ya shiga yayi parking ya fito ya buɗe mata yasa hannu ya kama mata hannu suna tafiya har suka isa bakin wata ƙofa wanda ake danna mata wasu numbers ta buɗe, itama ƙofar tasha ado da irin fentin zamani, a hankali Dad ya furta.
"To Fatima gashi Allah ya kawo ki gidanki kiyi addu'a kafin mushiga kuma ki shiga da kafar dama."
Kai ta ɗaga mashi alamar to tayi kamar yanda ya umarceta, wani katafaran parlour ne suka isa wanda yake ɗauke da kujeru iri daban-daban.
Kai gidan ya haɗu fa iya haɗuwa, saida Dad ya shiga ko ina ya nuna mata duk yanda gidan yake kafin suka dawo parlour suka zauna ya ci gaba da yi mata nasiha mai shiga jiki kamar haka.
"Fatima dan Allah kiyi hakuri ki zauna da mijinki lafiya, ki guji fishin mijinki kiyi masa biyayya kada ki biyewa son zuciyarki ya kaiki ga dana sani, wallahi Fatima idan kika zauna da mijinki lafiya zan maki duk abinda bakiyi tunani ba.
Fatima mahaifiyarki ta baki tarbiya iya bakin gwargwado dan haka idan naga akasin haka bazanyi kuka da ita ba, wallahi Fatima duk ranar da kika kashe auranki daga ranar babu ni babu ke sai dai ki naimi wasu iyayen amma bamu ba.
Fatima doni mo yidi ma pat yeccatama,to a nani gam hore mada, to a nanai ma gam hore mada dan Allah kiji abinda muka faɗa maki."
Kullum Dad maganarshi ɗaya kenan, saida Dad ya yi mata nasiha mai ratsa jiki kafin ya barta ya fita.
Motar Dad ta fita kenan tasu Ikram na danno kai
Ikram ita da ƙawarta Meena su kansu gidan ya baso sha'awa sun tabbatar da ƙawarsu tayi dacen gida bayan sunyi parking suka shiga gidan dama sun ƙira Faruok ya faɗa musu code number ƙofar, inda Dad ya barta a nan suka isketa ta kasa tashi sai hawaye da taketa aikin fitarwa.
"Gaskiya teema am bazan boye maki ba you have a big problem haba sai kace ba fulɓe ba, fulani an sansu da kunya da kauda ido da abinda suke so amma ke naki ko irin alkunyar nan babu haba Fatima don't kill ur self."
Murmushi Fatima tayi mai ɗauke da takaici ta girgiza kai ta ce
"Ikram, I know nobody will understand my feelings, ko ke bazaki fahimce ni ba har sai kin faɗa cikin irin halin dana faɗa."
"Allahumma ajirni fi masibati, dan wannan musiba ce Fatima ina naiman tsari tun yanzu."
Dariya Meena ta ƙwashe da ita dan jin abinda Ikram ta ce.
A hankali Ikram ta zauna inda take ta dafa kafaɗarta ta fara magana cikin rarrashi.
"Please Fatima ki farka daga mummunan mafarkin da kike dan idan baki wasa ba kina dab da rasa tunaninki dan wannan mafarki ne, Fatima wallahi Allah duk macen data samu miji kamar Faruok tayi sa'ar miji nakece reni meye Faruok baidashi da har kika likewa wannan makahon?"
"NAGARTA Musaddik yafi Faruok komi a wajena zan iya rabuwa da kowa saboda Musaddik dan haka kada ki kuskura ki muzanta abin sona.
Ikram kenan Allah hautuma be irin yide mi yidi musaddiq do ni."
Murmushi Ikram tayi ta koma ta jingina da kujera tana dariya, saida ta ɗauki lokaci tana kallon Fatima kafin ta ce.
"Fatima dan Allah bakiji kunyar faɗin Musaddik yafi Faruok NAGARTA ba kin sanko abinda ake nufi da NAGARTA? Anyways mubar maganar haka tunda naga har yanzu baƙya son gaskiya, amma Fatima bari na tambaye ki taya kuka fara soyayya da Musaddik bayan barina ƙasar nan?"
Murmushi Fatima tayi ta lumshe idonta kamar bazatayi magana ba ta buɗe ido ta kalli Ikram ta ce.
"Hmm long story Ikram soyayyata da Musaddik daga Allah ne."
"Naji amma ya kamata ki dan ban labarin haɗuwarku, amma ba nan ba, mushiga daga cikin bedroom dinki dan nasan yanzu ana dab da rako ango."
Ikram ta kama hannun Fatima suka haura saman, masha Allah suna shiga suka dinga bin ɗakin da kallo komi na ɗakin pink ne dama sunsan best colour nata kenan, ita kanta ɗakin ya yi mata kyau iya kyau ya tafi da imaninta.
Bakin gado suka zauna dukansu kafin Ikram ta ce.
"Teema ke naki sauraro da labarin wannan soyayyar taku."
"Hmm wata ranar Monday da mis.."
Kas maganarta ta tsaya ne sakamakon sallamar dasu Faruok sukayi tare da abokansa su uku.
Da sauri Fatima amarya ta rife fuskarta Faruok dai-dai inda take ya nufa ya zauna har suna gogar juna ya ce.
To
"Haba Amaryata daga zuwanmu kuma sai a rufe fuska?"
"Kai bama son iskanci kadai bari mu tafi."
Cewar Major Bilal.
Murmushi Faruok ya yi wanda ke ƙara masa ƙyau a koda yaushe, ɗaya daga cikin abokan nasa ne ya ce.
"Kaga Bilal gara muyi mutafi tun kafin ya kore mu gara mu tafi cikin arziki."
"Haka maganarka take Anwar dan haka sai muyi addu'a ko."
Sunyi addu'a kafin ƙawayen amarya su Ikram sukace masu sai sun bada kuɗin siyan baki kafin su tafi cikin wasa da dariya Bilal ya basu da hannunsa tunda sukazo Bilal yake kallon Ikram.
Bayan sun gama Faruok ya ce.
"To ai sai a tashi a tafi haka ladar ta isa."
"Au korarmu kake tun yanzu."
Dariya ya yi ya ɗauki hannunsa ya ɗaura kan kafaɗar Fatima ita ko nan mutuwar zaune tayi kirjinta sai dukan uku-uku yake.
Dariya sukayi gabaki ɗayansu suka tashi zasu fita har sunkai bakin ƙofa Bilal ya ce.
"Kai bama son iskanci kana nufin bazaka rakamu ba?"
"Kai kuna da matsala kunsan bana son nayi nisa da amaryata"
Yana maganar ne yana tashi a hankali ya ɗan sunkuyo da kai ya raɗa mata.
"Please kafin na dawo kiyi wanka ki ɗauro alwala dan godiya ga Allah."
"Kai wai kai wane irin dan iska ne da baza kazo ka rakamu ba."
Dariya Faruok ya fashe da ita sannan ya juya suka fita saida ya rakasu har wajan motocinsu suka fita mai gadi ya rufe sannan ya dawo, ɗakinshi ya wuce direct, bayan ya shiga bedroom ya ɗauki farin jallabiyarshi ya shiga badroom, bai wani juma ba a ciki ya fito da jallabiyar jikinshi yana goge ruwan da ke kanshi da towel.
Bayan ya aje towel ɗin ne ya juya ya fita, direct ɗakin gimbiya ya nufa yasa hannu ya tura ƙofa ya jita a rufe da key, cak Faruok yayi mutuwar tsaye dan yasan da gangan ta rufe ƙofar, ƙarfin hali yayi irin jarumta nan ta mazan fama ya fara knocking amma a banza bama tasan yanayi ba cikin sanyi murya ya ce.
"Please Fatima ki buɗe kofar kizo muyi sallah muyi addu'a idan yaso da mun gama sai ki rufe ƙofar please Fatima."
Tsaki tayi kawai ta gyara ƙwanciya, Faruok ya daɗe a tsaye bata buɗe ƙofar ba saida yaga da gaske take kafin ya juya ya koma ɗakinshi.
Faruok da Fatima haka suka ƙwana ko wanansu da abinda yake tunani su duka sai dai irin barawon barcin nan ya ƙwashe su.
Da asuba Faruok ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci dake kusa da gidansu wanda kana jin lokacin da ake ƙiran sallah.
Bayan Faruok ya dawo ya nufi ɗakinta yayi knocking ya ce.
"Fatima ki tashi lokacin sallah yayi idan yaso idan kika gama sallah sai ki koma ki ƙwanta."
Yana rufe baki ya juya ya koma ɗakinshi dan ya tabbatar da tajishi.
************
Da misalin 12:30pm
Ƙwance take sai juyi take da alamu yunwa takeji dan bazata iya tuna ranar data zauna ta natsu taci abinci ba, raban da tasa wani abu a bakinta tun jiya da zasu taho Pendo Ummi ta bata wani abu a cup ta sha, amma tayi wanka ta sauya kayan dake jikinta tasaka riga da wando irin fashion ne masu ƙyau sun ɗan kamata.
Fatima da taga babu sarki sai Allah yunwa na shirin kasheta yasa tatashi tun safe Faruok ke fama da ita ta buɗe ƙofa tazo suyi breakfast amma ta kiya, a hankali ta buɗe ƙofa ta fara tafiya kamar marar gaskiya, ajiyar zuciya ta sauke dan ganin babu kowa har parlour dake ƙasa kitchen ta nufa ta fara dube-dube taga duk ga komi nan na abinci babu abinda babu.
Gas ta kunna ta shiga fira arish potato.
Nan dai ta shiga girka abinda zata saka a bakinta, sauri-sauri take dan kada Faruok ya kamata.
Kafin ace maka me ko ina ya baɗe da kamshin girkinta.
Tsaye yake yana kallon duk wani bangare na jinta yana murmushi a hankali ya tako har inda take ya wani rungumuta ta baya ihu ta fasa ciki da tsoron shigowarshi.
"Please yaya Faruok meye haka?"
"Matata na kama ko na yi laifmeye
Ya furta cikin wata irin murya mai wuyar fasarawa..
Kash!!! kudaiyi hakuri muje zuwa..