GUMBAR DUTSE

G_D - 13

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

Follow me on Facebook

***

My Novels Group

***

Follow Me on Tiktok ***

Follow me on Instagram

***

Follow on Wattpad ***

Follow me on Whatsapp

***

My Business group

***

All @Khadeeja Candy

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣3️⃣

Bayan ya gama cin abinci sai da ya taba hira da Hajja Yelwa kadan, sannan ya shiga bangare Daddyn, a can kan ya dauki lokaci sosai suna jira da tattauna abubuwa, da hira ta yi dadi Daddy ya mikawa Ariz hannu suka taɓa,kowane yana dariya. Kai kace sa'anin ne suke hira ba uba da ɗa ba. Daddy baya cikin irin mutanen nan sa suke kunyar yayan ko jin nauyi mu'alama da su, dukan yaransa yana rayuwa da su babu tsanani, balle kuma Jawad da yake namiji, wani abun ma sai idan shi Jawad din ya ki, domin shi ne baya sake jiki da mutane, amman duk da haka Daddy babu ruwanka, shiyasa tasa ta zo ɗaya da Ariz domin Ariz wayayyen mutum ne mai son barkanci hira da nishadi.

Daddy yayi tari yana kallon Ariz dake ba shi labarin abubuwan da be sani ba.

"Kai mutumena, wato Ariz baka da kirki wani lokacin, shiyasa duk abun da aka ce ka yi bana musu"

Ariz ya bude baki.

"Aa Daddy toh kar fa azo ace na kashe wani ka yarda, Wallahi ba ni ba ne"

Daddy ya girgiza kai yana murmushi.

"Kasan Allah yau da zabbaɓi na tashi ina jikin nawa ba dadi, amman hirar nan da muka yi na ji jikin yayi sauki, na samu gwarin guiwar fita, Allah ya maka albarka Ariz"

"Ameen Daddy, amman da ka zauna ka huta ai, ko na iya yau, tun da Jawad zai wakilceka"

"Ai abun ba daya ba ne, na tura wani ne, akwai biyu da zan je, kasan talaka ba shi da hutu"

Ya fada yana mikewa tsaye. Ariz ya girgiza kai ya san Daddy na fadi haka ne kawai as covering up amman zancen talauci kan ai be taso ba.

"Haba Daddy Haba Daddy"

Daddy yayi murmushi.

"Yaro ne kai ba zaka gane ba"

A haka suka rabu, sai da ya isa gida sannan ya kira Adda Sa'adatu, da fari bata daga ba sai after kiran ya yanke sai ta biyo da nata kiran.

"Doctor ka kira bana kusa"

"Eh daman na sani tunanin haka, yanzu na fito gida Daddy yake fada min Jawad zai yi aure"

"Dazun ai kamar zan kira ka, sai kuma yara suka dauke min hankali, daman akwai wanda nake son hada su, ina yarinyar nan da na yi maka magana kwanan baya?"

Ya saka wayar a speaker sannan ya cire rigar jikinsa.

"Amman kina ganin Hajja Yelwa zata yarda? Ace gata kin nema masa mata"

"Ji wata magana Ariz, Hajja Yelwa ita ta haife shi ne? Mace da bata san zafinsa sai dadi har ta isa tace ita zata nema masa mata? Wallahi Tallah ba zan yarda ba, wato ta nema masa mata ta malleke matar kamar yadda ta mallake shi ta mallake ka kai ma"

Yayi dariya.

"Yanzu kuwa ban fito ba sai da na ci abinci"

"Ai shiyasa duk abun da tace baku musawa, har wacan uban ganin kowa ba daidai yake ba, amman indai abu na Hajja Yelwa ne baya musawa, ai duk ta barbada muku kun cinye, zuciya ta mutu, tohm Wallahi daga kai har shi babu wanda zan yarda ta nemowa mata, kara ma ku sani tun yanzu"

Ta katse wayarta, daman ya san za'a rina, wai an sace zanen mahaukaciya. Adda Sa'adatu ba kasafai ake zancen Hajja Yelwa da ita akare lafiya ba, yadda ta tsani Hajja Yelwa ko mutuwarta bata tsana haka ba. Wanka yayi ya shirya sannan ya fice daga gidan nasa da yake zama shi kadai sai sabon mai gadin da ya dauka.

BATULA POV.

A tsanake take tafiya, har ta iso bakin kofar gidan Malam Haruna Sabo, rike da sakon kudin da Baba Salisu ya bata a hannu. Ta shiga gidan ta gaishe da kowa da hannu tana murmushi domin dariya ya yanke mata, ganin take kowa kallon yar iska yake mata a kauye, alhalin wasu ma ba su da labarin abun da ya faru.

Ta yi alama da Malam Haruna take nema.

"Aiko yanzu ya fita duba shi waje, aiko ki aka yi ko?"

Matarsa ta tambaya tana wankewar karamar yarta kashi, Batula ta daga kai sannan ta juya ta fita, daman ba a saba bata sako ta ba wani ba, ta fi sha'awar danka sako ga mai shi musamman wannan da yake na kudi.

Fitowa ta yi gidan ta nufi inda take san zata same shi, daf da zata karya kwana wani yaro ya ya fito kadan ya rage su yi karo.

"Batula wai Baba Sabo yace ki zo, gidan Malam Arzika mai akuya yana jiranki"

Batula na jin haka ya dagawa yaron kai ta cira kafarta da babu talkami ta fara sauri har da hadawa da gudu ta canja hanya domin gidan Malam Arziki mai Akuya, yana yamma da gidan Malam Haruna Rabo. Ta yi tafiya mai dan nisa kadan sannan ta iso gidan dakin dauke da ginin laka,(kasa) sai Ɗakin wajen gidan da ya zama na dansa ne kawai aka yi ma ginin zamani na bulo da gambun kwano, shi ma filista ce kawai aka yi ba ayi fenti ba.

"Batula."

Ta juyo bayanta, sai da yi arba da mutumen da ta zo nema.

"Kudin ne ko?"

Ta daga kai, tana gaida shi, irin yadda take gaishe da manyan mutane, sannan ta taba gemunta alamar Baba ne ya aiko ta, ta sake yin alamar gida ta mika masa kudin da hannu biyu.

"Tohm, shi.. Shiga.. Nan dakin ki aje can gurin filo, sai ki fito idan na gama abun da nake zan shiga na dauka, kudin Tanko ne na ara"

Sunan Tanko kawai da ya fada sai da gabanta ya fadi, domin Mutunen da aka kira da Tanko ba yaron kirki ba ne, kusan kowa ya san haka a garin, ko wace irin mace fadawa yake, ko ya san halinsa na lalata, ita kanta bata tsira ba, ya taba gwada mata ta yi a wani can baya a dandali. Ta juya a hankali ta kalli kofar dakin dake bude an sako blue labule mai layi-layi.

"Dakin a bude yake, shiga ki aje ki fito mu tafi"

Tana maganar yana waige waige cikin hikima kamar mai tare mata kar mutane su gani.

Ta sake juyowa ta kalli Malam Haruna Sabo, a zuciyarta tana jin kamar bata aminta da hakan ba, amman bakinta baya iya musawa, 'Shiga ki aje, ki fito mu tafi'

Tun da har zai jirata, ai zata iya shiga ta aje kudi ta fito, ko da wani ya ganta tana da wanda zai shaideta, domin ana fada wani sa'in har cikin dakin nasa na waje, yake shiga da yan'matan da suka siyar da darajarsu. Malam Haruna kamar uba yake a gurin domin aminin Malam Salisu ne, indai har ba zata iya musawa Malam Salisu Abu ba to be kamata ta musa wa Malam Haruna ba, daman can musu ba dabi'arta ba ce. 'Hanzarta shiga ki aje ai kudi ba wani abu ba' ta ji kamar an rada mata, sai ta hada da gudu ta karasa bakin kofar dakin, kai ta fara zura ta kalli dakin dake a kimtse irin na samarin kauye sai kamshin turaren tsintsiya yake, ganin babu kowa a ciki ya saka bata kwarin guiwar shiga dakin ta nufi gurin katifar da aka lullube da sabon zanen gado, ta daga filon ta saka kudin ta maida, tsakanin juyowarta da rufe kofar dakin da aka yi ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. Sai ganin mutum ta yi tsaye a gabanta sanye da gajeren wando jikinsa babu riga.

Daga idonta, har bakinta da numfashinta rawa suke lokaci daya. Yakowa yake a hankali yana kallonta fuskarta dauke fa mugun murmushi, baya baya take tana girgiza masa kai, tsoro da fargaba na saka zuciyar zillo kamar zata fado. Ta juya da sauri tana kallon gefen dakin, ta matsa can tana hade hannayenta ta roke shi, tun da bata da murya balle ta yi ihu a kawo mata dauki. Matsawa yayi baya ya tsaya daidai kofar dakin yana kallonta.

Ta yi masa alama da ya barta ta tafi, idonta na cika da hawaye, zuciyarta na hararo mata Malam Haruna kwankwaso ko ya turo kofar dakin, amman shiru, har na tsawon mintuna goma sha biyar, sai magiya take masa, shi dai be ce mata komai ba, kuma ba matsa daga inda yake ba, kuma bata ga alamar zai bata hanya ta wuce ba.

Sai zuciyarta ta fara raya mata ko dai yana zaton ta zo masa sata ne, domin a lokacin da ta daga fillo ta ga wani kudin a aje gefe tare da kwalbar lemun roba guda biyu kowane an sha an raga. A take ta gamsu da shawarar zuciyarta, ta nuna masa katifar saitin da fillon yake, ta girgiza masa kai, domin bata da bakin yi masa bayani, be zama lallai kuma ace ya iya kurmancinta ba, sai ta nufi gurin ta daga filon ta dauko kudin da ta kawo jikinta na rawa har wasu na zubewa ta nuna masa, wai ya fahimci kudi ta kawo ba sata ta zo ta masa ba. Sannan ta hade hannayenta ta durkusa kasa tana rokonta ya barta ta tafi, nan ma be ce mata uffan ba, kuma be yi wani yunkuri ba. Ta fara dukan ginin dakin da hannayenta, wai ko za'a ji a taho.

"idan baki daina ba zan tsaba miki"

Ta janye hannu ta da sauri. Tun tana tsaye har ta sulale kasa ta zauna, haka ta kwashe kusan mintuna arba'in a dakin, babu abun da take sai hawaye, tunaninta gaba daya ua kulle, ta rasa dalilinsa na tsareta adakin, shi be bata hanya ta wuce ba, shi be ce mata komai ba kuma be taba ta ba. Hayaniyar mutane da ta fara ji ne yasa ta mike tsaye da sauri tana jin wata kalar Rahama na rabarta a tunaninta sauki ya zo mata.

"Ina take yar iskar yarinyar"

Saukar furucin da ya tsare rabin kwarin guiwarta.

"Aa ai karka bude, ka bari mutane su ga komai, yarinyar tana kokarin bata sunanta, shiyasa sai kananan maganganu ake a gari, muna musawa saboda mun san irin tarbiyar da muka ba yarinyar, ashe ta watsar"

Karara ta ji muryar Malam Haruna Sabo, bata san ta kai kasa zaune ba, har sai da ta ji tafin hannayenta duka biyu shimfide a ledar tsakar dakin. Ta kalli hannunta na dama, ta dago na hadu ta hada su ta rike, sai kuma ta dago ta kalli Tanko dake tsaye yana kallonta, shi kansa fuskarsa ta canja, ai ko ɗan iska baya son ace ɗan iska ne shi, balle har a kama shi.

Batula na kallonsa wasu zafafan hawaye suka sauko mata, Hayaniyar mutane tun tana jin mutum biyu uku har ta ka kasa fahimtar muryar kowa. A lokacin da aka fara banko kofar dakin ne ya matsa daga kofar

"Ta so ki wuce"

Ta sake dubansa, irin duban da zuciyarta ke iya fassarashi, sannan ta mike tsaye tana jin abun kamar mafarki, kamar ace wani tsuntsu ya zo ya dauke ta, ko kuma kasa ta rufe da ita, a bude dakin ba a ganta. Da wane ido zata kalli kowa, yanzu ta ya zata fara bayani? Waye da waye a waje? Ya rayuwarta zata kasance bayan duk wannan? Me Musa zai ce? Kawayenta? Umma Hindu? Waye zai bata amsar tambayoyin da zuciyarta ke ta aiko mata? Haske bude dakin da Tanko yayi ne ya cika bubushin idonta da hawaye ya cika.

"Tanko ashe baka da mutuncin? Abun ya wuce, matan ko'ina da ya zo ga yarmu?"

Tanko ya kai kasa yana dafe kai.

"Baba ayi hak'uri dan Allah, sherin shedan"

"Sherin shedan ko son zuciyarku? Tun yaushe kuke wannan abun? Wane irin lalacewa ce wannan? Har a cikin gidanku?"

"Dan Allah Malam Haruna bar maganar nan, ba abun da za a tattauna ba ne, ai idan bera da sata, daddawa da wari, munduwa ɗaya bata amo, ni daman tun tuni nake jin maganganu sama sama akan yarinyar nan, amman ban ce komai ba saboda ina jin kamar kazafi ne"

Cewar Baba Gali. Malam Haruna ya daka mata tsawa.

"Wuce mu tafi yar iskar banza da wofi"

Batula ta daga kai ta kalli Malam Haruna ido cikin ido, abun da bata taba ba. Hawaye ya cika idon. Malam Arziki Mai Akuya na shigowa ya kaiwa ɗansa duka.

"Kai kai babu ni babu kai yau, ka hada komai na ka ka bar min gida, ka zubar min da mutumci, ka zubarwa da uwarka, yau sai ka bar gidan nan, saboda me zaka kawo yarinya a nan ka lalata mata rayuwa, haka ka zama Tanko? Yaushe ka lalace? Ka ja mana abin kunya a gari"

"Baba ka yi hakuri dan Allah ka yafe min, ba ni na lalata mata rayuwa ba, ban kawo ta nan ba sai da amincewarta, shi ma sherin shedan ne da yardar Allah hakan ba zai sake faruwa ba"

Batula ta lumshe ido wani hawaye na dabam mai hade da dumi ya sauko mata, zafin kalaman Tanko ya saka ta ji kamar an saka takobi an rabata gida biyu. Hannu ta ji an fisgo da karfi ya janyo ta zuwa waje.

"Wani kukan zaki tsayawa mutane, bayan kin zubar da mutuncinki, har baiko an miki amman saboda baki da kunya kin iya daukar kafafuwa ki zo dakin saurayi, kwadayi, kwadayi mabudin wahala"

Ya jefota wajen dake cike da mutane, ta mike tsaye jikinta na rawa sosai har tana tangadi, kamar zata fadi, kunyar abun da bata aikata ba ya hana ta daga ido ta kalli mutanen dake ta assha da halinta, wasu kuma suna dorawa Tanko laifi. Bata san dalilin Malam Haruna na shirya mata wannan abun ba, kamar yadda bata fahimci me zai saka Tanko yayi kokarin shafa mata bakin fanti a jama'a ba, sai dai babban abun da bata fahimta a yanzu da take tsakiyar mutane? Me yasa suka taru? Waya fada musu tana nan? Bata tana ganin an yi haka ga kowa ba, ciki har da sananun matan da aka san sana'arsu kenan balle ita.

Malam Arziki dake ta kaiwa ɗansa duka a dakin yana kuka, ya fara kwaso kayansa yana watsowa waje, Tanko dai yana cikin dakin be yarda ya fito ba.

"Dan Allah ka kyale shi, yana da laifi amman ita ai ta fishi laifi, tun da ba karfi yayi mata, da yarda ta, har fa lemu suka sha suka rage gashi can a dakin, daga sako Batula?? Sako fa na ce Rabineni ya aikota ta kawo min, shiru shiru babu ita babu labarinta, har na fita da kaina na tafi, sai yace ai ya aikota, na dawo gida Zulai tace ta shigo amman ta fita, na fito nemanta ko'ina ban ganta ba, ashe ashe ita ta samu guri ta shige, sai na sake komawa can gurin Mai Gari, muna zaune fa sai jin muka yi bakin labari, wai an ga Batula ta shiga dakin Tanko ga mutane can suna jiran fitowarta"

Batula ta sake dubansa, tana jin ina ma zata iya magana? Bata taba bakincikin rashin sautin muryarta ba irin yau, bata taba jin kunya ba irin yau, bata san ɗacin bakinciki na hakika ba sai yau. Me ta yi? Wa ta tarewa wani abu? Bata da murya balle ta yi bayani, bata da shaida balle ta nuna. Ta daga kanta tana kukan da babu sauti sai hawaye.

"Allah kai ne shaidata, ka sani ban aikata ba, kuma ka gani sun zaluncin ne, ban san waya shirya ba, ban san wa na yi ma wani laifi ba, amman dai sun rufe duk wata kofar farinciki a gareni yau, sun wulakanta, sun saka min tufafi da b bawa ba, sun dilbiyani cikin kazantar da ba tawa ba, ALLAH KA ISAR MIN!!!"

Tana addu'ar tana daga hannayenta sama, duk wanda ya ganta ya san akwai abun da take son baki ya furta amman ba dama. Tassss ta sauke kanta tare da zazzafan marin da Alhaji Haruna ya kai mata a fuska, take bakinta ya cika da jini wani irin zugi da azaba suka rufa mata fuska.

"Aa aa karka dake ta, ai doka be magani, sai addu'a, jata mu tafi gida"

Cewar daya daga cikin dattijan da suke tsaye gurin.

"Wannan ai sai dai wani gidan domin Mai Gari ya fi karfin zama da wannan yarinya yanzu, da mutumcinsa da komai, sam ba zai yiyuwa ba"

Ya ja hannunta da karfi, suka fara tsarawa ciki mutanen da suke tsaya wasu ma yanzu suke zuwa. Batula ta daga ido tana kallon mutane hawaye na mata zuba, hancinta ya cika tab da majina sai ta baki take samu numfashi, ga bakin kuma yana zubar da jini. Batula ta hada ido da kawayenta biyu Kande da Basira, kowane su yana kuka, Sai ta girgiza wa Basira kai, alamar ban aikata ba, sai kuma ta fashe da wani irin kuka mai karfi, da ace tana da murya da kowa ya ji ihunta a ranar yau. Ta fisge hannunta daga rikon da Malam Haruna yayi mata ta fadi kasa kamar mahaukaciya, ta fara zana rubutu tana son ta fadawa mutanen abun da ya faru. Amman wa zai karanta? Wa yake da lokacinta da har zai tsaya ta gama rubutawa, ta goge ta cigaba da rubutun har karshe? Ba kowa zai yarda da ita ba idan ma ta samu damar hakan, sunanta ya riga ya bace, ko da kuwa ace ketta mata haddi Tanko yayi da karfi, irin jama'ar da aka tara mata ta san ya sauya kaddarata, Gobenta ta lalace.

Ta kaiwa bakinta duka da karfi jini ya sake zubo mata, ta saka hannayenta duka biyu tana dukan bakinta da wuyanta, yau ta ga amfanin iya magana, a yau ta tabbatar ita nakasashiya ce kuma ragaggiya, ta so ace a yau ta ɗandana dadin da yake cikin ni'imar murya. Ashe ayi maka magana ka iya bude baki ka amsa rahama ce, a yau ta ɗanɗana bakinciki da takaicin dake tattare da rashin murya, jan numfashi take da karfi tana jin kamar ta aro sauti ta isar da sakon gaskiyar yadda komai ya wakana, wata kila ko ba duka ba, wasu za su yarda da ita, ta shiru kasar gurin da kafafuwanta, ta debi wata da hannayenta ta watsar tana hawayen da su kadai suke iya sanar da bakincikinta.

"Wani nade tabarmar kunya da hauka duk ba naki ba ne, ta shi mu wuce gida"

Ya sake kama hannunta suka nufi hanyar gida, mata sai taka katanga ake ana lekowa daman abun tsegumi be kadan a kauye, ko da kuwa karami ne balle babba.

"Baba Baba, tsaya a tambaye ta, da yarda ta shiga ko da karfi yayi mata"

Wani matashin saurayi dake rataye da kwashen noma a kafada, ya biyo Malam Haruna yana fadar hakan.

"Dan Allah ku bar wannan maganar, wanda aka aiko gurina me kaita unguwar nan ma? Kuma ko da karfi yayi mata waya ce ta shiga dakin? Balle ma ba maganar yau ba ce, yara fa suka zo suna fadar an ganta ta shiga"

Malam Haruna be tsaya ba yana ta jan hannun Batula da karfi kamar wanda be san inda ta fito ba, kafufuwanta sai birgima suke cikin kasa saboda hawaye ya hanata ganin hanya. Matashin yayi tsaye yana ta kallon Batula kamar be yarda ba. Masu son ganin kwan suka rufa musu baya, mata wasu har da lullubin zane, kadan ne masu hijabai da gyale, ana tafe ana tsegumi, wasu na mamaki wasu na gasgatawa wasu na fadar daman sun ji kishin-kishin, wasu kuma na shaidar Zur...

________________

Drop your opinions....