G_D - 5
***
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 5️⃣
Be wuce minti biyar da shigowa falon ba, kanwarsa ta shigo rike da tray da ke dauke da kayan karyawa, ta yi sallama ta gaishe da Tsohuwar dake zaune kan kujera ta aje mata abun karyawar a dinning sannan ta juya zata fita.
"Husaina miyasa ba ayi shara ba?"
Ya fada yana kallon falon da ke nuna alamar ba ayi mopping dinsa ba. Husainar ta yi shiru tana kallon falon da ko son shigowa ba sa yi sai dole.
"Ai haka suke indai baka nan babu abun da suke min, duk abun da suke ganinka ne?"
Cewar Kaka tana tabe baki.
"Je ki dauko abu ki gyara gurin nan"
" Tohm"
Ta amsa dan dole ba dan ranta ya so ba, domin ko Hajiya da take kishiyar uwarsa, bata isa ta musa abu ba, sai dai ta kawo shawara cikin hikima balle kuma kanensa, ko kadan Jawad be daukar raini, be bada kofar haka be amince ko kallon raini ayi masa ba balle sa'insa, idan yace abu ya zauna kenan babu mai musawa sai mahaifinsa, yayarsa Hadiza da Hajiya sai dai su sauya masa ra'ayi cikin hikima da wayo ko shawara ba, amman ba ta hanyar tunkararsa kai tsaye ba.
Ta fice da sauri, tana fita tawainiyarta ta shigo dauke da nasa breakfast din, cikin girmama ta gaishe da kakarsa saboda yana tsaye ta isa dinning din ta aje masa abun karyawa sannan ta juya ta fice.
"Shiyasa ni na fi sha'awar komawa kauye cikin dangina, idan ni Allah ya karbi ran tawa yar, ai ina da yan'uwan da za su iya rike ni, ka zauna a gida ana wulakanta kamar zaman dole? Duk lokacin da na yi yunkurin komawa gida sai Hadiza ta hana, masu aiki idan an kawo sai yaran nan sun san yadda suka yi suka koreta, zaman nan baya min dadi sam"
Jawad ya shafa kansa ya murza goshinsa, domin abun da ya fi tsana shi ne surutu a cika shi da yawan magana, sannan ya mike tsaye ya nufi hanyar da bangarensa yake, sai da ya zagaya ta gurin da Stairs yake ya hau ta taka ya isa falon sama, sannan ya shiga dakinsa. Tufafin jikinsa ya fara cirewa yayi wanka ya fito yana ta kamshin expensive soaps hannunsa rike da tawul yana goge kansa.
Moisturizer mai kyau ya bi jikinsa da shi sannan ya nufi closet dinsa ya dauko tufafi marar nauyi ya saka, sannan ya sauko kasa ya nufi dinning, ko da ya zauna Kakarsa ta kusa cinye nata abincin, ya zuba ruwan zafin ya hada tea ya fara sha.
"Ka ga kauye ko?"
Ya daga mata kai yana cin biredi.
"Ka dade baka je ba, ka kamata ka shirya ka tafi bangaren mahaifiyarka ka gaishesu ka sada zumunci, ka san yan'uwanka na can su ma su san ka, tun da idan mu ne yau ba mu ne gobe ba, tsufa muke ta wata rana ma bama raye ku kadai za ku yi zumuncinku"
Nan ma kai ya daga mata.
"Kauye akwai dadi, zaka ga wasu al'adu da rayuwar da ba irin wannan ba"
Da ta yi zancen al'adu da rayuwar kauye, sai yarinyar da ya gani a kauye yar kurma ta fado masa rai, ya lalaba aljihunsa ya ji babu wayarsa, sai ya mika hannu ya dauki wayar Kakarsa ya shiga contact dinta ya nemo number kanwarsa daya ya kira wayar ta yi ringing har ta gama ba a daga ba, sai ya aika da sako da number. 'Ki zo yanzu' be yi minti hudu da tura sakon ba sai gata a falon da saurinta ta shigo da sallama daman idan suka ga sako sun san shi ne, domin Kaka ban da amsa waya da kira babu abun da ta iya da wayar sai kuma kunna fitila, ta nufo dinning din ta tsaya daga gefe.
"Ya Jawad ban san kai ba ne Wallahi"
Ya dago yana mata wani kallo mai kama da harara.
"Idan Kaka ce ba zaki amsa ba kenan?"
Ta yi shiru ta sauke kai kasa kamar zata yi kuka, karamin aikinsa kan wannan abun yace zai doketa. Ya sake daukar wayar Kaka ta rubuta mata sako.
"Shiga dakina ki dauko key akwai abu bayan mota ki kwashe"
Ta karanta sakon da ya shigo wayarta, sannan ta juya ta nufi bangarensa, ya shiga ta dauko keys din ta sauko ta fita, sai gata ta dawo ta shiga kitchen din bangaren ta dauko roba ta fita ta
Kwaso kuli kulin dake bayan motar ta shigo da shi.
"Ga shi Ya Jawad"
Ya kalleta kawai ya dauke kai sannan ya sake aika mata sako, sai da ta aje robar sannan ta iya bude wayar ta karanta sakon.
"A zubar, ki bawa Yusuf keys ya wanke motar"
Ta dauki robar ta juya ta fice.
" Ina ka samu Kuli kuli"
"Kauye"
Ya amsa a takaice sannan ya mike tsaye ya bar dinning din zuwa bangarensa. Wannan karon dakinsa na zane zane ya shiga, ya duba wasu abubuwan da be karasa ba sannan ya dauko sabon takardar ya fara sabon zane, a al'adar tafiye tafiyensa ya kan zana abubuwan mamaki da ya gani idan ya tafi wani gari ko kasa, ya aje saboda tarihi, haka yayi wannan karon ya zana yar kurma da ya gani har guri biyu a inda take tsalle da kuma inda take tsaye a dandali ya zana har da mutanen dandalin.
Kwarare ne gurin haddace abubuwa yana daya daga cikin dalilin da ya bumkasa nasarar, abu ne mai wahala ka fada masa abu ya manta, haka kuma kwakwalwarsa tana haddace duk abun da idonsa suka gani ko da sau daya ne.
A gurinsa, Batula abun mamaki ce domin kurma ce amman da take rayuwa da nishadi kamar bata da nakasa, gashi ta iya rubutu da karatu, sai kuma ganin dandali wannan ma wani abu ne sabo a gurinsa kasancewar be yi rayuwa a kauye ba, ba ma iya kauye ba, a Nigeria ma ba ciki ya girma ba. Cikin kankanen lokaci ya gama zana abubuwan nan biyu, a kasan hoton Batula ya rubuta sunanta, a gurin na dandalin kuma ya rubuta dandali daga kasa, kamin ya dauko wata takardar ya so ma zana gold din da ya gani da kuma yadda ake hakoshi. A lokacin da ya fara jin bachi na ziyartarsa sai ya aje ya tashi cikin natsuwa ua fice daga dakin ya shiga dayan dakin wanda ya kasance bedroom dinsa ya kwanta.
BATULA POV.
Sai da ta gama cika komai na gidan sannan ta dauko kwano aka zuba mata dumame ta zauna tana ci tana hurawa saboda zafi.
"Batula bari hura abinci babu kyau"
Ta dago ta kalli uban rikon nata dake gyaran rawani, sannan ta daga mishi kai alamar tohm. Ta maida kanta ta cigaba da cin abincinta.
"Malam fita za'ayi?"
Altine ta tambaya tana kulla gidar da bata samu kullawa a jiya ba sai yau.
"Eh yamma zan je yau sai dare zan dawo"
"Tohm Allah ya tsare"
Duk matan suka fada ban da Umma Hinda uwar masifa ita har yanzu bata sauka ba fushi take da Mai Gari.
"Batula, sai na dawo ko?"
Ta daga masa hannu, yaran suka yi masa Allah ya tsare sannan ya fice. Batula na gama cin abinci ta shiga ta dauki kuli kuli ta shiga gari talla, bata dawo ba sai Yamma shi ma saboda ta siyar ne. Tana aje bahon tallar ta yi alwala ta yi sallah la'asar azahar tun a gurin talla ta yi sallah ta. Sannan ta fice gidan zuwa gidansu kawarta Basira, tana shiga gidan ta samu Kande a zaune gidansu Basira ana mata tsifa.
Batula ta gaishe da kowa cikin kurmancinta sannan ta zauna kusa da Kande dake kasa, Basira kuma kan kujerar tsakar gida tana mata tsifa.
"Yanzu nake cewa zan aika idi ya kira ki, ashe kina tafe yar halak"
Basira ta fada sai Batula ta yi murmushi ta kama gefe daya na tsiron Kande tana tsefe mata da hannu.
"Gobe lalle za mu yi, ki karbi kudi gurin Umma ko Baba, tun da safe za mu je gidansu Ramatu ta yi mana kunshi da lalle, kin ga an kusa komawa makaranta hutu ya kare"
Batula ta dan yi shiru tana tunanin ta inda kudin zai fito, ba lallai Umma Hindu ta bata kudin kunshinba da ma ace Basira ta fada mata ne kamin yau, mutum daya ta san zata tunkara ya bata kudin babu jayayya shi kuma bata son zuwa gurinsa, gashi ba su saba yin abu dabam dabam ba sai a tare.
A kasa Batula ta rubuta musu.
"Mu bar shi har wani sati"
"Wani sati yayi nisa, gaskiya idan ba zaki yi yanzu ba ki bari mu dai mu yi"
Kande ta fada, sai Basira ta ce
"Ko ganin kike Umma ba zata baki kudi ba?"
Batula ta daga kai.
"Ki tambaya idan bata baki kudin ba sai mu bari sai wani satin ko da an koma makaranta ne ai za mu iya yi"
"Ko kuma mu yi namu ita daga baya sai ta yi nata idan Habibu zai dawo"
"Aa ba mu taba yin komai ba tare ba, idan dai ba a bata kudin ba sai mu hakura sai ta samu, ko kuma mu idan muka samu sai mu hada mu siya mata lalle da kudin biyan mai lalle"
Kande ta kebe baki.
"Tab ni yanzu ina na ga kudin bawa wani ni ma ta kaina nake yi fa, ita ma har da laifinta kullum babu babu sai kin tsaya an baki daga gida"
Basira ta zunguri kan Kande.
"To ya zata yi kande kamar baki san halin Umma Hindu da masifa ba, kuma saurayinta baya nan balle ta ce ya bata, mai tausaya mata a gidan fa Babba ne kawai"
"Ba tana zuwa talla ba, Wallahi ta dinga mata sata, ta rika sace mata kudi, tana yin nata, a kauyen nan fa duk ka dawo daga talla sai an baka kasonka, kina ganin wasu da shi suke siyan wani kayan auren ma, amman ita Umma bata bata komai, jiya nan ta gama fada min wani ya bata kudin tulu har dubu biyar wai gaba daya ta kaiwa Umma kuma bata bata ko sisi ba sai ma duka da ya biyo baya, ke ki rika cire kudi kina ajewa"
Batula ta girgiza kai alamar aa, saboda bata saba da sata ba, ita ko kudi aka bata ma bata saba ragewa ba balle har ta dauki na wani.
"Karki yi Batula, ki kyale Kande ki tambaya dai idan an baki sai mu yi, ki daina biyewa halin wannan marar kirki"
Basira ta fada tana kaiwa Kande rankwashi akai, sai duk suka yi dariya. Sai Magariba suka fito gidan Basira ta yi musu rakiya suna tafe suna hira Batula sai dai ta wara ido ko ta girgiza kai, gurin dariya kuma ta yi murmushi kusan haka hirarta take da kowa saboda bata magana, sai idan ta ji zata iya ne take alama da kurmancin ta fadi abu ko ta rubuta a kasa ko jikin takardar.
"Kamar wasa wai Batula zaki riga mu aure?"
Kande ta fada sai Batula ta yi murmushi tana jindadi, ba jindadin zata yi aure ta bar kawayenta ba sai dan ganin ita tana da nakasa kuma bata yawo ta talkami amman a haka ta samu mai sonta su ba su samu ba.
"Ba mamaki ma ki riga mu, ai wata rana irinku sun fi saurin yin aure karaf daya miji yake zuwa sai aure"
Batula ta nuna Basira dake maganar alamar ke fa.
"Ni ai na fada muku karatu ne a gabana, ni ina son idan mun gama wannan makarantar mu tafi ta gaba karatun lafiya nake son yi"
Batula ta kara dubanta cike da burgewa, daman tana yawan fada musu ita karatu take so tana ganin sha'awa yadda ma'aikatan lafiyar kauyen suke abubuwansu, ba mamaki ita kam kudurinta zai iya cika iyayenta za su tsaya mata, amman ita ko tace zata yi karatu Umma ba zata bari ba domin ance karatun akwai tsada sai an kashe kudi da yawa. Da suka kawo marabar hanya suka rabu Batula ta nufo gida Kande ma ta kama hanyar gidansu Basira kuma ta juya ta koma gida.
Batula gidan da sake saken yadda zata roki Umma Hindu kudin kumshin da kitso da ta san ba lallai ta bata ba, can wata zuciyarta ta zuciyar ta raya mata kar ma ta tambaye ta ta tafi kawai ta tambayi Baba, ta san zai bata ko nawa tace ba zai musa ba har ma da kari, matsalarsa daya zai ce zai taba jikinta. Da wannan tunanin ta yi sallah isha'i ta yi karatunta cikin rai domin babu sautin furuci. Bayan ta gama ta fito waje ta zauna kan tabarmar kaba, cikin hasken farin wata, yau kam babu ruwanta da zuwa dandali saboda ta siyar da kulinta da rana da dai ace ta yi kwantansa ne shi zai sakata tafiya dandali ko zata kara ciniki.
Tana zaune har Malam Salisu ya shigo gidan tare da babur dinsa ya aje a inda ya saba ajewa aka masa sannu da zuwa ya amsa kannana yaran da suke nan suna ta gaisheshi yana amsawa har ya haska Batula da fitilarsa ta dago masa hannu alamar sannu da zuwa.
"Yauwa Batula baki tafi dandali ba?"
"Daman ai kwantai ke sakata tafiya dandali tun da dai ita kam da mijin da zata aura, yau kuma ba ayi kwantan ba"
Cewar Salamatu tana kore sauro da dankwalin kanta. Malam Salisu yayi murmushi mai sauti sannan ya nufi dakinsa ya shiga, Kasancewar girkin salamatun ne sai ta tashi ta daura dankwalin ta nufi dakinta ta dauko abincin Malam ta nufi dakinsa tana ta kaurin wuta, domin ba a saba wanka bayan gama girki da itace ko kara ba, duk haka suke Altine ce kawai mai kokarin gyarawa kasancewar ta fisu kamantawa a tsabta.
"Batula Batula"
Malam Salisu ya kwala mata kira bayan gama cin abinci, daman ita kadaice yarinyar da yake ragawa abinci idan ya ci ya rage, ko yayansa da suke kanana baya rage musu sai ita. Batula ta tashi da sauri ta shiga dakin, sai ta same shi zaune yana tsantsagar hakori. A kasa ta zauna sai ya kai hannunsa ya kama hannunta ta bata tsokar nama biyu, yayi mata alama da ta cinye, sai ta kai baki da sauri ta mike tsaye sai ya rikota ya nuna mata kwanonin da ya gama cin abincin ta dauki kwanonin da ragowar abincin ta fito waje ta dauko wani kwanon ta juye sannan ta nufi dakin Salamatu ta kai mata kayan da Malam ya ci abincin, daman tun da ta kai masa abinci ta fito ta bar masa dakin.
Har zata zauna ta fara cin abinci sai kuma ta nufi dakin na Malam Salisu ta buga kofa ta shiga, tsaye ta fara yi alamar ta zo da bukata, sai ya tashi zaune yana murmushi ya dauki fitilarsa ya haskata.
"Ya aka yi? Me mike so Batula?"
Ta nuna masa kafarta ta masa alamar lalle ta nuna masa kanta ta amsa alamar kitso sannan ta masa alamar kudi.
"Gyaran ya tashi? Dadi da ke akwai son kwalliya,a baki kudi ki yi kumshi ko?"
Ta daga kai, sai ya yi mata alama da ta matso ta masa ya rage murya ya rada mata.
" Tafi dakin baki ki jira ni zan zo na baki kudin"
Ta bata fuska ta girgiza masa kai.
"Ke kina son in kyautata miki amman ke baki son kyautata min Batula? Idan kina min haka zan daina miki komai, dukan da nake tare miki ma sai na daina, makaranta ma sai na ce babu ruwana na cireki, yanzu da na siyo nama ko matana da yayana ba bawa ba amman ke na baki, idan baki son kudin shikenan ni ma sai na bata da ke, daga yau ni ma babu ruwana da ke"
Har ta mike tsaye ta juya sai kuma ta juyo cikin rashin jindadi ta tsaya gabansa.
"Ki tafi can ki zauna ki jirani"
Ta daga mishi kai, sannan ta juya ta fice kamar zata yi kuka.