09
9
***Bugu biyu taji yaya Aliyu ya ɗauki wayar tata, can ƙasan maƙoshinsa taji yace,
"hello my love...."
"Haidar na faɗa maka yaron nan Afeef akwai wata a ƙasa, ni dama na san sai haka ta faru... I knew it.... Wallahi na san dama sai ya bamu problem....... Na san za ayi haka...."
"wait..... Calm down Mimi, talk to me..... What's going on?" ya faɗa yana kokarin tashi daga kwancen da yake saboda damuwa da tashin hankalin da bai san wanne iri bane kuma,
"Wai me yaron nan yake nufi dani? Yanzu na kira shi akan maganar saki kaji irin banzar maganar da yake faɗa min dan rashin kunya?"
"easy Mimi, me ya fada miki? Cewa yayi bazai sake kiba?"
"something like this...... Yana maganar wai bai dandani zuma ta ba taya zai sake ni......"
"what....... Shi Afeef dinne yake iya fada miki wannan maganar? Yaron nan baya shaye Shaye kuwa? Ni zai nunawa ƙwaya...... Sai naci kutumar ubansa wallahi....." ya fada cikin zafin rai sannan cikin gaggawa ya katse kiran nata ya fara kiran wayar Afeef, da farko ya zaci kamar bazai dauka ba sai kuma yaji ya daga, cikin fushi yaya Aliyun yace,
" Afeef.... Ina wasa da kai? Da ni da Mimi cikinmu akwai sa'anka? Wacce irin magana naji kana faɗa mata saboda baka da mutunci ko?"
"Haba yaya Haidar me kuma ya faru?...."
"yanzu dai ka sakar min matata saboda naga abun naka rashin mutunci ne da iskanci....."
"shikenan zan sake ta...." ƙit daga haka Yaya Aliyu yaji Afeef din ya kashe wayar shi nan ya sake kokarin kiran sa amma wayar bata tafiya ya sakata a DND, kwafa yaya Aliyu yayi ya hau zagaye cikin bedroom dinsa tamkar zararre,
"ni Afeef zai kashewa waya? Ni? Matata zai ce zai dandani zumarta?" kasa zaune yayi ya kasa tsaye sai aikin kiran wayar Afeef yake yi amma bata tafiya wanda hakan ko kadan bai dameshi ba kawai cigaba yake da kira har dare ya raba kuma ya tsala,
Ita dai anty Mimi tana zaune tayi tagumi ta zubawa wayarta dake gaban ta ido tana kallonta zuciyar ta na tafarfasa kamar zata ƙone ko kuma ta tarwatse dan bakin cikin da take ji cikin ranta, wai ita Afeef zai fadawa haka? Wannan shine dalilin da yasa tun farko bata so aka hada wannan deal din dashi ba saboda zai iya samun dama yayi musu kowanne irin cin kashi yaso,
"why me? Why always me?" take fada cikin bakin ciki da damuwa, tunaninta ya katse ya tsaya cak daidai lokacin da kiran Aliyu ya shigo, numfashi ta sauke da kyar saboda nauyin da yayi mata, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa Afeef yayi sakin kowa ya huta dasu dashi,
" ya kuka yi dashi?" ta fada gabanta na faman faduwa da karfi,
"ya kashe wayar shi batare da mun gama magana ba...."
"Aliyu anya yaron nan babu abinda yake nufi kuwa? Nifa na jima ina zarginsa dama, is like zai bamu problem"
"ki kwantar da hankalinki my love.... Wallahi bai isa ba, nawa yake ma, dole sai ya sake ki ko baya so...."
"am confused....... Haidar am confused...... Wallahi na rasa wanne irin tunani zanyi.... Aliyu am lost ....."
"bake kadai ba.... Yaron nan ya goge min hadda gaba daya amma zanyi maganinsa"
Ajiye wayar suka yi a tare Mimi ta cije lips dinta na kasa cike da takaici ta zubawa wuri daya ido tana karkada kafarta ba tare ta san me zata yi tunani a wannan lokacin ba.
Kwana yaya Aliyu yayi a zaune bai samu bacci ba saboda damuwa da ɓacin rai da kuma tarin takaicin dake kai komo cikin zuciyarsa, ji yake da ace yana iyawa da yabi Afeef har calabar dan suyita ta ƙare, a fusace kuma a kidime da gari ya waye ya nufi gidan yaya faruk wanda Allah ya takaita basu yi saɓani ba saboda ya shiga wanka kenan idan ya fito zai shirya ya bar gari zuwa Abuja saboda wani taron gaggawa da aka kirasu matsayin su na ƴan jaridu, yanda yake huci sannan kana ganin fuskarshi kasan ba ƙalau ba ya sanya Jiddah matar yaya faruk saurin zuwa cikin bedroom dinsa inda yake wanka bayan sun gaisa da yaya Aliyun,
"Abbah kayi sauri dan Allah ka fito kar kayi irin wannan jimawar taka da ka saba yi cikin toilet...... Yaya Haidar ne yazo"
Komawa ta sake yi falo wurin yaya Aliyun wanda ke zaune ya dunkule dukkan hannayensa ya sarke su wuri ɗaya ransa a ɓace,
"na faɗa masa zai fito yanzu insha Allah...."
"ok nagode Jiddah...."
Bata zauna ba ta koma kitchen inda take hada breakfast, Aliyun na nan zaune Yaya faruk ya shigo sanye da rigar wanka dan yana fitowa daga bathroom kai tsaye falon ya nufo saboda gaba daya jikinsa yana bashi duk yadda akayi ba lafiya ba,
" Haidar lafiya kuwa?"
"Faruk ba lafiya ba, yaron nan Afeef nake son ka kira min a waya saboda ni inata faman kiranshi a waya amma bana samun sa...."
"yayi maka wani laifin ne? Me ya faru?"
"ka kira min shi first zanyi magana dashi"
"ok ina zuwa..... Bari na dauko wayata"
Yaya faruk bai kawo komai cikin ransa ba haka kuma maganar auren mimi da Afeef bata taba zuwa cikin kwanyarsa ba a daidai wannan lokaci bare har ya gane ko ya fahimci musabbabin neman da Aliyu ke yiwa Afeef, number Afeef ya kira bayan ya dawo cikin falon amma kuma bata tafiya,
Tsaki yaya Aliyu yayi kafin yace "shikenan rabu dashi ka daina kira.... Zanyi ta trying da kaina dama na zaci ko ni kadai yayi blocking...... Babu damuwa"
"wai me yake faruwa ne? Wani laifin yayi maka ko ƙaƙa?"
"no bai yimin laifin komai ba, dama munyi magana dashi ne jiya yake ce min baida lafiya to shine dazu na kira na duba shi naji ban same shi ba shiyasa hankalina ya tashi...."
"Allah ya bashi lafiya...."
"amin bari na wuce...."
"ba zaka tsaya kayi breakfast ba"
"No alhamdulillah...."
Sallama suka yi ya fita ya shiga motar sa ya nufi gida yana girgiza kai, ƙarar wayar shi ta sa ya kai duban shi kan wayar nan yaga mimi ce da alama itama hankalinta tashe yake saboda rashin samun wannan yaron,
"My dear ka same shi kuwa?"
"wallahi my love ban same shi ba yanzu ma kin ganni a hanya daga gidan faruk mun neme shi ta wayar faruk amma bata shiga...."
"Haba Haidar Meyasa kake haka? Idan asirinmu ya tonu kuma fa? Idan yaya faruk ya fahimci wani abu fa?"
"ba zai fahimci komai ba i promise you.."
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun...." ta faɗa cikin damuwa da tashin hankali, ita dai tun daga wannan lokaci komai nata ya rikice haka kuma ta shiga cikin damuwa, shi kuwa yaya Aliyu kullum baida aiki sai kiran wayar Afeef da tura masa da massages amma shuru baya responding ba kuma ya samunsa,
Daga call din har massages din duk Afeef yana gani amma babu wanda yake kulawa aikinsa kawai yake yi kuma shi ya saka a gaba har ya kwashe kimanin watanni uku a calabar kuma sai lokacin ya samu dan hutu dan haka ya nufi gida kamar yadda ya saba. Ya samu tarba sosai daga wurin mommy wacce yaga kamar ta manta da batun aurensa da yayi ko kuma ta sauko ne ta haƙura Allahu a'alamu, tuwon biskin masara ya samu tayi masa da miyar taushe kamar yadda ya bukata, miyar tasha man shanu da naman kaza sai kamshi take yi, Irfan ne ya dauko shi shiyasa tare suka ci abincin, bayan mommy ta haura upstairs Irfan ya kalleshi yace,
"ban ji ka tambayi anty Mimi ba alhali kuma naji kana ta tambayar mutanen gida daya bayan ɗaya...."
Murmushi Afeef yayi cikin ransa yana ayyana yanda zasu kwashe da yaya haidar da kuma anty Mimi din wanda ya san sun jima suna zaman jiran wannan lokacin na dawowarsa sai dai amma ko ɗar bai jiba bare har hankalinsa ya tashi, rayuwar sa yake yi hankali kwance ya barsu da matsalar su dan ba matsalar shi bace,
"na san tana nan lafiya ai....I knew she's fine"
"waye ya fada maka? To 2 days bata da lafiya ko aiki bata fita...."
"Allah ya bata lafiya" ya fada a hankali yana tunani a ransa,
"amin ya Allah..."
"kace ina gaida ta kafin inzo...."
"Insha Allah zan fada mata"
Bayan tafiyar Irfan part dinshi ya shige ya kwanta yayita shirgar baccin shi bayan ya kashe wayar shi. Anty Mimi tana zaune tare da hajiya kaka tana yankewa hajiyan faratanta Irfan ya shigo, bayan ya zauna ya kalli hajiya kaka yace,
"mijinki yana gaida ki shalelenki.... Ya dawo naje na dauko shi...."
"Au lele ya dawo shine bazai zo in ganshi ba?"
"yana nan zuwa ai idan ya huta, anty Mimi kema yace yana gaida ki" ai idan ta amsa masa to kujerar da suke kai ta amsa, tana jin su har suka ƙaraci hirar su akan shi Irfan ya tashi ya fita bata tofa tata ba aciki, bayan ta kammala yankewa hajiya farce ta koma bedroom dinta ta kira yaya Aliyu ta sanar dashi dawowar Afeef wanda tsabar rainin wayo harda sakon gaisuwa ya bada a kawo mata, ƙwafa yaya Aliyu yayi yace,
"ba dai ya dawo ba, barni dashi zanje har gidan in sameshi...."
Suna gama wayar yaya Aliyu ya nufi gidan daddy, part din Afeef yaje bai ko leka na mommy ba saboda bama ya son ta san yazo kai kusan kowa ma dake gidan baya son su san da zuwan sa, knocking ya jima yana yi wanda yana da tabbacin Afeef din yana jinsa amma yaƙi budewa ya rabu dashi har ya gaji da jira ya tafi, yanzu kam ya fara ji a jikinsa kamar maganar mimi na shirin zama gaskiya, kamar sai sun kai ruwa rana sannan Afeef din zai dawo cikin hankalinsa har ya cika musu alƙawarin da suka yi dashi ya yi musu abinda suke so.
Tsawon sati guda da dawowar Afeef din yaya Aliyu nata faman sintiri a gidan amma baya bude kofa haka kuma baya daukar waya bare reply na massages, daga mimi har yaya Aliyu sun gama zuwa wuya dashi sun ƙulu ƙarshe, shi dai sai yau ne yake jin zai iya fita sakamakon baccin da yayi na kwana da kwanaki yana hutawa, daukar wayar shi yayi jin kira ya shigo kamar yadda yanzu wayar bata rabo da kira kaca kaca, ganin yaya Aliyu ne yasa ya dan yi murmushi,
"hello.... Yay...."
"Afeef ka gama rashin mutuncin naka? Are you done?"
"yaya kana ina? We need to talk...."
"Ina office din mimi..... Talk about what?"
"ina zuwa yanzu...."
Katse wayar yayi ya fara shiryawa, jar t shirt ya saka sai blue din jeans da bakin agogon fata ya fesa turaren black oad ya dauki key din mota ya fita ba tare da yayi sallama da kowa ba.......