Shafi na ɗaya
🌏 YARIMA BAHJAT 🌏
Na
Harira Salihu Isah
(Uwar Batoorl)
𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠
اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW
Dukkan godiya sun tabbata ga Allah(SWT), da ya ba ni ikon kawo muku labarin sarauta kamar yadda na alƙawarta muku tun bayan kammala ƳAR KARUWA, amma da yake Allah bai nufa ba har muka yi SHAAMEEƘH da NAUYIN BAKI, sai yanzu Allah ya Ƙaddara, to alhamdulillahi, Allahumma ya ba mu ikon kammalawa lafiya, ya kuma haɗa mu a kan ladan duk abinda ya zo na faɗakarwa, ya yafe mana kura-kurai.
GAISUWA DA JINJINA
Ni Uwar Batoorl ina gaisuwar jinjina ga duk masoya masu ƙwarara guiwa da ƙarfafa guiwa a gare ni, a saya littafina a yaba mini, a alkairanta mini a kuma a bi ni da addu'o'i, ina jinjina a gare ku, Allah ya muku ninkin wanda kuke mini daga addu'o'i har abin arziƙi, Allah ya taya ni gode muku, madallah da ku.
MASU TALLA ƘOFA A BUƊE TAKE, KU HANZARTA DOMIN AYI INGANTACCIYAR TAFIYARNAN DA HAJARKU, KU KAWO TALLANKU CIKIN AMINCI A TALLATA MUKU SHI CIKIN ANNASHUWA DA SHAUƘI, KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAMBA ***.
MADALLA DA KUU, UWAR BATOORL TA KUUU.
SHAFI NA ƊAYA.....
MADUBI
A wasu lokuta da dama, Buri, Muradi, da Nufi, abubuwa ne mabanbanta da su ke bisa doron hanya ɗaya, domin ana iya ɗaura su a mizani guda, kamar yadda su ke sarƙafe da zare guda ɗaya, wato zaren Ƙaddara. Idan aka ce Ƙaddara ana nufin abinda Allah ya rubuta ya kuma zana zai wanzu a rayuwar bawa tun ma kafun samuwar bawan, abu ne wanda bawa ba ya taɓa kauce masa, haka kuma ba ya taɓa iya guje masa duk tsanani kuwa. Ƙaddara wata kalma ce da ke ɗauke da fuska biyu, tsari biyu, zubi biyu, zane biyu, wato kyakkyawa da kuma kishiyarta.
A zahirin gaskiya, muna saƙa burukanmu ne kawai da kuma muradanmu, haka ma muna nufin wasu lamuranmu ne ba tare da mun duba cewa Ƙaddara ba ta ba da zaɓi ba, tabbas Ƙaddara ba ta bai wa bawa zaɓi, duk da a wasu lokutan Ƙaddara ta kan zo kafaɗa da kafaɗa ne da muradan mu, amma a wasu lokutan shatale ƙafafuwan burukan mu take ba sani ba sabo, wanda hakan ya isa ya shaida wa bawa, wannan kalma ta, "Tun ran gini tun ran zane", wato bawa ba ya tsallakewa Ƙaddararsa.
Sarki ya yi wa Baiwa alƙawarin abinda ke cikinta sai ya mulki MASARAUTAR BAHJA har ma ya kai ga kanzaƙin raɗa wa abun cikin suna tun bai shaƙi iskar duniya ba, sai dai kuwa yayi shuka ne a idon makorwa, da saninsa ko ba da saninsa ba ma ce ba, domin masu haƙiƙanin gadon sarautar sun ce sa ji sa gani ta yadda za a binne tsohuwa da ranta.
To jama'a, ga dai buruka da muradai, amma kuma ba wanda ya san me alƙalamin ƙaddara ta riga da ta zana tun fil'azal.
YARIMA BAHJAT, waye Yarima Bahjat?
Masarautu uku ne, kuma mabanbanta, ɗaya bai yi kamanceceniya da ɗaya ba a ta ko wace fiska, kamar yadda ɗaya ba lallai idan ya na da labarin ɗaya ba, haka zalika a ko wanne masarauta da kalar badaƙala, ta'asa da zunzurutun rikitattun lamura da ke tafiya, waɗanda duk yadda za a ba ka su a taƙaice, ba za ka taɓa fahimta ba sai ka tsunduma cikin labarin gadan-gadan, idan kuwa ka na son banbance zare da abawa yadda ya kamata, to ka tabbatar da ka dangana har i zuwa shafin ƙarshe na labarin, sau da ƙafa ba tare da tsallake ko shafi guda ba.
****
⭐️
SHEKARU ƊARI DA ASHIRIN BAYA (1906).
MASARAUTAR BAHJA
"Ni Gamboji ɗan Rani jikan Fari, na yiwa baiwa Kubura alƙawarin abinda ke cikinta sai ya mulki wannan Daula, yaron da ke cikin ki zai mulki masarautar Bahja muddin ina numfashi, kai ko ba na numfasawa sai abinda za ki haifa ya hau wannan karagar."
Tsamurmurin tsoho kucuf ɗin ya dire maganar ya na yawatawa da zuru-zurun Idanuwansa, cikin tambatsetsen ɗakin, wanda ya ke musamman domin zaman ahalin gidan sarautar, a yayin tattauna muhimmiyar magana tsakanin su.
"Maganarka dutse sarkin sarakuna, sha kundum kake, girgije rufe samaniya, kwangiri ƙarfen jirgi, inuwar gajimare ga sanyi ga ruwa, garkami kake wandon ƙarfe, koren ganye maji yaji, ludayi mashaya, ka faɗa ta zauna, ko a so ko a ƙi dole a bi ta taka, hattara dai hattara dai......"
Yamushashshen busashshen hannun da tsamurmurin tsohon ya ɗaga, shi ya katse ƙirarin da ba-faden ke yi, ya kuwa yi ƙasa da kansa gami da ɗaga hannunsa yana jinjina, alamar ban girma ga tsohon.
Shiru ne ya ratsa isashshen ɗakin, kaf al'ummar dake ɗakin da suka ɗara goma sha, kawunansu na ƙasa, ba wanda yayi ƙwaƙƙwaran motsi, balle zancen ɗagowa, ko ayi tunanin samun mai ja da kalaman yamutsatstsen Sarkin.
Sai da ya gama kalle su da yanayinsu tsaf, sannan ya tsayar da idanuwarsa a kan wata dattijuwar tsohuwa, wacce ke zaune cikin shiga ta alfarma da alkyabbarta, kai ka ce ita ce sarkiyar.
"Magajiya"
Ya ƙira sunanta da dakakken muryarsa mai cike da isa irin ta Sarkin da ke ji da kansa, musamman ma ka saurari muryar da kyau kai ka ce, ba shi ne a ido a tsamure a bushe haka ba.
"Na'am! Allah yaja da ranku"
Dattijuwar ta amsa da basarakiyar muryarta, kanta a ƙasa har lokacin kamar dai ta sauran ƴan ɗakin.
"Dodon magauta dodon mahassada, sha kundum Sarki mai zamani goma, ka ga shekaran jiya ka ga jiya, yau ma ga ka kana ganinta, goben ma taka ce ba wata haufi, ka yi ƙira an amsa, ka tafi an bi ka, ka ce kuma dole ayi ta taka, Magajiya Uwar gari Innar Bahja ta amsa, ta gaishe da Sarkin sarakuna...."
Kambaban da dogarin ke yi ya dakata, saboda jinjina kai da tsamurmurin tsohon Sarkin yayi.
"Magajiya mun ba da ajiyar baiwa Kubura gare ku, mun ɗaura muku nauyin kula da ita da komai da ya shafe ta, daga nan har zuwa sanda za ta sauƙa, muna kuma kyautatta muku zaton za ku kula da komai cikin aminci, kamar yadda kuka saba a mabanbantan lokuta, domin tabbas ku ɗin masu adalci ne masu kula da na ƙasa da su mun shaida, duk yadda ake ciki kuma idan da wani abu, ku turo Jakadiya kai tsaye ta sanar mana."
Tsamurmurin tsohon Sarkin ya ƙarishe maganar ya na miƙe ƙafafuwansa, da idan ka kallesu a yanda suke, idan ba tafiya ka ga ya na yi ba, za ka ci Ƙur'ani da malami wajan cewa ƙafafuwan ba sa da sauran laƙar tafiya da mai su a kan diga-digansa.
"An gama shugaba, za mu kula da komai yadda kuka ce, mu na kuma yi mata kyakkyawar fatar sauƙa lafiya, Allah ya kawo mana Yarima na gaba lafiya, Allah ya raba su lafiya."
"Amin Ya Rabbi"
Kusan kaf jama'ar ɗakin suka amsa a fili amma da ladabtaccen murya, cikin girmamawa ga Magajiya da ma mai ɗungurungun gaba ɗaya Sarki Gamboji.
Gyaran murya da Sarki Gamboji yayi shi ya sanya dogarin tafa hannayensa, kafun kiftawar ido sai ga dogarawa fin biyar sun shigo, guda uku suka koma daga bayan Sarki, guda uku suka tsaya a gabansa suka baza manyan rigunansu, sai da Sarki Gamboji ya tsaya bisa ƙafafuwansa ya daidaita, sannan ya kuma yin gyarar murya, hakan ya sa cikin hanzari dogarawan gaba suka sake manyan rigunansu da suka baza, suka fara tafiya a sannu a hankali, ana tafe a na zabgawa Sarki Gamboji kirari da kambaba, har suka bi ta wata hanya suka bar ɗakin taron.
Da fitarsu ko ƴar daƙiƙa babu tsakani wasu dogarawan huɗu suka shigo, biyu suka tsaya daga gaban Magajiya, biyu daga bayanta, ta miƙe, sai da ta daidaita ta yi gyaran murya sannan su ma suka fara takawa har suka fice a ɗakin, su na tafe su na zabga mata kirari.
"Takawarki lafiya Magajiya, takawarki lafiya Uwar gari, gaba salamun baya salamun Innar Bahja, hattara dai hattara dai, gafara dai gafara dai ga mace mai kamar maza, mace wacce ba ta tsoron wowa, hattara dai hattara dai ga kallabi tsakanin rawwuna, dama da hauni lafiya dai zakanya, takawarki lafiya, gaba salamun baya salamun fara mai farar aniya....."
Haka yake ga tilon yaron Sarki Gamboji, wato Abdi mai jiran gado, yadda aka takawa mahaifinsa Sarki da goggonsa Magajiya ana kurara su, shi ma haka aka masa, sannan sauran jama'un suka fara tashuwa su na ficewa ɗaɗɗaya-ɗaɗɗaya, tun daga kan matar Abdi, wacce ta kasance uwar gida, mai bi mata, har zuwa ta ƙarshe, sai kuma ƴaƴansa wato jikokin Sarki Gamboji, daga kan manyan suka fara ficewa, duk wanda ya miƙe zai fita to sauran kan su na ƙasa, har dai ɗakin ya rage iya Jakadiya da kuma baiwa Kubura.
"Ma ji ma gani, idan tusa za ta hura wuta."
Jakadiya ta faɗa a zuciyarta ta na mai miƙewa tsaye bayan ficewar ƴar ƙaramar yarinyar Abdi.
Takawa tayi zuwa wajan da Baiwa Kubura ke zaune kanta a ƙasa.
"Kubura."
Jakadiya ta ƙira sunan baiwar fiskarta ba yabo ba fallasa, sai dai shiru Kubura ba ta amsa, kai babu ma alamar Kuburar ta san da wanzuwar halittar Jakadiya a wajan.
"Kubura."
Ta ƙira sunanta da ɗan ƙarfin sauti a karo na biyu.
"Ke Kubura!"
Ta sake ƙiranta a karo na uku, sai dai a yanzun ta kai hannu ta dafa kafaɗarta gami da jijjigawa, wanda hakan ya taimaka wajan dawo da Kubura duniyar zahiri cikin ɗimuwa da tarin fargaba, damuwa da tsananin firgici.
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un!"
Baiwa Kubura ta furta da muryarta mai sanyi sosai, domin damuwar da take ciki bai shafe sanyin muryarta ba.
Hannunta ta kai ta dafe mararta, da tun sauƙar kalaman Sarki na farko a kunnuwanta, ta ji maran ya wani irin karta mata, saboda yadda ta ji sauƙan kalaman nasa tamkar sauƙar aradu.
Ita Kubura ne sarki ke alƙawarta mata abun cikinta zai mulki Bahja? Bahja dai? Ƙasaitacciyar masarautar da ke da magada masu jiran gado ɗaiɗai har goma sha ɗaya, ƴaƴan sunna ƴaƴan aure, tsayayyun maza goma da mace ɗaya, iyayensu isassu ma su ji da kansu da sarauta, ita wa? Ita a wa? Wai kare da gudun layya.
Baiwa Kubura take ƙasƙantacciya ko a cikin bayi, lallai wannan kalaman na Sarki ba ta hanga ta ga dalilin yiwuwarsu ba, ko ta yadda za a yi su tabbata, domin tana da tabbacin kafun aje ga ingantan ƙaramin cikin jikinta, tuni za a shafe babin rayuwarta a doron ƙasa, kalamannan na Sarki na nufin gayyato mata mutuwa ne ta na zaman zamanta, duk da ma daman ta san za a rina wai an yi wa mai tsayuwar dare gafara, tun sanda ta shiga cikin jerin bayin da ɗan Sarkin zai kusanta, ta san da cewa kwanakin da suka rage mata a raye ƙidaddu ne, ga kuma wata masifar da ba a saka mata rana, ciki, wai ciki ne da ita, cikin da take da tabbacin samuwar sa ne zai sake kusanto da kwanakin mutuwarta, lallai idan Sarki Gamboji ya kasance tamkar mai magana da wahayi a bakinsa, komai ya ce zai tabbata, a wannan karon dole za a samu akasi, cikin jikinta ba ta ji kamar mai ingantuwa ba ne, balle a kai ga ya girma, har ma a haife shi, kai to ko an haife shi ma bisa lalurin hasashe, wa ke da tabbacin Yariman za ta haifa? Wa ke da tabbacin namiji ne ɗan tayin da ke cikinta? Sanin abinda ke cikin mai ciki sai Allahn da ya ajiye halittansa da kansa....
Taɓa ta da ƙiran sunanta da girgizata da Jakadiya tayi a lokaci guda shi ya katse mata zancen zucinta.
"Na'am, ranki ya daɗe Jakadiya, mai magana da yawun Sarki."
Baiwa Kubura ta yi maganar kanta a ƙasa ta na jinjina hannu ga Jakadiya, idanuwanta kuwa taf da ƙwalla.
Jakadiya ba ta amsa ba, sai hannayenta duka da ta saka ta riƙo kafaɗun baiwa Kubura ta taimaka mata wajan miƙewa tsaye, a lokacin da take ƙoƙarin tofa albarkacin bakinta, sai dai abinda ta gani ya sa ta haɗiye kalamanta ba shiri, sanin komai ya faru da baiwa Kubura a daidai wannan lokaci, lallai alhaƙin ayar tambaya a kanta zai faɗi, ita za'a iza wa jakar tsaba, to ai ko ba za ta bari ta amo da gashi ba bayan ba ta ci buzu ba.
"Na shiga uku, me zan gani Kubura?"
Da sauri Kubura ta juya da idanuwanta tabi inda Jakadiya ke bi da kallo.
"Jini! Cikin ya zube, shikkenan ya zube tun ba a je ko ina ba."
Kubura ta faɗi a zuciyarta tana runtse idanuwanta, cikin rashin sanin taƙamamman yanayin da za taji.
"Kin ga muje."
Jakadiya ta faɗa cikin azama ta na riƙo hannayen Kubura suka fice a ɗakin.
Ko da suka isa sashin Magajiya, ba su wani tsaya ɓata lokaci ba, da yake tun-tuni Magajiya ta sa an sanar da dogaran ƙofa, cewa Jakadiya da baiwa Kubura za su shigo wajanta.
"Rankishidaɗe Magajiya Uwar gari, Allah yaja da ranki, Allah ya taimakeki, Magajiyar Sarki, kwale-kwale jirgin Hausa..."
"Me ke tafe da ku?"
Magajiya ta tambaya tana mai katse Jakadiya.
Tiryan-tiryan Jakadiya ta kwashe yadda ta ga jinin a jikin Kubura ta sanar da Magajiya, ita kuma Magajiya ta aika ƙiran Ungozamar fada, Jakadiya kuwa ta fice domin sanar da Sarki Gamboji a kan kari.
"Allah ya taimakeki, wannan ganyen ba ki laulayi ba ki ɓari ne, wannan kuma ƴaƴan itaciyar haihuwa lafiya garau, wannan kuma....."
Ungozomar ta yi wa Magajiya bayanin duka magungunan cikin girmamawa, domin bayan ta amsa ƙiran Magajiyar ta zo da kayakinta, kafun ta fara komai sai da Magajiya ta nemi ƙarin bayani, saboda so take ta kula da ajiyar ɗan uwanta Sarki Gamboji cikin tsaitsani da ta-ka-tsantsan.
****
Jakadiya ta samu sanar da Sarki halin da ake ciki, ta kuma sanar masa da ƙiran Ungozomar fada da Magajiya ta aika ayi cikin gaggawa.
"Za ku iya tafiya"
Tsamurmurin tsoho Sarki Gamboji ya faɗa a taƙaice, hakan ya sa Jakadiya sake kwasar gaisuwa sannan ta miƙe ta tafi.
A zahiri a kan fiskar Sarki Gamboji ba za ka fahimci, damuwa ko tashin hankalin komai ba, amma a can cikin zuciyarsa tsoro ne tsantsa, na abinda ka iya faruwa ga cikin, musamman da ya kasance ƙarami, ya na cikin matakin hatsari ne, tunda bai yi ƙwari ba.
Tuna cikin zai iya zubewa ya sanya shi yin gyaran murya mai amo, dogarawan suka gyara manyan rigunansu ya miƙe tsaye, sai da suka raka shi har zuwa bakin turakarsa sannan suka tsaya daga bakin ƙofa, fadawan ƙofa suka buɗe masa ya shiga suka kuma jawo ƙofar suka rufe.
Cikin damuwar da ta bayyana a kan yamushashshen fiskarsa, da fatar ta gama tattarewa da yamushewa, ya ja wani kakkauran numfashi ya sauƙe, sanda ya tsaya a gaban wata daskararren ruwa a zahiri, amma ya na kai hannunsa kai sai ya koma narkakken jini, a haka ya ɗiba ya wanke fiskarsa, daga haka ya rufe ido ya fara karanta wasu kalmomin surƙulle.
A wani duhuwar baƙiƙƙirin ɗin kogo ya tsinci kansa tsirara haihuwar uwassa.
"Dodongaji na kan dutse, dodon gaji tsohon bamaguje, dodongaji..."
"Sarki Gamboji mun san me ke tafe da ku, sai dai komai da ya faru ko ya ke shirin faruwa ku ne kuka ja, tunda kun kwana da sanin a bar kaza a gashinta ya fi a figeta, domin maganarka daidai take da ƙararrawar jirgi mai ta da hankalin fasinja."
"Dodongaji kar ka ce mini cikin ya lalace kenan, kar ka ce mini duk yadda nake tunanin na buga sammako wani a tafe ya kwana, dodongaji kar ka....."
"Me yasa kayi shuka a kan idon makorwa?"
Boka dodongaji da ke zaune shi ba a sama ba shi ba a ƙasa ba, ya jefawa Sarki Gamboji tambayar ya na zuba wani abu a cikin wutan da ke a gabansa, wanda shi ma wutan ke hure a saman iska, shi ba a sama ba kuma shi ba a ƙasa ba.
⭐️
SHEKARU SHIDA BAYA (1900)
MASARAUTAR ANFA
Durƙushe take a kan guiwowinta, ga turtsetsen cikinta da yayi ƙasa, banda zufa ba abinda take sharcewa, wani irin murɗa, mararta ke mata, ga wani irin azabar da take ji a bayanta, domin ji take kamar a na bubbuɗa ƙashushuwan bayanta, ba dan kar a ce zafin ciwon naƙuda ba ne, da ta ce har ƙarar buɗewar ƙashin kunnuwarta na jiyo mata.
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Innalillahi wa inna ilaihiraji'un."
Kalmar shahada kawai take maimaitawa cikin tsananin azabar ciwo da ficewar hayyaci, ta na salatin tana kai hannunta baki ta rufe domin kada sautinta ya ja hankulan mutane.
"Rankishidaɗe dan Allah dan Annabi ki bari na ƙira miki mai karɓar haihuwa, ko kuwa na sanar da Jakadiya ta sanar da mai martaba halin da kike ciki, Rankishidaɗe haihuwa daga ni sai ke a nan ɗakin tamkar daɓawa kanki wuƙa za ki yi, ban taɓa haihuwa ba, ke ma wannan ne haihuwarki ta farko, ba abinda muka sani, idan wani abu ya faru fa Rankishidaɗe?"
Hadimar tayi maganar a sigar tambaya, ga hawaye wani na bin wani a fiskarta, saboda tsantsar tsoron abinda ka iya faruwa, ta san gidan sarauta ta kuma san hukunce-hukuncensu, idan wani abu ya samu Fulani Babba ko abinda za ta haifa, lallai-lallai ba za a bar ta da rai ba, a gefe guda kuma tsantsar tausayin Sarauniya Hajara ne maƙil a zuciyarta ya cika ya tumbatsa, ganin halin da take ciki, sosaima take tsoron haihuwa, domin ba ta san ciwon haihuwa ya kai har haka ba, bata ma taɓa ganin inda ake haihuwa muraran ba sai a yanzu, a baki take jin cewa haihuwa yaƙin mata, ba ta san dambarwar da ake wajan yaƙin ya kai har haka ba, lallai mata na cikin jarabawa.
"A..a...A'a"
Fulani ta fisgo maganar da ƙarfi saboda wani irin ciwon da ya sake murɗarta.
"Ba...ba..ba na so kowa ya san ina naƙuda...ba..ba..ba na so a san na haihu...ba zan iya bari a cutar mini da abinda zan haifa ba, ba zan iya bari ba, idan kuma na bari aka san da ina wannan halin, to banda yadda zan yi, ina ji ina gani, za a salwantar mini da rayuwar abinda Allah zai bani ba yadda na iya, na yi imani komai na faruwa ne bisa yarjewar Ubangiji, amma duk da haka sai ka tashi sannan Allah zai taimake ka, Fir'auna ma a baya Ubangiji ya ba shi iko ya dinga zuba ɓarna a ban ƙasa, balle kuma wasu azzalumai na zamanin yanzu da ba su ma kai shi ba, ba zan iya ba, ba zan bari abinda zan haifa ya salwanta ba."
Fulani Babba ta ƙarishe maganar a tare da wani irin kuka mai tsuma zuciyar uwar da ta san maƙiya na dakon jiran zuwar abin da za ta haifa, sun gama shirin salwanta shi tun bai fito duniya ba, ta kuma tabbata muddin su ka san ta na naƙuda a halin yanzu, to tun kafun ciwon azabar ta sake ta za su aikawatar da mugun nufin su a kan abinda ke shirin zuwa duniyar, ita da su kifi na ganinka ne mai jar koma, ta san da shirin su, dan haka a matsayinta na uwa za tayi komai dan kuɓutar da ɗan ta, ko da hakan na nufin ƙarshen rayuwarta ne.
Wani ciwon da ya kuma taso mata shi ya saka ta katse kukan don dole, ta kama nishi gadan-gadan, a kuma daidai lokacin ne suka ji an kama ƙofar ɗakin an turo.
Da wani irin sauri Hadimar ta waro idanuwanta cikin tsoron da ya fi na farko, kamar yadda a gefen Fulani babba tunanin shikkenan tata ta ƙare, shikkenan burin maƙiya ya cika, shikkenan za ta sha wahalar naƙuda a banza, tunda ta faru ta ƙare wai an wa mai dami ɗaya sata.
Duk ɓuyanta shikkenan sun ji labari har sun zo domin aiwatar da nufin su, hakan ya sa wani kuka ya zo mata a tare da nishin da yayi sanadin fitowar abin cikinta
TO FA! ƘAƘAƘARAƘAƘA!!
Follow my page's
●WATTPAD
@Uwarbatoorl96
●AREWABOOKS.
@Uwarbatoorl96
●TIKTOK
@Uwarbatoorl96