15
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (15)*👑
Dukkansu wajen sanye suke da shuɗin kaya mai duhu,sun ɗaure kunkuminsu da farin ƙyalle,haka kansu sanye da ɗankwali shima Fari. Wato an juya kalar kayan da nawa kenan,maimakon tunda abu ɗayane ya taramu a bamu kaya iri ɗaya,ahah saida aka banbanta bawa da mai ƴanci.
Lelleƙa wajen nakeyi amma banga mai irin kayana ba ko ɗaya,can sai na hango wasu mata biyu a takure kansu a ƙasa da irin kayana, hamdala nayi a raina,ko babu komai mutuwar yawa ai kaka ce, maza na fara dubawa amma ban hango wasu masu fafaren kaya ba. Sai can ana shirin fara taron wasu maza suka shigo su biyu, matasane domin bazasu wuce shekara sha takwas ba. Dukkansu sanye suke da kaya farare,sun ɗaure kunkuminsu da shuɗin kyalle irin nawa,kansu kuma sunyi naɗi shima irin namu ɗan kwalin,Ba kaman sauran mazan wajen ba wanda suka sanya Shuɗin Rawani su. Kallonsu nakeyi har suka ƙariso wajen. Na farkon ko kaɗan bayyi kama da bawa ba,gwara ma wanda yake binsa a bayan shi za'a iya ƙiransa da bawan,amma shima ba bawa muna bawa ba,domin jikinsu ko kaɗan bai nuna alamar wuya ko kuma halin ƙuncin rayuwa ba.
Haka kawai na tsinci kaina da ƙuramasa ido tamkar wata wawuya. Har saida ya kulada hakan ya juyo muka haɗa ido,saurin ɗauke nawa idon nayi tareda cigaba da jan rigata ina sunkuyar dakai,domin na rasa ma yanda zanyi.
Jawabi manyan malam dazasu jagoranci gasar suka fara yimana,wanda duk na zuzuta girman gasarne da kuma ilimi da mutum zai samu a ciki,saikuma na girman kyautar da mutum zai samu,yawanci ɗaliban da suke wajen wasu ba sunzo bane domin dukiyar kyautar,sai domin daraja da kuma matsayinka dazata ɗaga tsakanin abokan takararka harma da duniya baki ɗaya. Ga bawa kuwa wani abune da bazai taba samun tamkarsa ba,domin hatimin da ake bawa wanda yayi nasara zai bashi damar shiga ko ina a cikin nahiyar gabakiɗaya,sannan shida bauta harma da ƴayansa sunyi hannun riga. Wata zimma naji ta shiga jikina jin darajar da hatimin yake ɗauke dashi, Tabbas bazan taba yi da wasa ba wajen ganin nacinye wannan gasa,badani ba kodan ƴaƴana masu zuwa a nan gaba idan Allah yabani idan sukaji hanyar dana bi wajen ƙarba musu ƴan ci nasan dole zasuyi alfahari da ni.
A haka taron ya ƙare kowa na kaffa kaffa domin kada ya sakewa ɗan uwansa yaji cikinsa hakan yasa ya fishi samun damar lashe gasar.
Har Joda ta kama hanyar tafiya inda taga sauran ɗalibai matan suna bi taji wata ta finciko kafaɗarta, Juyawa nayi Domin ganin wacece. Wata yarinya ce wacce bazata wuce sa'anninta ba shekara sha shida,kayan jikinta kaɗai na kalla nasan cewar ba sa'ar sasanto na bane ballantana sa'ar faɗana. Saurin durƙusawa nayi tareda bata haƙuri tun bansan mai nayi ba.
Hakan danayi yasa ta rusuna daga abinda zata aikatamin,ko kaɗan ban shigo nan wajen da niyyar nuna ni wata ce ba,domin nasan idan cuta ta sukayi babu wanda zai ɗau mataki,idan kuma nina cutar dasu hakan zai iya zama ajalina.
"Ke jahilar ina ce zaki nufi masauƙin Masu ƴan ci,kodan kinga An baki damar shiga wannan gasar sai hakan yabaki damar taka inda matsayinki bai kai ba,maza kije ki nemi inda bayi suke kiyada zango,koda wasa naga ƙafarki a sashennan bada niyyar kinzo goge goge ba saina saka an karyamin ƙafarki"
"Kinyimin daidai Jalilah gabaɗaya ji nayi gasar tafita takaina danaga wai hadda waɗannan ƙazaman halittun a ciki,ni ban taba ganin inda ake bawa bayi dama ba kamar wannan Jami'ar,banda an tilas tamin mai zai kawoni wannan matsatstsen wajen"
Duk abinda suke faɗa ina sunkuye ina jinsu,ko kaɗan banida niyyar ja dasu,domin hakan baya daga cikin shirina na zaman wajen,saidai nayi niyyar ruguza wannan ji da kannasu da sannu zasu ɗauki rashin nasara su koma inda suka fito.
Ɗaukar ƙullin kayana nayi bayan na ƙara basu haƙuri nayi hanyar wani waje danaga bayin dasuke aiki a wajen suna bi. Cikin sa'a kuwa na samu wani Ɗaki da sauran bayi guda biyun suke ciki. A zahiri ba nan yakamata mu zauna ba,amma saboda Bakar ɗabi'a ta nuna ƙyamatar bayi yasa dole zamu zauna a sansanin bayin dasuke aika aikace,idan zamuyi karatu dole sai mun taka zuwa inda karatun zai wakana.
Sallama nayi na shiga,ɗaya ce ta amsamin,yayinda ɗayar bata kulani ba sai aikin gyara kayanta da takeyi. Gefe ɗaya na samu na ajiye nawa kayan,Ban zauna ba saina fita,domin inaso nagama duba wajen da haddace duk wani lungu da saƙo,hakan zai sauƙaƙamin sosai. Bayan nagama duba Majalisu na karatu,ɗakuna karatu da wajen ajiye litattfai saina fara zagaya wajen ina nazartarsa. Ƙarar nishin mutum naji a wani lungu,wasu samari guda biyu masu sanye da kayan ɗalibai masu ƴan ci a tsaye suna dukan wani mai kayan dalibai na bayi. Matsawa nayi sosai ta yanda bazasu ganni ba domin naga mai yake wakana. Wanda muka haɗa ido dashine ɗazu da safe,bakinsa duk jini hakama jikinsa,sun haɗu sai dukansa sukeyi. Saida sukayi mai isarsu kafin suka tsaya suna maida numfashi. Ɗaya daga cikine yafara magana.
"Dama tun shigowarka kake wani jiji da kai,ko ka manta kalar kayan dayake jikinka ne,kana bawa amma kanayiwa mutane jiji dakai,duk matsayi da mulkin mai mallakarka to kai baka kai matsayinmu ba,ko waye ya tsaya maka kai ɗin bawane dan haka dolene kasan matsayinka,idan ba haka ba kuma mu gyara maka zama kaman yanda mukayi maka a yanzu. Har ka isa muna maka magana ka sharemu,kana kallonmu kuma ido cikin ido?"
Karisa maganar yayi yana taka ƙafarsa tareda murzawa da takalminsa,runtse ido tayi yana daga zaune ya mimmiƙe ƙafarsa,sai numfarfashi yakeyi saboda dukan dayasha,domin har abu suka kwada masa akai.
"Zo mu tafi Thanim Kana bata lokacinka wajen yimasa kashedi da baki,bayan yaren jikinsa ma ya isa ya faɗamasa. Gobe kuma kazo kaida ɗaya abokinka ku haɗa mana ruwan wanka kafin mu tashi a bacci,idan kaƙi zuwa......hukuncinka sai yafi na yau. Sannan kada ka kuskura kayi gangancin shiga aji,waida niyyar zakaji abinda ake cewa bare har kayi tunanin yin takara da masu ƴanci hakan masu mulki,suma sauran duk zamu game dasu,babu wannan rainin badai akan mu ba"
Saida suka gama yi masa tujarar harda tofa masa yawu kafin duka bar wajen,duk abinda suke faɗa akan kunnena,zaro ido nayi banyi tsammanin Haɗarin wajennan yakai haka ba saida nashigo,tun a ranar farko har sun fara nuna halayensu na zakunan,daga maza har matan. Wai mai al'ummarmu suka zamane a yau gameda mulki?"
Jan sanyayyyun ƙafafuwana nayi na nufi inda mutumin yake, bayan sun tafi.
Tsugunnawa nayi daidai tsayinda zaiga fuskata nima kuma na karewa tasa fuskar kallo,tausayi yabani duk yanada duhun fata amma kuma kyakyawane sosai,amma saika ƙura masa ido zaka kalli hakan,sabanin in daga nesane iya izzarsa ce kawai take nunawa.
A hankali ya buɗe kumburarrun idonsa dasuka sha duka ya kalleni,tausayinsa ne yakara kamani dan ba ƙaramin duka yasha ba,badan yayi komai ba sai domin kawai yana bawa.
"Sannu"
Shine abinda na faɗa a hankali,har sannan idona bai bar kansa ba, yunƙurawa yayi zai tashi nayi saurin dakatar dashi ta hanyar riƙe hannunsa ina jijjiga masa kai.
"Karka tashi yanzu,jikinka akwai rauni sosai ka bari sai jikinka ya fidda wannan jini mai kaurin dayake tsayar da fitar jini tukunna kuma yayi ƙarfi,amma tashinka a yanzu cikin gaggawa zai ƙarawa raunin jikinka muni wanda hakan zai jawo........."
"Ke likita ce ?"
Kallona yakeyi ina bayanin,bai kai ga karisawa ba naji Sanyayyar maganarsa mai ɗauke da kaifi na amon Jaratan masa,a taƙaice yayimin tambayar sai kuma yayi shuru yaji amsa daga gareni.
Summ nayi bankai ga ƙarisa bayanin ba,ohh ni Joda taya zan iya boye sanina gameda abubuwane batareda kowa yasan nasani ɗin ba,gashi cikin ƙanƙanin lokaci har mutum ɗaya yaganoni. To inaga har tsawon shekara biyu nan gaba,anya kuwa zanyi basajar danayi niyyar yi a wajen.
Shuru nayi ban bashi amsa ba,yanzu ba lokacin wannan bane,karsashina ya tafi akan wanne irin taimako zan bashi wajen ganin yafita daga halinda yake ciki. Tunda na fara yin nazari akan magani hankalina yakan tashi idan naga wani a hali na jinya kuma zan iya taimakansa,koda maƙiyina ne bana iya yin biris dashi har sai naga yafita daga wannan halin,inaga kuma bawa ɗan uwana wanda yakarbi hukunci saboda matsayinsa.
"Karka motsa sosai,zanso kabani Daƙiƙa biyar ina nan dawowa bada jimawa ba"
Cikin hanzari nabar wajen badan zuciyata taso ba nanufi masauƙinmu inda kayana yake,bansha wahalar samun abinda nake buƙata ba,don dama na taho da magunguna wanda zan nemosu a taimakon kota kwana idan yasameni kokuma wani wanda yake tareda ni.
Na kulada kallon mamaki da mata biyun suke bina dashi,amma kota kansu banbi ba na fita da sauri zuwa inda nabar bawan Allah n.
Na isa kenan na sameshi yana tari,da karfi yakeyinsa kamar ransa zai fincike daga gangar jikinsa,daskarewa nayi ina kallonsa,lokaci guda na tuno da mahaifina lokacin dayake tari mai tsanani a cikin jirgin ruwa. Jarumin rayuwata wanda ban daɗe da saninsa ba yatafi ya barni har abada. Ƙwallar data fito daga idona nayi saurin daukewa tareda isa ga inda mutumim yake cikin Gaggawa. Dafa bayansa nayi ina yimasa sannu cikin tausayawa, dogon wani tari yaja daga ƙarshe mai ƙarfin gaske kafin ya amar da wani gudan jini baƙiƙƙirin dashi. Zaro ido nayi ina kallon jinin sannan kuma ina kallonsa.
Ɗaga fuskarsa nayi ina kallon idonsa,hannuna nasaka na buɗe ƙasan fatar idonsa na dudduba, hannuna kuma na sakashi akan ƙirjinsa tareda rufe idona,baiyi motsi ba kokuma wani sauti ballanatana har ya tureni,wanda hakan shine abinda nake bukata,domin kafin nagano mai yake damunsa ina buƙatar nutsuwa,shuru dakuma rashin hayaniya. A hankali nafara karanta saƙon jijiyoyin zuciyarsa daya bayan ɗaya har ta kaini ga kan wata jijiya a can cikin zuciyar tasa,abinda nagani yayi matuƙar ɗagamin hankali da firgitani,gaba ɗaya sashe guda na kusan zuciyarsa baya bugawa,jijiyiyin wajen sunyi sanyi matuƙa. Saurin janye hannuna nayi ina kallonsa cikin firgici. Shima kallona yake da mamakin mai nagano a jikinsa,amma kuma ya gagara buɗe baki ya tambayeni.
Hannuna yana rawa nafara goge jinin dayake jikin raunukansa da wani ruwan bishiya dana ta ce na zuba a wata kwalba,domin wanke ciwo irin haka. Sai dana gama wanke masa sannu a hankali tass kafin na ɗaure manyan da farin ƙyallen danazo dashi. Duk abinda nakeyi inayi ina kallon Ƙirjinsa inda zuciyarsa take. Gabaɗaya jikina yayi sanyi na kasa tantance mai nagani,dolene na kaiwa Baba almahdi ziyara da wannan zancen,domin shikaɗaine zai iya fayyacemin shi. Domin tsabar abun ya shigeni har jin ciwon nakeji a tawa zuciyar nima.
Muryars najiyo bayan nayi nisa a duniyar tunani.
"Shin ke wacece,kuma mai kika gani a ƙirjina daya sakaki firgici haka?"
Tambayar tazomin a bazata hakan yasa na duburburce na rasa mai zance masa taya zan faɗamasa gaskiyar dani kaina bam gama tantanceta ba, sannan ni wacece shima mai zance masa.
"Ni ba kowa bace,Babu komai babu abinda nagani, na wanke maka ciwukan Insha'allahu zasu warke da wuri kuma basazu bar tabo mai girma ba. Sai kakula ka kiyaye sosai nan gaba,domin mutanennan basuda imani indai ga wanda yake naƙasa dasune. Zasu iya komai na zalunci akan wanda sukeda iko dashi."
"Shikenan nagode da taimakonki zanso idan kin tafi ki nemomin wanda kikaga munshiga wajennan taredashi,nasan zaki gani fuskarsa saboda kallon dakikayi mana ɗazun bazai bari ki mance da fuskarsa ba"
Kunya ce ta kamani danaji furucinsa,miye sai yaƙara da maganar karshen to.
"Taya za'asan na haddace fuskar mutum idan ba hanyar danabi na haddace din aka bi ba. Ballantana ma ko ban taba ganinsa ba ai bazayyi wahalar ganewa ba,tunda muɗin tamkar balbalene acikin hankaki,in baka gane fuska bama zaka gane launi"
Ina gama faɗin hakan na tashi nabar wajen,ina jiyo zatin kallonsa a gadon bayana amma ban waiwaya ba,haka kawai naji kallonnasa yana min gizo a idona.
Kaman yanda na buƙata neman Ɗaya bawan na shiga yi a farfajiyar wajen,ban ganshi ba wani bawa ne mai shara dana bashi cikiya ya nunamin wani lungu akan innabi zan sameshi. Tafiya nakeyi har na sare da shiga wajen zan dawo saikuma na hangi wata farfajiya. Turaka ce a wajen guda biyu ba laifi sunada wadatar fasali ba kaman inda muka sauka ba,samunsa nayi ya haɗa wuta a bakin wajen yana gasa wani nama kamar tsuntsu,dama akwai jeji a wajenne daza'a iya kama tsuntsu na faɗa a raina.
Ɗagowa kansa yayi yanayimin kallon mamakin mai nakeyi a wajen,tun kafin ya fassarani da wata manufa nayi saurin faɗa masa abinda ya kawoni.
Yana jin bayanina ya tashi zumbur tareda yin wulli da tsuntsun dayake gasawa,ya fita da gudu hankali a tashe kaman wanda aka ce uwarsa da ubansa sun mutu. Mamakin razanar tasa nayi sannan na juya na kalli inda ya jefar da gasashshen tsuntsun. Haɗiye yawu nayi tareda cewa da zai jefar aida yabani a zuxiyata.
Juyawa nayi nakoma masauƙinmu, zanyi sallah na huta,zuwa dare nakeso naje wajen Baba almhadi Allah yasa nasamu ganinsa baya bayarda karatu ga ɗalibansa wanda zai yaye bana,naga yana bada muhimmanci a kansu sosai.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow