GUMBAR DUTSE

G_D - 16

by @khadeejacandy

***

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣6️⃣

Ta kai hannu ta share hawayenta tana jin mafarkin kamar zahiri, ta daga kanta tana kallon gurin inda take kwance, wani abu ne da ba za a kira shi da daki ba, ba kuma buhu ba, ba gidan sauro ba domin baka ganin wanda ke waje, kuma bata da tabbacin na wajen ma baya ganinta ko akasin haka, ta kalli fitilar kyaldir din zamani da aka kunna wanda ta haskaka karamin gurin.

  Sai gabanta ya soma faduwa, a ina take? Satota aka yi? Yaushe ta zo nan? Waya kawo ta? Ta fara tunanin inda bachi ya sace ta, idan bata yi kuskure ba, kamar da hudun magariba ta yi bachin, amman gashi dare yayi a nan, kuma tana cikin wani abu mai kamar buhu, ko dai mafarki take? Ta sake juyawa ta kalli ko'ina, gashi ba wani mai fadi ba balle ta mike tsaye a ciki. Ganin kamar bata da mafita ya saka ta koma ta kwanta, can kuma ta ji bata natsu da hakan ba, ta sake tashin zaune.

Ta fara lalaben ko'ina na karamin tintin da take ciki, kirjinta na bugawa da karfi, numfashinta na fita da sauri, ta fara buga abun tana girgiza shi, kyakkyawan idanuwanta suna ta zagaye abun da yafi kama da buhu a kwakwalwarta, a lokacin da ta hango zip a jiki sai kuzarinta ya karu, jikinta na rawa ta soma zukeshi tana yin sama da shi har ta bude gurin gaba daya, a nan ta lura ashe wata hanya ce da zata sadarda ita ga duniyar da ta sani, amman ba a gurin da ta sani ba, ta fara lekowa ta kalli ko'ina na harabar da ba zata iya shaidar ina ba ne, hankalinta ya fi karkara a gurin shimfidar data hango nesa da inda take, wata halitta ta gani, zaune kan karamar shimfidar lullube da hijabi, fuskarta na kallon wani sashen ta bata baya, hasken filitar dakr gefenta ne ya bata damar fahimtar mutum ne kamar ita, banbancin kawai ita a yarinya ce, wacan kuma kishiyar haka.

   Bayan ita babu wani abu da idanuwanta suka iya gane mata, sai tarin duhun dare da ya hana tunani hasaso mata inda take. Ta juya ta sake kallon gurin da ta farka bachin dazun wani babban zane ne mai kama da bargo aka shimfida mata, sai wani karamin filo dake saitin da Inda kanta yake, ta juyo ta sake kallon hallitar da take kyautata zaton mace ce, dai dai ko za a kasheta ba zata iya fadar waye ita ba, a dazun da ta ganta Sallah take a yanzu din ma haka. Bata bukatar umarni ko shawarar aikata abun da zuciyarta ta raya mata cewar shi ne daidai, dan haka ta saka kafarta waje a hankali, ya fito tana takawa kamar wanda zata yi sata ta nufi gurin da take kyautata zaton hanya ce, ta fara tafiya tana batar da sautin kafarta, a wayonta idan ba ta ji takun tafiyarta ba, ba zata san tana ciki ba ko ta fito.

Tafiyar bata yi nisa ba, tsoron dake cikinta ya bunkasa, bugun zuciyarta ya karu, ita ta bar nan din ita zata je? Bata san hanya ba, bata san me zai sameta a hanyar ba, idan kuma ta koma bata san waye wacan mutumen ba, aljani ko mutum, taimakonta zai yi ko cutar da ita? Ta ya ta samu kanta a nan? Ya zata fita? Amsoshi da bata san wa zai amsa mata su ba. Ta juya tana hango matar da sai a yanzu take sallame sallah. Bata yanke shawara ba, kafufuwanta suka soma dawowa da ita gurin da suke ganin nan ne mafita.

Ta tsaya nesa da ita tana kallonta zuciyarta fal da tsoro, cikin hikima da jarumta irin ta marasa tsoro matar ta juyo ta kalleta.

"Zaki yi Sallah? Ko cin abinci? Miye sunanki?"

Ta girgiza mata kai a hankali hawaye na cika idonta.

"A Hanya na tsince ke, ina tare da direbana, zaki iya tafiya gida idan kina so, yanzu aka yi Isha'i"

Yadda zata fada mata cewar bata iya magana, ba ta san inda take ba, balle ta gane hanya shi ne aiki a gurinta.

"idan kika bi nan, ki mike tsaye karki karya kwana, zaki bulla garin Sabau, ai zaki gane idan da zaki tafi ko?"

Ta daga mata kai, a ranta tana ayyana mutane irin wannan matar ba su da yawa, masu fahimtar mutum tun gabanin yayi bayanin abun da yake bukata. Ta hade hannayenta biyu ta mata godiya, sannan ta nufi hanyar gabata yana faduwa tsoron hanya, ga tsoron abun da zata je ta tarar ya cika ranta, gashi bata da tabbacin gaskiya matar ta ya fada mata ko saɓanin haka.

Tana gudu tana share hawaye har ta fara hango hasken gari da mutanen dake kai da kawo, kamar motar da aka karawa giya haka ta kara cira kafa ta isa bakin kasuwar garin dake kusa da dandali.

Gudun a dauke ta mahaukaciya ya saka ta ta kaita gudun da take tana ta haki, yanayin garin irin yanayin nan ne mai dadi da babu zafi babu sanyi, amman hakan be hanata hada gumi ba saboda fargaba da wahala, hankalinta be kwanta ba har sai da ta ganta bakin kofar gidan kasar da kakaninta da iyayenta suka mutu suka bari, ta daga kauren kofar da shi ne madadin ganbun kofar saka kafarta ta hannayenta rumgume a kirji, a zauren gidan ta fara lebewa ta zura kanta zata leka sai aka hasko fitila das sai kan fuskarta.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah Batula..."

Matar data haske ce take maganar tare da tasowa ta nufo kofar, Batula ta yi baya zuciyarta na raya mata dukanta za'ayi.

"Shigo, karki fita ko'ina babu abun da za'ayi miki"

Kallo ɗaya zaka mata ka karanci tsoron da yake bayyane a fuskarta, matar ta karaso ta kama hannunta.

"Ga Batula ta iso, Alhamdulillah"

Wani Dattijo dake zaune yana sharbar tuwo shi ma ya haskota.

"Batula, Allah mun gode maka, waya kawo ki? Hankalinmu duk ya tashi Hindu ta ce mana ta bar ki a hanya"

Wa zata ce ya kawo ta? Bata san me Umma Hindu ta fada musu ba, kar su ma su yi mata fahimta baibai, domin ita ma bata san matar da ya rage mata dogon zangon tafiyar da take ta fargabar yi ba.

"Kila wani ne wanda ta sani dan can garin ko?"

Ta daga kai da sauri tana amsawa ɗayar matar data taso ita ma ta iso gurin ta tsaya.

"Tohn ai Hindu ta isa barka, sai a fada mata ta dawo ga Batula ta zo, Wallahi da yarinyar bata iso ba, da sai na ga wanda ya tsayawa Hindu a garin nan, hankali duk ya tashi mun aika nemanki Batula, abincin nan ma ci kawai nake ba dan yana min dadi ba, zo nan"

Sun jefata a duniyar tunani da tambayar kanta, ko dai Umma Hindu bata fada musu abun da ake zarginta da aikatawa ba?

"Ita ma ai Hindu ranta ne ya bace har ta aikata haka, mutuwar aure ba wasa ba, ga kuma abubuwan da suka faru"

"Dan Allah Maijidda karki kara bata min rai, shikenan dan aurenta ya mutu abubuwa sun faru sai ta bar yarinya a hanya? Yaushe hannunka yake rubewa ka yanke ka jefar? A hannunta fa yarinyar ta tashi, bata saba da kowa ba kamar yadda ta saba da ita, ko lalacewa tarbiyarta ta yi wa za a zarga ba ita ba? Yarinya ba uwa ba uba, ga lalura da take tare da ita, mazan yanzu kuma da suke lalattaci daman mai iya maganar ma ba su bar shi ba balle ita, a duk rashin kula da saka ido ne, kuma Batula yarinya ce karama a hukuntata a mata fada, amman zancen kora saboda me? A koreta ta je ina? Wannan abun ma ai ba tarbiya ba ne sam ba, indai haka ne baku iya tarbiya ba"

Batula ta ji wani abu mai sirkin sanyi ya raba jikin zuciya, ko da ace Baba Auta ya yarda aikata uzurin da yayi mata ya isa ya kwantar mata da hankali, ta san Kanen kakan nata da fada Sosai, amman bata yi zaton idan abu ya sameta irin haka zai mata uzuri ba. Wanda ke rike da hannun Batula ta ce

"Ita kanta Hindu ta manta baya ne, yadda suke da margayiya, ko mutum Batula da yanka be kamata ta mata haka ba, dan na tabbatar da yarta Hindu ce ta aikata haka, Margayiya ba zata mata haka ba"

"Kin gani Talatu, raba kanki sa shiga lamarin Hindu, kin san bata ragawa kowa, ba dubin zata yi matar yayanta kike ba yanzu ne sai ta ci miki mutunci"

Cewar Baba Maijidda, Wanda aka kira da Talatu ta tabe baki. Baba Auta ya matsar da turen silver dake dauke da kwanonin samira gefe.

"Zo ga abinci ki ci"

Batula ta kasa matsawa har sai da Baba Maijidda ta isa da ita gurin tana rike da hannunta ta zaunar da ita. Baba Auta ya matsa matada tray abincin.

"A karo miki?"

Ta girgiza kai, bata jin ma zata iya cin abincin domin yunwa ta bace mata gaba daya, kallon tuwon dawar kawai take da koriyar miyar kuka.

"Ungo, a kaiwa Lawai ya nemo number Malam Dahe ya fada masa Batula ta iso ya dawowarsa"

Ya ciro wayarsa a aljihu ya mikawa wata karamar yarinya dake kusa da shi.

"Ita kanta Batula ai ta iya boka, ka bata wayar ta duba lamba Malam Dahe"

"Oh haka ne, Batula dubo number Malam Dahe, zaki ganta an saka hoton kwallo, akwai mai ice ba ita zaki taba ba, mai kwallo"

Ya mikawa Batula, ta karbi Nokia ta shiga duba numbers ta kamo ta danna kira sannan ta mikawa Kakan nata.

"Saka min lasifika, ba a aji sai an saka lasifika"

Batula ta saka hands-free ta mika masa, tana zaune shiru tana saurarensa har yayi wayar ya gama, sannan ta saka hannunta a tuwon ta fara ci bata dan tana jindadinsa, loma daya biyu ta cire hannunta, zata sude sai ga Umma Hindu ta shigo gidan tare da wata kanwarta da suke uba daya, kowa bata cewa uffan ba ta nufi wani dakin kasa zata shiga.

"Ke Hindu zo nan"

Ta yi kamar bata jin kanen mahaifin nata dake kiranta ba, ta masa banza ta shige ciki, tana shiga sai kuma ta fara bala'i.

"Ai saboda Ba Farida ko Shatu ba ne aka kashewa aure, su da suke yayanka, shiyasa baka ji bakinciki ba, auren shekara goma sha tara an kashe min dare guda, wai na dawo gidan ubana gidan gadonmu kace wai sai bar gidan saboda na baro wacan shegiya nakasashiyar munafuka, tohm Sai na gani a gidan nan idan matsayinmu ɗaya ne, ai Wallahi da na sani ma ba zan fita ba, ai ni ma ina sa gado a gidan"

Babu wanda ya taya ta, daman kuma Hausawa sunce munduwa ɗaya bata amo, Baba Auta ya san halinta ba zai yiyu ya rika sa'insa shi da ƴar ɗan'uwansa ba, Matan gidan kuma babu wanda ta ji zata iya bata yawun bakinta a yau.

"Batula, ta so muje daki"

Baba Auta ya dakatar da Inna Talatu.

"Aa can dai dakin da Hindu ta zauna zata zauna, kar ma ki soma yin abun da zai raba su, idan ta ga dama ta kashe ta, ai yar kanwarta ce, jininta ce, idai aka kika yi ba daidai ba dole mu yi magana tun da ba ke kika haifi kanki ba, kuma ba ke kadai kike da ikon da ita ba, ai dubin alakarku da margayiya da kuma ganin kamar kina cikin rufin asiri ya saka yarinya tun tana jaririya aka baki ita, kin san ba zaki iya ba kika tara hannu kika karba?"

Ya juyo gurin Batula.

"Ke kuma ki kama kanki, dabi'un da aka ce kina yi a can karki kirkire su a nan, kar na ji kar na gani, kuma fita ma idan ba ta aika ba karki ki yarda na ga kafarki a waje, na fada miki?"

Ta daga kai da sauri, tana jin ina ma ace idan suka ji gaskiyar abun da ya faru su yarda da ita. Tsoron abun da zai je ya dawo ya hana Batula shiga dakin da Umma Hindu take na kasa ta kwana, sai Baba Maijidda ce ta kawo mata tabarma kaba da mayafi ta karba ta shimfida ta kwana a gurin.

Sallah Magariba da Isha'i sai da ta zo Sallah asuba sannan ta rama su ta dora da asuba din, Inna Talatu dake can gefe tana dumamen tuwo ta ce.

"Batula, daga yau karki sake lattin Sallah, duk abun da kike da kin ji anyi kira ki aje ki yi sallah, kuma karki sake kwana baki yi sallah ba, idan mutum ya rike sallah akan lokacinta sai ki ga abubuwa suna zuwa masa da sauki"

Batula ta dago mata kai daga can bakin kofar da take zaune. Baba Maijidda ta soma magana da kamar rada.

"Ko fa lalacewa yarinyar nan ta yi Wallahi laifin Hindu ne, bata fada mata abun da ya dace"

"Unhm, ita dai Batula ai ta bata kanta, karamar yarinya haka ace ta san maza kala kala"

Inna Talatu ta fada, sannan ta cigaba da iza wutar karan, suna cigaba da tseguminsu ita da Baba Maijidda.