SAUTIN KARSHE

Chapter 7

by @amanarcool323

Washe gari Sudais na zaune a ɗakinsa yana duba wasu takardu ya ji saƙo ya shigo wayarsa, kamar ya share sai kuma ya ɗauki wayar yana dubawa, ko da ya duba Ilham ce, "Assalamu alaikum, barka da safiya, ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya? Yaya Sudais ban san me ya sa ka kasa fahimtar irin halin da zuciyata take shiga saboda kai ba. Na yi iya ƙoƙarina na danne abin da nake ji a kanka amma na kasa, kullum sai ƙara girma yake yi a zuciyata. Ka san ina son ka tun da daɗewa, sai dai ban san dalilin da ya sa ka ƙi karɓa ta ba, wata ƙila ko ba ni da tsari ne irin na matar da kake son aura? Yaya Sudais ka ji tausayina don Allah, ka taimaka mini, ka ceci rayuwata. Jiya bayan na dawo daga wurin Mammy, a gida an yi mini zancen za'a haɗa ni aure da Saddik ɗan gidan Alhaji Bashir, Yaya zuciyata tana cikin wani irin hali da ba zan iya bayyana maka ba. A duk lokacin da aka yi zancen aurena kai nake gani a idona.
Yaya Sudais da akwai yadda zan yi in cire ka a raina da na yi tun da daɗewa, ko dan na samar wa zuciyata sassauci daga azabtuwar da take yi a kan sonka. Don Allah kada ka bari a kai ni inda zuciyata ba ta so, alhali kana sane da komai, kai nake so, kuma kai nake fatan samu a matsayin mijina. Ko da ba za ka so ni kamar yadda nake son ka ba, ka tausaya mini, ka yi wa Dady maganar aurena, ina roƙon ka da ka dubi halin da nake ciki. Kada ka bari a yi mini auren dole, wallahi bana sonsa, kai nake so, ina sonka fiye da yadda kalmomi ba za su iya faɗa ba, ko babu komai ni ƴar uwarka ce, kuma bana tunanin za ka iya samun macen da za ta soka kamar ni, please have pity on me Ya Sudais". Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karanta saƙon nata, ajiye wayarsa ya yi ya ci gaba da duba takardunsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci ya kan tuna da kalaman Ilham, amma duk da haka baya jin cewar zai iya yi mata so na aure kamar yadda take buƙata. Yana kammala duba takardun ya shirya ya tafi, kasancewar ƙarfe tara da rabi zai gana da mutanen da Alhaji Sardauna ya haɗa shi da su. 

Ƙarfe tara da minti arba'in Sudais ne a cikin office ɗinsa tare da baƙinsa Alhaji Hali, da Alhaji Badaru, bayan sun gaisa ne, ya sa aka kawo musu ruwa da lemu, kaɗan suka sha, ko wanne fuskarsa ɗauke da murmushi. 

Alhaji ya gyara zamansa, sannan ya fara magana "Wato Adam, mun daɗe muna jin labarinka a wurin amininmu Alhaji Sardauna, da kuma yanayin yadda kake gudanar da ayyukanka. Matasan yanzu ba kasafai ake samun masu hankali da hangen nesa irin ka ba, muna jin kyawawan bayanai game da kamfaninka ne, shi ya sa muka ga ya dace mu zo mu gana da kai, idan zai yiwu muna son mu yi haɗin gwiwa a wasu harkoki na kasuwanci da kai. Saboda akwai abubuwa da za mu amfana da juna a cikinsu".

Sudais ya jinjina kai, ya ce "Ma sha Allah, to ina sauraren ku".

Alhaji Badaru ya ci gaba da faɗin "Ga wannan file ɗin ka duba. Duka bayanan suna ciki". Ya yi maganar tare da tura file ɗin a gabansa. Ɗaukar file ɗin ya yi, ya buɗe ya fara duba wa. A hankali ya ɗago da kansa ya kalle su, kafin ya mayar da dubansa ga file ɗin. Sai da ya gama duba wa sannan ya rufe, ya kalle su yana faɗin "Ma sha Allah, na duba dukkan bayanan da suke ciki, kuma in sha Allah babu wata matsala zamu yi wannan tafiyar da ku".

Cikin jin daɗi Alhaji Hali ya ce "Ma sha Allah, muna godiya sosai da sosai, Allah ya taimaka ya yi mana jagora". Ya amsa da "Amin" basu wani daɗe ba suka yi masa sallama suka tafi. 

Suna barin office ɗin Sudais ya jingina jikinsa da jikin kujera yana lumshe ido. A hankali ya ce "Alhamdulillah komai zai zo mini da sauƙi" wayarsa ya ɗauka ya kira ogansa na wurin aikinsu, bugu biyu ya ɗaga, Sudais kamar a gabansa yake ya gaishe shi cikin girmamawa. Oga ya amsa yana tambayarsa ya ayyuka? Sudais ya ce "Alhamdulillah" 

"To ma sha Allah, ya ake ciki game da aikin da aka ba? Ina fatan dai ka fara binciken?" Oga ya tambaya.

Sudais ya ce "Oga dalilin kiranka ma kenan, mutunen da aka bani aiki a kansu yanzun nan suka bar office ɗina, sun zo ne akan suna son haɗa kasuwanci da kamfaninmu . Oga duk da zargin su ne ake yi ba'a tabbatar ba, amma jikina yana bani akwai wani abu a tattare da su, sai dai ban nuna musu komai ba, kuma na amince da buƙatar da suka zo mini da ita, daga yanzu zan fara bincike a kansu". 

Oga "Very good, shikenan ka bi komai cikin tsari kamar yadda ka saba, ka da ka bayar da wata dama da za su gane cewar kana bibiyar al'amurransu. Allah ya taimaka ya dafa maka". Sudais ya ce amsa da Amin yana faɗin "In sha Allah Oga zan kiyaye". Daga haka ya yi masa sallama tare da ajiye wayar. Sake lumshe idanunsa ya yi, tunanin Abbansa ya dawo masa cikin ƙwaƙwalwarsa, ya fara tuna ranar da Abbansa zai bar duniya, da irin maganganun da ya furta kafin rai ya yi halinsa. Duk da a lokacin yana da ƙaracin shekaru, bai fi shekaru goma ba, amma ya san maganganun da Abbansa ya faɗa akwai ayar tambaya a cikinsu, sake runtse idonsa ya yi, yana jin wani zafi a cikin zuciyarsa, "Sudais, ka ja ƴan uwanka a jiki, bayan Uncle ka da ku yarda da kowa, mutane ba abin yarda ba ne, duk yadda kake da mutum zai iya cutar da kai ta inda baka yi zato ba, ƙalilan ne masu gaskiya da amanar da ba za su iya cutar da wanda suke tare da shi ba. Sudais ana cutar da al'umma ta inda ba a yi tunani ba, wannan ƙasar tamu tana buƙatar gyara. Ina fatan Allah ya cika maka burinka domin ka yi maganin azzaluman ƙasar nan masu fuska biyu, sannan ka ɗauki fansar cutar da aka yi muku, Sudais an cutar daku, Allah ya baka iko da nasarar gano ta in da aka yi muku wannan cutar, ina matuƙar son wurin da nake aiki, da AS...."

Dafe kansa ya yi da ƙarfi, jin yana barazanar rabe masa gida biyu, bayan tuna kalaman Abbansa, "In sha Allah Abba sai na gano azzaluman da kake magana a kansu, sai na bankaɗo asirin duk wasu miyagun mutane masu cutar da al'umma, sai na gano cutar da aka yi mana, wallahi ba zan yafe ba, ba zan haƙura ba, saina cika maka burinka Abbana koda hakan yana nufin zan rasa rayuwata ne". 

*****

Wani irin fitinannen ciwon kai Halima ta tashi da shi yau, amma a haka ta daure ta yi girki, bayan ta kammala ta zuba na su Inna a kula, sannan ta shirya ta wuce asibiti domin ta sake duba jikin Abida, Ma'u kuwa tana makaranta sai ƙarfe biyu za ta dawo. Ko da ta isa. A harabar asibitin ta tarar da Aliyu a zaune, wuce shi ta yi kasancewar a cikin jama'a yake ya sa ba ta kula shi ba. Da sallama ta shiga ɗakin, Inna na zaune tare da wata ƴar uwarta da ta zo duba jikin Abida, gaishe su ta yi, suka amsa suna yi mata sannu da zuwa. Halima ta zauna tana faɗin "Washh Allahna, wallahi da ƙyar na ƙaraso asibitin nan Inna, saboda ciwon kan da yake damuna". Inna ta ce "Ashsha subhanallah! Sannu Halima, to kuma ba kya jin daɗi shi ne za ki biyo hanya? Ai da kin bari zuwa gobe idan kin ji sauƙi sai ki zo" . Shiru ta yi ba ta yi magana saboda azabar ciwon da kanta yake yi. Turo ƙofar aka yi da sallama, likita ne ya shigo Aliyu na biye da shi a baya, gaisawa suka yi da su Inna kafin ya wuce ya sake duba jikin Abida dake ta bacci. Aliyu ya kalli Halima ya ce "Ke lafiyarki kuwa?" Ba ta iya amsa mishi ba sai Inna ce ta ce "Ba ta da lafiya ne?".

"Me yake damunta? Ba ta da lafiya kuma shi ne za ta zo nan? Me ya sa ba ta kira ni ba?" Aliyu ya faɗa yana kallonta, Likita ne ya zo zai wuce bayan ya gama duba jikin Abida yaga Halima dafe da kai, har zai fita sai ya ji ana faɗar ba ta da lafiya, tsayawa ya yi yana faɗin "Subhanallah! Ba ta da lafiya ne?". Ya tambaya cike da kulawa. Aliyu bai bashi amsa ba "Inna ta ce "Eh kanta ne yake mata ciwo". 

Likitan ya dubi Aliyu ya ce "Ai ina ga bai kamata ta zauna a haka ba, ya kamata a duba ta, saboda ciwon kan nan ba shi da kyau". Kasa magana Aliyu ya yi, "Inna ta ce "Haka ne ciwon kai bashi da saɗi, ina ne za a duba tan?" Ta yi tambayar tana kallon likitan. Ya ce "Ku biyo ni muje". Daga haka ya bar ɗakin, Inna ta riƙe Halima dake dafe da kanta suka fita. Aliyu tsaye ya yi ya jingina da jikin ƙofar, haka kawai ya ji zuciyarsa na bugu da ƙarfin gaske. Bayan kamar minti ashirin sai gashi sun dawo hannun Inna riƙe da ledar magani, zama suka yi, ta ɓalla mata maganin ta karɓa tasha. Inna ta ce "To ki ɗan kwanta ki yi bacci ko da na awa ɗaya ne in sha Allah ciwon kan zai sauka. Kaga Gadanga mutanen nan suna da tausayi. Daga gwajin da suka yi mata har maganin da suka bayar dubu biyu ce suka karɓa, Allah dai ya saka musu da alkhairi, wannan ai kamar kyauta suka yi". Ya amsa da "Amin" Kwanciya Halima ta yi, Aliyu ya dinga binta da kallo, sannan ya mayar da kallonsa ga Abida. Ajiyar zuciya ya sauke tare da juya wa ya bar ɗakin.

*****

Tunda ta tura masa saƙon nan ta kasa samun sukuni, bini-bini ta duba wayarta ko za ta ga ya mayar mata da amsa amma shiru babu reply. Zama ta yi a ɗakinta tasha kukanta har ta gode Allah, kafin ta tashi ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito, abayarta kawai ta saka ta fita daga ɗakin. A falo ta tarar da Momy zaune tare da Dady, cikin dashewar murya ta ce "Dady good afternoon". Ɗago da kansa ya yi yana kallonta, yadda yaga gabaɗaya idanunta sun kumbura. "Ilham lafiya na ga idanunki sun kumbura haka kamar wadda ta yi kuka?". Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Dady kaina ne yake ciwo, shi ne ya sauka har cikin idona". "Subhanallah! To kin sha magani ne?". Ya tambaya yana kallonta

"Eh Dady na sha".

Momy na son yin magana domin ta san ƙarya take yi babu wani ciwon kan da take yi, ta san kuka ne ta yi saboda ta ce sai ta auri Saddik, "Ilham" ta ji Dady ya kira ta, ɗago da kanta ta yi ta ce "Na'am Dady". 

Ya ce "Momynki ta sanar da ni cewar kin aminta da Saddik, kenan kin haƙura da Yayan naki?". Ya yi maganar yana murmushi. Ilham ji ta yi kamar ta ce masa a'a ba ta amince ba, amma tuna gargadin da Momy ta yi mata ne ya sa ta ce "Eh Dady". 

Dady ya ce "To ma sha Allah, na ji daɗin haka. Duk da Sudais na so ki aura ba Saddik ba, amma babu komai shima Saddik ɗin ɗan gida ne, in sha Allah zan yi wa Bashar magana sai ya sanar da shi kin amince ya zo ku gaisa". Shiru ta yi ba ta ce masa komai ba. Momy kuwa wani irin daɗi ne ya kamata, ta ce "Ma sha Allah, ai Alhaji da Saddik da Sudais duka ɗaya ne, fatan mu dai Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokaci musha biki". Dady ya amsa da "Amin".

Ilham kuwa tashi ta yi, ta bar falon ta koma ciki ta dasa sabon kuka.

****

Ƙarfe ɗaya Halima ta farka daga baccin da ya ɗauke ta, Alhamdulillah ta ji sauƙin ciwon kan sosai, Inna sai sannu take yi mata, Aliyu da shigowarsa kenan cikin ɗakin ta farka, duban ta ya yi ya ce "Idan kin ji sauƙi sai ki tashi ki koma gida, kinga lokacin dawowar waccan yarinyar ya kusa, kar ta zo ta tarar da gidan a rufe". Halima ta kalli Abida dake bacci har yanzu ta ce "Inna wai ba ta farka ba ne?". "Inna ta ce "A'a ta farka ɗazu da safe, allurar bacci suka sake yi mata saboda ta riƙa samun isasshen bacci, duba da yanayin aikin da aka yi mata". Jinjina kai ta yi, ta ce "Allah ya ba ta lafiya". Inna ta amsa da "Amin" sannan ta ɗauki maganinta da aka ba ta, da kular jiya da suka zo da ita, ta yi wa Inna sallama ta tafi, bin bayanta Aliyu ya yi, sai da ya tabbatar ta samu abin hawa sannan ya koma ciki.



Amanarcool
***