08
8
***Zuba masa ido tayi kawai tana kallonsa cikin ranta tana jin wani irin bala'in tausayinshi saboda yana yin abu kamar wani wanda ya ɗan taɓu ko kuma ya zautu banda haka yanzu kalli fa a yanda ya fito ya taho office dinta dan kawai ya kirata a waya bai jita ba,ɗan tsakin da taji ya ja ne ya dawo da ita cikin hayyacinta,
"wannan yaron ko bacci yake yi bai tashi bane..... Na kira tana ta ringing bai yi picking ba"
"may be bai tashi daga bacci ba...."
"amma anya kuwa yana gari..... Nifa bana ganin shi ko a family house"
"shine dai nima ban sani ba dan na jima ban ganshi ba nima...."
"to babu matsala dai, zuwa anjima zan sake taɓa shi inji"
"ok"
"bari naje gida na shirya na fita office"
"ok to thank you"
Tashi yayi ya fita amma sai faman waiwayenta yake yi kamar yau ne ya fara ganin ta yayin da ita kuma ta janyo wani file ta bude ta fara rubutu aciki.
Bayan da Afeef ya koma bakin aikinsa gaba daya tattara maganar aurenshi da anty Mimi yayi ya ajiye a gefe dan a takaice ma shi ya manta da cewar akwai wani aurenta a kansa, baya waya da kowa sai Irfan kadai idan ya samu lokaci sai kuma mommy da daddy suma din kawai yana kiran su ne saboda ya kwantar musu da hankali domin duk ranar da basu ji shi ba hankalinsu tashi yake suyi ta tunanin ko ba ƙalau ba,kusan kullum sai yaga miss calls din yaya Aliyu amma bai taba kiran sa back ba abinda ya fara ƙonawa yaya Aliyun rai kenan shida anty Mimi dan a ganinsu wannan rainin wayo ne dan suna neman abu a wurin shi bashi ne zai bashi lasisi ko kuma damar wulakanta su ba yadda yaso,
Misalin ƙarfe 1 harda rabi na dare ya kira Irfan, yana kwance cikin dakinshi kuma dawowarshi kenan daga aiki, jin Irfan ya daga wayar ya sashi yin murmushi kafin a hankali yace,
"wai bacci kake yi?"
"wallahi idona biyu yanzun nan naje na dauko anty Mimi daga hospital na dawo da ita gida....." ai sai lokacin Afeef ya tuna da maganar auran shi da ita da kuma uban kiran wayar da yaya haidar ke ta faman yi masa babu dare ba rana,
"ohh matata ka dauko min daga aiki kenan.... Thank you for taking good care of her for me....."
Dariya Irfan yayi yace "you see your life?"
"yanzu dai menene labari? How is everyone? Ya anty Mimi hope she's fine?"
"baka da number dinta ne kake tambayata? Call her and ask....."
"yanzu ma sai da na gama waya da ita before na kiraka" ya fada cike da tsokana,
"kamar gaske...."
"am serious young man"
"yanzu dai wai zuwa yaushe zaka dawo?"
Ɗan dogon numfashi ya ja sannan a hankali yace "i don't know gaskiya.... I can't say, but idan na samu time zan zo"
Sun jima suna hira kafin suka yi sallama kowannensu ya ajiye waya, Irfan tunani yake yi cikin ransa anya kuwa anty Mimi da Afeef suna communicating? Dan bai ga alamar hakan ba dan baya mantawa tafiyar Afeef dinma shi take tambaya wai abokinsa yana nan kuwa taga bata ganin shi kwana biyu shi kuma yace ai ya koma calabar bai yi mata sallama bane? Daga haka yaga tayi shiru bata sake yin maganar ba,
A bangaren Afeef kuwa yana ajiye waya ya ɗan yi shuru na wasu yan mintuna kamar me yin tunani, iya gajeren wando ne a jikinsa tashi zaune yayi yana shawarar to ko ya kira yaya Aliyu yanzu? To kuma idan ya kirashi yanzu anya dare bai yi ba? Fasa kiran nasa yayi ya koma ya kwanta kan yar karamar katifarshi, kullum shi kadai yake kasancewa a ɗan karamin dakin nashi saboda tarbiyar da iyayenshi suka bashi duk wata rayuwar shashanci bata burge shi kuma baya cudanya da ita.
Jugum anty Mimi tayi bayan ta danna number yaya Aliyu tana jiran taji ya ɗauka, yana ɗauka taji yace,
"my love akwai wani labari ne?"
"gaskiya yanzu na fara zargin yaron nan da sanin sa yake kin daukar call dinka..... Kullum fa yana yin waya da Irfan, yanzun nan Irfan ya fita daga cikin bedroom dina kuma ya tabbatar min da ko a daren jiya sun yi waya, anya kuwa babu wani abu da yake shiryawa, ta yaya za ace baya ganin miss calls dinka and bai taba calling dinka back ba.... "
" calm down my love, bari zan sake kiran sa, mu bashi benefit of doubt.... Zan kirashi zuwa anjima sai naji me zai ce kuma wanne uzuri zai bamu.... "
" ka san me? Kawai idan ka same shi kasa shi ya sake ni a lokacin tunda already time din yayi har yana neman ya wuce.... Ni na gaji da wannan maganar guda daya, na kasa gane me yake nufi dani am tired.... "
Shi kansa yaya Aliyu jikinsa yayi sanyi da wadannan maganganun da yaji daga gareta amma sai ya dake yayi ta maza wurin kwantar mata da hankali, abun yana daure masa kai to me yasa Afeef zai yi masa wasa da hankali har haka? Rasa amsar da za ta dace da wannan tambayar tasa yayi dan haka ya tashi ya hau zagaya cikin dakin sa yana tunani,
"me Afeef yake nufi? Anya yaron nan yana da gaskiya kuwa?"
Kiran Afeef din ya fara yi a waya sai dai har tayi ta tsinke bai dauka ba, sake kira yayi nanma shuru ahaka har sai da yayi masa miss calls guda biyar a na shidan kuma yaji ya kashe wayar hakanne ya harzuka yaya Aliyu cikin takaici da damuwa yace,
" Afeef ni zaka kashewa waya? Okay yayi maka kyau...."
Wuni yayi cikin bakin ciki da takaici da ɓacin rai kuma har lokacin wayar Afeef a kashe dama yawanci sai dare aka fi samun sa, bai faɗawa Anty Mimi yanda suka yi da Afeef dinba kawai ya bar abin cikin ransa yana ta kokarin samun hanyar da zai shawo matsalar ko kuma ma ya magance ta gaba ɗaya.
Afeef yana ganin kiran yaya Aliyun yaƙi dauka saboda ko ya dauka bai san me zai ce masa ba shiyasa kawai ya zabi ya ki dauka din daga karshe da yaga baida niyyar daina kiran sai kawai ya kashe wayar wanda bai sake kunnawa ba sai da ya zo kwanciya da daddare, yana kunnawa kiran yaya Aliyu na shigowa, dauka yayi,
"Afeef menene haka? Haka muka yi da kai?" shuru Afeef yayi bai ce komai ba har sai bayan da yaji yaya Aliyun yayi shuru sannan a hankali yace,
"yaya haidar you are angry why? Kayi hakuri ni na manta ne ma gaba daya da wannan maganar fa, sannan 2 days banida lafiya kuma aiki yayi min yawa ka san yanayin aikinmu am soo sorry please" ajiyar zuciya yaya Aliyu ya sauke wanda yanzu yaji ya dan samu nutsuwa sannan kuma damuwarshi ta ragu,
"to ai Afeef duk kamata yayi kayi min bayani ba wai kayi shuru ba, baka picking calls dina baka kirana back..."
"am sorry yaya...."
"yanzu ya jikin naka? Dama akan maganarku ne da Mimi, time yayi da zaka sake ta..."
"alhamdulillah jiki da sauki,ok to shikenan yaya babu matsala zan sake ta..."
"yawwa Afeef nagode sosai, Allah ya bar zumunci, mun gode, tnx alot.... This means alot to us..."
"you are welcome yaya"
Sallama suka yi Afeef ya dora wayar akan kirjinsa ya lumshe idanuwansa sannan a hankali yace "am sorry yaya... I can't..... Dan Allah ka yafe min"
Da murna Aliyu ya kira anty Mimi bayan sun gama waya da Afeef tana dauka yace,
"my love ki fara shirin dawowa gareni dan yanzun nan muka gama waya da Afeef..."
"ya sake ni dinne?"
"no, ai saki ke zai kira ya fada miki my love, munyi magana"
Dan gajeren tsaki ta ja kafin tace "kai ma kana da abun haushi haidar, tunda ka same shi meya hanaka kasa ya sake ni?"
"zai sake ki baby.... Na fada miki munyi magana dashi"
Bata sake ce masa komai ba ta katse wayar dan haushi tana faman kunkuni, "wannan wanne irin rainin hankali ne kuke yimin daga shi har kai din, tunda ka same shi menene amfanin kirana da zai yi" shi dai yaya Aliyu duk tunaninshi zuwa washe gari Afeef zai sakar masa matarsa amma sai yaji shuru sannan koda ya kira wayar Afeef din rai da rai tana kashe, abin da ya sake ƙonawa anty Mimi rai kenan ganin har an sake share sati ɗaya babu wata sabuwar magana, bata son kiran Afeef din a waya amma gani take yanzu ya zamar mata dole ta kirashi da kanta tunda shi Aliyu ya kasa samun sa bayan kuma Irfan ya tabbatar mata da kullum shi suna yin waya da Afeef din.
Tana zaune tsakiyar gadonta ranta a cunkushe haka ma fuskarta ta soma kiran wayar tashi kuma bata san dalili ba haka kawai ta samu kanta dumu dumu cikin tsoro tsoron da bata san ko na menene ba ga faduwar gaba dan kirjinta tara tara taji yana duka musamman ma da taji wayar ta shiga har ta fara ringing,
"Assalamu alaikum.... Anty Mimi"
Lumshe idanuwan ta tayi ta finciko numfashinta da kyar take taji bakin ta kamar an kulle dan ta gagara furta koda kalma ɗaya,
"Hallo.... Anty Mimi" taji ya sake fada daga bangaren shi, daurewa tayi ta bude bakinta da kyar tace,
"Afeef baku gama magana da Haidar bane?"
"wacce magana?" take taji gabanta ya yanke ya faɗi da mugun karfi haka kuma tsoron da take ji shima ya sake karuwa da kaso mafi yawan na baya da take ji,
"maganar sakina da zaka yi...." shuru taji yayi kamar bama ya tare da ita,
"hello....."
"ina jinki anty Mimi.... I can hear you"
"maganar sakina da za ka yi ko baka ji ba"
"naji anty Mimi, yanzu ya za ayi?"
"ka sake ni shine yanda za ayi"
"yaushe?" taji ya bukata cikin rainin hankali banda haka ta yaya duk zai rinka yimata wadannan tambayoyin marassa amfani,
"yanzu" ta fada cikin bakin ciki da kuma bacin rai,
"ok to amma ai akwai abu ɗaya da bamu riga da munyi ba...."
"menene?" ta tambaye shi cikin sauri bakinta har yana rawa,
"ban dandani zumarki ba kamar yadda ka'idar take... "
Ji tayi idan har ta tsaya bashi amsa to tabbas za ayi abinda ba zai haifi ɗa mai ido ba, cike da bacin rai ta katse wayar tare da cilla jifa da ita ta fada can kan sofa bata faɗi a ƙasa ba, kugunta kawai ta rike cike da takaici, tabbas biri yayi kama da mutum, dama ashe ba banza ba yake ta faman yi musu yawo da hankali? Anya Afeef bazai basu matsala ba akan maganar sakin nan? Da sauri ta nufi wayarta ta dauka hannunta yana rawa tayi dialing number Aliyu..........