HAULA HABEEB

BABI NA TARA

by @amdeeytejjdunique587

BABI NA TARA





Ranar Ɗaurin Aure

HAZ Mansion

Ango Habeeb

Yana kwance a kan sofa, sweat pant ne a jikinsa ash color, ba riga sai murɗaɗɗen jikin da ko ina sai ma sha Allah. Kai ka ce ɗan wrestling ne. Idanuwansa a lumshe suke, kai ka ce barci yake yi, amma system ɗin da ke cinyarsa ma kallo yake yi a ciki. Kallon abin da ya faru ranar da wannan mahaukaciyar yarinyar ta zo masa office, ya yi split ɗin daidai wurin, ya cut sannan ya delete, yana jan tsaki.

Salim ne ya shigo ya same shi a haka, don a parlour yake. Kallonsa ya yi da mamaki, ya ce, “Wai kai me yake damunka ne?” Bai jira amsa ba, don ya san ba samu zai yi ba, ya ci gaba da faɗin, “A ce yau ɗaurin aurenka, yanzu fa sha biyu da arba’in da ’yan kai, ƙarfe ɗaya ake nema, kuma bayan juma’a ne auren nan. A ce wai kana kwance, ko alamun shiri ba ka yi.”

Bai nuna ya ji shi ba, balle ma ya ba shi amsa.

Salim ya gyara zama, ya fuskance shi sosai sannan ya ce, “Dude, ka san wani abu? Na san ba son auren nan kake yi ba, but ina so ka sani, tunda har ka riga ka amsa cewa ka karɓi auren, ina so ka yi haƙuri ka kau da komai, ka nuna farin ciki a fili. In sha Allah za ta zame maka alheri. Na san ko yanzu ka ce ma Daddy ba ka son auren zai fasa ɗaurawa, amma ka sani zai yi matuƙar farin ciki idan ya ga ka amshi zaɓinsa hannu biyu kana murna. Idan kuma ba ka so, shikenan ni zan je in gaya masa a janye auren. Ka ga idan ya kunyata a idon jama’a a kan ɗan da yake tunanin ko wuta ya ce ya faɗa, zai faɗa. Shikenan burinka ya cika.” Tashi ya yi zai fice, don lamarin Habeeb ya fara yi masa haushi.

Har ya fice bai ce masa ƙala ba, sai kallo da ya bi bayansa da shi har ya fice.

Shi kuwa yana fita ya bi ƙofar baya ya shige, don ba ya so hayaniya da tsokanar abokan wasa. Yana shiga ɗaki ya faɗa ban ɗaki ya yi wanka. Cikin mintuna da ba su wuce talatin ba, ya shirya tsaf cikin farar shadda da ta ji aiki na nuna wa sa’a. Ya yi kyau matuƙa, sai baza ƙamshi yake yi, kai ka ce shi ne ango.

Yanzu ma ta ƙofar baya ya bi ya fita, saboda masu zolaya. Yana fitowa haraba, ya samu an shirya motocin tafiya wurin ɗaurin auren, ana shiga. Shi ma shiga ya yi.

Sai ya kullo ƙofa, kafin ƙamshin turarensa ya kai ga mai hari. Juyowa ya yi ya kai dubansa gare shi da mamaki, don bai yi tsammanin ganinsa ba.

Yana zaune ya kwantar da kansa a jikin kujerar, kyau kam, Innalillahi. Farar shadda ce shi ma a jikinsa, ya ji aiki na gani na faɗa. Anko ne shi da Salim, sai dai aikin jiki ya banbanta. Sai hula da ya murza wacce ta dace kayan. Idanuwansa sakale da sun-glasses.

Bai ce wa Salim ƙala ba, har ya gama kallon nasa. Shi ma bai ce masa ba, an yi kai-da-kai.

Gate aka wangale, ɗaya bayan ɗaya suka fice suka ɗau hanyar masallaci. An yi sallah, daga masallaci aka wuce wurin ɗaurin aure. A masallacin anguwar su Anti Ummi ne za a ɗaura. Jama’a kuwa sun cika maƙil kamar za a kifa musu ƙwarya. ’Yan uwa da abokan arziƙi dama waɗanda sun zo ne kawai, wasu kuma sun zo ne don su ga HAZ Family.

Abokan Habeeb kuwa an sha ado na kece raini, don su ma sun zuba kyau ma sha Allah. Shi kuwa gogan, da ƙyar Salim ya shawo kansa ya fito ya shiga cikin abokai. Fuskar nan kuwa iya ƙoƙari ya yi wajen sake ta a wurinsa, amma ga mai kallo, hmmm.

Shi kuwa Salim sai murmushi yake zubawa kamar shi ne ango. Yana tsaye kusa da shi, ba ya matsawa ko nan da can. Sai gaisawa suke da jama’a fuska a sake. Photographers kuwa aiki ya samu, sai ɗauka suke. Masu waya ma haka. Shi dai yana tsaye, sai Salim ya mintsile shi ya yi yaƙe.

Daga cikin masallaci har an fara shirin ɗaurin aure, aka yi gadan-gadan ba ɓata lokaci. Waliyyai har sun fara tattauna abin da ya dace kan ɗaurin aure, kamar yadda addini ya tanadar, an yi nisa. Sai kuma aka ji sanarwar a dakata.

Abin da ya ba kowa mamaki kenan. Mata da ƙawayen amarya waɗanda suka leƙo don jiran a ɗaura su je su yi wa amarya guɗa, da sauran masu sauraro daga ciki, har sun fara ƙus-ƙus. Ba su kaɗai ba, har maza ’yan ɗaurin aure su ma, ganin har kusan mintuna talatin ba wani labari, nan ƙananan maganganu suka fara tashi, kowa na tofa albarkacin bakinsa.

Can kuma aka sake sanarwa a shirya, za a ɗaura aure. Bayan kammala komai bisa doron addini da al’ada, kowa ya baje malafar kunnuwansa yana jiran sanarwa mata da maza na waje da na gida. Nan aka sanar da abin da ba shi kowa ya zata ba, ba shi kowa ya buɗe kunne don ji ba.

“An ɗaura auren HAULA da HABEEB a bisa koyarwar addinin Islama, da sadaki mafi daraja, lakadan ba ajalan ba. HAULA ta zama matar HABEEB. Allah ya ba da zuri’a ɗayyiba.”

Wani shiru wurin ya ɗauka, kai ka ce mutuwa aka yi, kafin daga bisani maganganu suka fara tashi, kowa na furta abin da ke bakinsa. A wani irin hargitse, Salim ya kai dubansa ga Habeeb, kansa na wani irin sarawa. Shi kuwa ba za ka ce ga yanayin da yake ciki ba. Juyawa kawai ya yi ya shige mota. Hawaye suka zubo wa Salim a kan kuncinsa masu ɗumi, wata karyewar zuciyarsa ta yi. Abokinsa Fahad ne, ganin yanayin da yake ciki, ya kama shi ya shigar da shi mota, don ya san kukan me yake yi.

Mata da ƙawaye da ke tsaye ƙofar gate ɗin su amarya, suka haɗa ido. “Hibba ko Haula?” Suka tambayi kansu, da zakwaɗin gulma da ke cin kowacce, suka koma ciki don kai labari.

HAZ Mansion

Ta tashi daga cikin taron mutanen da take, ɗakinta ta shige. Ba ta tsaya a parlour ba, har bedroom, nan ma sai da ta shige bathroom ta murza makulli. Lokacin kiran har ya katse, kafin ta yi yunƙurin kira, wani kiran ne ya sake shigowa. Ɗauka ta yi, murya ƙasa-ƙasa a ɗan hassale. “Ta ce Smart, wai meye haka kake min wannan kira kamar na ci bashinka? Na ce ka daina kirana akai-akai irin haka. Taro muke yi, ko so kake sai asirinmu ya tonu?”

Cikin faɗa a hassale, ya ce, “To ba dole in kira ki ba, haka muka yi da ke. Ina batun yarinyar da muka yi kan cewa da ita za a ɗaura auren? Amma kawai na ji abin da ban zata ba. Me hakan yake nufi?” Cikin fushi ya ƙarashe maganar.

“Yana nufin komai,” ita ma ta faɗa a hassale, don ranta ya fara ɓaci.

“Me kake zato? Tunanin ka ka fi kowa wayo ne? To, kada ka manta waye Salahu ko? An gaya maka mahaukaci ne shi. Da daga nan an fasa aure kawai, sai in ce ga mata bai santa ba, bai san daga inda take ba, kawai sai ya aure ta. Sauran ’yan uwansa fa, daga ina zan fara? Me ya sa ba ka da tunani, mtsww?” Ta ƙarashe maganar da tsaki.

Shiru ya yi, kafin daga bisani ya ce, “Kuma haka ne, ni ma yanzu na fahimta. Amma kina ganin waccan yarinyar za ta ba mu abin da muke so?”

“Ka bar wannan zancen, za mu yi daga baya. Ka san akwai jama’a yanzu, kuma zan fi samun natsuwa, sai mu tattauna abin da ya dace.”

“Okay, ba damuwa.” Daga haka ya yanke wayar daga can.

Ta yi murmushi bayan ta sauke wayar daga kunnenta. Ashe duk bayan jira da ta daɗe tana yi, nasara zai zo mata cikin sauƙi, don ga shi komai yana tafiya yadda ya dace, ba wata matsala. Ta yi murmushi, kafin ta fice daga ɗakin.





A parlour kuwa, ’yan ɗaurin aure ne suka dawo. Daddy ne a gaba, su Salim suna biye da shi, da su Uncle Bulama, amma banda Habeeb, don shi sashensa ya wuce kai tsaye da abokansa. Shi ma Salim ɗin wucewa ya yi ɗakinsa. Kallon Mommy da fitowarta main parlour kenan, tana yi wa masu aikin abinci magana Daddy ya yi, sannan ya ce ta same shi a ɓangarensa. Daga haka ya wuce. Sai da ta gama maganar da take yi, sannan ta rufa masa baya.

A can parlour na Daddy kuwa, kowa ya hallara, duk manyan family ɗin har waɗanda suka zo aure. Bayan Mommy ta shigo, Daddy ya ce ta je ta kira mai Gwaggo.

Haula

Yau tunda ta tashi take jinta wata iri. Ta kasa morar kanta. Tunda ta yi sallar asuba da ƙyar ta kwanta, ta kasa tashi a inda ta kwanta, don ko gado ta kasa samun arziƙin komawa. A inda ta yi sallah a nan ta kwanta. Ba irin maganar da Gwaggo ba ta yi mata ba, amma ta yi shiru, ba don ta kasa tashi ba ko ba ta ji ba, sai don yadda take ji an ɗaure ta. Ba ta taɓa jin irin wannan yanayin ba tunda take.

Yanzu ma Gwaggo ce ta shigo ta same ta a inda ta bar ta tun ɗazu. “Haula, wai ke, yau me ke damunki? Tun safe kike kwance a nan, ba irin maganar da ban yi miki ba kin share ni. Ko abinci ba ki ci ba, ga shi har rana ta yi. Ko ba ki da lafiya ne?” Cewar Gwaggo cikin kulawa.

Kuka kawai ta fashe wa Gwaggo da shi. Nan hankalin Gwaggo ya tashi, a rikice ta fara tambayar ta me ya faru, me ke damunta. Ta rungume ta tana rarrashinta haɗi.

Sai da kukan ya fara sassautawa, kafin ta ce, “Gwaggo, ba na jin daɗi ne, kuma lafiyata ƙalau. Wani yanayi nake ji kawai, wanda ba zan iya ba shi suna ba, amma tunda nake ban taɓa jin irin haka ba.” Cikin kuka ta ƙarashe maganar, don ita kanta ba ta san me ke damunta ba.

Sake rungume ta Gwaggo ta yi. Ta yi mata addu’a, ta tofa mata, kafin ta ce, “Ki tashi ki ci abinci. In sha Allah, ko ma me zai faru alheri ne.” Ta janyo farantin da ta haɗa mata abinci a ciki. Shayi ta fara ba ta a baki, a hankali  ta karɓa, sai da ta sha rabin kofi sannan ta kau da kanta. Abincin shi ma ta buɗe lafiyayye, sai tiriri yake yi yana tashin ƙamshi. Ƙofar da aka ƙwanƙwasa shi ya katse hanzarin da za ta ɗaga mata abinci a baki.

Tashi Gwaggo ta yi ta je ta buɗe ƙofar. Mommy ce ta bayyana. Saƙon da Daddy ya sanar mata ta yi, wucewarta ta yi ba ta jira ta amsa ba. Cikin mamakin dalilin kiran ta dawo cikin ɗakin. “Ki ci abincin, ina zuwa. Alhaji ne ya aiko a kira ni, ina zuwa yanzu.” Mayafinta ta ɗauka ta yafa, ta fice, kafin Haula ta fara tsare ta da tambayoyin da ita ma ba ta san amsarsu ba.