GUMBAR DUTSE

G_D - 10

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣0️⃣

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

Follow me on Facebook

***

My Novels Group

***

Follow Me on Tiktok ***

Follow me on Instagram

***

Follow on Wattpad ***

Follow me on Whatsapp

***

My Business group

***

All @Khadeeja Candy

KHADEEJA CANDY ✍🏻

------------------------------------------

Daddy ya sauke ajiyar zuciya.

"Ya kamata ki tafi gida, kar ki yi dare, Sufiyanu ya dawo min da ke, gashi ban da dakin ajeki"

Anty Sa'adatu ta kalli mahaifin nata dake maganar da zolaya.

"Daddy... Na saba zuwa gidan nan na kai har 10 na dare fa, kuma be ma isa ya dawo da ni ba yanzu, ai sai dai na koreshi, na ci gida"

Daddy yayi wata dariya da be saba yi ba sai idan yana tare da yayansa.

"Saboda kin kashe shi?"

"Saboda na haifi mishi yara kuma ai tare da ni aka samu arziki"

"Wallahi karya kike ko da ya zo neman aurenki da kudinsa, kuma ke ma kudin kika gani kika bi"

"Daddy kana mantawa ne, ni fa ina daga cikin matasan matan nan masu tasowa da abun hannunsu, kai kanka yanzu bana jin ka fi ni rufin asiri"

Daddy ya yi dariya, Jawad ya kalleta ya tabe baki, daman shi ba gwanin dariya ba ne, murmushi ma ba kasafai yake samun muhalli a fuskarsa ba.

"Idan za a bada zakka sai a saka sunanmu a list"

Anty Sa'adatu ta yi dariya.

"Karka damu Daddy ku ne first"

"Ina yarana? Na fada miki ki daina zuwa gidan nan ba da su ba ko?"

"Daddy ni ka haifa ba su ba, amman sai ka nun kamar ka fi son su da ni"

Daddy ya girgiza kai.

"Kurciya na damunki, ku wuce muje mu ci abincin rana"

"Ni na ci abinci, amman tun da da kai ne Daddy zan kara, kuma Daddy ka daina kaiwa har yanzu baka ci abincin rana ba haba"

"Tohm ya za'ayi neman Halak da wuya Sa'adatu, amman yanzu ai na kusa huta tun da Jawad ya dawo kusa da ni, shiyasa nake ta gabatar da shi gurin mutanena saboda nan gaba kadan shi zai tsaya a matsayina"

"Allah ya nuna mana"

Sa'adatu ta fada, Daddy ya amsa da Ameen Sannan ya kalli Jawad sai dai kamin yayi magana Jawad ya ce

"Ni na ci abinci, Hajiya ta ba ni abinci"

Ya karasa yana kallon Anty Sa'adatu domin ya san halinta, sai ta tabe baki sai dai bata ce komai ba sai da Daddy ya yi gaba yadda ba zai jita ba sannan ta ce.

"Allah yasa Hajiya ta maka barbare ta mallakeka ta juya ka yadda take so"

Ya daga kafaduwansa alamar be damu ba sannan ya juya yana kwatanta mutuwar ya nufi bangarensu, Anty Sa'adatu kuma ta bi bayan Daddy.

Jawad na shiga bangarensu ya Gwaggo ta kalleshi.

"Har ta tafi"

Ya girgiza mata kai alamar aa domin be ji zai iya amsa mata da baki ba, sannan ya haura sama ya shiga dakin da yake zane zanensa ya bude window ya zuba hannayensa aljihu yana kallon shuke shuken da suke bayan dakunansu, sai dai zuciyarsa tana wata duniyar wani tunanin yake na dabam. Wayarsa ce ya katse guntun tunanin da ya fara jan zarensa a kwakwalwarsa, ya ciro wayar dake vibration ya duba, kamin ya kara a kunne. Yayi shiru yana sauraren mai magana kamin ya ciro hannunsa daya ya shafa kansa.

"Okay, but ba abun sauri ba ne Ariz zamu iya bi a hankali"

Ya fada sannan ya juyo yana kallon dakin idonsa suka sauka akan zanen da be karasa ba na Batula da kauyensu.

"Alright"

Ya sauke wayar yana kallon yadda ya zanata kamar ta yi magana, ga kuma sunanta a jiki, dayan gefen kuma kauyensu ne da wasu abubuwan da suka yi arba da su a kauyen. Ya maida wayar aljihu ya nufi kofar fita yana kallon yadda gurin yake son mopping mai kyau domin kanensa ba sa masa mopping yadda ya kamata. Ya fito dakin ya shiga office dinsa dake dayan bangaren, cikin takun natsuwa da kasaita ya karasa gaban teburin ya saka duka hannayensa da karfinsa jiki yana kallon screen din desktop dinsa dake bude. Ya dan ja karami tsaki yana lumshe ido, mails ne masu yawa aka turo masa wasu ma be san ta iya zai fara duba su ba, mafi yawa daga kamfanin da suke aiki a tare ne dake Japan.

Ya bude idon tare da jan kujera ya zauna, ya fara duba wasu, yana jin wayarsa tana vibration amman yaki dagawa saboda baya son abun da zai raba masa hankali gida biyu. Yayi awa biyu a gurin yana replying wasu sakonnin da shi ya kamata ya maida da kansa, wasu kuma yayi ma Manager sa forwarding dinsu, daman Managen nasa baya barin sako ya shiga wayar Jawad sai ya tantance, matukar ba sakon kamfani ba ne wannan kam kai tsaye gurinsa yake zuwa, amman sauran sakoni na mutane ko wasu abokan aiki ko neman shiga sai an tantance Jawad yake dubawa, idan ya yi iya abun da zai iya sai ya turawa managensa sauran ya karasa replying din.

Ya fito a daidai lokacin da aka soma kiran sallah a babban Masallacin na gidansu, sai kawai ya zarge dakinsa ya shiga Bedroom ya dauro alwala ya fito yana ta kamshi kai kace wani sabon turaren na saka, yana saukowa Gwaggo na kokarin mikewa tsaye rike da sandarta.

"Gwaggo ina za a samu mai shara da mopping, amman namiji bana son mace"

"Namiji kuma? A gidan nan?"

Ya daga mata kai.

"Ko wajen gidan dai a wajen gidan zai rika sharewa?"

Ya girgiza mata kai, hakan yana nufin cikin gidan zai rika gyarawa kenan.

"Mace ta fi, sai dai a brma maka tsohuwa haka mai gyara"

"Ke kuke daukar abubuwa da zafi, ƙasashen da suka ci gaba ba su san banbancin jinsi ba, kuma ni ko da nake can maza suke min komai, namiji nake so"

"Maina mu fa nan hausawa ne, kuma musulmai, muna da banbanci da su, yanzu gida kamar wannan za a ce namiji ne yake shigowa nan yayi goge goge?"

Kuna da son daukar abubuwa da zafi, ni dai namiji nake bukata

Ya fada a ransa a zahiri kuma be ji zai iya tsayawa gardama da ita ba dan haka ya saka kai ya fice daga falon, a zuciyarsa yana yanke shawarar zai tuntubi Ariz kawai a nema masa ko kuma Hajja Yelwa ita ce bata musa masa a komai, ba mamaki shi ma aminin nasa Ariz ya ce ba haka ba.

Gwaggo ta bi jikan nata da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai.

"Shiyasa wasu basa sha'awar kai yaransu kashen farar fatar nan, gaba daya rayuwarsa ta zama ta turawa, magana ma kamar yakin duniya sannan yake yi, Allah ya kyauta"

Ta fara takawa tare da walking cane dinta ta nufi dakinta dake kasa.

BATULA POV.

Batula har ta yi soma bachi tana ji ana tashinta da shuri, sai ta zabuta ta zauna tana murza ido.

"Tashi Musa na waje yana jiranki"

Tana jin an ambaci sunansa ragowar bachin dake idonta ya tsinke ta mike tsaye da sauri, bata hankara ba ta zubar da ragowar kudinta ta nufi gurin da buta take ta dauka ta wanke fuskarta sannan ta gyara daurin dankwalinta ta saka talkamin da ta gani ta fice, daman shi mayafi saka shi ba al'adarta ba ce sai idan zata tafi wani guri na musamman ko makaranta, talkamin ma dan yana Musa ne da ba zata saka ba. Ta fita waje sai ta samu mutane a shimfidar Malam Salisu da alama yana da bakin dare.

Da fitilarsa ya haska mata gun da Musa yake tsaye yana jiranta nesa da su, bata tafi ba sai da ta karasa gurin mutanen da suke shimfidar ta gaishe da kowa sannan ta nufi gurin da yake cike da kunya, shi ma kallonta yake har ta karaso. Shi ya fara zama kan wani babban dutse da yake gurin sannan yayi mata umarni da ita ma ta zauna ta zauna tana mika hannunta ta dauko wani karamin kara dake gabansu ta soma zane cikin hasken farin wata.

"Batul, ya gida ya kwala biyu?"

Ta hada hannayenta duka biyu ta masa alamar amsawa tana murmushi.

"Maa Shaa Allah, ina mai baki hakuri ban samu  kawo miki tsaraba ba, saboda tafiyar ta zama ta gaggawa ni kaina ban shirya tafiyar ba, dole ce ta saka na zo"

Ta kalleshi irin kallon dake dauke da tambaya mai alamar lafiya? Sai dai hannayenta ba su motsa ba.

"Tsakani da Allah Batul ina sonki, duk lokacin da  naji wani abu game da ke marar dadi hankalina yana tashi, kuma sherin zuciyata tana son ta rinjaye ni, amman idan na tsaya na yi nazari sai soyayyarki ta rinjaye duk wani abu da zan ji ko zuciya zata saka min"

Ta nuna kanta da alamunta na kurmancin ta masa alamar tambaya, domin shi be yi boko ba balle ta rubuta masa ko da kasa ne, ita kuma babu bakin magana haka dai suke ta rayuwarsu yana fahimtar wani abun wani abun kuma sai dai ya hakura. Ya sauke ajiyar zuciya.

"Babu wani abu, kawai dai abun da nake son fada miki shi ne, ki yi taka tsantsan da rayuwa, na san ke marainiya ce amman ki kula da kanki da tarbiyarki, duk wani abu da zai zubar da mutuncinki ki nisance shi, kin san kauyen nan abun magana baya kadan Batul, kuma wani abun ko dan a bata maka suna ko a lalata alaka za a iya fada ko a kirkiro, amman ni komai za a fada akanki ni dai ina sonki kuma tsakani da Allah nake sonki, dan Allah Batul ki rike mutuncinki"

Ta daga mishi kai, zuciyarta cike da rashin gamsuwa, ƙwaƙwalwarta kuma cike da tambayoyi.

"Zaki iya tafiya gida, dare ya soma daman daga dandali nake na ce bari na jiyo ta gurinki na san kina sa ran zuwana ko?"

Ta daga kai tana murmushi.

"Tohm gani na zo, yanzu ki shiga gida ki kwanta  ki huta, gobe da wuri zan zo sai mu tafi dandali"

Ta fadada murmushi ta mike tsaye tana jefar da karan da ke hannunta ta kabe jikinta.

"Na gode sosai, sai da safe ko?"

Ta daga mishi kai, sai kuma ta daga masa hannu ta yi masa bye bye. Ta juyo ta nufo gida shi kuma ya bi ta gabansu Malam Salisu ya wuce bayan ya sake gaishe su.

Ta shigo gida cike da far'a da farinciki domin ta cire rai da zuwansa sai kuma gashi ya zo.

"Batula, ina kika samu wannan kudin?"

Ita ce tambayar da Umma Hindu ta fara mata a lokacin da ta shigo gidan, Batula ta kai hannu ta kwance zanenta ta duba gefe da gefe a zatonta ta kulle kudin ashe sakadasu kawai ta yi a jikinta. Ta yi kuriiii da ido tana kallon saitin da Umma Hindu take zaune tana hasketa da filitilarta da batirin yayi sanyi bata da wani haske sosai.

Batula bata gama tunanin amsar da zata bawa Umma Hindu ba, ta sake daka mata tsawa.

"Ina kika samo wannan kudin dan ubanki?"

Jikinta ya fara rawa, ta fara kwatantawa da hannunta alamar tukin mota tana misalta dogon mutum farin na dazun shi ya bata, sai dai Umma Hindu bata gama fahimtar misalin nata ba ta sake daka mata tsawa.

"Uban waye ya baki wannan kudin?"

Ta nufi daki da sauri ta dauko littafanta ta fito cikin hasken farin wata ta rubuta wanda ya bata kudin cewar Alhajin da ya zo dazun ne, ya bata bayan ta nuna masa inda yake nema. Ta mikawa yar Umma Hindu ta karanta ma mahaifiyarsu

"Kuma kudi mai yawa haka kika san ki boye da kanki? Batula?"

Cewar Umma Hindu, Larai ta tabe baki.

"Ai tambayarta ya kamata ki yi kiji saboda me ya bata kudin? Ba wai boyewa kawai ba"

Altine ta bushe fitilar aci balbal tana gyara kwanciya ta ce.

"Wannan yarinyar da kike gani idan ba a mata tsaye ba, sai ta kai kanta ga halaka ta kai ki ke da kike rikonta, ko ince ta kaimu gaba daya, domin abubuwa nake ji akanta marasa dadi, wani abun ma ba zai fadu ba"

Umma Hindu ta ja tsaki.

"Allah ka raba mu da hassada, komai bakinciki mutum be isa ya ce yarana ba su da tarbiya ba Wallahi"

Altine ta tashi zaune.

"Hassadar me? Daga ana taya ki kiwo? Ke da kin ji abubuwan da ake fada akan yarinyar nan ai Wallahi ko ruwa ba zaki sha ba, domin bakin shafentin da take son shafawa Malam na tabbatar idan ya sani ko ya ji ba za ku kwana a gidan nan ba Wallahi"

"Sannu yar sarkin munafukai, daman ke hassadarki dai zamana a gidan nan ta yayan da na zuba, to Wallahi ko mutuwa malam yayi n aci gida balle ina raye, idan kin fasa sanar da shi abun da ake fada a gari Allah ya kwashe miki albarka ke da zuri'arki, cikinku ba uban da nake tsoro Wallahi"

Umma Hindu ta fada cike da izza da masifa.

"Ni Altine ina mai tabbatar miki yau sai kin yi kwanan bakinciki, ba dai haka kika ce? Yar matsiyata, daman ina ta kame bakina ne saboda kar ace daga ni aka ji, domin mai kishiya be mutuwar Allah, amman yanzu sai kin gane kurenki Wallahi"

Ta yi kwafa, Larai ta bushe da dariya.

"Uhm wai shege yi da mai uba"

Umma Hindu ta zabura zata mike tsaye.

"Yayana da na haifa da cikina ba su saka ni bakinciki ba sai ke, kullum cikin sanyo min abun magana kike a garin nan, kuma kin sani gidan nna muna zagaye da makiya amman ke duk abun da za a yi min fade baki gudunsa saboda ba ni na haife ki ba ko"

Umma Hindu zata kama Batula, ba shiri Batula ta ranta a ana kare ta fita waje da gudu domin ta san dukanta zata yi. Kuma ta san ko zata kasheta babu mai kwatarta a gidan nan yau kam.

"Aiko yau sai dai ki kwana a waje, sai na ga wanda ya tsaya miki a gidan nan"

Kuka sosai Batula take tana rakube waje ta kasa shigowa cikin gidan kuma ta kasa tafi wani gurin, daman kam bata da inda ya fi gidansu ai, kuma ta san duk wanda zai mata tsaye a yau idan ba Malam Salisu ba sai ta sha duka. Ta dade a waje har sai da Malam Salisu ya gama da suka mutanensa sannan ya haskota da filita.

"Batul zo nan? Me ya faru?"

Ta nufi inda yake jiki babu kwari ta zauna kan shimfidar tana hawaye.

"Bakin halin uwar taki ya tashi ko?"

Ta yi shiru ba tare da ta daga kai ba.

"Zauna nan bari sai na tashi sai mu shiga tare"

A nan ta daga kai. Alamar tohm

"Batul ki daina damuwa, duk abun da aka miki ki rika fada min, kuma duk abun da kike so ki fada min, kin ga Musa ma ya dawo ba mamaki zancen aurenku ne, kin san kuma ni zan miki komai ko? Ki kwantar da hankalinki ni kawai abun da nake so idan na ce ki yi ki yi idan na ce ki bari ki bari, idan kika bani hadin kai da goyon baya babu abun da zaki nema ki rasa, kuma ina mai tabbatar miki ko aure kika yi babu abin da zai samu alakarmu kuma zan cigaba da kyautata miki fiye da yaya, ke ai kin san yadda nake son ki bana son yayana haka ko?"

Ta yi shiru bata ce komai ba sai hawaye take.

"Duk abun da na yi magana da ke ko na yi dake ina son ya zama sirri ne da babu wanda zai sani har mu mutu, jin ki nake kamar wani bangarena na jikina, ba dan kin zo a karkashin Hindu ba, babu abun da zai hana ni aurenki, saboda kina da natsuwa ni na san duk abun da zai faru ba zaki taba bari a ji ba ko?"

Ta daga kai tana share hawaye, har kai hannu da nufi taba ta sai kuma wata zuciyar ta raya masa idan wani yana labe yana kallonsu fa?

"Tashi mu tafi cikin gidan na ji me kika yi?"

Ta mike tsaye zuciyarta ba dadi ta shiga gaba shi kuma ya saka talkaminsa ya bi bayanta suka shiga cikin gidan tana ta bin jikin gini kamar zata shige ciki. Yayi sallama Larai ta amsa masa sai ya kama hannun Batula ya karasa tsakar gidan da ita.

"Na san dai ba zai wuce Hindu tace zata doke ki ba? Me ta yi?"

"Miye ba bata yi ba yarinya karama kamar wannan ta san ta samu kudi mai yawa ta boye? Kar ta bawa uwar dake wahala da ita? Abu sai ka ce yar kishiya?"

Larai ta fada kamar ita aka tambaya, Umma Hindu ta yi karaf ta ce.

"Ina ruwanki? Ke aka tambaya? In kuma kina da alaka da batula ne sai na ji, ka ji min wani iyayi karan kada miya"

Altine ta nuna ta da hannu.

"Ai dake ke baki da gwani, ba a miki gwaninki ba a burge sai kin bi mutum da sheri, halinki ne ta dauko ai, da alama zuri'ar ku babu na albarka, kai Malam kai ne kullum kan gaba gurin tare mata fada ko nuna mata gata, tohm gashi nan ana yama ɗiɗi da kai a gari cewar tare kuke"

Malam Salisu ya juyo ya kalli uwargidansa Altine. Umma Hindu da Larai suka saka salati da sallalami, har Salamatu dake ɗaki sai da ta fito waje rike da zane tana tasbishi, Zuciyar Batula ta buga da karfi, yaran da ba su bachi ba suka lafe kamar basa gidan.

"Ah ah ka ji ki da wani zancen banza! Kishi yayi ta janku kuna hauka da fada abubuwan da hankali ba zai kama ba"

Ya fada zuciyarsa na rawa sai dai be yarda ya nuna ba.

"Sherin me? Zancen gashi nan yana ta bin gari Malam? Ai ji zaka yi tun da amininka na san za su ji zu zo su fada maka, ance duk abun da kake mata na lallashi ta tausayi kana yi ne saboda tana baka abin da kake so, ita da uwar rikonsu ba su da maraba gurinka"

Malam Salisu ya saki hannun Batula ya nuna kansa da duka hannayensa biyu yana daga kafadunsa.

"Niiiiiii"

Altine ta ce

"Ahab.... Ai ita ma aka ce ta fada da kanta ita ta bada labari, shiyasa komai take so kake mata"

"Wannan maganar ba daga bakinki ya kamata a jita ba Altine, shekara da shekaru muna tare miye baki sani ba na halina? Wannan zancen na yan adawa ne masu bakinciki da dan abun da nake samu da kuma rufin asirin da Allah yayi min"

"Ni kam na san halinka shiyasa da aka fada ban yarda ba, amman koma minene ai ita wannan butulu ita ta kulla maka shi"

Malam Salisu ya kalli Batula dake hawaye kamar ruwa.

"Batul? Me kika fadawa mutane ina miki? Dakata ma tukuna me nake miki?"

Ta girgiza kai.

"Batula wani abun na ke miki?"

Ta girgiza kai.

"Bayan alheri da kyautata ban san wani abun da nake miki ba, ga yayana ga mata har hudu indai ba neman bata min suna ba mi zai kai ni ga wannan muguwar dabi'ar? Subhanallahi"

Batula ta matsa baya tana kuka.

"Ko wani ya saka ki ki fadi haka?"

Ta girgiza kai, ta nuna kanta ta girgiza kai ta girgiza hannayenta.

"Batula akwai abun da nake miki"

Ta yi alamar aa.

"Innalillahi Wa'inna Ilaihirra'un"

Ya cire hullar kansa. Umma Hindu ta ce.

"Babu wani wanda zai fadi haka, ita dai Altine ita ta shirya abun ta saboda tana bakinciki da ni tana yi da yayana da cigabana, daman kulawar da kake bawa batula be mata dadi ba, kuma zaman da nake a gidan ya isheta shi ne take neman dalili, daman ai ta fada wai yau ba zan yi kwanan farinciki ba, tohm Allah ya kai mu gobe lafiya sai na yi kararki kotu"

Malam Salisu ya daka musu tsawa.

"Miya kawo zancen kotu a nan kuma? Neman kuke ku zubar min da mutumci? Wannan maganar ai ta cikin gida ce, kar ma a fitar da ita waje, kuma koma waye ya fada ni na bar shi da Allah, gaskiya zata yi halinta, amman ni ban san wani abu tsakanina da Batul ba bayan kyautatawa, idan ita ta yi sharin ko wani ya sakata gaskiya zata fito, amman ni na fi yarda da zancen makiya, domin Batul tana da hankali ba zata yi haka ba, kar na sake ji wata magana makamanciyar wannan a gidan nan"

Ya haske ma Batula gurin shimfidarta, ta nufin gurin ta kwanta tana hawaye tsoron dukan da Umma Hindu zata mata ma sai ya fice mata a rai. Tunani ya zama mata biyu, Altine ta kirkiro haka da gaske, ko kuma dai mutanen waje sun fara lura da abubuwan da suke faruwa ne har ya saka suka zarge haka? Domin ta san kawayenta ba za su tona mata asiri ba.