GUMBAR DUTSE

G_D - 4

by @khadeejacandy

JAWAD POV.

A bangarensa ya faka motar ya fito ya doshi hanyar shiga katon falon da aka kawata da kale kalen duniya, a bude ya samu kofar falon daman idan Kaka tana zaune a falo bata yarda a rufe kofar sai dai a bude tana ganin wanda zai shiga ko ya fita a harabar.

"Oyooyoy oyoyo an dawo"

Ta tarbe shi da far'a tana tabi da hannayenta da fatar jikin ta janye saboda tsufa. Ya saki fuska kamar zai yi murmushi kuma ba murmushin ba.

"Kaka kina nan zaune?"

"Eh ashe yanzu zaka dawo, abun kari nake jira su kawo min har yanzu ba su kawo ba, ai na fada maka idan baka gidan ba ayi min gata, wata rana fa sai an gama na rana ake hadewa a kawo min, ko kuma a kawo min shi a bar shi a nan sai idan na sauka na gani"

Jawad ya kalli agogon falon da ya nuna karfe goma har da yan mintuna, a gurinsa normal ne zai iya kaiwa 12pm ma be karya ba, amman a gurin kakarsa hakan ba daidai ba ne domin ita tsohuwa ce kuma tana da ulcer be kamata ace sai rana ta yi sosai za a kawo mata abinci ba.

Ya juya yana rike da keys din motar ya fice daga bangaren ya koma bangaren matar uban tasa, ya murda kofar falon dake cike da sanyin ac ya shiga.

Kanensa yan mata dake zaune a falon suna ganinsa kowace ta sha jinin jikinta, suna masa sannu da zuwa, be amsa ba daman be zama lallai ya amsa gaisuwarsu ba, idan ya daga musu kai ma sun yi sa'a, kuma a dolensu gobe su sake gaisheshi idan kuwa yayi umarni jiki na rawa ake yi domin sun san waye shi tun kamin ya dawo kasar, a yanzu kuma da yake zaune a gidan sun fahimci shi ba kanwar lasa ba ne.

Jawad ya kalli yayarsu Hannatu ya ce.

"Miyasa ba a kaiwa Kaka abun karyawa ba har yanzu?"

Hannatu ta kalli Husaina.

"Husaina ba a kai abinci ba?"

"Eh na manta"

Ta sauka kan kujera ta nufi kitchen da sauri. Hajiya Aisha ta fito ta kofar baya ta shigo falon tana fadin.

"Ba ku kai mata abun karyawa ba? Ai ban sani ba, a tashi maza maza a kai mata, aikin wani lokacin da mun gaji sai kowa ya manta, shiyasa na fadawa Alhaji muna bukatar karin masu aiki a gidan nan"

Ta karaso ta zauna kusa da yaranta fuska na nuna damuwa na rashin kai abinci da ba'ayi ba.

"Ina kwana"

Jawad ya gaisheta ba tare da ya kalleta ba, daman gaisuwa ce kadai abun da ke shiga tsakaninsa da ita sai idan zai tambaye ta abu ko yana bukatar karin bayani.

"Lafiya kalau, Jawad an dawo sannu Alhaji ya wahalar da kai, abun da baka saba ba"

Ta fada tana murmushi. Jawad be sake cewa komai ba ya juya ya fice daga falon ta bishi da wani banzan kallo.

"Turo shi ta yi ya zo yayi fada ita mai jika, toh an ki akai ai tun da kika zabi zama a gidan surukinki sai kin ga shiga uku kuwa, in ban da lalacewa mata daga ta auri ya dauko ki ya rike, yanzu ta mutu ki kama guri ki zauna kamar gidan daki, kuma ki ce zaki mana iko?"

"Kuma fa Wallahi Hajiya idan Kaka tana da kunya ba zata zauna gidan nan ba, tun da yarta ta mutu to miye na zama"

Cewar Hannatu.

"Wai ni za ayi ma bakinciki, bata jidadin yarta ta mutu lokacin da suke gidan suna morar rayuwa ba, shi ne ita ba zata koma kauye ba ko? Toh sai ta mutu a nan ai, baki ga an saka ɗan ya baro kasar waje ya dawo gida ba? Saboda shi ne namiji ko? Ya gaji Alhaji tun da duk mata na haifa babu namiji ko ɗaya kar na cinye arzikin ni kadai, tun da ita yarta yara biyu kawai ta haife, ai bakinciki take da kuce"

Firdausy ta yamutsa fuka.

"Shiyasa ni ai babu ruwana da sha'aninta, ba dan ma dawowa Ya Jawad ba Wallahi ko rahama ta ba zata gani ba"

Hajiya ta ce.

"Sai ku lallaba ta siyasa tun da kuna ganin halin Jawad din ba mutumci ne da shi ba, abu kadan zai doke ku, ni kuma na yi magana ace dan ban haife shi ba, shi bakin hali yayarshi munafurci, ai na fisu iya siyasar mu tafi a haka"

Ta kalli Hassana.

"Ke ta shi ki bi sawun yar'uwarki ki kai masa na sa abincin kamin ya fara bakin halin nasa, ban da rashin kunya mata ta mutu ki zauna bangarenta shekara kusan ashirin sai dai azo a ganki a koma ke ki je"

Hannatu ta tabe baki.

"Har da fa laifin Daddy domin shi na hana ta komawa, ko kwanan baya kamin Ya Jawad ya dawo ai sai da ta ce zata tafi ya hana"

"Shiyasa ni ma na kawo yan'uwana ai ga kanena nan ga kanwata, duk yadda ba aso ni ma sai yan'uwana sun shiga cikin dukiyarsa, kuma kasuwancin zinari da yarda Allah sai Dawood ya koya ya ci arziki sai dai a mutu, Allah be ba ni yaya maza ba amman ya ba ni kanne maza da mata kuma da su za'aci arziki"

Tana maganar tana yatsina fuska, kamin ta mike tsaye ta nufi dayan bangaren na katon falon tana kiran mai aikinta.