YARIMA BAHJAT

Shafi na biyu

by @uwarbatoorl96

YARIMA BAHJAT 🌏

Na

Harira Salihu Isah

(Uwar Batoorl)

SADAUKARWA

Wannan labari kacokam na shi sadaukarwa ne gare ku ƴan uwana

HAUWA'U SALIHU ISAH

IKILIMA SALIHU ISAH

SALIMA SALIHU ISAH

TUKUICI

A ko da yaushe muddin Uwar Batoorl za ta ɗauki alƙalami da sunan rubutu, to tabbas zai kasance tukuici ne a gare ka SIR ABUBAKAR SADEEQ, CEO LAFAZI WRITERS ASS. Tare da ɗaukacin members namu, Allah ya agajemu a lamuranmu ya tallafa mana alƙalumanmu.

GORO

Littafina goro ne a gare ku Iyayena da Mijina, Allah ya jiɓanci lamuranku duniya da lahira, Rabbi ya muku buɗi ta alkairin duniya da lahira, yanda kuka tsaya kuma kuke kan tsayawa a lamurana, Rabbi ya tsaya muku duniya da lahira..

FATAN ALKAIRI

ina miƙa gaisuwa da fatan alkairi gare ku

MALAM LAWAN M. PRP

da Yayana MALAM YUSUL GUMEL

Yadda kuka ba da gudumawa a rubutuna, Allah yayi riƙo da hannayenku a komai har ƙarshen rayuwa, Allah ya kuma saka da maɗaukakin sakamako.

MASOYA MABIYA LABARAN UWAR BATOORL, KU NE UWAR BATOORL, IDAN BABU KU TO TABBAS BABU UWAR BATOORL.

SHAFI NA BIYU

⭐️

"Zancen banza zancen wofi ma kenan, wai ƙafa ya mutu ya bar takalmi, wannan ai labari ne da kunne ba zai ɗauka ba, yaushe ma Fulanin ta fara naƙudar da har za a ce an nemi abinda ta haifa sama ko ƙasa an rasa, ah, akwai lauje cikin naɗi."

Fulani Samira tayi maganar cikin karaji da tsantsar ɓacin rai, domin gani tayi ana shirin yi mata sakiyar da ba ruwa, ya za a yi ma ta gama shirinta tsaf, sannan a ce Fulani ta haihu ba abinda ta haifa, kai ba a ma san me ta haifa namiji ne ko mace ba, wannan yana nufin lalata shirinta na tuntun da ta gama tun kafun shigowarta gidan sarautar kenan, ina ba zai saɓu ba wai bindiga a ruwa, ba za ta bari a yi mata sagegeduwa ba.

"Allah ya huci zuciyarki giwar mai martaba, fara mai farar aniya, farar mace alkyabbar mata, nan a ganki nan a barki, kuturwar uwa zama dake dole, ke ce a kan gaba saura sai dai su biyo bayanki, tauraruwa a zuciyar mai martaba, uwar ɗakina aljanna mai masoya da yawa, ina gwanar wata ga tawa...."

"Ke Suwaiba dakata da wannan ɓaɓatun naki, maza-maza kiyi hanzarin feɗe mini biri har wutsiya, garin Yaya haka ta faru? Ki faɗamun gaskiyar yadda aka yi aka haihu a ragaya, yaushe ma Fulanin ta fara naƙuda ba labari?"

Fulani Samira ta jehowa Hadimar tambayar, domin tana gaf da ɗaura hannu a ka ta kwarma ihu, idan ba ta ji sahihancin zancen ba.

"Uwar ɗakina kin san ba zan miki ƙarya ba, wallahi haka zancen yake tsaf na rawaito miki shi babu wai, Fulani Babba ta sauƙa amma babu abinda ta haifa babu labarinsa, da ina tafiya ne naji wasu dogarawa na maganar, wanda da alama an sanar da Mai martaba ne a lokacin, to tun kafun wankin hula ya kai ni dare, nayi maza na je har sashin Fulani domin ganin ƙwaƙwaf, na kuwa gano har hanji, domin ganin idanuwana da jin kunnena, Fulani kuka take haiƙan-haiƙan tana surutai, a kan dai wannan labari da na kawo miki."

Baiwa Suwaiba da ta karkace tana zuba zancen cikin ƙwarewa a munafurci, har da gyara zamanta irin ta kawo labarin arziƙin nan, wacce a ganinta ya ma ci a yaba mata har ma da ƙarin tukuici.

"Tashi ki fice."

Fulani Samira ta faɗa cikin hanzari ta na nunawa Hadima Suwaiba hanyar fita.

Cikin hanzari Hadimar ta miƙe ta na sake kurara Fulani Samira, gami da ba ta haƙuri Allah ya huci zuciyarta, wani kallon da Fulani Samira ta mata saboda ɓata mata lokaci da take yi, ya sa ta fice da mugun sauri har tana tuntuɓe.

Fulani Samira ta kai gauro ta kai mari, a cikin mamakeken ɗakin nata, wanda ya haɗu ya kuma gaji da haɗuwa, da kayan alatu na gidan sarauta.

Sam ta kasa yarda da maganar, ya ma za'a a ce wai Fulani Hajara ta fara naƙuda ba labari, a kan me? Cikin nata ma yaushe ya shiga watar haihuwarsa?, wannan labarin ƙanzon kurege ne kawai.

Ganin tsayawa saƙe-saƙe ba nata ba, domin ba zai fitar mata ba, sai kawai ta wuce ta rufo ƙofar ɗakinta da kyau, duk da ta san babu mai shigo mata sai da izininta, ko da kuwa mai martaba ne da kansa, amma kuma saboda tsaro wai ba domin tsoro ba.

Tana rufe ƙofar ta ƙarasa wajan adakarta, ta ciro wani jan ƙyalle da wasu wuri masu kamar awarwaro da sarƙa, saka na hannaye tayi sannan ta saka na wuya, kana ta ɗau jan ƙyallen ta ɗaure fiskarta da shi duka, ta kuma durfafi kusurwar bangon ɗakinta ta kudu, ta na zuwa ta kai hannunta na hagu ta dafa bangon.

"Buɗe buɗe Aljani tsagau."

Ta faɗa da wani irin murya kamar ba nata ba.

Abun mamaki, bangon da yake shafe rass babu ko alamar ƴar gurji a jiki balle ɓuli, sai ga shi kamar daga sama, wani ƙofa ya bayyana a wajan, hannunta na hagun ta kuma kai wa ta dafa, ƙofar ta buɗe ita kuma ta shige, shikkenan kuma ƙofar ta shafe babu ita babu alamarta a ganin ido, ta ɓace ɓat.

Cikin wani siririyar hanya Fulani Samira ke tafiya har sannan jan ƙyallen na rufe da idanuwanta, sai da tayi tafiya mai ɗan tsayi, sannan ta tsaya ta juya baya da gefe da gefenta tana faɗin wasu ɗalasiman tsafi, ta kalli sama ta kuma kalli ƙasa, a daidai lokacin ƙasan daidai inda take tsaye ya zurma da ita ta rufta, ba ta tashi bayyana a ko ina ba, sai zaune a gaban wani dattijo da babban rigarsa da rawaninsa da zabgegen carbinsa a hannunsa, ga shi dai kamar malami, amma kallo ɗaya za ka yiwa ƴar ɗakin ta shi ka tabbatar mashahurin boka ne ba malami ba.

"Barka la'anannen malami la'anannen Allah"

Fulani Samira ta faɗa har lokacin idanuwanta a rufe.

"Barkar ki dai hatsabiya ɓatacciya Samira, in ce dai lafiya ko?"

Dattijon ya tambaya ya na nuna fiskarta da ƴar wata tsinke da ya ɗauka mai kama da fiffiken mujiya, ɓat jan ƙyallen fiskarta ya ɓace, ya zamana su na kallon juna da dattijon.

"Ina fa lafiya, ai kamar yadda lafiya ba ta kai mutum asibiti, banza ba ta kai zomo kasuwa, to haka ba za ka ganni siƙau ba wata damuwa ba."

"Ungulu ba ki jewar banza, to ina sauraranki Samira"

Dattijon ya faɗa cikin kwanciyar hankali yana mai cigaba da jan zabgegen carbinsa.

"Fulani Hajara ta haihu, amma wai an nemi abinda ta haifa sama ko ƙasa an rasa, kuma ma ba a san me ta haifa ba, na kasa yarda da zancen, duk da daga majiya mai ƙarfi naji, majiyar da ba za ta mini ƙarya ba, amma duk da haka jikina na bani wannan zancen banza ne, zance ne mara tushe, shiyasa na...."

Dakatar da ita dattijon yayi, ta hanyar ɗaga yatsarsa guda ya ɗaura a saman bakinsa, ta kuwa yi shiru ta zuba masa ido.

Nuni yayi da Ƙwaryar da ke gefensa, da wani irin jaja-jajan ruwa kuma baƙi-baƙi ke ciki, ƙwaryar da kansa ya baro gefen dattijon ya dawo gabansa, zabgegen carbin da ke hannunsa ya saka a cikin ƙwaryar, abin mamaki, duk iri ƙanƙantar ƙwaryar da ƙarancin ruwan ciki, haka zabgegen carbin ya shige tamkar an jefa allura ga kogi, kafun kiftawar ido, abinda ya faru a lokacin da Fulani Hajara ke daf da haifo cikin jikinta, kamar photo mai motsi haka dattijon bokan ke ganin komai a idanuwansa, ya ga Hadimar da ke wajan, kamar yadda ya ga Fulani Hajara da ke naƙuda, har zuwa sanda ta haihu, bai ga abinda ta haifa ba, haske kawai ya gani, sannan ya ga wani iska ya fice a tare da hasken,...duk abinda ya faru tsaf ya gani.

"Namiji ta haifa"

Ya faɗa yana jinjina kai, saboda tabbas ya ga alamar namiji ne, da mace ta haifa da zai ga alamar abinda zai nuna masa cewa mace ce a cikin hasken.

"Ina jaririn yake? A ina zan same shi? Domin na rantse da ƙarfin tsafi sai na raba shi da numfashinsa."

Fulani Samira ta tambaya cikin hanzari, zuciyarta na wani irin bugawa, ga baƙin ciki ga tsoro.

"Kar ki neme shi Samira, kar ki sha wahalar neman shi, domin a yanzu haka da muke magana, ya na wata nahiyar ta daban, yayi nisan da ko kin neme shi ba za ki same shi ba..."

"Amma dattijo..."

"Kin bar kyau tun ranar haihuwa Samira."

Faɗin dattijon yana mai saurin dakatar da abinda za ta ce, kamar yadda ta katse maganar da yake yi.

"Samira ni da ke duk a hanyar ɓata muke, da ma duk wanda ya bi ta farkin da muke, amma ɓatana bai sa na kasa gane ƙaddara, ko kuwa na ce zan ja da abinda yake tabbatacce kuma rubutacce ba, banda wannan ikon, mu bokaye, malaman tsubbu, matsafa har ma da ƴan bori, duk abinda kika ga mun yi kuma aiki ya ci, to dama Allah ya rubuta tun-tuni mai afkuwa ne, shiyasa ya ke bamu sa'a a kan abinda yake a rubuce zai faru, Samira kin sani duk da ni la'ananne ne kuma ɓatacce kamar dai ke, amma ba na ƙarya, gaskiya duk ɗacinta ina faɗinta, tun farko sai da na ce miki cikin Hajara Allah ya tsaga masa shan ruwa a duniya, amma ke kuwa kika ce kin ji kin gani za ki yaƙi hakan, shiyasa na naɗe hannaye na ƙyaleki in ga iya gudun ruwanki, na bar ki da kalmar da ake faɗin ga fili ga mai doki, ki sha sukuwa ke da ƙaddara."

Dattijon ya ƙarishe maganar ya na sanya hannunsa cikin ƙwaryar ya fito da zabgegen carbinsa, sai ga carbi a bushe ras kamar ba daga cikin ruwa ya fito ba.

"Zuwansa duniya tabbatacce ne, kamar yadda mulki ga ɗan da za ki haifa, ya ke tabbatacce rubutacce, dan haka ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a randa."

"Da ace za'a dawo da lokaci baya, kuma a ce na san da naƙudar Fulani Hajara, to ko da raba ɗan da za ta haifa na nufin raba ruhina da gangar jikina ne sai na kashe shi, dattijo ko da kuwa ɗan da zan haifa ne zai yi mulkin ƙasar Anfa, amma ba na son duk wani abun da zai kawo masa togaciya ko tsaiko a hanyarsa, zan tabbatar da na share hanyar ya zama fili fetal, ko tsinke ba zai tarar ba balle wani abu wai mutum, dole ɗan da zan haifa ya zame ɗa ɗaya tilo ga Mai martaba Takawa Sarki Ahmad, ta yadda zai gaji sarauta cikin aminci, mu shumfiɗa mulki mai cike da izza da ƙasaita, kalar mulkin da ba wani mahaluƙin da ya taɓa shumfiɗawa a doron ƙasa."

Fulani Samira ta dire maganar a wani irin sauti, mai nuna yadda giyar mulkin ke ɗibarta tun ba ta kwankwaɗa ba.

"Wannan buri naki tabbatacce ne, ni La'anannen dattijo kuma ɓatacce zan tsaya miki, zan taimaka miki Samira har zuwa ƙarshen numfashina, sai dai ina mai sake jaddada miki, ki kula da ƙaddara, ki raba hanya da abinda ya ke a rubuce a allon ƙaddara, kuma muddin kika yi haka, to a komai na ishe ki, kiyi imani da hakan."

"Dattijo ina so wannan yaron ya mutu, tunda ba zan same shi ba ko na neme shi to lallai-lallai ina so ya mutu a yau ba sai gobe ba, sannan ba na so Fulani Hajara ta sake samun rabo da mai martaba."

Fulani Samira ta faɗa fiska babu alamar wasa bare sassauci.

"Hahahaha! Samira bayan taɓewar da kika yi, har da toshewar basira ke damunki, Samira ke jahila ce...."

"La'anannen dattijon!"

Fulani Samira ta ƙira sunansa da murya mai kauri da ke nuni da gargaɗi, domin kalamansa na son wuce rawa da makaɗi.

"Samira fadata kika zo, idan naje fadarki dole na ba ki matsayinki ta mai ɗakin Sarki Ahmad, amma a nan dole ni ne mai fada ni ne mai matsayi."

"A mini aikin da na ce"

Ta faɗa fiska a murtuƙe.

"Ba zai mutu ba saboda hasken da ke a tare da shi, sai dai bayan rashin mutuwa, ko wace iriyar cuta, azaba, masifa ko bala'i da kike buƙatar a tura masa, a yanzu-yanzu cikin sauƙi zan aika masa shi."

Dattijon ya faɗa yana baza zabgegen carbinsa a gabansa, ya dunƙule hannunsa a tsakiyar zabgegen carbin, sannan ya rufe idanuwansa.

"Ki faɗi ko me kike so Samira, an yi an gama, ki kwantar da hankalinki tamkar kin yi filo da gawa."

Yayi maganar ya na mai ɗaurawa da karanto wasu surƙullen tsubbu, jira ya ke ta faɗa abinda ta ke so, domin duk abinda za ta ce ta na furta shi ya tabbata.

"Ya lalace, ina so ya lalace, kuma kada ya taɓa waiwayo masarautar nan, kuma...."

"Da wanda kika faɗa da wanda ba ki faɗa ba duk sun tabbata a kan shi, ni La'anannen dattijo kuma gagarabadau na gama da wannan aikin, ba zai taɓa waiwayo masarautar nan ba, ya tafi kenan tafiya ta har abada, lalacewa kuma mafi muni zai yi, domin ba zai bi addinin gaskiya ba, zai ɓata bat kamar yadda ni da ke muka ɓata."

Da babu gwanda ba daɗi, shi ne ga Fulani Samira, tunda a rashin uwa a kan yi uwar ɗaki, to ta amshi hakan, duk da kuwa zuciyarta ba ta nitsa da haka ba.

"Za ki iya tafiya, amma ki sani kamar yadda aka saba, aljanun da suka miki aiki, za su amshi ladar aikinsu a inda suka saba, sannan ki tsumayi ciki a ko wani lokaci, domin rabon wannan jariri shi ya hana ki samun ciki, kamar yadda rabon cikin da za ki samu ya dakatar da wanda Hajara za ta haifa a gaba, amma ki sani, iya ƙoyinki kenan, iya shi kaɗai za ki haifa a kaf rayuwarki, dan haka ki kula, na san kin fini sanin me nake nufi, akwai taɓaɓɓu kamarki a masarautar ku, har ma da waɗanda suka fi ki taɓewa, kin kuma san karatun abinda ka yi shi za a maka, yadda kika dage kika yi iya fafutukar ki wajan ganin kin zubar da cikin Hajara, to haka kema mutane da yawa za suyi wannan ƙoƙarin a kan ki, hallau wajan haihuwarma, dan haka ki kula, ki iya takunki, "

"Ban ci kasuwa ba, rumfa ba za ta faɗa mini ba dattijo, suyi, su gwada idan su na ganin za su iya, ai bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane, kura kuma ta san gidan mai babban sanda, ni Fulani Samira nayi musu zarra, murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya, na yi imani da kai dattijo ba za ka bari hakan ta faru ba, ni da nake da kai, to mai babban ubangida ai ya huta, mai ƙaramin ubangida kuma ya wahala, dan haka ko a wasa Akuya ba za tayi gasa da Kura ba, Fulani Samira nake, hatsabiya, kuma jajirtacciya, wacce ta ɓata ɓat, nayi nisa ba na jin ƙira, a kan cikar burina ba abinda ba zan iya yi ba, domin ko salwantar da rai ba yau na fara ba, dan haka duk wanda ya shiga gaba na yayi kwanan kabari, domin ina mai rantsuwa da kaifin tsubbu da tsafi ba zan ƙyale duk wanda yayi gigin taɓa lafiyar abinda zan haifa ba, tun daga ciki har ya fito duniya kuwa."

"Samira wanzami ba ka son jarfa, to ki dai bi a hankali, domin idan juninki sammako, wasu a tafe suka kwana."

"Kamar yadda kowa ya san kifin fadama ba ya gasa da na gulbi, ni Samira na fi ƙarfin su, na kuma wuce sanin su."

Fulani Samira na ƙare maganar ta kama tafiya, domin tuni jan ƙyallenta ya koma idonta, kafun kiftawa da ido wannan waje da ya rufa da ita ya iyo sama da ita, tana jin tashin sautin amon la'anannen dattijo, yana sakin wani iriyar dariya ta rashin imani, sai da tayi tafiya kamar yacce tayi a zuwa, sannan ta tsaya ta faɗi kalmar da ta faɗa a zuwa, sai ga ƙofa kawai a gabanta, ta na taɓawa da ƙafarta ta hagu sai ƙofar ta buɗe, ta na shigewa kuma ta kulle ta ɓace ɓat ta shafe kamar ƙofar ba ta taɓa wanzuwa ba.

Sai da Fulani Samira ta cire ƙyallen da wurin ta maida su tsohuwar adakarta ta ajiye, wacce ta yi wa kyakkyawar ɓoyo, ta baro wajan ta na niyar shiga bayi ta jiyo a na bugun ƙofarta, guntun tsaki ta ja gami da fasa shiga bayin ta ƙarasa ta buɗe ƙofa, fiska a murtuƙe ba alamar dariya ta fice a ɗakin ta na taku ɗaɗɗaya cikin wani irin isa da taƙama da izza.

"Takawarki lafiya giwar mai martaba, aljanna mai masoya da yawa, fara mai farar aniya...."

"Ya aka yi?"

Ta tambaya ta na dakatar da hadiman.

Saƙo aka sanar mata na abinda ya faru, wanda mai martaba ne ya aika a sanar mata, hakan ya sa ta jinjina kai gami da ba su umurnin tafiya, ta juya ta koma ciki, sai da ta yi wanka ta shirya cikin wasu tausassun kaya da alkyabba, sai tashin ƙamshi take, sannan ta nufi ficewa a ɗakin, ta na fitowa Hadimai suka mara mata baya su na mata kirari, har zuwa sashin Fulani Hajara.

Sai da aka sanar da isowar Fulani Samira, aka kuma yi mata iso sannan ta shiga, a daidai lokacin ne kuma ta ɗauko damuwa ta yaɓawa fiskarta, kallo guda za ka mata ka shaida tsantsar firgici, da damuwa da tashin hankali da take ciki.

"Barka da shigowa Fulani Samira"

Faɗin wani kamamme kuma nitsattsen fari kyakkyawan dattijo, ko da yake ba za'a ce masa dattijo kai tsaye ba, domin shi ba tsoho har can ba ne, kuma dai shi ba yaro matashi ba, yana dai tsaka-tsakiya, shekaru arba'in da ƴan kai zuwa hamsin.

Cikin tsantsar damuwa sautin muryarsa ya fito, sai dai cikin kulawa da tausayawa ya ke kallon Fulani Samira, domin damuwar da ya gani kwance a saman fiskarta kwatankwacin damuwar da Fulani Hajara ke ciki ne.

Cikin sauri Fulani Samira ta ƙarisa inda Sarki Ahmad ke zaune tare da Fulani Hajara, tana zuwa ta zube a ƙasa ta kama kuka.

"Na kasa yarda, na kasa aminta da labarin da ya iske ni, dan Allah Yaya ki ce mini ba haka bane, ba abinda ya samu Yarimanmu, mai martaba..."

"Kuyi haƙuri ku daina kuka, in sha Allah Yarima zai dawo gare mu a yau ba sai gobe ba, lungu da saƙon ƙasar Anfa da kewaye za'a bincika, in Allah ya yarda za'a samo Yarima TAJUDDIN, kuma za'a hukunta duk mai ruwa da tsaki a lamarin nan"

Sarki Ahmad ya dire maganar yana ji a zuciyarsa ɗan sa bai yi nisa ba, lallai-lallai yana ma cikin masarautar, kuma za'a samo shi in sha Allah, domin tunda aka sanar da shi baƙar labarin, sam-sam ya kasa gasƙatawa, wasa ne kawai, kuma zai yi maganin duk wanda ya masa wannan mugun wasar.

"Yaya!!"

Fulani Samira ta ƙira sunan da take faɗawa Fulani Hajara, da muryar kuka.

Hannayenta Fulani Hajara ta riƙo, hawaye ɗaya na bin ɗaya, da muryarta da ta dishe ta fara magana.

"Sun raba ni da abinda na haifa Samira, ko kallo ɗaya ban masa ba, na san dai na haihu, amma ban ga abinda na haifa ba Samira, azzalumai kuma mugaye sun cutar da zuciya da ruhina, hatta da gangar jikina sun cutar da shi, ciwon da naji lokacin haihuwar har a yanzu yana damuna, amma kuma ciwon dake a zuciyata ya shallake wannan, Samira sun cutar da ni, sun cuce ni, sun zalunce ni, ina jin ciwon da baki ba zai iya furta shi ba.."

Da kuka sosai Fulani Hajara ta ƙarishe maganar, yayinda take jin tsokar zuciyarta na mata wani irin raɗaɗi da ciwo, kalar raɗaɗin da ko a cikin uwaye, ba ko wacce uwace za ta gane zafin da take ji ba.

Fulani Samira rungume Fulani Hajara tayi tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, duk da ita ma ƙwallar take yi.

"In sha Allah mai martaba zai samo mana Yarima, zai dawo mana da shi a jikina nake jin hakan Yaya, muyi haƙuri muyi addu'a, amma Yaya meyasa ba ki sanar ba da kika fara naƙudar? Da wataƙila duk haka bai faru ba."

Fulani Samira ƙarishe maganar da tambaya, cike da tsantsar damuwa.

"Samira ban san naƙuda bane lokacin da ciwon ya tsikare ni, a lokacin dana san naƙuda ne kuma azzalumai sun yi nasarar gusar mini da hankalina, a haka har na haihu, daga ina haihuwa kuma ban sake sanin me ya faru ba har sai lokacin da wasu hadimai suka shafa mini ruwa na farfaɗo."

Fulani Hajara ta faɗa tana mai jin ciwo sosai a zuciyarta, yadda komai ya gudana na dawo mata, wanda hakan yayi sanadin ƙaruwar sautin kukanta, zazzaɓi kuwa a take ya rufe ta, ciwon kai dama tuni take fama da shi, ikon Allah ne kawai ya sa ta haihu lafiya ma.

"Yanzu kika fara kuka, baki ga komai ba ma Fulani Hajara, sai na tabbatar da idanuwanki sun makance ta dalilin kuka, mu zuba ni da ke da duk wanda ma zai kawo mini tasgaro a hanyata, shege ka fasa, ni Samira sai na tabbatar da duk wanda ya shiga hanyata ya shiga azaba, tafiyarsa ƙiyama sai ta fi masa haɗa hanya da ni......"

"Fulani Samira!"

Dam!!!!

****