GUMBAR DUTSE

G_D - 12

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her +234 ***

Follow me on Facebook

***

My Novels Group

***

Follow Me on Tiktok ***

Follow me on Instagram

***

Follow on Wattpad ***

Follow me on Whatsapp

***

My Business group

***

All @Khadeeja Candy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣2️⃣

Ya shiga bangaren mahaifinsa yana sanye da sleeping dress da be canja ba, domin daga bangaren Hajja Yelwa ya fito.

  A falon farko ya samu mahaifinsa sanye da jallabiya, yana zaune akan kujera ya dora kafarsa daya remote a hannunsa yana kallon Aljazeera.

"Wa'alaikumussalam"

Ya amsa yana dan juyowa kadan ya kalli Jawad da yayi sallamar. Jawad ya zauna kujerar dake dama da Daddy yana mika masa gaisuwa.

"Good Morning Dad"

"An tashi lafiya?"

"Alhamdulillah"

Ya dan kalli news din kadan sannan ya maida kansa gurin wayarsa. Daddy ya aje remote din hannunsa bayan ya rage volume kana ya cire gilashin idonsa.

"Jawad"

Jawad din da aka kira ya kalleshi sannan ya amsa.

"Naam"

"Wata magana ce aka zo min da ita, tun a lokacin da ka dawo, sai kuma yayarka jiya ta sake min maganar, yau kuma da na shiga mu gaisa da Gwaggo kana bachi ta sake min maganar"

Jawad ya sake fuskantar Daddy da kyau ganin yadda yake maganar cike da annashuwa, a take ya karanci abun da mahaifinsa yake son fada.

"Aure?"

Daddy yayi murmushi.

"Dadi da kai akwai basira, ka canka daidai"

Jawad yayi murmushin gefen baki kadan.

"Adda Sa'adatu zata maka magana, Gwaggo ma ta yi, sai wa kuma Daddy?"

"Hajiyarka, ita ma ta damu, kasan ko mace ce ta kai munzalin aure sai an mata hankali yake kwanciya balle namiji"

"Saboda Mace ta fi hasari Daddy, ni ai namiji ne, amman dai kun kawo magana mai kyau, ina fatan samun ta gari, Allah ya kawo lokaci"

Daddy ya dan watsa masa wani kallo.

"Allah ya kawo lokaci?"

"Yeah kasan komai lokaci ne"

Daddy yayi murmushi mai sauti.

"Mace ake cewa wannan ba namiji ba, saboda ita mace jira take sai an zo ance ana sonta, amman namiji nemowa yake yi. Yanzu dai ba wannan ba akwai wanda kake so? Ko kuma kake hangen hankalinta ya kwanta maka? A nan ko a can"

Bakinsa a rufe yadan yi motsi da halshensa kamin ya bude a tausashe ya amsa

"Babu"

"Ka tabbata? Domin bana son sai an shiga maganarka daga baya ka taso mana da zancen wata"

"Babu Daddy, akwai dai wanda muka yi soyayya amman dai mun rabu"

"Miya raba ku?"

Daddy ya tambaya, Jawad ya yamutsa fuska yana kallon Daddy da murmushin rashin gamsuwa.

"Daddy wannan personal life dina ne, amman i promise you yanzu bama tare da ita"

Daddy yayi dariya mai sauri.

"Mr I know my Right, yanzu zamu iya shiga mu nema maka mata? Ko kuma shi ma private life dinka ne? Mu bari ka nemo da kanka?"

Ya shafa kansa yana murmushi.

"Za ku iya, for now bana da wata wanda nake so, kuma ban san ta ita zan fara ba, bana ma da lokacin wannan"

"Tohm mu da muke da wannan lokacin zamu nema maka, kuma kai ma sai ka bude ido idan ka ga wanda ta yi maka sai ka mana magana, a bincika aji ko yar gidan waye ce, daga nan kuma sai mu ga abin da Allah zai yi"

"Alright"

"Good, at anytime ka shirya sai ka fadawa Hajiya ko ni kalar matar da kake so, da sifofinta, wannan ma zai taimaka"

Jawad ya daga girarsa.

"Daddy can we talk about business, ko wasu abubuwan? Wannan maganar auren wasu ne suke ganin ya kamata na yi fa ba ra'ayinka ko ra'ayina ba ne"

"Gwaggo, Sa'adatun, da Hajiya Yalwa ne wasu?"

Ya runtse duka idon biyu, yana jin nauyin abun da ya fada kamin ya bude ido daya, ya kalli Daddy alamar rashin gaskiya da kyautawa. Daddy ya girgiza kai yana murmushi.

"Be careful Boy"

"Haba Daddy yanzu ai na wuce a kira ni da yaro"

"Da kyau Tsohona"

Daddy ya fada sai duk suka yi dariya a tare. Daddy ya kalli agogon falonsa ya sake duban Jawad.

"Zaka iya tunawa wani mutum da kuka gaisa kwanan baya? Wanda ya same ni a nan cikin gida?"

Jawad ya dan yi shiru alamar nazari.

"Raheem Turaki?"

"Good, akwai meeting da zan yi da shi by 11am, sai dai bana jindadin jikin nawa, kuma akwai meeting biyu da zan tafi, ina tunanin kai zaka wakilce ni"

Jawad ya tattara girarsa guri daya

"Amman Daddy baka ganin kamar shi ya kamata ya zo ya sameka? Ka girme shi a kasuwanci, haka a shekaru"

Daddy yayi murmushin manya, ya kai hannunsa ya dauki medical gilashinsa dake hannun kujera ya saka a idonsa.

"Wato Jawad, har yanzu kai yaro ne, kuma har yanzu baka san komai a fagen kasuwanci ba, tunaninka yana iya inda aikinka da ƙwarewarka suke, saboda kai ana sonka ana son aikinka kai ake tararwa, amman a cikin masu zuwa gurinka a zahiri da kuma ta hanyar sadarka har ku yi meeting babu wadanda suka haife ka ko suka yi jika da kai"

"Akwai"

Ya amsa kai tsaye.

"Tohm kamar hakan ne, bukata tana saka mutum ya gurfanar da kansa a inda biyanta yake, durkusawa wada ai ba gajiyawa ba ne, shi kasuwanci ba kamar zanen motoci ba ne irin ba ku, mu irin na mu zai iya sakawa ka hau jirgi ka tafi ta kararda dan shekara 20 ko kasa da haka ku yi kasuwanci da shi, wacan karon da ya zama shi yake da bukata a gurina ai ka ga shi ya kawo kansa, duk da yake ba mutum ne mao girman kai ba, a yanzu din ma zan iya kiransa kuma ya zo, amman saboda ina son ka koyi wasu abubuwan daga safgogina, shiyasa zan turaka, ka ga yadda matasa yan'uwanka suke kasuwanci"

Ya tabe baki.

"Gidansa zan tafi?"

"Aa office, Haroon zai turo maka Venue, Direban Hajiya zai kai ka gurin"

"Zan iya tuka kaina Daddy ka sani"

Daddy ya kankance ido.

"No, cikar girma ne a kai ka a mota a bude maka ka fita idan ka gama a bude maka ka shigo a dawo da kai, akwai inda kake bukatar yin abu da kanka, amman gurin abokan chuɗanyya, goyayya, bar isa da dukiya ta yi aikinta"

Jawad yayi murmushi karatun da Daddy ke zuba masa yana shiga cikin kansa.

"Zan zabi mota mai cika ido"

"Yanzu kake magana yarona, show them who you are, let them know where are you from, and let the success make the noise"

Ya mikawa Daddy hannunsa a dunkule shi ma ya mika masa suka buga. 🤜🤛

"Allah ya kiyaye hanya"

Zancen dress ne kadai Daddy be masa ba, domin ya san abu ne mai wahala a samu wanda zai iya buge Jawad ta bangaren iya dressing da saka tufafi masu tsada, yana da dress code for every event ko da kuwa fita ce kawai ta shan iska.

Bayan Fitarsa Daddy ya kai hannunsa ya dauki wayarsa dake aje kusa da inda ya aje gilashinsa dazun, ya gyara zaman gilashin a idonsa sannan ya bude wayar ta fara tabawa, ya kara a kunne. Jimmm yayi na dan lokaci kamin ya ce

"Kai kullum ina fada ku koyi sallama idan kun daga waya amman baka jin magana"

Ariz yayi dariya daga dayan bangare.

"Daddy da sannu zan koya, mantawa na yi kasam numberka har tag na yi mata na Assalamu Alaikum"

"Saboda fadar gaskiya?"

"Aa saboda idan ka kira ni kar na manta na ce hello na ce Assalamu Alaikum, wasu ko ban ce musu ba ai ba zaka gane ba"

"saboda kana ganin na yi tsufan da ba zan iya fahimtar komai ba ko?"

Ariz ya kyalkyale da dariya.

"Hahaha Daddy rigima kake nema da ni dai yanzu da safen nan ko karyawa ban yi ba"

"To ka zo nan ka karya mana, Hajiyar ta gama komai tun safe kasan bata wasa da cikina, idan ka zo sai mu tattauna maganar da nake kira ka akai zai fi"

"Okay Daddy gani nan zuwa"

Daddy ya sauke wayar yana murmushi tare da kallon Hajiya Yalwa wacce ta shigo falon a yanzu, saboda bata da natsuwar ruhi har sai ta ji dalilin kiran da Daddy yayi ma Jawad, kullum tsoronta kar a shirya wani abun ba da saninta ba.

"Da wa kake waya haka baki har kunne"

Ta zauna kusa da shi, tana murmushi

"Ɗana ne Ariz"

"oh albishir yayi maka haka ne Babban Yara?"

"Ni ne dai zan masa albishir"

Ta kara washe baki, tana juyawa ta kara duba katon falon.

"Ina ɗana har ya fita? Ko be shigo nan ba?"

"Ya shigo, mun tattauna abun da zamu tattauna, har na tura shi wani gurin ya wakilce ni"

"Maa Shaa Allah, Mu albishir din be shafe mu ba kenan?"

Daddy ya aje wayar hannunsa ya kalleta da kyau.

"Kin san maganar da kika taba min akan Jawad kina cewa a ganinki ya kamata yayi aure?"

Ta amsa da sauri.

"An yi haka"

"Toh yanzu dai ya amince"

Hajja Yelwa ta dora hannu a kirji tana washe hakora kamar gaske.

"Allah Baban Yara? Alhamdulillah Allah mun gode maka, kai dole na yi sadaka, Haba yanzu na ji magana, amman yaro yayi shiru ko zancen aure aka masa yace shi be tashi ba"

Hajja Yelwa bata kai karshe zancenta ba ta tsinkayo muryar Daddy yana waya da Sa'adatu tare da yi mata albashir din abun da suka tattauna. Sosai ta cika da murna jin dan'uwanta ta amince zai yi aure, daman abin da take ta jira kenan, ta sha tunkararsa da zance sai yace mata shi babu wanda yake so kuma ba zai yi aure dan wasu ba sai dan ra'ayinsa, saboda dan'uwan nata murdadden mutum ne, kuma Gumbar Dutse, sai dai kuma ta san abu ne mai wahala ya musawa Daddynsa, domin ya kanbi shawarar Daddy idan ya dora shi a hanyar wani abun ko da kuwa baya so.

"Tohm sai a yi kokari a zakulo masa wanda zata dace da shi kin san dai yanayin dan'uwan na ki"

"In Shaa Allahu Daddy, ni daman amincewarsa kawai bake jira akwai wanda nake son hada shi da ita"

"Tohm Allah ya taimaka"

"Ameen, wannan albishir haka Daddy ai dole na baka turaren yar Fillo a rika turara maka daki da shi kuma ana maka kabbasa"

+234 ***

Daddy yayi murmushi mai sauti be sake cewa komai ba ya aje wayar. Hajja Yelwa ta ja gutun numfashi ta sauke tana kallon mijinta.

"Sai nake ga kamar ba a kyauta min ba, idan aka ce Daughter ce zata nema masa mata ba ni ba, alhalin kuma ina raye, duk wanda zai so ɗana yayi aure ai a bayana yake, duk da dai ba a hannuna ya tashi ba, amman na san halinsa ciki da waje, na san hallayensa da irin matar da zata dace da shi"

Daddy yayi Dariya can cikin makoshinsa.

"Ni fa mantawa na yi kina nan zaune, daman abun da ya shafi Jawad ai ba a isa a ja da ke ba, karamin aikinki ne ki bar ni ki zabe shi"

Ta burkita hannayenta.

"Ah ah tohm sau nawa aka yi kuma?"

"Tohm a gafarce ni, yanzu ai wuka da nama suna hannunki, duk yadda kuka yi da ɗanki babu wanda zai magana, daman ke ce ko ita Sa'adatun za ku nema masa"

"Tohm, Allah ya ba mu iko, amman dai idan ana zancena ka daina saka Daughter ita ma fa ƴata ce a karkashina take"

"Wato indai son Girma ne bar miki kayanki ko? Ba ki data biyu"

"Alhajina na kaina"

Ta kwanto jikinsa tana dariya. Daddyn ma dariyar yayi yana kara juyowa ya kalleta.

JAWAD POV

Ya sauko a gaggauwace saboda baya son yayi latti a gurin da zai wakilci Daddynsa domin lokaci ya kusa. Hada ido suka yi da Ariz dake zaune a kusa da Gwaggo ya fada kafafuwanta suna magana kadan kadan kamar ba sa son wani ya ji. Jawad ya tabe baki daman ya san sai idan ba su hadu ba, gulmar gidan gaba daya babu wanda Gwaggo take jin dadin yinsa da ita irin amininsa Ariz, haka shi ma wani iri na gidansu Ariz sai dai ya ji Kakarsa tana fada shi be san da shi ba, idan aka masa ba daidai ba a gidansu Daddy yake fadawa ko Gwaggo su dauki mataki ko su yanke hukunci.

Tsabanin Jawad da baya iya fadawa kowa matsalarsa ko da kuwa damuwa zata kashe shi, sai idan an fahimta an kawo masa dauki.

Jawad ya banbanta da aminsa sosai, kuma ya banbanta da yan gidansu, domin be cika son yawan magana ba, hakan kuma ya samo asali ne tun daga lokacin da yake cikin hannun mahaifiyarsa yana jindadinta sai mutuwa ta dauketa, daga nan ya fara shiga damuwa, sai kuma mahaifinsa ya dauke shi ya maida shi kasar waje da karatu. A makaranta ma ya zama ana bullies dinsa, saboda kasancewar vakar fata, Kuma ga shi da hazaka sai ya zama na yara da yawa suna jin haushinsa, yayi ta fuskanta tsangwama amman be taba fadawa iyayensa ba.

Daga nan rayuwa ta canja masa ya zama ba shi da abokin shawara ko fadawa damuwa, ba ya shiga tsafgar kowa kuma ya saba gudanar da rayuwarsa shi kadai, wannan abun ne ya girmar da shi har yanzu, baya iya shawara da kowa, baya iya fadawa kowa damuwarsa, kuma baya iya zama yayi hirar awa 1 idan ma ya zauna sai dai yayi ta saurare ko ya daga kai ko ya girgiza, idan ta masa dadi ne zai rika jefo tambaya ko wata kalmar sama sama, idan kuma hirar bata masa dadi ba sai ta saka shi ciwon kai saboda be son yawan surutu.

"Mai shara kake son a dauko maka kuma namiji? Malam nan fa ba kashashen turai ba ne"

Ya kalli Ariz yana saka agogonsa, amman be ce komai ba, daman ya san wani lokacin tunanin Gwaggo da Ariz yana zuwa daya, ko kuma shi Ariz din ya goya masa baya ko da kuwa ya san kakarsa ba akan daidai yake ba.

"Abun da na gani kenan, da ayi haka, ai kara yayi aure, shiyasa dazun da Alhaji ya shigo ya sake masa magana, idan ma babu wanda yake so a nan ai akwai su da yawa a can wajenmu sai a zabo masa"

Jawad yayi wani murmushin gefen baki, Ariz kuma ya mike tsaye yana fadin.

"Haba Gwaggo, duk fadin duniyar a rasa inda za a nemowa Jawad mata sai kauye.? Kin fa san yadda ya tsani kazanta, duk yadda ake kokarin tsabta shi sai yace haka be mai ba, balle kuma yar kauye, ga shi ba ya son kauyanci ko kadan Haba dai"

Ariz be gama rufe ba Jawad ya tari numfashinsa.

"Ina ruwanka? Kai zaka zauna da ita?"

Mamaki ya hana Ariz rufe baki...

"Oww... Okay"

Ya kalli Gwaggo dake musu dariya.

"Gwaggo dan Allah a samu wata yar kauyen kayau, ko kuma a gino masa wata a kasa a aurowa wannan Yaron"

Jawad ya fadada fuska da murmushi, ya sani sarai Ariz ya kira shi da yaro ne saboda ya ji haushi, domin ya tsani ace masa yaro.

"Can you be my driver? I need to go somewhere"

Ariz ya daga masa yatsansa na tsakiya. 🖕 As Fuck You, Jawad ya fice fuskarsa da annuri yana matukar kaunar aminsa kamar yadda Ariz din ma yake kaunarsa tun suna yara.

"Kin ga acan duk wanda ta aure shi zai ta sha wahala a rayuwarta"

Ariz ya fada bayan Jawad din ya fice, Gwaggo ta ce.

"Ni ma ai na fadi haka, ni na rasa halin waye ya dauko, babu mai wannan halin a danginmu sai idan can dangin mahaifinsa, domin Mahaifinsa ma ba haka yake ba"

"Allah kadai ya san halin waye ya dauko, ko kuma shi ya kirkiro halinaa ba"

"Ba Mamaki, ka san yaran zamani abubuwa suke na Allah wadai"

"Allah ya kyauta Gwaggo, bari na tafi na karya ban yi breakfast ba, kuma Daddy ma yana son magana da ni"

"Tohm a fito lafiya, Allah ya maka albarka"

"Ameen"

Ya amsa sannan ya fice falon ya nufi bangaren Hajja Yelwa. Sai da yayi knocking sau biyu sannan ya shiga, daman ya saba haka gudun kar ya shiga ya tarar da abun da ba daidai ba.

Dawood ya dago ya kalleshi ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya kalli Ayra da ke watsa masa wani irin kallo fuskarta dauke da murmushi.

"Sannu da zuwa, ina kwana?"

"Da ban kwana ba zaki gan ni.?"

Ta yi murmushi.

"Hajiya tana bangaren Alhaji a kira ta?"

"Na ce miki gurin Hajiya na zo?"

Nan ma ta yi murmushi, shi ma murmushin ya mayar mata sannan ya nufi dinning, tana ganin haka sai ta tashi ta bi bayansa tana tafiya a hankali. Kasa kasa Dawood da ja gudun tsaki da bakinsa dake ta warin hayaki ya mike tsaye ya bar falon yana jin haushin kanwar tasa.

"Breakfast zaka yi?"

Ta tambaya tana bude Warmers din da Hajja Yelwa ta siya gurin Khadeeja Candy, kamshin farfesun kayan cikin na dukan hancinsa. Ya kalleta

"Eh Wlh, yunwa nake ji sosai"

Ta fara zuba masa, sai da ta hada masa komai sannan ta ja kujera ta zauna ta inda ita da shi za su fuskanci juna, sai wani lumshe ido take tana budewa ga kamshin humurar yar Fillo da ta saka ta gama cika masa hanci.

Ba zai yi ba karya ba, Ayra na daga cikin dalilin da ya saka yake son shigowa bangaren Hajja Yelwa, domin tana ba shi kulawa yadda yake bukata, tana nan nan da shi, ga shi yana jindadin yadda take kallonsa kan azo kan murmushinta.

"Ba ni labari"

Ya katse shirun dake tsakaninsu. Sai ta aje wayar hannunta ta dan sosa gefen hancinta.

"Labari."

"Uhm-mm, ina da ina kuka je satin nan?"

"Kawai daga Kano, sai Lagos, sai Abuja to Lagos, then Lagos to Abuja"

"Kina son aikin nan ne kawai, amman sam be dace da mace ba"

"Akwai aikin da ya dace da maza be dace da mata ba?"

"Uhmmmm kamar dai wannan, kin san ba kowane namiji yake son ace matarsa tana yawo ba, zai kawo maganganu, da tasgaro akan neman aurenta ko auren ma"

Ta dan wara ido.

"Yana daya daga cikin dalilin da ya saka na samu tasgaro a aurena na farko, domin mutunen da na aura ya so ya hana ni cikar burina, sai kuma aka yi rashin sa'a bana son sa"

"Yauwa daman ina son na miki wannan tambayar, miyasa kika aure shi bayan kuma kin san baki son shi?"

Ta motsa baki.

"Hajja ce ta tsaya kai ta sai na aureshi, kasan idan an fi karfinka dole ka yi hakuri"

"Shiyasa auren be yi karko ba, duka duka be wuce wata bakwai ba"

"Watan na bakwai ma ai a nan gidan..."

Ya yanke zaren zancen data dauko sakamakon hango Hajja Yelwa da ta yi ta shigo falon. Ariz ya juya ya kalli inda take kallo.

"Ariz, ka zo kuma ba a kira ni ba?"

"Ayra tace zata kira ki, na hana daman breakfast na zo yi"

Da ido Hajja Yelwa ta yi ma Ayra alama da ta tashi a gurin, ba musu Ayra ta mike tsaye ta bar dinning din Ariz ya bita da kallo, domin ta cika mace, kuma ta kai a kalleta.

____________________

Masu karatu me kuke hasashe? Bari na ga masu zurfi tunani. 👌