GUMBAR DUTSE

G_D - 8

by @khadeejacandy

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 8️⃣

Tun a ranar da Batula ta yi zancen damuwarta da kawayenta, sai ta samu sassauci a zuciyarta, daman ta dade tana son labartawa wani damuwarta amman babu hali.

Bayan wannan kuma sai ta saka ma kanta wata sabuwar doka, ta kange kanta daga duk wani abun da zai janyo kusanci tsakaninta da Malam Salisu, kai masa abinci ne a gona ne kawai ya zame mata dole, saboda bata isa ta tacewa Umma Hindu ba zata ba, sai ta yi wayo idan zata je sai ta ja daya daga cikin yaran gidan kanana, idan haka be samu ba sai ta biya ta gurin Basira ko Kande su karata idan suna kusa..

Idan ya shigo gidan kuma ya bukaci ta zo sai ta ki, ta koma cikin yaransa ta kwanta kamar yadda Basira ta bata shawara, haka kuma ta daina zuwa masa da bukata balle shi ma yace zai bukaci wani abu daga gareta. Hankalinta be kara kanwatawa ba, sai da suka koma makaranta, da zarar safiya ta waye zata dauki tulu ta nufi korama kamin haske ya gama fitowa ta cika kayan Umma Hindu da ruwa, idan ta karya ta dauki jakarta ta saka uniform ta wuce makaranta, da rana kuma idan sun dawo za ta fita talla sai yamma zata dawo, wani lokacin idan ta ji zata iya ta tafi dandali idan ta gaji kuma ta kwanta da wuri.

............

Can cikin bachi ta ji ana kiranta ana bubbugata da karfi.

"Ke Batula... Batula ki tashi Baba na kiranki"

Ta bude ido ta zabura da sauri.

"Baba na kiranki yana waje"

Yar wajen Baba Altine ta fada mata tana kora sauro da dankalinta. Har ta yi kamar ta koma ta kwanta, na dama saboda kowa yana jin lokacin da aka ce Malam Salisu yana kiranta, bata isa ta ki zuwa ba, cikin rashin kuzari da bacin rai hadi da na fuska ta mike tsaye ta dauki dankalinta ta daura tana turo baki gaba ta nufi kofar gidan kamar zata yi kuka.

"Tohm Batula ke ma kin fara abun nan na rashin kunya da sauran yan'uwanki suke yi? Ke da yan'uwanki suke yabo? Kin ga yadda ta fita kamar tace ba zata ba?"

Cewar Salamatu tana kebe baki gafe. Sai Umma Hindu ta karba mata.

"Uhmm, ni ai idan ina hukuntata a gidan nan laifina kuke gani, amman wacan ragaggiyar da kuke gani bata jin magana sam, ni kadai na san bakincikin da take kunsa min"

"Ah lallai yau na gani, kin ga yadda take ta wani bankara saboda an tasheta tana bachi, wato girma ne tana yi kawaye na hure mata kunne Allah ya kyauta"

"Ameen, yau sun bar mana nepa"

Umma Hindu ta fada sannan ta kai kwance tana kallon guluf din dake haske tsakar gidan. Batula na fita waje ta hango Malam Salisu zaune kan tabarma tare da bako sai ta dan daki ranta, ta san ba zai fara mata wani abu a gaban mutane ba. Sai da ta kusa isa sannan ta fahimce ba kowa ba ne duke a gaban Mai Garin sai Masoyinta Musa, mamaki ya cikata yaushe ya zo be sanar mata ba, yawancin idan zai zo ya kan kira wayar gidansu a kawo mata ko kuma ya kira ta Mai Garin a bata ko a sanar mata. Farinciki zuwansa ya lullubeta har ta manta da babu talkami a kafarta bayan kuma ta san yadda yake mata fadan saka talkami a ko wane lokaci domin baya kaunar ganin sahibar tashi babu talkami ko kwaliyya.

   Cikin jin kunya ta karasa gurin, ta risina gefen tabarma tana satar kallon Musa da ke labarin Jos da Mai Gari.

"Garin fa ance suna da sanyi, ga yayan itatuwa kala kala"

"Gaskiya akwai kayan lambu sosai"

"Maa Shaa Allahu, to sannu fa da kokari"

Ya fada cike da far'a sannan ya kalli Batula

"Batula.. ga angon ya zo mana babu sanarwa, an iso cikin dare"

Batula ta sauke kanta kasa gaba daya tana dan murmushi. Shi ma murmushin yake

"Tafiyar ce kamar zan yi kamar ba zan yi ba, shiyasa ban fada ba, kuma ba dadewa zan yi ba daman na zo ganin filin da aka siya min ne can yamma da gari"

Malam Salisu ya gyara sama yana washe hakora

"Maa Shaa Allahu, an sake siyen wani filin kuma Musa? Tohm Allah yasa albarka"

Ya amsa da Ameen sun dan taba hira da Mai Garin, sannan Musa ya masa sallama ya mike tsaye ya nufi gurin da suka saba tsayawa ya tsaya.

"Tashi ki tafi ku gaisa"

Batula ta mike tsaye ta cike da kunya ta nufi inda yake tsaye, Malam Salisu ya dan juya musu baya kadan. Suna hada ido kunya ta rufe ta ta saka hannayenta ta rufe fuska.

"Batula baki jin magana ko? Kin ki koyi yawo da talkami"

Ta bude fuskar tana tattara zanenta gaba, ta boye kafafuwan.

"Ai na gani, haka kika fito babu talkami kin fara bachi ne"

Ta daga mishi kai. Sai kuma ta yi masa alama da waya ta kara a kunnenta, domin haka hirarsu take sai da ta yi masa n kurame shi kuma ya furta mata, saboda be yi boko ba be iya karatu ba ita kuma bata iya magana.

"Eh ban kira ba saboda ban dauka zan zo yanzu ba, fatan dai na same ku lafiya"

Ta daga kai tana murmushi farinciki. Ya daga kai kadan ya kalli saitin da Malam Salisu yake zaune ya kalli Batula.

"Ya makaranta kina nan kina zuwa?"

Ta daga mishi kai, sai ya kura mata ido har ta soma tsarguwa, domin ba kallo ne irin na soyayya ba, be ma saba yi mata irin wannan kallon ba. Can kuma sai ya ce.

"Ina Umma tana lafiya?"

Ta daga mishi kai, tana karantar yanayinsa.

"Na zo miki da tsaraba amman ban bude komai ba sai gobe zan kawo miki, kayan marmari kawai na zo wa su Baba da su"

Ta yi murmushi ba tare da damuwa ba, duk kuwa da ta san a duk lokacin da yayi tafiya ya kan kawo mata tsarabanta dabam ne. Ta nuna hannunta ta nuna shi ta yi alamar tambaya, karfe nawa ya zo nan.

"Da magariba na iso"

Ta rausayar da kai. Sun dan dauki lokaci a haka kamin ya ce.

"Ki shiga ciki dare na yi, sai gobe idan na dawo"

Ta kalleshi sai kuma ta yi murmushi ta yi masa baibai ta juya tana tafiya, tsaye yayi a gurin yana kallonta tana yi tana dan waigensa, shi kuma yana tsaye gurin har ta isa gurin Mai Gari ta dauki ledodin da suke nan ta shiga cikin gidan sannan Musa yayi tafiyarsa.

Ta san halin uwarta da kuma kishiyoyinta dan haka ta aje sakon bakin kofar Malam Salisu har sai da ya shigo, ya bada umarnin Larai dake da girki ta raba ta bawa kowa da yaransa shi ma aka ba shi dabam.

Bachi ya dade be dauki Batula ba, saboda farincikin dawowar Musa, har mafarkinsa sai da ta yi,  washe gari ta tashi cike da kuzari da farinciki, tana gama cikon ruwa ta dora dumame suka karya, bata saba wanka da safe ba amman saboda shi ta yi wankan safe ta shafa mai har da su hoda ta shafa kwalli a ido, ta saka uniform dinta ta dauki jakar da littafanta suke ta fito da sauri domin kowa ya tafi ya barta saboda ta tsaya gyara. 

Tana fitowa kofar gidan ta samu Malam Salisu yana gaisawa da wani, da alama bako ne daman gidan na su kullum cike yake da baki kala kala, ta fara gaishe da Malam Salisu da ta dafa kafadarta kadan ya dauke hannunsa, sannan ta gaishe da wanda suke tsaye da alamunta na kurmanci.

"Yauwa sannu ko makaranta zaki yi"

"Ai bata magana, haka take shekara da shekaru, shiyasa na saka ta makaranta saboda ta samu ta iya karatu abun ya dan rage mata, tun da bata da uwa ba uba, marainiya ce ni nake dauke da komai nata"

"Allah sarki, abun tausayi Allah ya saka maka da alheri"

Mutunen ya fada cike da tausayi yana kallon Batula wanda ta fara tafiya.

"Baba ko zata iya nuna min hanyar kamin ta wuce"

"Aa ranka ya dade ni na kamata na kai ka da kaina bari na dauko hulla"

"Karka da mu, zata iya nuna min kai idan ka kimtse sai ka taho"

Mai Gari ya amsa da sauri.

"Kwatancen nata sai a hankali tun da ba baki, anya zaka gane?"

"Zan gane"

"Ai bari ma kar ta wuce sai ta kaika gurin tun da hanyar makarantar ne, Batula"

Malam Salisu ya kirata sai ta juyo ta dawo.

"Ki nuna masa hanyar Jirwai gurin su Malam Yusufa, sai ya aje ki, ki shige makaranta, yanzu ina kimtsawa zan zo na tarar da kai"

Mutunen ya mikawa Mai Gari hannu daya, Mai Gari ya saka hannu biyu cike da ladabi ya gaisa da shi.

"Na fa gode Allah ya saka da alheri"

"Bismillah"

Ya nunawa Batula motarsa, sai ta wuce gaba yana bayanta har suka isa, Mai Gari kuma yana bayan shi, kamin Mutumen ya kai hannunsa Mai Gari ya riga shi ya bude masa gidan baya.

"Aa ai yau ban zo da direba ba, na zo da kaina ne, tun da za a shiga cikin abokan da aka taso tare be kamata ka nuna wani abu ba"

"Haka haka ne... Ai kai babu ruwanka da rayuwar karya, komai a sannu kake ana son mutum haka"

Yayi murmushi ya bude Driver seat ya shiga, sannan ya kalli Batula.

"Baba fada mata ta zagaya dayan gefen ta shiga gaba"

"Ai tana ji mayarwa ne kawai bata iyawa, amman duk abun da zaka fada tana ji"

"Oh Maa Shaa Allahu"

Ya kirga kudin da zai kai 50k ya mikawa Mai Garin, a take Mai Gari ya zama karamin mutum, kamar zai kai kasa tsabar murna da farinciki.

"Na gode sosai, wannan hidima haka, gashi za a hadu da tsohon abokaina can ma na san za'ayi hidima"

"Tohm ai haka rayuwar ta gada, an dade ba a hadu ba, abokaine tun primary school, taron tsofin abokai ne"

"Allah ya tsare Allah ya kai lafiya"

"Ameen"

Ya rufe motar sannan ya kalli Batula da ta natsu sosai domin bata taba shiga babbar mota mai tsada ba a rayuwarta irin wannan, ganin bata rufe kofar da kyau ba ya ce.

"Batula sunanki ko? Sai kin kara bude kofar kin rufe da karfi"

Gurin budewar ya gagareta domin ba irin motar data saba bace, sai ya mika jikinsa da hannunsa ya kai ya bude kofar ya rufe.

"Tohm haka ake, Batula mai sunan Mamana"

Ta yi murmushi ta daga mishi kai, sai ya ja motar yayi reverse suka kama hanya. Sai da suka wuce Mai Garin ya shigo gidan baki har kunne daman irin wannan bakin yake so masu badawa.

"Masu kudin birni babu ruwansu da rayuwar karya, mutum kamar Alhaji Raheem Turaki, ama, ya shigo garin nan babu wani burga babu wani alfahari kamar ba mai kudi ba"

Salamatu dake lekon motar ta ce.

"Ai wasu haka suke, idan ka ga dagawa sai dan talaka ko wanda ya tsinci arziki, amman dan gado babu ruwansu da nuna isa"

"Kalli dai ki gani, Matashi da shi be wuce 37 ba amman Allah ya bude masa ta ko'ina arziki yake samu, kusan manyan masu kudin birni da yan siyasa abokan huldarsa ne, kai baka ce ma a garin nan ya tashi ba, arziki kashi, Allah ka yi ma Yayanmu haka"

"Ameen amman dai Malam be kyautu ka tura Batula ita kadai ba"

Umma Hindu ta ja tsaki.

"Ammn dai kin san komai lalacewa dan zaki yafi karfin garwurtaccen bunsuru, ko a hauka yake wacan mutumen ba zai yi komai da nakasasshiya ba"

"Ai ba aure ko Lalata ba, kin san fa wasu masu kudin arzikinsu ba na Allah ba ne kar ya wuce da kanta"

"Ai da shikenan mun huta ma"

Ta sake fada cike da nuna halin ko'in kula.

"Alhaji Turaki, ai sananne mutum ne ba zai yi haka ba, ai na san shi kawai dai ya kwana biyu be zo nan ba ne"

Haka dai suka yi ta tattaunawa Mal Salisu ya so ma ba su labarin iyayensa. Tun da suka kama hanya Batula take ta komai na motar daga kan sitiyarin har gurin da sanyin ac ke fita babu abun da bata lura da shi ba.

"Aji nawa kike a makaranta?"

Ta daga yatsanta ɗaya

"Aji biyu? Primary 1"

Ta girgiza kai, alamar Aa tana murmushi, shi ma dai ya fada ne kawai amman ina zai kalli yarinya kamar ita yace aji biyu sai kace mai koyon yaki da jahilci.

"Jss 1"

Ta girgiza kai.

"Oh SSS 1"

Ta daga kai.

"Maa Shaa Allah, ki ce kin kusa gamawa, sai aure"

Ta rufe ido tana dariya.

"Na jidadin ganin kina karatu abun da muke ta kokarin ganin an inganta kenan a arewa, na yaba da mai rikonki gaskiya ya kyauta"

Ya kalleta kadan yana tukin a hankali.

"Yanzu zaki iya rubuta komai da hausa ko turanci? Kuma zaki iya karantawa?"

Ta daga kai.

"Tohm rubuta min na gani"

Ta daga jakarta da babu zip ta ciro littafi da biro ta tambaye shi da hannu me zata rubuta.

"Rubuta Raheem Turaki"

A kokarinta na burge shi ta rubuta ta nuna masa.

"Alhaji Raheem Turaki"

Ya karanta sai yayi murmushi.

"Waya ce ki saka Alhaji? Ke kika kai ni maka?"

Ta girgiza kai.

"Masu kudi Alhaji ake ce musu shiyasa na rubuta"

Ta rubuta masa, ya karanta.

"Tohhhhhh, ni mai kudin ne kenan? Interesting, ke kika ba ni kudin? Ko kuma Baba Mai Gari ya fada miki ina da kudi ne? Fada min gaskiya"

Ta yi murmushin da ya bayyana hakoranta.

"Aa ni ban taba ganinka ba, be taba ba mu labari ba, amman yanzu ai ka bawa Baba kudi mai yawa, kuma kana da babbar mota"

Ya bude ido.

"Duk wani Mai Babbar mota kenan Alhaji ne? Ai ban sani ba, amman kin ga kin kara min ilimi yanzu da na mai babban mota na san mai kudi ne"

As usual ta yi murmushi tana nuna masa kwanar da za'a bi, ya shiga kwanar ya cigaba da tukin, can kuma sai ta masa alama da ya tsaya da hannu. Sai ya faka gefe ta nuna masa kofa, sai ya kai hannu ya bude mata kofar. Ta bude littafi ta rubuta masa idan ya mike zai sake kwana hannu dama sai kasuwa a nan zai tambaya ina shagon Malam Yusufa akwai shaguna da Katon shago mai shaguna da yawa, (Plaza) nan ne gurin. Ta ba shi kadardar ya duba ya karanta.

"To ke a hanya zan barki?"

Ta karbi littafi ta sake rubuta masa.

"Ni idan na shiga kwanar nan zan isa makaranta"

Ta saka kafafuwanta waje ta fita.

"Ina talkaminki?"

Ya tambaya domin ya lura da kafarta a lokacin da zata fita motar. Ta girgiza masa kai.

"Ba ki da talkami?"

Ba zata iya tsayawa dagon bayanin cewar bata saka talkami ba dan haka ta daga masa kai. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya mika mata, nan ma ta girgiza masa kai alamar ba zata karba ba.

"Karbi mana, ba ni na baki ba, idan kin je sai ki saye talkami da shi"

Ta karba da hannu biyu tana risina, ta yi masa alamar godiya, ta yi masa bye bye tana murmushi sannan ta rufe masa motar da mugun karfi, ya tsaya a gurin har sai da ta shiga kwanar sannan ta kama hanyar data rubuta masa, mutanen da suka ga saukowa sai kallonta ake wasu na mata kallon ta fito a babbar mota, wasu kuma na mata kallon zargi.

JAWAD POV.

Anty Sa'adatu, ta gyara zamanta wayarta a kunne.

"Zan iya sanin me da me kuke da shi?"

Daga daya bangaren Hajiya Aisha ta amsa.

"Gaskiya muna da kaya masu kyau, komai kike bukata muna da shi, kuma ba wai yabon kai ba, turarukanmu suna da kamshi sosai"

"Eh ni ma wata kawata ta fada min ku, tace kayanku suna da dadi sosai ba algushu, yanzu dai zan iya sanin me da me kuke siyarwa"

"A bangaren kamshi muna da Turaren Humra

Khalta humra

Dufr humra

Pink humra

Oil perfumes

Royalty in a bottle

Liquid gold

Emperor

Turarenwuta

Halut

Hawee

Farce dufr

Sandal original

Sandal flakes

Turaren kabbasa spray da kabbasa mix set na Kaya

Turaren carpet and curtains linen"

"Okay Maa Shaa Allahu, ba ku da package ne ina son na siyawa kaina kuma ina son na siyawa wata cousin dita da zata yi aure"

Hajiya Aisha ta yi dariya.

"Hajiya aiko mu muke da packages, muna da

Bridal package, mai suna Jameela’s package gold package, sai kuma Isha’s package shine silver package, da kuma Maryams package shine bronze package, kuma duk wanda kika gwada a ciki za ki jidadin fiye da tunaninki"

Anty Sa'adatu, ta kalli Jawad dake tsaye rike da karamin plate din fruit tana masawa Hajiya Aisha.

"Okay wannan line na ki mai *** kina Whatsapp da shi"

"Eh ina Whatsapp da shi Hajiya"

"To zan miki magana ta Whatsapp, sai ki aiko min da Price din kowane da account Details, zan fara siya na ji yadda naki kayan yake, domin dai na ji Kawata Khadeeja Candy tana ta kodaki, ni kuma duk abin da ta yarda da shi na yarda da shi na san In Shaa Allahu ba za a samu matsala ba"

"Ita ta gwada ta jidadi ne shiyasa kika ga haka, In Shaa Allah zaki jidadin kayanmu Hajiya, ai ba mu da na biyu"

"Tohm na gode, sai mun yi magana"

"Tohm a huta Lafiya"

Hajiya Aisha ta fada cike da mutuntawa duk da yake bata taba ganin Anty Sa'adatu, amman halinta na karamci ya hana ta kaskantar da kowa. Anty Sa'adatu ta aje wayar a hannu kujera tana fadin.

"Na manta ance min har da Interior take siyarwa, amman bari na yi searching dinta Instagram ance tana using Jisma Interior Decor"

Jawad ya kalleta yana cin grape irin kallon nan na wacece.

"Wata mai siyar da kaya ce, humra da Interior ance kayanta na da kyau sosai"

Ya dauke kai, daman magana bata dame shi ba, sai na kusa da shi yayi magana shirin be yi ko daya ba.

"Ba zaka daina cin abin hannun matar nan ba ko Jawad? Daga bangaren Hajja Yelwa ka fito fa ka shigo da fruit, idan baka yi hankali da matar nan ba, Wallahi sai ta mallake ka domin na lura burinta kenan ace kowa da komai yana karkashin ikonta, ko da yake ta samu sa'arka ai tun da gashi nan abincinta kake ci, duk abun da ake fada akan matar nan baka gani"

Jawad yayi murmushi yana cigaba da cin fruit dinsa hankali kwance kamar ba da shi Anty Sa'adatu take ba. Wani dogon tsaki taja na takaici.

"Duk duniya dai baka da mai fada maka gaskiya sai ni, ni ce yayarka uwa daya uba daya ko ka so ko ka ƙi dole na fada maka gaskiya, domin na lura duk abun da ake kai ba gani kake ba, sai wani jiji da kai na tsiya"

Wannan karon sai da ya kalleta sannan yayi murmushi, daman ya san halin yayarsa tun sunana kanana mafadaciya ce, shi kuma sarkin jinkai ne, be kuma fasa cin fruit dinsa ba sai da ya cinye tasss.

"Uhm, kwanan baya ai Ariz ya biya gidana yake fada min wai Momy tana nan tana nema muku mata"

Sai a lokacin ya yi magana.

"Ita ma Momy mallake ni zata yi?"

"Ba zata mallake ka ba, amman ai zata iya hada baki da Hajja Yelwa a sama maka wata matar ta bangarensu ayi ta munakisa, ni ba yarda zan yi ka yi aure ta bangaren Hajja Yelwa ko Momy ba, sai dai ka nemawa kanka mata ko kuma ni na nema maka"

Ya maida kansa kasa yana murmushi. Gwaggo ta cire hijab din da ta sallame Sallah ta kalli Anty Sa'adatu.

"Sa'adatu ki daina kiran kishiyar uwarki da sunanta, Babanku ma yayi magana yayi magana har ya gaji, yayi kawo min kara har ya hakura, haba matar uba ai uwa ce, ni kaina ba dadinta nake ji ba, saboda Hajja Yelwa bata da mutunci, amman dai ke a matsayinki na ya ki sauke hakkinki mana"

"Wallahi har kasa ya nade ba zan taba son Hajja Yelwa ba, ban mata da yadda ta cutar da mu ta cutar da uwarmu ba, yanzu kuma take kokarin ganin sai ta mallakemu"

"Babu wanda yace ki so ta, amman hakkinta ki bata biyayya ki mata tun da ta riga ta auri ubanku kuma har da zuri'a, ki kirata yadda kowa yake kiranta mana Hajiya, ba dole sai kin ce Hajja Yelwa ba"

Ta tabe baki, Jawad ya mike tsaye rike da plate din ya fice daga falon, a ka'ida idan ya ci abu inda ya ci nan yake barin plate sai dai a dauke amman yau saboda ya bawa yayarsa haushi ya fice da plate din zai kaiwa Hajja Yelwa, daman duk ka nuna masa baka son abu shi kuma sai aikata saboda haushi ya kasheka.

Ya isa bangare ya tura kofar falon ya shiga ya isa dinning ya aje plate din ya juyo.

"My Son, Ayla sata soya wainar fulawa ko kana so ta soya da kai?"

Hajja Yelwa ta tambaya tana kallonsa, ba tare da ya juyo ba ya girgiza kai alamar aa ya fice. Hassana ta ce

"Hajja Anty Sa'adatu ta zo fa, dazun da naje kai abincin rana na ga shigowar direbanta, yana ta sauke kaya"

Hajja Yelwa ta tabe baki.

"Kin san ai ita kishiya ce, ba zata shigo nan ba sai zata tafi, duk ita ta dauko bakin halin uwarta, kuma takama take da kudi ita ga yar kasuwa kuma ga ta matar Makama"

Ayla ta tabe baki.

"Adda Yelwa, ke ma kike kula wannan, kudin banza tun da ba nemansu muke a gurinta ba"

"Shi ne kawai take takama da shi, kuma ta samu sa'a kasuwancin nata ya karbu shiyasa, amman sannu a hankali sai ta zama abar tausayi Wallahi, ai ramen kura sai yayanta kuma duk wanda yayi min kan kara sai na masa na itatuwa, yadda uwarta ta gaji ta bar ni haka ita ma zata gaji da bar ni"

"Allah ya nuna mana wannan ranar, Wallahi haushi take ba ni kamar na kasheta, ita da wannan shegiyar Kakar ta su, ta zo ta yi zaune a gida kamar gadonta"

Hajja Yelwa ta kalli kanwarta.

"Ayla wani abun ai ba laifinta ba ne, laifin Alhaji ne shi ya kamata ya koreta ya maida ita can kauye amman ya ki, mugun asirin da shegiyar matarsa ta masa Habiba be sake shi ba har yanzu, asirin ne yake ta aiki a kansa shiyasa na rasa gane kan mijina, kina ganin har yanzu da ta mutu sonta yake, kuma da ya tashi magana zai fara uwargina na, ko mamansu ba haka take ba, Shekara nawa da mutuwar mata yaki ya manta, har yanzu yayanta ne suke cin moriyarsa a gida nawa yayan ya ajesu gefe kamar su ba haihuwarsu yayi ba, ko kuma ni dan Allah be ba ni namiji ba"

"Wallah kuwa Adda Yelwa, yanzu kam ai kin ci gida, ke ce uwargida ko anki ko an so"

"Shiyasa ai na ke ta kokarin ganin ya saka Dawood a cikin al'amurran kasuwancinsa, ya kamata a ce mun san komai shi ma ya samu nasa, kuma mu san alkaluman dukiyarsa, next of a king, ma fa Jawad yake sakawa daga Jawad sai Sa'adatu yarana be taba saka kowa ba, filin da ta gina Plaza yanzu take kasuwanci ai nashi ne, haka kawai rana daya ya tara mutane wai wani filinsa na unguwa kaza ya bawa Sa'adatu, ni yarana mota wannan sai na kai na kawo yake siya musu, ita kadai ce ƴa, kara ma Jawad ace namiji ne, amman ita ban da tsabar kiyayya da kishi babu abun da take da ni"

Cike da bacin rai da bakinciki take maganar har muryarta na canjawa kamar zata yi kuka.

---------------------------------

Ma su karatu me kuke hangowa? Akwai fa gwarama a litattafin nan, ba kadan ba.