G_D - 9
***
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Zaku iya Karanta GUMBAR DUTSE a Wattpad & Arewabooks @KhadeejaCandy
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 9️⃣
Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢
Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, Ramadan din nan ma ta shirya muku Ramadan promo karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***
......….....
Sai da ta kusa isa bakin kofar makarantarsu da babu gate ta tuna ta bar littafinta hannun mutumen da take ma kwatancen hanya, da sauri ta juya ta kama hanya tana gudu tana kalle kalle, daman ta san ba lallai ta same shi a inda ta bar shi ba, ko da kuwa a kafa yake tafiya balle yana da mota, sai dai sanin inda zai tafi ya taimakata sosai wajen takawa da kafa ta isa yar kasuwa ta ratsa mutane tana dubawa har ta hango inda ake mutane suke da yawa, gurin wata babbar plaza.
Manya da kananan motocin suke tana dubawa har ta yi arba da motarsa, karasa ta yi gurin ta tsaya ta kara tantancewa da gaske motarsa dince sannan ta nufi gurin da mutanen suke tana dan lekawa, ta inda abun ya zo mata da sauki akwai maza da mata a gurin, ta yi ta ganin wadanda ta sani amman hankalinta yana gurin bakon mutumen da ya tafi mata da littafi. Hayaniyar ya hanata samun isa gurinsa domin yana zagaye da mutane sosai, gata ita kuma ba wani tsayin azo a gani ba balle ta yi zaton zai hangota, da ma ace an fara taron kowa ya natsu wata kila zata samu ya hangota.
Tsayi ta yi har ta gaji, ganin zata bata lokaci, ta yi biyu babu, babu makaranta babu samun ganinsa ya saka ta juya ta fita daga wajen, har ta wuce sai kuma ta juyo ta nufi gurin motarsa, ta kai hannu ta murda kofar ta jita a rufe, sai ta sake juyawa ta kalli ko'ina ta ga hankalin kowa be kanta ta kai hannayenta ta leka bakin gilashin motar, aikuwa sai ta hango littafinta na English a front seat aje, ta sake murdawa ta ji motar na zata budu ba, ta zira yatsunta ta gurin gilashin motar nan ma ba zai shiga ba, sabuwar idea ce ta zo mata sai ta zauna a gurin ta bude littafinta ta yi rubutu akai, ta cire takardar ta fara jikata da yawu tana yi tana tofawa har ta jika takardar da kyau sannan ta manna masa jikin gilashin motar ta gefen da idan ya zo budewa zai gani, sannan ta dawo ta dauki littafanta ta kama hnayar makaranta.
A ranar sai da aka zaneta da kyau a jiki da hannu saboda ta makara sosai, aka saka ta tsintar ledodi sannan aka barta ta shiga aji, ganinta da kudi mai dan kauri ya ajin da yawa tambayar ina ta samu, sai ta fada musu wani ta nunawa hanya ya bata kudin, wasu sun yarda wasu kuma suna mata kallon da wasu daga daidaikun jama'ar garin suka fara mata.
Da aka tashi break ne, Basira ta karbi kudin ta saka a jakarta ta boye mata.
"Batula, ba dole ne idan an tambaye ki ina kika samu kudi mai yawa sai kin fada ba, kin san kauyen nan abun magana baya kadan, ko tambayarki aka yi kice aika ne"
Ta daga mata kai, Kande ta gyara hijab dinta tana shan kankarar zobo ta ce.
"Basira ba boye kudin zaki yi ba, fitar mana zaki yi mu kashe, kin san da taje ta bawa bakar matar nan kara mu kashe"
Basira ta watsa mata harara.
"Mu kashe kamar ya? Ita bata da uzurin kudi ne? Ai ta fi mu bukatar kudi tun da kin san yadda take wahala kamin ta samu"
Batula ta girgiza kai ta kai hannu a jakar Batula zata dauko kudin da nufin ta diba ta ba su, sai Basira ta hana.
"Ba abun da za mu taba ciki, tashi muje"
Ta rika hannunta suka tashi, sai da suka taba tafiya kadan sannan Basira ta juyo ta kalli Kande da bata ko motsa ba balle alamar tashi, abun da ke nuna ta fusata da abun da Basira ta yi, Batula ta yi mata alama da ta taso su tafi sai ta girgiza kai.
"Kuje ina nan"
Basira ta juya suka cigaba da tafiya, Batula na yi tana waigenta domin bata son ran daya daga cikin abokanta ya bace, da suka tafi siyen awara da kudin Basira, Batula ta yi mata rubutu ta mika mata.
"Basira kudin ya kai 5k ku dauki daya daya dan Allah, kin ga Kande ta yi fushi"
"Idan ta yi fushi sai me? Munafukace yarinyar nan"
Batula ta bata fuska ta kalli basira alamar bata jidadin maganar ba, domin ba son abun da sai bata kawancensu su ukun nan ko kadan. Basira ta yi murmushi ta karbi awara ta suka juya ko da suka zo sun tarar Kande har ta koma aji, da suka shiga sai suka zauna kusa da ita suka bude awara, bata jira tayinsu ba ta kai hannu ta dauka ta fara ci daman haka suke abun su komai tare. Da aka tashi daga makarantar ne suka kama hanyar gida, Basira ta bata kudinta a marabar hanya.
"Idan kin je ki boye abun ki kar ma ki bari Umma ta gani, idan kin tashi siyen wani abu sai ki siya a boye"
Ta daga ta saka kudin cikin littafinta domin wando ta ne da aljihu. Batula ta musu bye bye ta wuce su biyu suka kama hanya domin gidajensu a layi daya suke.
"Bana jindadin abun da kike min Basira, ba yau kika saba ba, ko magana nake haka kike kwatse ni, bana son haka"
"Wata rana halinki ne sai a hankali, dazun a gabanki ake cin naman Batula baki ce komai ba"
A tsawace Basira ta ce
"Tohm me zan ce? Ni na san inda suka ji zancensu? Kuma idan baka yi taka tsantsan ba ma aka shafa maka za'ayi lamarin karkarar nan kamar baki san shi ba"
"Toh miye amfanin abota idan baka kare dan'uwanka ba? Kenan ni ma za a iya zama dake a zage ni? Shiyasa nake son Batula bata san munafurci ba, da kika ga ta zo da kudin nan sai kice ta boye abun ta tun da ita bata san me ake ciki ba, amman yanzu ganinta da kudi haka ai sai ya kara sakawa a zargeta, kuma In Shaa Allahu maganar nan tsakanin ni da ke ta fito, inda ba wani gun Batula taje ta yi maganar nan ba, ai da mu kadai ta yi magana"
"Ni ce munafuka kenan! Shi kike nufi ko Basira?"
"Ni ban ce ba"
"Lallai Allah ya isar min, haka kawai zan tafi ina fadar sirrinta? Yadda muke tare sai kuma na jidadi idan mutane suna yi da ita?"
Ta fashe da kuka, Basira ya shiga bata hakuri tana rarrashinta, sai kuma ta ji babu dadi na zarginta da fada mata magana da ta yi kai tsaye. Haka suka yi rabuwar rashin dadi Kande tana jin Basira ta zarge, Basira kuma tana jin rashin dadin zargin da ta yi mata.
Guraren karfe hudu Batula ta yi wanka saboda ta san masoyinta yana a gari zai iya zuwa ko ya ci karo da ita a hanya, dan haka ta gyara har da su farar hoda ta shafa kwalli a ido kuma ta yi digo da shi a goshi, ta yi lining da bakin kwalli a bakinta ta shafa manshafi sama, sai gata ta fito achanchan da ita, hoda har a wuya, tana tsaka da daura dankwali, Mal. Salisu, ya shigo da saurinsa da uban rawani yana kiran Batula, ta fito rike da dankwalin a hannu.
"Zo zo Alhaji Raheem Turaki, yana nemanki?"
Tana jin Alhaji Raheem Turaki littafinta ya fado mata a rai, sai ta karasa da sauri tana lulluba dankwalin banbalasta akanta madadin daurawa. Sai da ta fara lekawa sai ta gan shi tsaye jikin mota kusan mutum shida na zageye da shi, bata tafi ta sai ta juyo da nufin dawowa ta yi zaton ko karar ta ya kawo yace ta laka masa takardar a mota.
"Tafi mana yana nemanki"
Ta juyo da dan tsoro ta fita tana kallon inda yake tsaye, sai da ta kusa isa sannan ya juyo ya kalleta sai yayi murmushi, murmushinta ne ya karfafa masa guiwa ita ma ta yi murmushin ta maida hannunta daya baya dayan kuma yana rike da dankwalinta mai sulbi.
"Mamana ko?"
Ta daga mishi kai, sai ya juya ya bude motar ta dauko littafinta ya rufe motar, tana ganin littafin sai ga hakoranta a waje.
"Kin yi kyaun kai, na ga sakonki kuma ga littafinki na kawo miki"
Ta tara hannu biyu ta karba tana dariya sannan ta yi masa jinjina da hannunta, alamar ta gode.
"Hope dai ba a doke ki a makaranta ba, saboda littafin nan?"
Ta girgiza kai.
"Ranka ya dade saboda wannan shegen littafin ka dawo?, Haba ranka ya dade ni ina ce ko wani abun ne mai muhimmanci?"
Cewar Malam Salisu. Sai yayi murmushin kasaita yana kallonta.
"Ta san muhimmancin ilmi ne shiyasa, ana son haka, irinsu karfafa musu guiwa ake, yadda take amfani da ilmi da basira ya burge ni"
"Duk da haka dai ranka ya dade littafi ne ba wani abu ba, be kai ace sai ka dawo ba"
"Ba komai Baba"
Ta juya ta kama hanyar kofar gida daf da zata shige ta juyo ta dago masa hannu domin ba karamin dadi ta ji ba da ya dawo mata da littafinta, shi kuma yayi mata murmushi, kana ya kalli Malam Salisu ya ce.
"Idan ta gama wannan makarantar kuka ga tana da ra'ayin cigaba da karatun, dan Allah ayi min magana zan dauki nauyin komai nata"
"Ah Ah, Maa Shaa Allahu, tohm Allah ya saka da alheri ranka ya dade, In Allah ya yardar zan sanar maka, Allah ya saka da alheri ashe dai rabo ne da yawo da kai, Alhamdulillah"
Mal Salisu na ta godiya, a nan ma sai da ya kara musu alheri sannan ya tafi suna daga masa hannu. Batula bata wani yi murna da jin zai dauki nauyin karatunta ba, domin ba karatun take so sai kamar yadda take son aure ba, ita bata ki ma an cireta a yanzu an yi mata aure ba, bata taba tunanin cigaba da karatu bayan gama secondary school ba.
"Ranka ya dade ai da kace masa akwai wasu yaya, su ma sai ya taimaka musu ilmi ai kowa yana son shi"
Umma Hindu da fada domin albishir din be mata dadi ba, saboda ba yarta aka ce za a dauki nauyi ba.
"Kowa ai rabonsa yake ci, su ma idan suna so ai akwai ngo da suke daukar nauyi kuma yawancin na garin nan ta karkashina suke biyowa kin sani, sai a saka su ciki ai, su dai dage su yi abun kwarai, ba shiririta ba, ita ma kokarinta ya janyo mata"
"Shishiginta dai, da iyayi daman a idonka ai Batula ce kawai yarinyar kirki sauran duk shara ne, musamman ni yarana kamar ba kai ka haife su ba, sai ka yi ta banbanta su da sauran yaya"
Tana maganar tana harararsa tana zunguren baki, Malam Salisu ya san waye Umma Hindu da halinta dan haka ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, domin karamin aikinta ne yanzu ta tada balli a fara jin hayaniyarsu a waje.
Batula ta fita tana ta rabon ido amman har ta siyar da gulli-gulin ta dawo bata yi arba da Musa ba, da dare ma tana ta tabon ido ko zai sallamo ya kawo mata tsaraba, ko kuma ya so taɗi amman shiru ba ko daya, har ta gaji ta yi bachi.
JAWAD POV.
Bayan sallah isha'i Anty Sa'adatu na shirin tafiya Gwaggo ta dube ta ce.
"Sa'adatu, na zaki tafi ki gaishe da Hajiya ba?"
Ta yamutsa fuska.
"Ke ma dai kamar tsoronta kike Gwaggo"
"Ba tsoro ba ne, kin ga yanzu ni ce uwarku duk abun da kika yi cewa za'ayi ni na doraki a hanya, kuma dai a ba daidai ba ne, ki shigo gidan nan ki wuni ki tafi baki shiga kin gaida matar gida ba, matan ubanki ce ko kin ki ko kin so babu abun da zai canja"
"Ni Daddy ma na so na gani Wallahi, gashi be so ba har zan tafi"
Ta kalli Jawad dake taba system.
"Muje ka rakani na gaishe da Hajja Yelwa Mommyka"
Ko kallonta Jawad be yi ba balle ya amsa mata ba. Daman magana ba damunsa ta yi ba, kuma Muryar tasa ba wani dadi da ita ba, idan yana magana sai ka ji shi kamar wani boss.
Ba dan Gwaggo ta saka baki ba, ba zata shiga bangaren Hajja Yelwa ba domin yau ba zo da ra'ayin shiga ba. A bakin kofa ta tsaya,kamshi turaren yar fillo Collections da Hajja Yelwa ta turara falonta da shi na kai mata ziyara a hanci, babu karya kam indai kamshi ne da inganci a bar wa yar fillo abunta, indai ka yi amfani da turarenta ko makiyi sai ya yaba maka.
Kanenta yan wajen Hajja Yelwa, babu wanda ya gaisheta, saboda haushinta suke ji kamar yadda ita ma take jin haushinsu da mahaifiyarsu, bata kalli inda suke ba har aka kirata mata Hajja Yelwa ta fito da far'arta tana mata sannu da zuwa.
"Daughter ki shigo ki zauna mana"
"Aa tafiya zan yi dare yayi, daman dai na shigo ne kawai na gaishe ki"
Hajja Yelwa ta yi murmushi.
"Maa Shaa Allah na gode sosai, Allah yayi albarka yaran duk suna lafiya ko?"
"Lafiya Kalau, sai da safe"
"Tohm Allah ya tashe mu lafiya, a gaishe da gida"
"Gida ya ji"
Ta amsa mata a tsaitsaye ta fito fuska ba yabo ba fallasa ta dawo bangaren Gwaggo.
"Na shiga mun gaisa, ni zan tafi duk abun da aka miki Gwaggo ki fada min"
Jawad yayi murmushi ba tare da ya kalleta ba, duk yadda yake da fada yayarsa ta fishi neman fitini, domin shi be fada sai da dalili, kuma shi da kowa yi yake idan aka saba masa, ita kuwa ta dauki karan tsana kirikiri ta dorawa Hajja Yelwa, ko da yake ta wani bangaren tana da gaskiya, amman dai idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama, domin Hajja Yelwa ba kanwar lasa ba ce.
Gwaggo ta tashi ta sandarta tana dangawa ta raka Anty Sa'adatu dake dauke da kulolin abincinta domin ko ruwan gidan bata yarda ta sha idan ta zo cewa take Hajja Yelwa zata zuba mata wani abu a ciki. Mikewa tsaye Jawad yayi ya bi bayansu yana sanye da kanana kaya facing cap a kansa sai kamshi yake zubawa.
Da suka fito harabar gidan, ta bangaren da Daddy yake suka hango motocinsa da wasu bakin motocin alamar ya dawo, Anty Sa'adatu na bude baki kenan zata yi magana suka hango Daddy ya fito bangarensa tare da wani matashin suna tafe suna tattaunawa abun da suka san ba zai wuce business ba.
Daga can Daddy ya dagowa Jawad hannu yayi kiransa alamar ya zo, Jawad ya taka a hankali ya tafi fuskar nan a daure kamar kullum. Daddy ya dafa kafadar Jawad yana murmushin dake nuna alfaharin uba ga dansa.
"Turaki, wannan ne ɗana Even through dai ba shi na fari ba, amman kusan shi ne a komai nawa saboda shi ne kadai ne namiji da Allah ya ba ni, kuma yayi karatu sosai ya gina kanshi"
"Madallah haka ake so"
Furucin da ya fito kenan daga bakin mutumen da aka kira da Turaki.
"Jawad meet Turaki, Turaki Meet my Son"
Mutumen ya mikawa Jawad hannu yana gabatar da kansa.
"Sunana Raheem Turaki, abokin kasuwancin mai gida ne, ta wani gafen"
Turaki ya gabatar da kansa ta wannan hanyar ne just to humble Jawad domin ya hango ji da kai a tare da shi da kuma yadda yake shamkamshi. Jawad ya daga masa hannu irin na girmamawa, ba tare da ya mika masa nasa hannun sun yi shakking ba, domin yadda ya gabatar da kansa a gareshi be masa dadi ba, ko a ido za a iya shaidar Turaki matashi ne, sai dai kuma ba kamar Jawad din ba, ba dan kasuwanci dake dalili ya san mahaifinsa ba zai yi hulda da sa'ar kanensa ba, ko ma yace ɗansa, domin ba abun mamaki ba ne idan aka ce Daddy ya kusa haihuwar Turaki ko ma ya haife shi.
Daddy na kallon Turaki da murmushi, Jawad kuma yana kallonsa kawai babu annuri har ya hanna ma Daddy Horn ya ja motarsa ya fice.
"Yana da arziki da yawa ne Daddy? Har yake jin zai iya hada kasuwanci da kai?"
Daddy yayi murmushi yana maida hannayensa baya.
"Ba laifi, matashi ne mai zamani a yanzu, yana cikin masu dama kamar dai kai, sai dai banbancinku, shi ya samu kudinsa ta hanyar kasuwanci ne kuma yana cigaba da haƙa, shiyasa muke sharing wani bangaren na kasuwancinsa da shi, ka san shi neman kudi babu inda ba ya jefa mutum, musamman ace maka kasuwancin ne, zai iya hada ka da tsoho ko yaro, kamar dai yanzu, shi ya hada shi kasuwanci da sa'ar babban yayansa ko babbansa ma zance, ni ma ya hada ni da shi, shiyasa nake ta turaka cikin harkokina saboda akwai darasi da ilmi mai fadi da nake son ka koya, kuma ka iya"
Daddy ya daga kai ya kalli katon gidan nasa.
"Wata rana kai zaka rike gidan nan, wata rana kai ne uba, kai ne kaka, shiyasa nake ta kokarin hada kanku, musamman kai da kake namiji"
Da Jawad ya kalli mahaifinsa sai ya ji tausayinsa ya kama shi. Anty Sa'adatu ta karaso inda suke tsaye tana tsokanar Jawad.
"Daddy idan kana ganin Jawad babu ruwanka da kowa"
Daddy yayi dariya mai sauti.
"Ke dai baki rago komai daga halina ba, mita da fada, ko kadan baki dauko halin mahaifiyarki ba, Margagiya mace ce mai hakuri mai kawar da kai, ga karamci, Allah ya mata rahama"
Duk suka amsa da Ameen har Gwaggo dake can bangarenta tsaye, gaba daya fuskarsu sai ta sauya kowa ya tuno da wani bangare na rayuwa, Gwaggo na tunanin ƴarta, Daddy na tunanin matarsa ta farko uwargidansa, Jawad da Anty Sa'adatu kuma na tunanin mahaifiyarsu.