ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

15

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


#THE TRIO OF TALES 

(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.




*SHAFI NA SHA BIYAR*


Kwananta biyu da ƴar uwarta amma ba za ta ce ga halin da Ma'u take ciki ba, wanka sai ta kama hannunta ta kaita har bayi tayi mata, hatta ruwa wannan sai ta bata ta sha idan bata bata ba to ko kwana za su yi Ma'u ba zata tambayi ruwa ba.


Hankalin Jidda ba'a karamin tashe yake ba tayi kuka har kaman ba gobe tayi ta rokon su akan su kai mata ma’u ko asibiti ne amma babu wanda ma ya kulata bare su nuna sun san da su take.


Yau ta fitar da ma’u harabar gidan inda iyakacinsu nan ne, akwai masu wanki akwai masu shaye shaye akwai masu hira, kusa da su wata ta zo ta zauna Jiddah da tayi wani irin zuru zuru ta kalleta hawaye na cika mata idanu tace


“Don Allah har sai yaushe ne za su bar mu mu tafi? Babu wani da zai iya kiran hukuma a cecemu? Iyayenmu na chan a tunaninsu sun sama mana rayuwa mai kyai ashe rami suka haka suka binne mu ba tare da sun sani ba…”


Yarinyar ta sauƙe numfashi tana dafa kafadan jidda tace 

“Da haka za ki saba amma bana tunanin hukuma za su iya aiki akan waennan azzaluman, ta wani bangare ma zan iya cewa bakinsu daya da manyan, kin ga gidan nan ban san shekara nawa yayi yana existing ba amma ni a karan kaina shekaruna shidda, idan kin ga kin fita an sayar da ke ne ko an yi safararki zuwa wani ƙasa da babu yadda za ki yi zama dole, za’a turaki aikatau ko ma zinace zinace, babu yadda kika iya jidda gwara ki saki jiki Ma’u kuma Allah ya bata lafiya don wasu dayawa sun shiga irin wannan trauma amma da kansu suke overcoming har ma su yi adopting wannan rayuwa da muka tsinci kanmu”


Jidda da zuciyarta yake bugawa da karfin gaske tace 

“idan iyayenmu sun neme mu fah?”


“Na gayamiki ba ta yadda za ki sadu da iyayenki jiddah, su karan kansu basu san ta inda za su fara nemanku ba komai da aka yi fake ne”


Hawaye ne ya shiga zubowa jiddah tana kallon Ma’u dake zaune kawai kaman wacce aka dasa idanunta wuri guda ba uhm ba uhm uhm.

“Akwai Allah in shaa Allahu za mu fita, in Allah ya so ya yarda rayuwarmu ba zai tagayyara ba”


Ta karasa da kuka, tana jin labari ana safarar mutane, tana jin labarin irin waennan duniya na karkashin kasa amma bata taba sanin da gaske suna nan cikin al’ummarmu ba, suna amfani da ‘ya’yan wasu don biyawa kawunansu bukatu, suna zaluntar iyaye su yi musu shigo shigo ba zurfi su yi musu illah mafi muni a rayuwa.


“Ke!”

Ta ɗaga kai ta kalli Shadow

“tashi mu je!”

“Ina?”

Ba tsoro tayi tambayar don ta ci alwashin ba zata taba jin tsoro ko shakkarsu ba, duk kuma wanda yayi mata a cikinsu za ta rama sai dai su kasheta.


“Kin tashi ko sai na saɓeki a kafaɗa?"

“Allah ya tsari jikina ya hadu da kazantaccen jikinka…”

Ya kai hannu da niyyar marinta tayi saurin mikewa tsaye ba zato ta ji….


****


Iska ne mai karfi ake na alamun ruwa zai iya saukowa any moment, kasancewar farkon shigar daminar ce ba kowa ke da tabbacin zuwan ruwan ba hakan ya sa wasu dayawa basu yanke al’amuransu ba, kaman da wasa ruwan kuwa ya zo da karfinshi wanda tun yamma ya fara zuba har tsakar dare bai daina marka-marka ba.


A daidai lokacin Diva tana zaune cikin motarta hankalinta na ga jikin mirror din motar kofan motar a bude yake duk jikinta kuma na ta waje wani hayaki take busawa tana sake nazarin motar.


Tun arangamarta da sheikh ta lura da motar amma bata taba zaton ita motar ke bibiya ba sai a kwanakin nan biyu bayan ta manta ma da wani sheikh da wa’azinshi. 


Tana so ta fahimci me suke so da ita hakan ya sa ta biyo hanyar da ta tabbatar babu wani motsi na jama’a ga kasancewar ruwa ko ina tsitt ko wani mahaluki na gidansa yana bacci.


Ta kusa mintuna goma a haka kan ta sauka ta nufi motar, sai suka yi saurin kunnawa suka yi baya in ta matsa gaba sai su yi baya, wani irin bacin rai take ciki idan zaka yi abu da ita kayi kawai bata son rufa rufa ko wani kumbiya kumbiya, rai a bace ta dawo motar ta zauna tana kokarin yi wa motar key sai ta tsaya chakkk, hannu ta kai za ta dora kan wukarta ta ji an saka igiya ba zato an shake mata wuya daga seat din baya, wani azababben zafi na shigewar makami na ratsa har kwakwalta daga kasan hakarkarinta da alama wuka ne suka soka mata kuma ba karamin shiga yayi ba.


Kokawa suka fara duk yadda ta so ta ma rike igiyar abin ya ci tura har sai da ta kusa suma suka saki sama sama ta ji an janyeta waje kusan mutum hudu ne suka shiga dukanta da kafa da hannu, gabadaya ta jiggata ta fice a hayyacinta, da kyar suka barta ganin tana aman jini, cikin azaba ta runtse ido jin sun juyata sun sa wuka suna wani zane daga kafadarta daga nan suka juya suka tafi suka barta anan yashe ruwa na zuba mata chab chab chab.


Ta tattare duka kuzarin da ya saura mata cikin wani irin karfin hali ta mike tana ganin jiri lalube take saboda idanunta sun rufe da jini dake zuba mata daga kanta da goshinta ga ruwa kuma hannunta ya sauka a kan Tire ta ji shi flat alamun sun fashe shi, jikinta babu inda baya rawa haka ta kama motar ta mike hannunta daya na hakarkarinta da azabar ya fi na ko ina tana tafiya cikin layi idan bata nemi taimako ba mutuwa za ta yi.


A lokacin duka rayuwarta ne ke flashing a saman idanunta, wani irin tsoro ne ya mamaye ranta idan ta mutu bata san ta ya za ta fuskanci ubangiji ba, babu abin da ya taba girgizata a rayuwa irin tsoron mutuwa a yanzu kuma dama haka abin yake.


Daga nesa take hangen wutar mota, bata tsaya ba ta cigaba da tafiya cikin wani irin layi da juriya, ƙiiiiiiiii haka motar ta taka wani irin birki bayan ta dan bugeta kadan don matukin ba wai ya kula da ita ba ne, bata fadi ba sai dai jikinta rabi na ga motar, da sauri ta ji karar bude kofa, sai ta ji ana magana amma ba zata ce ga abin da ake cewa ba.


Ta tafi luuuu za ta fadi ta ji an tare ta, ta ji sadda hannun wanda bata sanin ba ya sauka kan wukar hakarkarinta ta ji sautin salati daga nan bata san me kuma ya faru ba ta karasa ficewa hayyacinta.


****


Jingine yake da kujera kafarsa a harde kaman ko da yaushe shigar larabawa ce jikinshi fari sol din jallabiya da yalkinta ya bayyana tsadarsa, golden color din jubba sai gutra fara tass da ya dora a kanshi idanunshi sanye da farar madubi da ya kara masa kyaun zati.


Hannunshi wani takarda ne yana dan dubawa daga gefe yake jin maganan Ammar.


“Ammar ka fahimta mana ba ni da wani interest kan Twins enterprises duk yadda su Abba suke so nayi aiki chan ba zan iya ba abubuwan gabana kadai sun ishe ni”


Ya faɗa yana rufe takardar tare da dora idanunsa farare tass kan Ammar.


“Muna bukatar kwakwalwarka a kamfanin nan, kuma field dinka ne harkar kasuwanci amma ban san meyasa kwata kwata baka son alakanta kanka da abin da ya zame mana dole ba, abubuwa dayawa suna faruwa a cikin kamfanin nan yanzu su Abba shekaru sun ja ba komai ne suke iya yi ba abubuwa sun mini yawa a kullum kuma samun ɓace ɓacen kudade ake ba na wasa ba”


Ɗan hararsa shehi yayi cikin muryarsa mai natsuwa yace 

“Duk babu mai iya gano bakin zaren kuma aka ce sai Irshad? Ka daina saka ni magana Ammar ku yi ko ma menene amma ni kam ba zan sa kaina ciki ba”

Yana kai nan ya mike ya nufi shige wa dakinshi, Ammar ya girgiza kai bai san meyasa a duniya idan akwai abin da shehi ba ya mayar da hankali kai su ne dukiya da kuma kadarorin iyayensu.


Dab zai shige Ammar yace 

“Ammm Maamah tace gobe ne za mu je gidan su buduruwarka ko?”


Da gayya ya fadi hakan don ya ci nasarar dakatar da shehin ya juyo ya zuba mishi ido bai ce komai ba Ammar ya tuntsire da dariya.


“Kana kallona ba zance zaka je ba?”

Tsaki tsiriri ya ja ya juya kawai ya shige amma fuskarsa a dan sake yana girgiza kai.


Kai tsaye rigar saman ya cire ya fito balcony dinshi ya tsaya idanunsa zube wuri guda wasu abubuwa na zuwar masa kai, ya jima tsaye nan kan ya kai idanunsa kan agogon hannunshi sai ya juya ya koma dakin kai tsaye ya shiga bayi yayi alwala tare da fitowa ya mayar da rigarsa ya nufi kasa don tafiya sallar magrib da dab ake da kira.


****


"Ni kam Shaly kun ji daga uwar dakinku kuwa?”


Jagaban da shigowanshi gidan kenan ya fada don yayi ta kiran layinta baya shiga, bata cika kwana waje ba ko ta kwana to asubar fari zata shigo gidan, haka bata zama inda babu dayansu na awanni dayawa kuma tun jiya da rana bai sanyata ido ba yanzu ana neman magariba bata shigo gidan ba.


Dukkansu suka mike tsaye obafiya yace


“Tun jiya da ta fita bamu ji daga gareta ba jagaban…. Tattaunawar da muke kenan don babu wanda ya samu layinta, mun ta shigowa Hajjo na cewa bata dawo ba….Anya kuwa lafiya?”


A kan fuskarshi suka karanci tashin hankalin da ya fara shiga don idan akwai abin da jagaban ba ya wasa da to Diva ce.


“Me yasa kuka barta ta fita ita kadai? Kun sani tana da makiya dayawa kaman yadda nake da su me amfaninku a tunaninku na haɗa ku ne kawai ku zauna zaman banza a gangarta? Maza ku bace duk inda take ku nemomin ita”


Skipo yace

“Diva fa ko ita kadai ce ba abin wargi ba ce, na tabbatar babu abin da aka isa a yi mata don nan gani nan bari ce wallahii”


Tsaki jagaban yayi

Zai yi magana zubash tace


“Kila dai wani business din take yi mai muhimmanci amma nima ban yarda wai don tana ita kadai wani abin zai iya samunta ba”


Jagaban da yayi shiru yana jin zuciyarsa na rawa ya san ko ma menene ba daidai bane don hankalinshi ya ki kwanciya a ranshi yake jin ba kalau ba, zai yi magana cikin fusata ya ji wayanshi na kara.


Zarowa yayi ya daga cikin wani salo ya furta 


“Ya nee?”


A take ya zare idanu duka cikin wani kalar murya marar daadin saurare ya furta


“Whatttt?”


Duk sai suka razana wayan hannunshi ne ya nemi faduwa jikinshi har tsuma yake amma ya kasa magana sai sauraron dayan bangaren yake cikin tashin hankali wayar ta zame a hannunsa.


“Jagaban menene! Me ya faru?”

Suke jero mishi, ba su kadai ba hatta da sauran ‘yan daban da suke cike da gidan sai da suka matso ya furta


“Sohana!”

Sai ya girgiza kai…..