G_D - 17
***
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢
Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 1️⃣7️⃣
JAWAD POV.
Hankalinsa gaba daya ya tattara ya koma kan aikin dake gabansa, yana kallon wayarsa na ringing be daga ba har sai da ya gama abun da yake tsab sannan ya dauki wayar ya duba kiraye kiran da aka masa, kira biyu ya bi, na Ariz bayan ya gama waya da shi, ya kira yayarsa.
"Jawad, na kira baka daga ba"
"Uhm na gani yanzu"
"Yaushe zaka shigo?"
Ya dan yi shiru be bata amsa ba.
"Akwai maganar da nake son mu yi ne, kuma akwai abun da nake son nuna maka"
"Gobe....?"
Ya fada da sigar tambaya, saboda ya san if goben yayi mata.
"Tohn Allah ya kaimu"
Ta san yafi sha'awar fita da yamma dan haka bata bata lokaci gurin tambayarsa time ba. Ya aje wayar ya mike tsaye yana sauke gajiya, hamma ta biyo baya, idanuwansa suka sauka akan zanen da be karasa ba, na Batula da mutanen garinsu, yayi ta kallon hoton na dan lokaci kamin ya dauke kai ya fice daga dakin.
Wanka yayi ya shirya cikin kanana kaya ya dauko rike da keys a hannunsa sai kamshi yake, be samu Gwaggo a falo ba dan haka ya leka dakinta sai ya same ta rike da carbi tana ja, karamin plasma dake dakinta yana kunne tana ta kallonta hankali kwance.
"Gwaggo zan fita"
"Tohm a dawo lafiya, na san baka son ina tambayar ina zaka je, kar kace ina maka shishigi"
Yayi murmushi ya daga mata hannu, ya juyo ya fito ya nufi kofar fita falon, sai da ya biya ya dauki abokinsa Ariz sannan suka shiga gari, be dawo ba sai kusan goma, kamin ya dawo Hajja Yelwa ta masa kira uku na nuna kulawa wai ya dawo dare yana yi bata son yana dadewa a waje. A bangarensu yayi parking ya fito rike da ledodi ya shigo bangaren, har dakin Kakarsa ya shiga ya aje mata sannan ya fito ya shiga nasa dakin. Yana kokarin cire agogon hannunsa kira ya shigo, sai ya amsa ta apple watch din.
"Wai har yanzu baka dawo gida ba Son?"
"Na shigo gida yanzu"
"To ka zo ga abincinka yana jiranka"
"Na ci abinci gidan Momy, tare da Ariz muka fita, da muka kawo Momy ta kawo mana abinci"
"Tohm ai duk daya ne, can din ma ai gida ne, bari na bawa Ayla ta kawo maka tea"
Nan kam ba zai iya cewa aa ba domin shi masoyin shayi ne, sai dai kuma ba Ayla yake ra'ayin ta kawo masa ba, dan haka ya ce
"Hassana ko Husaina"
"Okay tohm"
Hajja Yelwa ta amsa ba dan ranta ya so ba. Sai da ta auna daidai lokacin da take kyautata zaton yayi wanka ya shirya cikin pajamas kamar yadda ya saba, sai ji yayi ana knocking kofar dakinsa, a zatonsa Gwaggo maybe take son yin wata maganar da shi, domin kanensa iyakarsu da shi falon basa shigo masa daki komai uzurin da suke da shi, suna shiga dakinsa ne kawai idan zasu gyara masa. Ya mike tsaye cike da mazantaka ya isa kofar ya bude, ga mamakinsa sai yayi arba da Ayla ita ma tana sanye da nata kayan bachin.
"Adda Yelwa tace na hauro har sama na kawo maka, su Husaina sun yi bachi"
Be karbi tea da take rike da shi da hannu biyu ba, kuma be ce mata komai ba ya maida kofar ya rufe. Wulakanci halinsa matukar aka tsaba da ra'ayinsa, yana daga cikin dalilin da ba kowa ke son shiga tsagensa ba. Haka ya kwana be sha tea ba, domin yana jin kuiyar hadawa kansa, kuma gashi be karba wanda Hajja Yelwa ta aiko masa ba.
Washe Gari, bayan yayi sallah asuba yayi addu'o'insa ya sake komawa bachi, be farka ba sai sha biyu har yan mintuna na rana, wayarsa ce farkon abun da ya fara dubawa, sannan ya tashi zauna yana murza ido, rabon da yayi bachi haka mai nauyi har ya manta. Kiran Hajja Yelwa ne har hudu, mika yayi ya mike tsaye yana dan wartsakewa sannan ya nufi bandaki, ya dade yana kallon kansa a madubin dake gabansa bayan ya dafa jikin madubin, manyan kuma kyakkyawan idanuwansa da suka yi ja sosai yake kallo, to him it's normal daman idan yayi bachi mai nauyi da tarin mafarkai ya kan samu kansa haka.
Ya kai hannunsa daya ya debi ruwan ta watsawa fuskarsa, sai kuma ya saka hannu biyu yana cikowa yana wanke fuskar, sanyayiyar ajiyar zuciya ya sauke, ya matsa baya ya cire tufafin jikinsa ya nufi shower ya bude ya tsaya ruwan na zuba masa tsakiyar kai suna saukowa jikinsa, sanyi ruwan na ratsashi har cikin zuciyarsa, ya hade yawu a hankali ya jima a haka, sannan ya murza tsadaden sabulu yayi wanka, bayan ya gama ya dora da wani wankan ya tsabtace kansa daga najasa sannan ya kai hannu ya dauki wani blue tawul, a zuciyarsa be yarda da tsabtar tawul din ba, dan kawai babu wani ne ya saka ya daura shi ya fito, farar riga da wando kawai ya saka be shafa komai ba ya fito dakinsa ya sauko, suka gaisa da Gwaggo.
"Yau bachin ya zagayo, ko baka da lafiya ne"
Yayi murmushi.
"Na fiki lafiya"
Ya nufi kofa ya fice daga apartment din ya nufi bangaren Hajja Yelwa, yana shiga falonta tana sauke waya daga kunne.
"Kai nake kokarin sake kira fa, gaba daya yau baka shigo ka karya ba, mahaifinka har ya fita"
"Na yi bachi ne"
Ya amsa mata kamar an amsa dole, daman idan yayi bachin ya tashi baya tashi da dadin rai. Yaja kujera ya zauna, Hajja Yelwa na tsaye bayansa zata kai hannu ta taba shi ya dan matsar da kansa.
"Lafiyata kalau Hajja, na saba irin wannan bachin mantawa kika yi"
"Tohm Allah kara lafiya, nikam hankalina ya tashi"
Ta zauna kusa da shi, sai da ya fara cin abincin sannan ta ce.
"My Son, dan Allah ba dan ni ba, ka daina nunawa Ayla kyama, ban jidadin abun da ka yi mata ba jiya, yaran nan duk sun yi bachi ita ma har ta fara na ce ta tashi ta hada tea ta kai maka har dakinka sai gashi aka karba ba ta dawo da shi, Ayla ai yar gida ce ba bare ba, kawai dan baka tashi tare da mu ba ne kake kallonta a dabam, amman a gidan nan ta karasa wayonta"
Be ce komai ba yana ta cin abincinsa kamar ba da shi Hajja Yelwa take magana ba.
"Tausayi ma take ba ni, yarinya da ita aure wata bakwai ya mutu, arzikinta ma bata haihu ba, kuma yadda take da kyaun jikin nan take gyarawa ko wata budurwa albarka"
Nan ma be ce uffan ba, kuma ba zai ce ba, ta dage tana ta fada masa wasu kyawawan halayen Ayla da be san da su ba. Ya zari tissue ya goge bakinsa, ya tada kansa ya kalli agogon GMT dake tsaye falon sai ya mike tsaye ganin lokacin sallah yayi.
"Ba na ki karbar tea da ta kai ba ne saboda ita ta kai, na ki karba ne saboda ta haura min har sama, and she knock my door"
Sai a yanzu ya bata amsa maganarta ta dazun, Hajja Yelwa ta yi wani murmushi mai hade da zungudin baki.
"Za a kiyayye ranka ya dade ɗana na kaina, zata gyara"
Ta bishi da kallo har ya fice, sannan ta taɓe baki.
"Har abada ɗan kishiya be taba zama naka, ji yadda yake wani bada umarni, da uwarsa ce zai yi haka? Kai Maryam bata koyawa yayanta tarbiya ba Wallahi, sun yi gadon bakin hali"
Ta karasa tana jan tsaki.
Sai bayan sallah La'asar, Jawad ya sake wani wanka daman ka'ida ne indai zai canja tufafi dole ne sai ya sabunta sabulu a jikinsa, ya fi sakewa a cikin kananan kaya musamman idan zai fita cikin abokai ko yan'uwa, Bakin wando ne ash t-shirt sai Facing cap Wanda ta kasance baka, talkaminsa ma baki, yadda yake bulbula turare sai ka dauka karar da kwalbar zai yi gaba daya, ya dauki wani oil perfume ya shafa a wuyan hannunsa ya hade hannayen ya murza. Daga wayarsa sai wallet da keys ya dauka ya fito dakinsa yana turawa kanwarsa sakon ta zo ta gyara masa dakin ta gyara bangaren kamin ya dawo.
"Ina za aje haka ango? Ga kamshi ga kyau"
Yayi murmushi.
"Gurin fitinanniyar jikarki zan je"
Yana fadar hakan Gwaggo ta gane Adda Sa'adatu yake nufi cikin dariya ta ce
"Yau zumunci za aje kenan, tohm hakan yayi kyau, a gaishe ta"
"Zata ji"
Ya fice kamshi na masa rakiya. Ya zabi motar da ta fi kowace tsada kamar mai kokarin bawa makiya tsoro. Sai da ya biya wani karamin super market ya siyawa yayan yar'uwa kayan tande tande sannan ya isa gidan, kida na tashi a motarsa kadan kadan, ga wani sanyi da ya cika motar mai kwantar da hankali.
Ya faka harabar gidan, ya kashe motar yana kallon kofar falon Adda Sa'adatu, a ka'ida idan ya zo gidan yaranta da gudu suke zuwa tarboshi shiyasa yake zuwa musu da tsaraba, amman yau shiru, be ga sun fito ba. Ya bude motar ya fito ya nufi kofar falon yana kai hannunsa da nufin budewa sai ya ga kofar a bude, ya shiga ciki yana san ran ganin yaranta.
"Sannu da zuwa, ka zo a daidai"
Cewar Adda Sa'adatu tana masa marhabun baki har kunne. Ko da wasa be kalli yarinyar dake gefenta ba har ya nufi kujera ya zauna. Sai dai an samu tsabanin ra'ayi domin tun da ya turo kofar falon ya shigo yarinyar take kallonsa har ya zauna.
"Zinatu.. Wannan kanena ne Jawad, shi ne wanda nake fada miki"
Yarinyar da sunanta ya dace ta kamaninta ta murmushisa tana bawa idanuwanta abinci a fuskar namijin da ya cika kuma ya kai, saboda siffarsa da zatin surarsa.
"Jawad, ga Zinatu baka santa ba amman dai yau ka santa, mun hadu da ita ne a Airport na Abuja, sai gashi kuma ashe yar garin nan ce"
Nan ma gogan be dago ba, sai raba ido yake yana son hango yaran Adda Sa'adatu.
"Zinatu ku gaisa mana..."
Ta dauki dakiku kamin ta iya furta gaisuwa muryarta na rawa.
"Ina wuni...!"
Jawad ya dago idonsa ya sauke cikin nata, sai ta yi hanzarin maida nata idon kasa, ya tsareta da kallo, ba irin ba kauna ko soyayya ba, ba na mamaki ko burgewa ba, wani irin kallo ne na kokarin kure gaskiyar mai karya, kallonta yake babu kyaftawa ita kuma ta gagara sake kallonsa tsayar da idonta guri daya ma ya gagara.
"Bari na dauko miki abu ina zuwa"
Adda Sa'adatu ta fada sannan ta mike tsaye ta shiga wani bangare na falon, shiru shiru bata fito har na kusan minti talati, kamar dai ta ba su guri ne su san juna. Jawad ya mike tsaye idanuwanta suka fara kallonsa daga kasa zuwa sama, lallai ta yi hasara kyakkyawan namijin da ko wace mace zata so ya kasance Jaruminta.
"Baka yi mamakin yadda Kaddara ta sake hada mu ba?"
Ya juyo ya sake dubanta, madadin da hango tsana, sai ta hango soyayya da kauna ta shekaru masu yawa.
"Haka kaddara zata yi ta sake hadamu, sai zuciya ta yi ta yaudararki, ki yi rayuwa da bakinciki"
Ya bata amsar cike da izza da isa, yana mata kallon tsana. Ya hade yawu da karfi, ta mike tsaye da sauri ta fice daga falon. Jawad ya dawo ya zauna yana jin kamar numfashinsa gurbacewa sakamakon arba da yayi da ita.
Bayan wasu mintuna goma Adda Sa'adatu ta fito rike da jaka, ganin babu bakuwa ya saka murmushinta gushewa.
"Ina yarinyar nan take?"
Jawad ya kalleta ya kalli inda Zinatu ta zauna kamar ba shi ake tambaya ba.
"Wani abun ma yi mata Jawad?"
Nan be ce komai ba.
"Na zama dole ka so ta ba, amman tana daya daga cikin yan matan da nake kyautata zaton idan har ma same ta zaka ji dadi, saboda kyakkyawa ce, tana da tarbiya, kuma yar masu kudi, idan baka maka ba zan iya duba maka wata daman su hudu ne, ban ma san zata zo ba, hanya ce ta biyo da ita ta nan ta biyo mu gaisa sai kuma ga shi ka zo"
Ya ciro wayarsa ya fara tabawa.
"Wulakanci ka yi mata Jawad?"
"Bata min ba a samu wata"
Ya amsa mata amman hankalinsa da idonsa suna kan wayarsa.
"Indai haka zaka rika wulakanta ni akan yan matan da zan samo, to sai na cire hannuna, domin na tabbatar idan Hajja Yelwa ce ba zaka mata haka ba, tun da ita ai baka mata musu, waya sani ko ita tace maka kar ka so matar da zan samo maka, tun da ka dauke ta ka maida uwa, gaba daya ka manta da irin zaman da ta yi da Mama, ka manta irin makirci da zalunci da take yi ma mahaifiyarmu lokacin da take raye, Mamanmu ta sa aka aurota amman cikin gidan mijinta aka maida ita shara, babu irin azabar da bata ganawa mahaifiyarmu ba... Amman duk ka manta"
Ta karashe cikin kuka. Jawad ya dago ya kalleta a tsanake.
"Ban manta ba, kuma ba zan manta ba, ita dai wannan yarinyar bana sonta ba saboda ke kika kawota ba, sai dan saboda ta ƙi a lokacin da nake sonta, na santa fari da bakinta, ke kuma dabi'unta, kyaunta da kudin gidansu kawai kika dogara, baki ma san wacece ita ba"
Ta share hawayen ta zauna.
"Kun taba soyayya da ita ne?"
Yayi shiru be amsa mata ba, alamar ba wannan tambayar yake son ta yi masa ba.
"Kai yanzu wace iri kake so? Ka san dai ba zan yarda Hajja Yelwa ta nemo maka mata ba, Momy ma sai da ta yi min wannan gargadin, kuma ba za a nemo yar karamin gida ba, dan ba zai yi mu narka dukiya mu kashewa yarinya ba a kawo mana ita babu abun albarka"
Ya mike tsaye ya fice daga falon, backseat ya bude ya dauko tsarabar yaranta ya dawo falon ya aje ya fita ya shiga motarsa yayi ficewarsa daga gidan gaba daya...
Hmmmmmm
Me kuke hasashe?