GUMBAR DUTSE

G_D - 11

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

Follow me on Facebook

***

My Novels Group

***

Follow Me on Tiktok ***

Follow me on Instagram

***

Follow on Wattpad ***

Follow me on Whatsapp

***

My Business group

***

All @Khadeeja Candy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣1️⃣

Batula bata taba kwantawa da rashin bachi a ido ba irin na wannan daren, tunanin gaskiyar da zata jefata a matsala da kuma wanda ya fara fitar da zancen ya hana bachi rabar idonta, tun da take a rayuwarta bata san wani abu tashin hankali ba sai a daren yau.

  Da can duk wani tsoro da take ji be wuce dukan Umma Hindu ba, wannan kuma ya wuce duka da zagi kadai, bata san iya hukuncin da Umma Hindu zata mata ba.

  Baba ma zai iya korarta wata kila har a fasa aurenta, zata zama mujiya a tsakanin sa'aninta gashi abun tsegumi baya kadan a kauye.

Sai kusan Asuba bachi ya dauketa, kiran sallah farko ta farka ta tashi zaune, tsillin abun ya dawo mata a zuciya, ta dade zaune sannan ta tashi cikin duhun asuba ta lalaba fasashiyar butar da Bata da murfi ta zuba ruwan zafin da suka kwanta ta fara shiga bandaki ta yi fitsari data fito, sai ta nufi murhu ta dauki gawayi ta tauna a bakinta ta wanke bakin sannan ta saka yatsanta ta goge hakoranta ta wanke bakinta tass kamar yadda take yi kowace safiya, bayan ta gama ta yi alwala ta shiga dakin Umma Hindu ta dauko hijab dinta ta fito waje ta shimfida dankwalinta ta fara sallah tana karatun a cikin zuciyarta, tsabanin yadda kowa yake yi da bakinta saboda ita bata iya furuci.

Bayan ta gama ta kwanta a gurin ba domin bachin ba tana ta kallon sama har gari ya fara haske, sauran yaran gidan suka fara tashi bachi tare da manyan masu haramar sallah suka fara. Batula dai tana kwance guri daya, har sai da safiyar ta waye gaba daya sannan ta sake shiga dakin Umma Hindu ta yi mata ina kwana da yarenta na kurmanci, Umma Hindu ta watsa mata harara ta dauke kai. Batula ta fito ta cire hijab dinta waje ta aje kan ginin madafa ta daura dankwalinta ta dauki tulu ta fice daga gidan. Gurin kawayenta ta nufa daman tare suke zuwa diban ruwa takan biya musu ko su biyo mata balle kuma yau da take son magana da su sosai saboda abun da ya faru da dare.

Gidansu Kande ta fara biyawa ta shiga cikin rashin sakin fuska saboda damuwar dake tare da ita ta kasa boyuwa. Ta dagawa Inna su Kande hannu alamar gaisuwa sai ta amsa mata sama sama ba kamar yadda ta saba ba.

"Batula yau Kande ba zata je dibar ruwa ba, sai anjima"

Batula ta juyo ta kalli mahaifinyar Kande dake maganar, abun da bata taba mata ba, ko da Kande ba zata je diban ruwa ba ita da kanta take fada balle kuma ka'ida ne kullum da safe sai sun debo ruwa. Batula ta daga mata kai ta juyo ta fice daga gidan ta nufi gidansu Basira. Kamin ta karasa gidan ta hadu da Basira a zaure ta fito rike da kwalla alamar ita ma diban ruwan zata je.

"Yanzu fa ku zan biyawa, sai ga ki kin zo"

Batula ta kalleta kawai sai ta juya suka kama hanya.

"Batula, me aka miki?"

Batula bata amsa ba amman hawayen da suka sauko mata a lokacin da ta tambaya sun bata amsar ba lafiya ba.

"Ke"

Ta dabata ta juyo da ita.

"Me aka miki? Umma Hindu ce ko?"

Batula ta share hawayenta, ta kama hannunta suka nufi hanyar rafin, so take su kai inda kasa take da taushi so that ta samu damar rubuta mata abun da yake faruwa, saboda ita ba kamar su ba ne da suke iya magana da fadar abun da suke a duk lokacin da suka ga dama.

  Kasancewar sun tararda mutane a rafin shi ya hana Batula rubutawa kawarta damuwarta, sai kawai taja ta tsaya suna jiran a rage su samu dayan gefen su dibi ruwan, suna haka Kande ta iso da tulunta. Batula ta kalleta tana mamakin zuwanta bayan kuma mahaifiyarta tace ba zata je diban ruwa ba.

Bayan mutanen sun rage ne, Batula ta fara cika tulunta, Basira da kande ma suka cika, sannan suka zamu guri suka zauna nesa da sauran mutanen da suka rage a gurin.

"Miya faru Batula? Dazun na ga kina ta hawaye"

"Hawaye kuma?"

Kande ta tambaya. Sai Batula ta fara rubuta musu abun da ya faru a gidansu jiya da dare, tana yi tana hawaye, idan suka karanta sai ta goge ta sake rubuta wani, da haka har ta fada musu abun da ya faru. Basira ta cika da mamaki.

"Innalillahi, toh taya wannan maganar ta fita?"

"Wata kila mutane sun fara kula ne suna saka ido, ni kaina maganarce kawai ban miki ba, saboda kar ace abakina aka ji, amman wannan maganar ta yadu a kauyen nan, mutane har cewa suke ba wai Baba Mai Gari kadai ba, har mutanen dake zuwa bakunta gidanku wasu kina sakar musu jiki shiyasa suke baki kudi"

Basira ta kalli Batula dake hawaye cike da rauni

"Ni kaina na ji maganar nan amman Wallahi ba ni na fade ta ba"

"Ke ma kin san babu yadda za'ayi mu bayyana wannan sirrin, sai idan shi Baba ne ya fadawa wani shi kuma ya fitar, shiyasa dazun da kika zo Inna ta hana ni fitowa makota sai cewa suka wai tare da muke ake, wai idan ba mu yi hankali ba sai kin koya mana ko kuma ace mu mika lalata ki"

A karancin shekarun Batula, zancen zata lalata kawaye ko kawaye su lalata ba shi ne damuwarta ba, ita dai tsoronta daya kar a fasa aurenta, kar Musa ya ce ya yanje, domin shi ne kadai mutumen da zai iya aurenta da nakkasar dake tare da ita, idan har abun da ake fada yanzu yayi silar da Musa ya fasa aurenta to wa zai aureta? Kuma zata zama mujiya a cikin mutanen kauyen.

  Ga kasa sake rubuta musu komai ta mike tsaye ta dauki tulunta ta dora akai tana ta share hawayen da ba su gama zubo mata ba, bata tsaya jiran kawayenta ba ta kama hanya tana tafi tana jin kunyar mutanen da take haduwa da su a hanya ganin take kamar kowa kallon yar iska yake mata, alhalin kuma ba kowa yake da labarin ba.

Ta juye ruwan a tukunyar kasa dake kusa da kofar dakin Umma Hindu ta fito, rigarta na janyewa daga kafadarta saboda wuyan ya mata yawa, da zata koma zafin ba ta biyawa kawayenta ba, sai ta tafi ita kadai tana cikin cikawa Basira da Kande suka iso.

"Haba Batula, daga wannan maganar sai ki fusata kuma? Kin san dai mu ba zamu yarda da zancen mutanen gari ba, ko da baki fada mana ba balle kin fada mana gaskiya, babu abun da zai bata kawancenmu"

Batula ta kalli Basira dake zancen sai dai bata ce komai ba, Kande ta tsaya dayan gefenta ta ce.

"Ina ganin kamar kamata yayi ki hada wani plan da zai tona asirin Mai Gari hakan zai wankeki daga zargin mutane kuma za a san wanene Baba Mai Gari"

Basira ta karba mata.

"Eh ya kamata ki yi wani abu da zai wanke ki a idon mutane"

Cikin hawaye ta girgiza musu kai alamar ba zata iya ba, idan ma tace zata yi ta ina zata fara? Ita kan bata da wannan wayon ko basirarda zata iya sarrafa azancinta ta fitar da kanta daga wannan ramen data fada, bata da murya balle tace zata masa ihu idan ya taba ta, ba ma lallai ya sake taba ta ba a yanzu saboda ya ji abun da ake ta fada akansa.

"Me za'ayi?"

Bata sake komai ba ta cika tulunta ta dauka ta nufi gida, tun daga ranar Batula bata sake biyawa Kande ko Basira tafiya deban ruwa tare ba, Basira dai ta kan biyo mata amman bata zuwa tare da ita, ta fi sha'awar ta tafi ita kadai, a cikin gidan kuma ta zama tamkar jaba, babu mai rabarta, daga matan Malam har yayana dake jin haushinta kamar su kasheta saboda ance tayi ma mahaifinsu sheri, Malam Salisu ma be sake bin ta kan Batula ba, iyakancinsa da ita amsa gaisuwa.

Abinci idan aka hade mata da sauran yaran gidan da suke cin abinci tare, sai su yi ta watsa mata bakaken maganganu suna jefanta da munafuka butulu, wai duk hallacin da Babansu yayi mata ya fi sonta da su amman sai da ta yi masa sheri, idan ta zauna cin abincin bata wuce loma uku ko hudu sai ta tashi saboda yadda suke musguna mata.

Idan ta fita talla sai ta yi ta tsarguwa saboda tana ganin kamar kowa kallon yar iska yake mata, idan ta dawo tallar kuma sai ta boya a cikin daki bata fitowa sai da dalili, ga Batula yarinya ce mai far'a mai son wasa da dariya amman a dole ta sauya. Musa ma tun daga wacan ranar be sake zuwa ba, bayan kuma ya mata alkawarin dawowa su tafi dandali tare.

A kullum tunaninta daya ta ita maganar nan ta fita har ta yi saurin yado haka? Waya fada? Ko kuma wa ya gani? Yanzu idan Musa ya fasa aurenta wa zai aureta tana kurma kuma tana yar'iska.?

Wata ranar Lahadi Batula ta zaune a daki, daya daga cikin yaran Umma Hindu ya shigo.

"Batula Baba na kiranki"

Ta ji gabanta ya fadi, tsoro ya bayyana a fuskarta waya sani ko wata maganar ce ta ta so kuma a yanzu? Ta taso ta fito tana sanye da zane dabam riga dabam dankwalinta ma dabam fuska a yamutse ga firgicin abin da zata je ta karar ga kuma damuwar da take ciki.

Tana tafiya kamar an mata dole har ta isa kofar gidan ta fita, ta ga Baban tare da wasu mutanensa da kuma babban motar a fake, gefen gidan.

Da sake dubawa da kyau sai ta yi arba da mutumen nan da ya taba rage mata hanya kwanan baya har ya bata kudi mai dan kwari. Ba kasafai take manta fuskar mutane, ko daga nesa ta tana ganinka zata iya hassada ce fuskar mutum balle kuma har ace wata alaka ta hada ku da ita. Ta kai kasa tana gaishe ta mutanen da suke gurin ta maida idonta kasa.

"Batula ko?"

Ta daga kai ba tare da ta kalli mai kiran sunan nata ba.

"Wani sha'anin ne ya kawo ni, na tambaya ina kike aka ce kina ciki sai na bukaci a kira ki mu gaisa"

Ta dago ta kalleshi ta maida kanta kasa.

"Ko baki gane ki ba?"

Be wani santa sosai ba, amman haduwar da yayi da ita a wacan lokacin ya karanci yadda rayuwarta take, yarinya ce mai son mutane mai far'a tsabanin yadda ya ganta a yau.

"Ta isa tace baka gane ka ba? Ranka ya dade, ai kai ne ma ka yi kokari da ka gane ta, ku da safgogi suka yi ma yawa"

Cike da natsuwa yayi murmushi mai sauti irin na su na matasan masu kudi.

"Ya karatun Batula?"

Ta daga hannayenta tana amsa masa karatu Alhamdulillah da yarenta na kurmanci.

"Shi kan ina zai san wannan? Kawai ki daga masa hannu ya isa"

Ya sake yin murmushi.

"Wani abun aka miki dai ko? Na ga yanayinki kamar bake ba? Ko baki da lafiya ne?"

Ta girgiza kai. Malam Salisu ya dan ja numfashi.

"Wato abubuwa ne da suka je su dawo, kasan duk ka rike yaro kuma abun nan ya zama tsakani da Allah wani lokacin sai ga butulci ko kuma abin da ranka be so ba, amman dai tun da saboda Allah ake, wannan ya kawar da komai"

"Akwai wata matsala ne Malam?"

Alhaji Turaki ya tambaya.

"Aa ba sha'aninku ba ne ranka ya dade, abar wannan maganar kawai, abu dai ne yi shi domin Allah amman yana son ya taba kimata da mutumcina a garin nan, rikon Batula yana neman ya zame min kaya, ya janyo min dariyar abokan gaba, amman ba komai Allah zai bayyana gaskiya"

Ganin kamar Malam Salisu baya son sanar masa ya saka be sake tambaya ba, sai kawai ya saka hannunsa aljihu ya dauko kudi ya dari biyar biyar ya kirga 5k ya mikawa Batula, sai ta girgiza kai ta ki karba.

"Haba karba mana, waya yake maida hannun kyauta baya idan bake ba?"

Jin Malam Salisu ya fadi haka sai ta kai hannu ta karba ta yi masa godiya sannan ta juya ta koma cikin gida. Alhaji Turaki ya kalli tsagagen agogon hannunsa.

"Tohm ina ganin ni zan kama hanya daman bude masallacin nan kawai ya kawo ni, sun matsa sai na zo da kaina, ina da abubuwa da yawa a gida yanzu haka jirana ake"

"oh mutane ai sai Allah, ba za a barka ka huta ba, yaushe ka zo garin nan ai ko sati biyu ba ayi ba"

Cewar Malam. Salisu.

"Mutane ai sai hakuri"

Ya fada sannan ya saka hannunsa aljaihu ya dauko kudi mai kauri ya mikawa Malam Salisu, ya karba da hannu biyu yana godiya. A daidai lokacin ne Batula ta fito dauke da bahonta na talla, ta kalleshi ya kalleta sannan ta mika hanya. Alhaji Turaki ya matsa kusa da motarsa, Direbansa ne ya bude masa mota ya shiga ya zauna sannan ya rufe motar ya shiga ya fara ja suna daga masa hannu har suka daina hango shi.

Tana tafiyarta a hanya, aka sha gabanta ta mota, ganin motar mutumen dazun ne ya saka bata tsorata ba, sai dai ta tsaya cak bata karasa ba, har sai da suka yi baya kadan suka tsaya daidai ita, Alhaji Turaki ya sauke gilashin motarsa daga back seat.

"Ina zaki je? Idan hanyar mu ce sai mu rage miki tafiya?"

Ta girgiza kai, har lokacin babu far'a a tare da ita. Sai direbansa ya leko ta cikin motar.

"Baki so? Ko kuma ba hanya ɗaya za mu bi ba?"

Ya tambaye ta da yaren kurmanci, babu shiri ta zaro ido tana mamaki ina ya iya yarenta. Shi kansa direban sai da yayi dariya ganin yadda take mamaki kamar wanda ta ga wani sabon abu. Ta sauke bahon kanta ta fara magana da shi da yarenta tana masa alama da hannayenta irin yadda kurame suke yi.

"Daman ka iya kurmanci.?"

"Eh sosai"

Ya bata amsa.

"Da gaske?"

"Gashi ina yi kuwa"

Sai murmushi ya cika fuskata hakoranta suka bayyana ta rufe fuskarta, shauki ya saka ta manta da yaren kurmanci suke magana tsabar zumudi.

"Tohm kace kai ma ka iya maganar ta su kenan?"

"eh ranka ya dade, ai na yi koyarwa a makarantar korame kamin na samu wannan aikin"

"Maa Shaa Allah, amman ban tana sani ba"

"Eh da yake ba kai ka duba Cv na ba, PA dinka ne, kuma abu irin wannan be taso ba shiyasa"

Alhaji Turaki ya koma ya kwanta jikin motar yana kallon yadda Batula ke baje basirarta tana magana da yaren nata.

"Amman kai kana iya magana"

"Eh, ni na koyi yarenku ne kuma na koyar, saboda yana burgeni"

Ta mata amsa, sai ta yi dariya for the first time ta ji wanda ya furta cewar yarenta ya burge shi.

"Ke miyasa baki magana?"

"Ni ma ban sani ba, haka dai na gan ni"

"Shikenan, zaki tafi ko mu kama hanya?"

"Aa ni ta nan zan bi babu nisa, ku tafi Allah ya tsare"

Ya juya ya kalli ogan nasa.

"Ranka ya dade wai nan kusa zata tsaya"

"Okay then let's go"

Direba yayi mata sai anjima ya fara jan motar sai ta dago musu hannu tana musu bye bye hakora a washe, Alhaji Turaki ya dago mata hannu yana murmushi, shi kam yarinyar na burge shi, musamman idan tana murmushi da alama ba zata yi fitina ba, zuciyarsa ta raya masa.

Daman can kuma Batula yarinya ce mai shiga rai, da daukar hankali, ko sau daya ka ganta sai ka ji ta burgeka.

Tun da ta fita bata dawo ba sai da ta siyar da kuli kulin gaba ɗaya domin ta san halin uwar rikon nata bata son kwantai.

Tana dawowa daga tallar, zata shiga gida Malam Salisu ya kirata daga can inda yake zaune, sai ta juyo ta nufo inda yake gabanta na faduwa domin tun bayan hayaniyar da aka yi a wacan daren wata doguwar magana bata sake shiga tsakaninsu ba. Ta risina kasa tana rike da kwanonta na talla ganwonta a hannu.

"Batula, karbi ga kudi nan, sako ne aka ce aba Malam Haruna rabo, yi maza tafi yanzu ki kai masa yana can gurin gidansa, hanzarta jira yake, babu wanda zan aika ne shiyasa, da ba zan aike ki ba, domin yanzu babu ruwana da ke"

Ta kai hannu biyu ta karba ta mike tsaye sannan ta dauki kwanon tallarta ta juya da nufin shiga gida ta aje kwalla da ganwon, sai ya dakatar da ita.

"Tafi yanzu ki kai masa, ba sai kin shiga gida ba, tafi da kayan tallarki saboda ya san daga gurin talla kike kar ya saka ki wani aikin"

Na musu ta sake juyowa ta cira kafa ta fara tafiya da hanzarinta, mutumen da aka ce ta kaiwa sakon kudin aminine ga Malam Salisu, kusan ya san komai na sirrinsa shi ma kuma ya san nasa.

JAWAD POV.

Sleeping dress ne a jikinsa hannunsa daya a pocket dayan kuma yana rike da wayarsa dake kunnensa.

"Kamar nawa ake bukata?"

Ya dan yi shiru, ya juyo.

"Alright zan yi ma PA magana sai ya tura a Foundation, zai yi kyau ayi kamar rijiya uku haka tun da ance kauyen ba su da ruwa"

Ya nufi kofar dakin ya bude da dayan hannunsa.

"Okay then"

Ya sauke wayar ya fara saukowa a hankali.

"Gashi nan ma ya fito bari na baki shi"

Gwaggo ta mika masa karamar wayarta ya kalleta sannan ya karba ya kara a kunne bayan ta duba sunan dake jiki.

"Gwaggo ta fada wai kace a nema maka mai shara namiji?"

Kamar ta san ba zai amsa ta ba, ta cigaba.

"Ka yi tunani na neman mai gyara muku bangarenku daban, daman ni ba son shigowar yaran nan nake ba, domin Hajja Yalwa zata iya hada baki da su ta saka maka wani abun a dakinka, amman dai hakan ba zai saka a dauki namiji ba, madadin haka ma me zai hana ka fara tunanin aure? Ka samu matar da zata gyara maka ko'ina ma hankali kwance?"

Nan ma be ce mata komai ba.

"Ka isa auren nan Jawad ba wai baka isa ba, idan ma baka da wanda kake so ka bar min wuka da nama a hannuna, ni san kalar matar da zata dace da kai, ko da yake kai ba a maka gwaninta, idan kuma ka fi son ka nemo da kanka to ka nemo ba wani abun ba ne, amman ban da bangaren Hajja Yalwa, domin karamin aikinta ne ta ce zata hada ka da Ayla, tun da ganin take kamar ta mallakeka ko ma na ce ta mallakeka din gaba daya"

"Zan aje wayar"

Ya fada cike da gundura da kalamanta, daman shi ko labarin arziki kake ba shi zai iya cewa ka cika masa kunne balle kuma wannan.

"Tun da an fara maganar Hajja Yalwa ai dole ka aje waya, an tabo inda baka son a tabo, to Wallahi komai mallakar da ta yi maka ba zan tana bari ta aura maka mata ba sai idan bana numfashi, balle kuma Ayla da take bazarawa"

Dip ya kashe wayar ya mikawa Gwaggo.

"kokarin kai karara gurin Adda Sa'adatu ba zai sauya komai daga abun da na yi nufi ba, namiji zan kawo wanda zai rika gyara bangaren nan, so ba amfanin fada mata maganar da har ta kwana biyu"

Ya fada sannan ya aje mata wayar ya nufi kofar fita.

"Kai kan wane irin kafiya ce da kai Jawad? Shikenan idan ka hau abu ka zauna babu wanda ya isa ya sauya maka ra'ayin? Wannan rayuwar da turawa da kuke dauka ba koyar addini ba ce, ace mutum idan ya zana layi wani be isa ya zana masa wani ba?"

Be san me take fada ba, domin tun da ya saka kai be juyo ba balle ga saurareta. Bangaren Hajja Yalwa ya shiga turaren turaren yar Fillo collection ***. Na masa barka da zuwa, ko da ya shiga ya samu har sun kusa gama karyawa domin yau be tashi da wuri ba. Hajja Yalwa na ganinsa ta mike tsaye da sauri ta ja masa kujerar da ya saba zama ya zauna, sannan ita ma ta zauna tana murmushi.

"Yau kan makara my son, har ina cewa idan muka gama karyawa baka fito ba, zan tafi da abun karyawarka da kaina na tashe ka"

"Na kwanta late, ina kwana"

Ya fada fuska ba yabo ba fallasa, ta amsa masa da murmushi tana bude masa Warmers din dabam, daman taban take zuba masa nasa abincin a kulolin data siya masa na musamman gurin Khadeeja Candy. Kanensa duk suka gaishe shi, Ayla taja kujera baya ta tashi ta fice daga dinning din. Shi kuma yayi Bismillah ya fara cin a abincin da Hajja Yalwa ta zuba masa, sannan ta fara masa hira, yadda take kula da shi kai ka rantse ita ta haifeshi.

Yana gama cin abincin sako ya shigo wayarsa, ya bude sakon na Daddynsa ya duba.

"Ka zo yanzu nan ina nemanka"

Ya mike tsaye, ya dauki tissue ya goge bakinsa, daman tuni ya matsu ya bar gurin, domin idan akwai abun da ya tsana a rayuwarsa shi ne dogon zance, a duk lokacin da ya zauna kuma sai Hajiya ta rika ba shi labarin abubuwa da wanda ya kamata ya sani da wanda be ma shafe shi ba.