G_D - 14
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢
Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***
Follow me on Facebook
***
My Novels Group
***
Follow Me on Tiktok ***
Follow me on Instagram
***
Follow on Wattpad ***
Follow me on Whatsapp
***
My Business group
***
All @Khadeeja Candy
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣4️⃣
"Do you have an appointment with him?"
"Uhm..."
Ya amsa ba tare da ya bude bakinsa ba, gaba daya ya cika gurin da kwarjinsa da kuma kamshin turare, kai kace sauran duk ba mutane ba ne. Ta duba computer dake gabanta cike da kwarewa da kuma sanin makamanar aiki, ta sake duban Jawad.
"May I know your name, or the name on the appointment, sir?"
Ya ciro tsadaddiyar wayarsa aljihu ya yi rubutu ya juya mata ta kalli wayar.
"Abdullahi Wambai"
Ta karanta sannan ta sake maida hankalinta gurin system din sannan ta dauki wani karamin kati ta yi rubutu akai, few seconds ta dago ta kalleshi.
"You may go in, second floor, right-hand side, last office. All the best, Sir."
Ya nufi hanyar bayan ta mika masa wani karamin kati, sai ya saka hannunsa daya aljihu dayan kuma rike da karamin katin. Da ya isa inda ta fada masa sai tura kofar office din da ya kasance na glass ya shiga, sai ya samu wani namiji zaune a ciki, gefen teburin mutumen kuma kofar wani office din ne. Mutumen da ke zaune a office din yayi ma Jawad maraba da zuwa.
"Thank You"
Ya fada sannan ya mika masa karamin luxury card din. Mutumen na dubawa, sai ya mike tsaye. Kalli computer dake gabansa yayi rubuce rubuce sannan ya taba wani red button dke gefen teburi, few seconds button din yayi blinking twice in green color.
A take ya dago kai yayi ma Jawad umarni da ya shiga. Jawad ya nufi office din ya tura kofar ya shiga with full confidence.
Raheen Turaki yana jingine jikin kujerarsa yana kallon Jawad har ya iso gaban teburin, wayarsa kuma a speaker yana wata tattaunawar kasuwanci da wani. Jawad be tsaya an taya masa ba, ya zauna a one of the visitors chairs, Raheem Turaki ya dago ya zauna daidai tare da miko masa hannu.
Jawad ma ya mika masa nasa, suka gaisa.
"I will call you back, Mr. Clinton. I'm about to go into a meeting now."
Ya aje wayar, sannan ya mike tsaye yana duban luxury wristwatch dake daure a tsintsiyar hannunsa.
"A cikin kowane lamari na rayuwa, da kasuwancina, ina martaba lokaci, domin shi ne kadai abin idan ya subuce wa mutum baya dawowa"
Ya zagoyo ta inda Jawad yake zaune, idanuwan Jawad suna biye da shi fuska ba yabo ba fallasa.
"Ina son ka dauki sabon karatu, a yau"
Ya karasa yana dafa kafadar Jawad din, sannan ya taka gaba kadan kamar zai tafi.
Jawad ya juyo ya kalleshi cike da izza.
"Mahaifina ya bukaci na wakilce a nan ne saboda mu tattauna abun da ya shafi kasuwanci, ba sanin muhimmanci lokaci ba"
Raheem ya yi murmushi
"Karka damu, zan koya maka duka..."
Ya fice ba tare da sake cewa komai ba, haka Ma Jawad be kara wata kalmar ba, kokarin rike kansa yake ya san idan har zai sake furta wata kalamar a yanzu ba alheri ne zai fito daga bakinsa ba. Gudun lalata alakar dake tsakanin mahaifinsa da wannan mutumen dake kokarin kureshi ya saka dole ya hade bacin ransa.
Ya kalli agogon hannunsa, he is just 15min late, ya san darajar lokaci saboda ya zauna da turawa ya san yadda suke bawa lokaci muhimmanci, amman nan da can ai akwai banbanci, yan Afrika ba su san wannan ba.
Sai yake ganin kamar Raheem Turaki yana kokarin wulakanta shi ne kawai.
Yana dago kasan a hankali, yalwataccin idanuwansa da ba kasafai ake ganin irinsu a gurin namiji ba, suka sauka akan hoton wani karamin yaro dake aje kan teburin. Yaro ne da ba zai wuce shakara ɗaya, ya kurawa hoton yaron ido sai kuma yayi murmushi kadan, ya tuna da nasa mahaifin, har a yanzu da yake da girma Daddy yana da hotonsa a office dinsa, hotunansa yana karami zuwa matashi har yanzun da yake saurayi.
Can kuma ya bi office din da kallo, kusan sai da ya tantance komai na cikinsa sannan ya ciro wayarsa ya gwada tabawa, na tsawon mintuna talati sai kuma ya dago ya mike tsaye ya fito daga office din.
"He said you should wait for him until he comes out of the meeting. He will be back."
Jawad na fitowa, mutunen dake tsaron kofar ya fadi haka. Jawad ya hade yawu da karfi yana dan cizon bakinsa. Yayi ma mutumen alama da pen, sai ya dauko biro da paper da sauri ya ba shi, Jawad ya karba yayi rubutu a kai sannan ya aje paper a gurin da pen din ya fice cike da izza.
After like one hour da ficewar Jawad, Turaki ya shigo tare da wata, PA ya bashi sakon da Jawad ya bari.
"Mutumen da ka bari a office be tsaya ba, amman dai ya bar wannan sakon a baka"
Turaki ya karba.
"When he returns, tell him he wasn't worth my time"
Ya kebe baki bayan ya karanta takardar ya jefar da ita a kasa, ya kalli budurwar, da irin kamaninsa ne a fuskarta.
"ɗan iskan yaron nan ne fa Jawad, Kin kara ganin halin nasa ko? Gaba daya yaron nan ba shi da mutunci, Wallahi ba dan mahaifinsa ba ni ko kallo be ishe ni ba, haka fa yayi min lokacin da kuka samu tsabani, na kira ina son jin ba'asi sai cewa yayi kar na sake kiransa, mahaifinsa baya bata lokaci gurin ganawa da kowa, daman ya fada min jikinsa ba dadi Jawad zai zo a madadinsa, saboda ya san gurina zai zo shi ne ya bata min lokaci da jiransa har na mintuna goma shabiyar"
Ya karasa yana jan tsaki, sannan ya nufi office dinsa. Matashiyar dake sanye da black abaya rike da takardu ta juya ta kalli kofar fita office din, kamar mai tunani, sai kuma ta juyo kan takardar da Turaki ya jefar ta kura mata ido, harafi bayan harafi take karanta rubutun Jawad, sai kuma ta risina kasa ta dauki takardar ta rike a hannunta, ta maida numfashi a hankali sannan ta nufi cikin office din Turaki.
"Na bata kusan 15min ina jiransa, ya shigo kenan uzuri ya kamani, sai na ce ya jira na dawo, yanzu haka shigowa ta kenan office din, ban same shi na sai sako da ya bar min wai ban cancanci lokacinsa ba, haka ake rayuwa? Wallahi ba dan kai ba Alhaji, ba zan ma bata lokaci ina jiransa ba"
Ta nemi guri ta zauna tana sauraren wayar da Turaki yake, guntuwar takardar boye a hannunta.
"Shi kenan ya wuce, Ameen Ameen"
Ya aje wayar ya kalleta.
"Ki koma da takardun kawai, tun ya tafi daman abun da za mu tattaun akai ne, kuma ya nuna min halinsa na rashin mutunci"
Ta kalli Turaki, sai dai bata ce komai ba ta tashi ta fice rike da takardun.
JAWAD POV.
Daddy ya sauke wayar daga kunnensa zuwa aljihunsa.
"Ka kyauta kenan? Na turaka saboda ka wakilce irin wakilcin da zaka min kenan.? Wani kasuwanci ne dake tsakanina da shi na million of naira, yanzu da ba mutum ne mai fahimta ba, zamu iya samun matsala akan haka, saboda ni nake neman kulla alaka da shi ba shi yake nema na ba"
Jawad ya ja numfashi a hankali ya sauke.
"Zan gyara Daddy, ayi hakuri"
Daddy yayi murmushin jindadi.
"Allah yayi maka albarka, idan baka gyarawa ai kaima kanka sai ka cutu, domin abokanai hulɗalka ma sai ka ga suna ja baya, domin ita duniya ko da kai ko babu kai zata cigaba kuma komai na lokaci ne"
Jawad ya jinjina kai, alamar gamsuwa.
Hajja Yelwa dake tsaye a gafe ma ta yi murmushi.
"Haka ake so, tafi ka huta daman Daddynka ya zo ya wahalar da kai ne kawai, amman ina kai ina irin kasuwanci shi"
Jawad ya juya daga balcony din ya nufi bangarensa yana jin kamar ace Turaki yana kusa da shi a yanzu. Daddy ya fara saukowa daman yana shirin fita ne Raheem Turaki ya kira kawo karar Jawad din da shi ma be dade da dawowa ba saboda akwai tazara daga unguwarsu zuwa unguwar da companyn Turaki yake, wannan dalilin ne ya saka suka yi Lati shi da Driver da Daddyn ya saka ya kai shi, amman Turaki be masa uzuri ba, saboda yana da cikinsa a zuci.
"Alhaji mijin Hajiya, dan Allah ka rika lallabawa da Jawad mana, wannan fadan yayi yawa"
Tana maganar murya a tausashe cike da kirsa.
"Idan ma baya son tafiya, ko shiga mutane irin wannan ba ga Dawood nan ba? Kasan Maina fa ba son shiga mutane yake ba, wanda magana ma sai an yi kamar ana yi balle kuma kace zaka rika turashi cikin mutane, amman ga Dawood nan zai iya maka komai da yardar Allah"
"Ina turashi a irin abubuwan nan ne, saboda ina son rayuwarsa ta canja, ya zama mai son shiga mutane, saboda yau da gobe sannu a hankali so nake ya maye gurbin abubuwa da yawa nawa, domin aikinsa na yanzu kusan irin kasuwncina ne, kin ga banbanci kadan ne"
"Toh amman ba ga Dawoo...."
Bata karasa ba, Daddy ya daga mata hannu.
"Dan Allah ki daina min maganar Dawood, yarom da be iya komai ba sai Shaye shaye, kina sane da yadda yaron nan yake min barnar kudi, shiyasa na canja masa gurin aiki, tohm irin wannan zan dauka na tura ya wakilce ni a guraren kasuwanci? Ai sai na ji kunya ma"
Daddy ya fada ransa a bace ya shiga motar da direbansa ya dade da bude masa.
"A dawo lafiya, Allah ya tsare"
Ya amsa da ameen, tana tsaye gurin da murmushi har aka fice da shi sannan ta juyo ta koma ciki, Cup din da ya sha tea da shi a falon nasa ta dauka ta nufi bangarenta ranta a bace, tsabar bacin rai da cup din a hannu ta shiga dakin Ayla.
"Kullum bacin rai kuke saka ni a gidan nan"
Ayla dake kwance tana chatting ta dago ya kalleta.
"Me ya faru.?"
"Miye ma be faru ba? Gaba dayanku ba ku jin maganata ba ku daukar shawarata, saboda me na kawo ku a gidan nan ba saboda ku amfana ba, amman sam ba ku gani, ke kin butulce min babu yadda ban yi ba ki karanta kasuwanci ko aikin office, kika ki ke ala dole sai flight attendant kike son zama, haka yaran nan kowa na taro sai yace ga abun da yake so, ita wannan ta karanci likita, ita wannan nurse, ita wannan ta zabi bangaren jini, sai kace masu cutuka a a gida ko gado, shi kuma wannan dana samu ya karanci kasuwancin ya maida kansa wani iri shaye shaye nan tun ba a sani ba har an sani a yanzu, saboda me mace take son ta dace da gidan aure ba da saboda ta janyo yan'uwanta su dangwali roman arziki ba, yayanta kuma su samu, amman babu mai ba ni hadin kai kullum cikin saka ni bakinciki kuke"
Ayla ta tashi zaune da kyau.
"Adda Yelwa, kina son saka kanki a damuwa ne kawai, ban san miyasa kike son dole sai mun shiga cikin dukiyar Alhaji ba"
"Baki ga yadda sauran yayansa suke wadaka ba? Komai su yake sakawa babu ni babu yan'uwana babu yayana"
"tohm ai kowa yana da abun yi, dama ace ba mu da abin yi ne shi ne zamu damu, sauran yayan da kike magana kuma yayansa na cikinsa ba bare ba, kuma su biyu ne ba wasu da yawa ba, yau ko mutuwa yayi gadon da zaki samu ke da yayanki ya ninka wanda su za su samu, to miye abun ta da hankali a ciki? Yaranki biyar fa Adda"
" Lallai na tabbatar da baki da hankali a yau, ko kuma dai kurciya ce take damunki? Wa yake lisaafi gado? Ke baki san Jawad shi kadai zai dauki kashin mace biyu ba? Firdausi da Hannatu? Sa'adatu ce kawai zata dauki kashi ɗaya, da Harira, amman a yanzu ga shi nan suna ta ci a dukiyarsa, ita wannan Sa'adatun da bata kaunata ba da shi ta jingina ta yi arziki ba? Jawad din ma na shi ya kashe masa kudi ba har ya kai inda ya kai? Ai ni yarana ba su mori wannan ba, idan abu za su siya matukar mai tsada ne sai sun bi ga karkashin mahaifinsu ko kuma ni, amman su fa? Sa'a ai har korin arziki take min, Jawad idan be cin ma mahaifinsa a kudi ba ya kusa, gashi komai na duniyar Jawad yake sakawa, Allah kadai ya san irin abun da zai samu kamin ya mutu, shikenan ni dan ban haifi namiji ba sai ace ba zan mori arziki ba? Kyauta wannan mai tsoka rabon da ta shiga tsakani da Alhaji tun last year, amman yayan yan'uwansa matarsa ko watan can da wuce sai da shegiyar tsohuwar can Gwaggo ta saka ya siya wani gida, amman ni nawa ai ba yi musu yake ba, mata bata raye amman har yanzu kishi take da ni saboda an masa muguwar mallaka"
With so much confuse Ayla ta ce
"Tohm yanzu ai aikin gama ya gama, me kike so a ayi?"
Ta aje cup din a kasa sannan ta zauna saman gadon kusa da kanwarta.
"Ayla ke da Dawood kusan a gidan nan kuka karasa girmanku, musamman ma ke nake saka rai, kina kallom yadda nake ta kai da kawo akan mu samu rayuwa mai kyau, Alhaji ba irin sauran mutane ba ne, yana wadata komai, amman dai ba yadda nake so ba, musamman ni ba wani son yi min alheri yake ba, daga ke sai yaran nan ne za ku share min hawaye, su kuma ba jin maganata suke ba, kananan kuma har yaushe suka gama karatun secondary suka shiga jami'a ai za a dade, amman ke kina da sauki kai da fahimta, me zai hana ki aje aikin nan naki ki koma makaranta ke ma ki karanci kasuwncin nan ko na shekara biyu ne ki yi diploma, Sai ya shigar da ke cikin abubuwansa, ki duba fa ki gani babu abin da na sani a game da kasuwancinsa, idan ma zai tattauna wani abu sai dai yayi da wadacan, yau idan ya fadi ya mutu, ai wata dukiyar ma ba su fadi inda take ba"
Ayla ta saka dariya tana mamakin yadda idon yar'uwarta ya rufa, ta san akwai kishi ita tana taya ta, domin bata son duk wani abun da ya shafi uwargidan Alhaji, amman bata yi zaton tunanin Addarta ya kai har haka ba.
"Ai ba shikenan ba, yanzu kin ga Alhaji dazun ya fada min, Jawad ya amince zai yi aure har yace a nemo masa mata"
Ayla ta ja tsaki.
"Tohm shi ne me? Jawad din ɗan gwal ne da ake ta murna saboda yace zai yi aure? Kar yayi auren mana wa yayi ma kansa, ni ko a karance karance-karancen novels da nake ban taba ganin inda ake ta murna saboda wani ya amince zai yi aure ba, idan ma be yi aurenba ina ruwan wani?"
Hajja Yelwa ta saki baki tana kallonta cike da takaici.
"Wai miyasa kika tsani Jawad ne? Amman nan Ariz ya shigo kina ta watse masa hakora kamar kofar gari"
"Muna da kyakkyawar fahimta da Ariz ne"
"Shi kuma Jawad mummunar fahimta kuke da shi? To sannu Malamar Darasi, to ki yi dai yi a hankali domin uwar Ariz aminiyar Margayiya ce, kina kallo Maryam ta mutu amman har yau idan Hajiya Binta bata min magana, kuma duk abun da ya tashi a gidan nan indai ya shafe ni bata taba zuwa, gurin wacan tsohuwar ma idan ta zo har ta fita bana sani, wata rana ma sai dai ta aiko a dauketa taje can gidanta ta wuni, duk wata hidima da uwa ko kishiyar uwa zata shiga ta yi, ta tare min ita take yi ma Sa'adatu, Jawad ne kadai ya ki bata hadin kai, shi ma kuma ba kyale shi ta yi ba, to irin wannan matar har kina da lokacin ɗanta? Kuma shi Jawad din da na samu kansa yake ba ni girma yake saurare kike ganin zan yarda na rasa haka daga gareshi? Ke baki ma ganin yadda arziki ya taso masa yanzu?"
Ta daga kafadunta.
"Ina ruwana da arzikinsa?"
"Ina nuna miki hanya idanuwanki da kwalwarki na toshewa"
"Ni ba zan sake yarda a karkata tunani ba, kowa yana da ikon yayi rayuwarsa yadda yake so, haka kika saka ni auren tsoho sa'ar kakana saboda kawai yana da kudi, gashi nan ya maida ni karamar bazawara"
"Mtawsssssssssssss"
Hajja Yelwa ta ja dogon tsaki ta tashi ta fice daga dakin cike da wani sabon takaici.
BATULA POV.
Yana isa bakin gaban gidan Malam Salisu ya jefar da ita kasa da karfi gaba jama'ar dake zaune a shimfidar Malam Salisu.
"Yarinya dai ta lalata kanta da tarbiyarta, kuma ta janyo maka abun kunya a gari, domin kara ace wani gurin aka aikata shi ba gidanka ba"
Malam Salisu ya taso cikin wani yanayi dake nuna bacin ransa ya karaso inda Batula take zube a kasa ya kama hannunta.
"Ba a biyewa zuciya, tunanin babban da yaro ba ɗaya ba, be kamata ka mata haka ba"
"Ranka ya dade, wannan yarinyar ai har kai bata bari ba, Wallahi kazafin da ta yi maka a garin nan kuma ta fara yada shi idan ka ji ranka ba zai so ba?"
"Malam Haruna ai babu komai tsakanina da Batula sai alheri, tsawon shakarun nan na kula da ita na mata tarbiya iya yadda zan iya, sai idan wani halin ta dauko waje dabam na gida ba"
Malam Murtala ya taso daga inda yake zaune yana fadin.
"Tohm Wallahi ni ma na ji, abun dai babu dadi, ana ta rade radi"
Ta kai bakinsa kusa da kunnen Malam Salisu cikin girmamawa ya rada masa a abu a kunne, a take yanayin Malam Salisu ya kara sauyawa sai ya hade rai sosai ya girgiza kai yana sake hannun Batula da yake rike da shi.
"Ai babu, komai a tsakanina da Batula sai alheri, abun da kike ta fada kenan Batula? Bata min suna kike son yi? Me ya same ki haka? Amman da yake gaskiya ta yi halinta ai yanzu kowa ya gani"
Babu abun da Batula take sai hawaye idonta gaba daya ya kumbura kwayar ta yi ja kamar an watsa mata barkono, sun zagaye ta sun rufe duk wata hanya ta zata bullo aga haskenta. Anan wasu suke fadar ai har cewa ake ma wasu bakin dake zuwa gurinsa shi yake turata gurinsu.
Malam Salisu ya sallami kowa sannan ya saka aka dauko masa Batula daga waje domin bata iya ma takawa da kafarta tsabar kuka ya ci karfinta, aka shigo da ita cikin gidan, aka aje ta gaban kofar Umma Hindu, sannan ya aika a kira masa Musa da Kawunsa. Babu bata lokaci Musa ya iso tare da Kawunsa wanda shi ne ya wakilci mahaifinsa gurin nema masa auren Batula.
Cikin yanayin damuwa da bacin rai suka iso gidan, Musa na sanye da riga dabam wando dabam irin na mutanen karkara.
Malam Salisu yayi musu izini suka shigo har cikin gidan, aka ba su gurin zama, sannan ya aika yarsa ta kira Umma Hindu da tun da abun ya faru take cikin daki bata fito ba.
Daker Umma Hindu ta fito daga dakin nata ta zauna bakin kofar ɗakinta, idonta na zubar da kwalla tana tarewa da tsohon zanen atamfar da ta lulluba da shi.
Malam Salisu yaja numfashi sannan ya mikawa Musa da Kawunsa hannu suka gaisa.
"Ko da yake dai, abun ba na gaisuwa ba ne, lamarine da be yi ma kowa dadi ba"
"Bari bari ai babu dadin fadi Ranka ya dade, ni ganin nake kamar ma ba gaskiya ba ne"
Malam Salisu ya sauke ajiyar zuciya yayi jimmmm.
"Tohm, Allah dai ya kyauta, ni dai na kira ku nan ne, saboda saukin nawa nauyin, Batula dai gata can ta jawa kanta abun kunya, ko ince ta janyo mana"
Duk suka kalli Batula da kanta yake cikin cinyoyinta tana ta sharbar kukan da ba shi da sauti.
"Kuma abun ba ita kadai ya shafa ba, domin ni duk bayan wannan abun da aka ce an kamata tana aikatawa, ni kam a da na shirya zama da ita, sai dai radin radin da na ji ana ta yi a gari na kazafin da ta yi min ko aka sakata tayi saboda ta bata min suna, ko kuma aka janyo min sauka daga wannan sauratar, tun sa makiya suna da yawa, kuma mutane da yawa suna jin haushin yar sarautar nan da nake kai, suna jira a sauke ni a ba su, ba zan yarda makiya su min dariya ba, dan haka ni yanzu na cire hannuna daga duk wani abun da ya shafi Batula, shiyasa na kiraku na fada muku, yau din nan zata bar gidana, dan haka idan ka ji zaka iya da lamarin aurenta to sai ka bita can gurin danginta, daman dai ni ban hada komai da ita ba, matata ce ta hada kuma ita ma zamanta yau ya kare a gidana, idan har ka ji kana sha'awar hada zuri'a da ni, to akwai yara sai ka duba wanda zata maka, idan kuma Batula kake so, sai ka bi ta can gurin dangin ubanta ko uwa, ni dai ba zan iya ba, na yi iya abun da yake nawa"
Tun a lokacin da ya ambaci saki Umma Hindu ta zabura, dafe da kirji tana kallonsa.
"Zama fa ya kare ka ce Malam, me kake nufi? Ga yara ga komai saboda dan wannan abun da ta aikata? Ai kanta ta aikatawa ba wani ba"
Malam Salisu ya kalleta a hankade. Batula ma ta dago da sauri, tun da ake ta juya zancen bata dago kanta ba sai a yanzu da maganar Saki da kuma kora ya shigo ciki.
"Abun da ta aikata ne kike kiransa da ɗan? Hindu? Shiyasa ai nace zaman mu ya kare, domin babu yadda za'ayi ace ta yi duk wannan abun ba tare da saninki ba, dole ba zaki rasa sani ba, waya san ma ko tare da ke ake bata min sunan a gari? Ko kuma ke kike turata gurin mazan? Saboda kin raina ni, gashi sam bana jindadin zama da ke, ga fitina, yarana ba za ki je da ko ɗaya ba, ni zan rike abuna"
Kawun Musa ya fara kokarin shiga tsakani, sauran matan kuma babu wacce ta hana, sai ma kara zugawa da Altine take.
."Wannan hukuncin da ka yanke yayi daidai, saboda yarinyar tana zuwa da kudi mai yawa ta kawo mata, ko baki aka yi sai ta kawo kudi mai yawa, idan an yi magana tace su suka bata, ita kadai ce ƴa a nan ne kullum ita suke bawa? Ita ma ai ta ci amana saboda ta ga ba yartaba ce shiyasa ta lalata"
Umma Hindu ta buga kafa a kasa.
"Ahayye nananaye. Altine idan aka sake ni sai ki zuba ruwa kasa ki sha, ai inda Malam ne ke ma baki wuce ya sake ki ba, mutumen da be iya komai ba sai aure aure"
"Tohm kin ga halin naki ko? Shiyasa na ce zamun mu ya kare, ki tafi gidanku na sake ki yarana kuma zan rikesu, ki kwashe duk abun da yake naki ki bar min gidana ke da Batula"
Kalmar da ya furta ta saki ta saka Umma Hindu tabbatar da abun da Malam Salisu yakr fada.
"Ka saki ni Malam? Kace ka sake ni? Karka manta ka taba min saki biyu baya"
"Ina sane, zan aiko miki da takardarki"
"Haaaa, Salisu ka yi ma makiyi abun da suke so, ka sake ni ko? To ka sakowa kanka bala'i da masifa, Wallahi sai ka yi nadama, ba kana ganin ka sake ni ka huta ba? Ai baka huta ba, mu zuba ni da kai"
Malam Salisu ya kalli Musa.
"Musa zaka iya tafiya, daman dai na kira ku ne saboda na sauke nauyi na... Idan kuma..."
"Aa Ranka ya dade, ni kawai na hakura da Batula, Allah ya bata wani, daman ni ma ina ta jin maganganu amman bana son yarda, kuma wannan abun kunyar ina zan kai shi ko na ce zan aureta.?"
Batula na jin haka ta taso da sauri ta nufo inda Musa yake zauna tana girgiza masa kai, bata ko san lokacin da ta rike hannunsa da karfi ba, wasu zafafan hawaye na sauko mata.
Ta dage sai bayani take masa da yarenta na kurmanci, so take ya fahimce ta yayi mata uzuri.
Da fari kallomta yake cike da tausayi domin yana sonta, sai dai kuma tuna da yadda garin yake da kuma mutanen cikinsa, ya saka ya fizge hannunsa.
"Kina kurma Butula, na rufa miki asiri zan aureki, ashe ke ba yarinyar kirki ba ce? Miyasa zaki yi ma kanki haka? Haba Batula"
Ta girgiza kai tana ta masa alama da ba haka ba ne da hannu.
"Ai ta ci riba, ko ni ba zan baka shawarar aurenta ba, tun da ni ma gashi ta kashe min nawa auren"
Cewar Umma Hindu, Batula ta nufi gurin Umma Hindu ta rike kafafuwanta har bata gani da kyau, Umma Hindu na matsa baya zata janye jikinta, Batula ta fara maganar da ita daga zuciyarta tana jin ina ma ace zata jita.
"Ban aikata ba Umma Hindu, wani sheri ne aka shirya min, ke uwa ce kin san halina tun ina jaririya ke kika rike ni, dan Allah ki yarda da ni, ki yi tunani ki shaidai ni, Ya Allah ka saja mata wannan tunanin a zuciyarta, kowa yaki ya fahimci kowa ya ki yarda da ni, kaicona ni Batula kaicona...!!!"
Bata ankaro ba ta ji an fisgota, wata Yayar Umma Hindu ce dake aure kusa da su ta iso saboda an labarta mata abun da yake faruwa, Inna ta rike duka hannayenta biyu ta jefar da ita kasa.
"Sakarkar banza, kin bata tarbiyar ki kin janyo mana abun fadi, kina kurma kin kara janyowa kanki bakinciki"
Batula ta rike ce a kasa ta rasa kafar wa zata rike ya fahimce ta, ta dago daker ta bi fuskokinsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
"Yanzu, ba za ku yarda da ni ba? Har da kai Musa? Inna Zali ke ba baki yarda da ni ba? Umma Hindu yau dai ba zaki min uzuri ba? Haka za ku min Baba? Baba Altine, Baba Larai, babu wanda zai yarda da ni?"
A zuciyarta take furucin da ba zata iya furtawa da baki ba. Ta sunkuyar da kanta hawaye na diga wasu na bin wasu kamar saukar ruwa.
" Batula...!"
Ta dago ta kalli saitin da take jin muryar kawarta Basira, sai dai hawayen bakin ciki sun tare ganinta bata iya ganin fuskar kowa a yanzu. Ta ji ya rikota ana kokarin rabata da kasa da take zaune.
"Wallahi duk kazafi ne da sheri, Bafula bata aikata ba, shirya mata aka yi, saboda ana tsoron asiri ya tonu, Wallahi Batula ba yar iska ba ce"
Take Umma Hindu ta fara zagin Basira tana fadin duk su suka lalata mata tarbiya...
Inna Zali ma ta saka baki. Batula ta kama hannayen Basira ta janyo kawarta zuwa kasan da take zaune ta rumgumeta da karfi ta kamkameta ta runtse, tana jin wani irin yanayi a zuciyarta da bata taba samun kanta a ciki ba....
___________________
Bayan ni waya ji tausayin Batula?
Wacece yarinyar da Raheem Turaki yake fadawa Jawad ne ya zo?
Kuna ganin akwai mace mai irin halin Hajja Yelwa?
Tsakanin Hajja Yelwa da Adda Sa'adatu waye zai nemawa Jawad matar aure? Kuma da wa zai aminta?