KAIFI ƊAYA

10

by @ummishatu1111

10


***Zuciyarshi cike da saƙe saƙe kala kala ya nufi office din anty Mimi yana driving yana lissafin yanda zai bullowa wannan lamarin da haka har ya ƙarasa hospital din,

Kai tsaye office dinta ya shiga bayan yayi knocking, suna zaune ita da yaya Aliyu kan kujera 3 sitter wacce ke girke cikin office din daga gefe ɗaya,

"Afeef wai me kake nufi damu ne? Munyi magana dakai munyi alkawari munyi yarjejeniya, har kudi na baka dan komai ya tafi bisa tsari amma ka dawo min dashi yanzu kuma tsawon watanni ina shan kanka akan ka sakar min mata ta amma abu yana neman faskara sai faman wasa da hankali kake yimin....... To yanzu kazo ka sake ta ne ko me ya kawo ka? " tunda yaya haidar ya fara wannan bayanin Afeef ya zuba musu ido yana kallon su daga shi har anty Mimin, baiyi magana ba sai da yaji yaya haidar ya ɗiga aya alamar ya gama sannan ya ja ajiyar zuciya a hankali ya sauke yace,

" Yaya kuyi hakuri da ɓata muku lokaci da nayi a baya, wallahi ko kadan hakan ba da niyya nayi ba sannan ba wai da son raina bane it wasn't intentional..... Amma yaya ni ina ganin da mu hakura da maganar sakin nan kawai mu dauka haka Allah ya kaddara kuma ya tsara sannan zamanku da ita ya kare ne shiyasa har aka yi haka..... " ai daga Anty Mimi har Yaya Aliyu jin maganarsa suka yi tamkar saukar aradu ko kuma saukar guduma a tsakiyar kansu, zaro ido Aliyu yayi yana kallon Afeef cikin fushi da fusata yace,

" kai me kake nufi ne, what do you mean? Ba zaka sake ta ba ko yaya? Mun nemi shawararka ne da zaka zo kana ce mana haka Allah ya tsara? Zamana da mimi bai kare ba dan mutuwa ce kadai zata rabamu...."

"yaya Haidar mu daina yaudarar kanmu......let's stop deceiving ourselves Wannan itace gaskiya, kun rabu da anty Mimi ni kuma na aureta and bana jin zan iya sakinta bare har ta dawo gareka in fact dama ban aureta dan in saketa ba..."

Tsaye anty mimi ta mike ba tare da ta sani ba jikinta yana faman rawa fuskar ta cike da tashin hankali, ta kasa magana ta kasa koda kwakkwaran motsi, shima yaya Aliyu tashi yayi daga zaunen da yake dan bai ga alamar cewa Afeef da wasa yake ba dan babu alamar wasan a tare dashi dan yana magana ne cike da nutsuwa da kuma gaskiya,

"lallai ka cika maci amana..... Ka cika mazambaci kuma mayaudari Afeef....... Amma ina son ka sani Mimi ba kalar matarka bace, wallahi ko kana so ko baka so sai ka sakar min mata tunda baka da mutunci.... Nafi ka hauka"

"yaya wannan fa ba maganar cin amana bane maganar gaskiya ce wallahi ba zan saketa ba sai dai idan mutuwa nayi sai ta koma maka amma indai ina raye to kun gama zaman aure....."

"Afeef me nayi maka? Me muka yi maka da ka zabi ka tarwatsa rayuwar mu ka wulakanta mu? Ashe dama ba taimakonmu kayi niyyar yi har cikin zuciyarka ba? Wannan wanne irin yaudara ne?" Anty Mimi ta fada idanuwanta sun cika da kwalla dan tsabar bakin ciki da tashin hankali,

" ka bude kunnen ka da kyau ka jini Afeef, na rantse da girman Allah ko sama da ƙasa zata hade sai ka sakar min mata ta, na fika iskanci kai karamin dan iska ne, ka bar ganin kana shan kwaya wallahi na fika tijara ƙwayarka da neman matanka da kake yi duk a tafin hannuna kake..... "

Jin abubuwan da yaya haidar ke fada masa yasa kawai ya mike da niyyar ya tafi yabar musu office dinma gaba ɗaya, wani kukan kura yaya Aliyu yayi ya nufe shi ya finciko shi ya fara kifa masa mari baji ba gani amma ko gezau baiyi ba,

" wallahi ko zaka kashe ni ba zan saketa ba....." wani wawan marin ya sake kifa masa, ƙara anty Mimi ta ƙwalla kamar wacce keda aljanu ko kuma take shirin tayar dasu babu shiri yaya Aliyu ya nufeta, juyawa Afeef yayi ya fita daga cikin office din fuskarshi rado rado da shatin yatsun yaya Aliyu saboda marin da yayi masa ba na wasa bane gashi bahago ga kuma fushi da zuciya duk a lokaci guda, shima a kule yake kuma a fusace ya koma gida, yana shiga yayi parking motar sa ya nufi cikin part dinsa ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskarsa, idanuwansa jajur saboda bacin rai haka itama fuskar shi tayi ja musamman wurin shatun hannun yaya Aliyu, shi ba wai yana son anty Mimi bane kamar yadda ya san itama ba sonshi take yi ba amma zasu zauna ahaka har lokacin da zasu koyi son junansu wannan alkawari ne ya daukarwa kansa, ba zai taɓa sakinta ba duk bala'i, kashe wayar sa yayi yai zamansa cikin bedroom dan baya son kowa ya ganshi.

Kamar wata mai aljanu haka anty Mimi ta koma ta zubawa yaya Aliyu ido wanda yake rike da hannunta hawaye na bin kumatunta,

"kaga irin abinda na jima ina fada maka ko.... Kaga ni ko? Dama sai da na fada maka mu nemi wani mu biya shi zai yi mana abinda muke so amma kace baka yarda da kowa ba kai sai shi...... Gashi yanzu yace ba zai sake ni ba kuma na san maganar na iya zuwa kunnen su Abba..... Hajiya tana jin wannan maganar cewa zata yi in tare a gidansa shikenan an rabamu..... Wallahi bazan iya zaman aure da kowa ba sai kai.... Mutuwa zanyi yaya Aliyu..... Wallahi mutuwa zan yi na sani.... " wannan shine abinda take ta fada tana hawaye,

" Yaron nan yaudara ta yayi ya shammaceni Mimi, he deceived me.... Amma nayi miki alƙawari ba zan taɓa barinsa har yayi nasara a kanmu ba.... Bai isa ya rabamu ba.... "

Numfashi take yi sama sama kamar mai ciwon asthma ko wani ciwo mai kama da haka, sam bata ma fahimtar abinda yake fada dan ta jima bata cikin hayyacinta kafin ta dawo daidai amma kuma a mugun hargitse take, tare suka fita daga office din nata anan ta bar motar ta ya dauketa a tashi zuwa gida, ta kasa magana dan ko kalma daya bata iya fita daga cikin bakin ta ba har suka je gida duk sai bata tabbaci yake na cewa zai shawo kan wannan matsalar, bedroom dinta kawai ta shige ta kwanta kan gado tana hawaye, tun tana kukan zuci har ta fara na fili babu wanda ya sani ko kuma ya san halin da take ciki daga ita sai yaya Aliyu sai kuma Afeef. Shi kam yaya Aliyu bayan ya ajiye ta ya wuce gidanshi fashe fashe yaje yayi kamar wani mahaukaci haka ya zama daga karshe ya yanke jiki ya fadi da kyar ya iya kiran yaya faruk yazo ya kai shi asibiti, 

Washe gari anty Mimi bata fita aiki ba kuka kawai take yi ta kasa cin abinci saboda bakin ciki, bata so su ɗaga maganar har ta fito manya su ji dan idan su Abba suka ji to kashin su ya bushe gaba daya sannan dole Afeef shine da nasara dan ta san su Abba baza su taba goyon bayan su ba bare har su biyewa wannan shirmen nasu, sam bata da labarin abinda ya faru da yaya haidar har sai da aka sallame shi daga asibitin ya koma gida sannan ya kirata yake sanar da ita, tagumi ta rafka cikin ranta tana cewa yanzu ita ya zata yi? Wayarta ta dauka ta fara rubutawa Afeef massage, ai durkusawa wada ba gajiyawa bane,

Yana tsakiyar cikin dakin sa yana training kamar yadda ya saba yi duk safiyar duniya sai yayi wannan training din na awa ɗaya ko mintuna talatin yaji shigowar massage, bai buda ba sai da ya gama training din ya zauna yana hutawa lokacin ne ya bude massage din nata,

_Bai kamata ka zama silar rushewar farin cikinmu ba matsayin ka na jininmu, bai dace ka kasance dalilin zubar hawayena ba Afeef, nida yaya Aliyu wanne laifi muka yi maka? Karka manta alkawari fa muka yi da kai, Afeef na roke ka da girman Allah ka tausaya mana ka sake ni._

Shuru yayi yana kallon massage din yana sake karantawa bayan ya karanta a Karon farko,sai faman jujjuya sakon yake yi acikin zuciyarsa daga karshe ya ajiye wayar ya tashi ya shiga toilet saboda gaba daya ya hada gumi wanka kawai yake bukata daidai wannan lokaci, bai ko kula da massage din nata ba bare yayi reply al'amuransa ya cigaba da yi hankali kwance,

Tun bayan da yazo gari bai je family house dinba sai yau ya kuduri niyyar zuwa, blue din shadda yasaka amma bai saka hula ba, agogon azurfa ya daura a hannunshi ya fita, gidan umma ya fara shiga wato ɓangaren Abba baƙi suka gaisa babu kowa a gidan sai ita kadai, fitowa yayi ya shiga ɓangaren Ammi itama din dai sai ita kadai dan hatta Irfan baya nan haka itama Suhana shiyasa bai wani jima ba yace bari yace wurin hajiya, yana fitowa ya hango yaya Aliyu da anty Mimi da alama tare suke, shima yaya Aliyu ya gano shi lokacin da yake fitowa daga part din Abba fari shiyasa ya nufoshi a fusace,

"kai.... Dama neman ka nake yi, yau babu inda zaka je sai ka sakar min mata ta"

"ta ina ta zama matarka?" Afeef din ya fada yana yi masa kallon raini,

"a gidan uwarka ta zama, ni zaka rainawa hankali? Dan kutumar ubanka ka sakar min mata"

"to idan matarka ce menene alakata da maganar sakinta?"

"ka sakar min mata dan kutumar ubanka..."

"ba kutumar ubana ba sai dai naka ai uba bai fi uba ba......" wani wawan mari Aliyu ya kai masa yasa hannu ya tare, cikin zafin rai yace,

"ka bar ganin ina rabuwa dakai wallahi duk abinda ka sake yimin sai na rama, Mimi kuma ba zan saketa ba zan kai ta gidana and i will have her on my bed ko kana so ko baka so....."

Shake shi yaya Aliyu yayi ya fara kai masa duka shima yana ramawa daidai lokacin yaya faruk ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya fito daga cikin motarsa ko kashewa bai yi ba ya nufe su cike da mamaki,

" Aliyu..... Haba ya haka? Kai Afeef sake shi, ku bari mana.... Haba Haidar ya kake fada da ƙanin ƙanin bayanka..... Afeef har nawa yake da zaka rinka kokarin fada dashi?" yaya faruk ya fada cike da mamaki, ita dai anty Mimi kuka ta saka ta shige cikin sashen hajiya da gudu, 

" wannan yaron ɗan iska ne bashi da mutunci faruk, da ka barni naci ubansa...."

"Ka fadi duk abinda zaka fada amma daga yau ban yarda ka sake kula mata ta ba bare har ka dauko ta acikin motar ka......" 

"Afeef ya isa haka jeka ka tafi abin ka, kar na sake jin bakinka...." yaya faruk ya fada har lokacin shi dai yana cike da mamaki sai yanzu ya fahimci abinda watakila shine musabbabin fadan nasu ta yuyu kishi Afeef yake yi saboda Aliyu ya dauko mimi a mota shiyasa har ta kai su ga haka, 

" Ɗan ƙwaya..... Dama idan banda ƙwaya da neman mata ku sojoji me kuka iya..... Ka sha tana karanta maka hauka ko..... Zanyi maganin ka" 

Shi dai Afeef bai sake kula shi ba saboda maganar da yaya faruk yayi masa ya wuce cikin motarsa yama fasa shiga wurin hajiyan ya fita daga cikin gidan ransa a ɓace, wannan kallon da yawancin mutane ke yi musu su sojoji yana ɓata masa rai, ai a ko ina akwai ɓata gari kuma akwai mutanen kirki ba duk soja ne ke wannan harkar ba, 

Bayan tafiyar Afeef yaya faruk kama hannun yaya Aliyu yayi har zuwa cikin runfa, 

"Haba Aliyu me yasa zaka biyewa Afeef bayan ka san shi yaro ne, ai bai kamata ba a ce ka tsaya kana fada dashi sai kace wani sa'anka...... Idan akan matarsa ne ka rabu dashi kar ka sake bata lift shikenan, duk da na san yar uwarka ce amma hanyar lafiya sai abita da shekara "

Shuru yaya Aliyu yayi saboda baya jin zai iya fadawa faruk gaskiyar abinda ke faruwa duk da shine abokin shawarar shi kuma babban amininshi........