Chapter 30
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
Na gode Masoyana, kun sake karɓan labarin nan a karo na biyu godiya ga My Arewafanmily godiya ta gode sannan ina jinjina ga waɗanda suka kasa jira suka zo suka siya document duka na gode sosai Allah ya bar zuminci Amin.
*Ƙarshe..*
Haka Sunaima da Sulaiman suka cigaba da Renon Cikin jikinta Cikin Soyayya da aminci Duk wani gata Takowani bangare ba inda Sunaima bata gani ba Itakam sai dai ta kara godema Allah a kullun tayi sallah sai tayi addu"an Allah ya jikan Sunaira Allah ya haska Kabarinta har gaban Abada bazata ta taba mantawa da yar"uwanta ba.
Bata da wata damuwa Su Wasim dai da gaske sun zama ya"yan Baba da Inna Basama Damuwa yanzu Daga Sunaimar har Sulaiman sun daina Damuwa dasu ko sunzo gidan basa nuna Rigima Kamar baya in zasu tafi Har Bye bye suke musu sun Riga sun zama ya"yan Inna.
Ranar Har korafi Sunaima tayi mai Bayan sun dawo Daga gidan Inna Ranar Lahadi chan yakaita ta wuni Sai Dare yaje ya Daukota kallonsa Tayi yana Driving kafin tace"Saraki da gaske kabar ma su Inna yaran nan ko..?
Yana yar dariya yace"Eh mana kin Dauka wasa nake yi..Wasim da Wafiyya na inna da Baba ne,In kika Haifi mai sunan Maimartaba ko Fulani sai na barma su Hajiya su kuma kinga an raba ne ba Cuta ba Cutarwa..!
Tana Hararansa tace"In na Sake haihuwa kuma sai ka kaima Maimartaba ko..?
Yana Dariya yace"Kai Tanque Baby kin Tunamin ya kamata Maimartaba da Abba su samu kyakyawan Tukwaicin Auramin wannan Zankadediyar yarinyar ga Son girma ga Dadin zama ga baiwa ga Basira ga Dadin chan din..!
Sunaima Hararansa kawai take yi Shi kuma yana Dariya kafin ta kada kai Tana Fadin"Allah ya shiryamin kai Saraki..!
Hannunta ya rike da Hannu Daya ya Dafa Cikinta atare Daya Turo yace"Ameen Sunaimata..Allah ya Jikan Sunaira yasa ta Huta..!
Dukkansu Cikin wani yanayi suka kalli Juna kafin su amsa da Ameen Ameen Daganan sukayi Shuru har suka isa gida ba wanda ya kara mgana Daga alamun yau Mutuwar ta Dawo musu Sabuwa,barin ma Sunaima da sai da Sulaiman ya zauna yana Lallashi kuka ta sakamai wiwi kamar karamar yarinya.
Cikin Sunaima na Shiga wata na Shida komai ya Sauya Abaya Datake gudun Sulaiman yanzu kuwa tafi shi ma son abun Tun yana mamaki Har dai ya Fahimci Ciki ne ya sakata Haka,Bata gajiya yanzu Shine ma yake Tsausayamata Saboda Cikin Dake Jikinta ammh ita bata Tsausayin kanta.
In ya dawo yaga tazo ta Rabe Daga Jikinsa tana Kifta kananan idanuwanta da bakinta kamar kuma yadda yace zai fara Dariya yana jan Karam Hancinta Daya kara Girma Yana Fadin"Uhm an zo za"a Tsotsemin Ruwa jiki..!
Shagwabe Fuska take yi kamar Zatayi kuka tana Fadin"Ni ko Saraki..Bakomai..!
Sai yayi Fuska yana Fadin"Nan fa Daya..Nan a baya ina Binki kina min Wulakanci ni da Hakkina yanzu kuma kin ga ke keda Riba sai wani nanemin kikeyi ke gashi ba ke Kadai ba Ran Mutum Biyu ni Sulaimanu Ya kike so nayi da Raina kalli Wuyana sai Faman Bushewa nake yi a tsaye kamar karan Dawa..!
Yafada yana Tattaba wuyansa Sunaima Sai ta Turesa tana Fadin"Nima bani ke kawo kaina ba..Cikin ka ke kawoni..!
Yana Dariya yace"bawani yarinya..Salon wayau ne kina Fakewa da Ciki kina Tsotsemin Ruwan Jikina..!
Sai Sunaima ta fara Hawaye tana Fadi "Naji bakomai..Nima indai ina da Hakki aka Hanani mutum shi da Allah..!
Yana Dariya ya Rike bakinsa Tana kokarin Daga kafa Ya taddaota ta baya ya Hadata ita da Cikin ya Rumgume ya kamkame yana Fadin"Abun bai kai haka ba Gimbiyata..Wasa fa nake miki ke kuma baki bani kunyar tsokanata ba.Ni naki ne Har Abada Sunaima ba ruwan jikina ba ko Jinina na yarda Duk ki Tsotse Riban auran kenan Mata tafi Miji kokari..!
Yafada yana Tusa kanta Cikin Wuyanta Kokarin Zame kanta take yi Tana Fadin"Ni ka kyaleni..!
Cikin kwaikwayonta yace"Nidai A"a..Ban yarda ba sai an Turani kan gado an yi su..!
Bata bari ya karisa ba ta Juyo da Sauri Har Cikinta na amsawa tace"Na shige su Saraki..!
Yana Dariya yace"To in baki so na Karisa muje mu kashe Arna..Nifa ina jin Dadi fa..Kinsan bayan Darajan aure Duk iskancin Dan Bariki bai isa yaci mai Ciki ba sai Aure..Shi ke da wannan Baiwar..!
Yafada yana kai Hannunsa wata Jahar tana jinsa batasamu mgana ba illah Fadi datake"Bakin ka baya Haila Saraki..!
Yana kara kamkameta yace"Ina fa zai yi Haila..ai Haila sai Sunimaita mai Kayan Dadi..!
In tace zata Biyema Saraki ko Kwana zasu yi bakinsa baya Shuru sai tasamu Dama ta Hade bakinsu Waje daya suka fara bama juna Muradinsu Daganan Da tsayuwa ta gagara aka Koma aka Zube saman Cafet ysu anan aka ssha Shagali zaku sha mamakin yadda Sunaima taja duka Ragamar Tafiya ta Sarrafa Sulaiman yadda ya kamata Duk da Cikin Jikinta kamkameta yayi yana Hawaye Cikin Wata irin Murya yake Fadin"I love u Sunaima..Kada ki barni..Kada kema ki Mutu ki barni bazan iya rayuwa baki ba wannan karon mutuwa zan yi..!
Sai da ta Rufe mai baki itama kukan take Share share kukan Kauna Soyayya da Sadaukarwan kukan kaddaranta datajata zuwa wannan Babin ayau sai gasu dukkansu suna kamkame da juna suna Share ma juna Hawaye kauna da Sadaukarwa duk alokaci Daya.
To haka dai Rayuwar ta Cigaba da Tafiya sai da Cikinta ya shiga wata takwas sannan sukaje sukayi Siyayyar kayam Haihu kala kala Both side mace da namiji Duk an yi Scan ance Namiji zata Haifa ammh Saraki yace su ba Allah bane so ba yadda zasu Beliving kam abunda suka Fada.
Saraki yasa an gyarama Sunaima Shashen Sunaira na Upstair inda Laila ta Zauna Daman Alhaji isa yace ya bar mai Duka Kayan baya Bukatar ko Daya shi kuma bayason ya Ga wani abu Daya Danganci Laila yasa aka Kwashe komai aka maida BoyQuaters,aka sauya komai na Shashen komai Sabo nan Sunaima Zata Dawo da Zarar ta Haihu ita tace ma ya barshi ma Dakinta ya isheta yace A"a yagaji da Biyota gwara ta dawo kusa dashi,Dakin kuma bazasu manta dashi ba yana cikin Tarihinsu na Rayuwar auransu shi da ita.
Dole tayi shuru ta zubamai ido BoyQuaters ma ya gyara yace Sani Direbansa zai Dawo nan shi da iyalansa sannan magajiya ma da Samira chan zasu koma wannan Shashen baya son ganin kowa daga shi sai ita sai yaransu..
Kuma tsarin yayi in zasu aiki sai su Shigo in sun gama su koma barayin su Sani kuma abunda yasa ya Dawo dashi kusa dashi Mutum ma Rahma ne ko Saboda Sunaima da kuma yadda Sani ya zama kamar kani a wajensa Sai da ya nemi Shawaran Sunaima da Hajiya suka basa Goyon baya Dari Bisa Dari.
Sunaima Cikinta na Shiga wata tara Ta Daina zuwa asibiti Duk da bata Dauki Hutun Maternity ba Sister Aneesa tace ta bari sai ta Haihu sannan ta Dauka ammh yadda take Fashin zuwa ne yasa Dole aka Sallamata Sulaiman ke hanata zuwa ganinta tayi nauyi sosai.
Sannan yanzu tadaina Rabansa Shi din daya Rabota sai ta Kama Turesa Tana Fadin"Haba Saraki baka ga Tsausayina bakasan Halin da ni ke Ciki bane..?
Kallonta yake yi in tace haka Sai ya Jinjina kai yace"Lalle naga Halin Dan adam..Abun naki ashe hawa ne da Sauka bansani ba wannan kwanaki kina Nemana kina manne dani sai da kika gama Tsotsemin Ruwan jiki..Wato Shime yanzu an gama Cin Moriyan ganga za"a yada kwallonta ko..!ni Lokacin kin Taba tambaya ta wani yanayi nake ciki Saboda ke naki ya fito ko..?
Yafada har da Sauya Fuska Yanzu itama taganesa in yana Tsokanarta Amsa take basa cikin aDanne Dariyanta tace"Ai Lokacin bani bane..Urborn bby dinka ne ba ruwana..,!.
Da sauri yace"Bana son kage..Kada ki kullama yarona Tun kafin ya fito Duniya..Malama kece fa kawai kice kina gefe kina Harbin karkasana..!
Sunaima na Dariya tace"Eh naji bakomai in ma na Tsotse ai hakki na na nema..!
Tafada Lokaci Daya tana Dagamai gira Cikin rike baki yace"Hakki..?lalle ma yarinyar kin fara Samuwa..Bakin ki haka ya Bude bansani ba..?
Yafada yana Dariya itama Dariyan take tana Fadin"Eh mana ai na Daina maka kuka yanzu..kana min zan rama..!
Gira ya Daga yana fadin"Wato kan mage ya waye..Sunaima an yi wayau yanzu..!
Dariya yake sakata yasa ta Rike Cikinta Tana fadin"Sosai ma nayi wayau yanzu.!
Kumatunta ya ja yana Fadin"Wani Wayau..?Tukunna dai..Kefa girman ne kawai da shekarun ba wayau. !
Kwabe Fuska tayi Tana Fadin"Nice ma girman ba wayau ko Saraki..?
Yana Dariya yace"To ina kika ga wayau.?Zaki hada wayanki da na Saraki ne..?Yarinya ina kika je ina kika Taka a wannan Duniyar..?Bari Maza bisa kanki..!
Yafada yana Dariya sosai yadda Zata Kule yaji Dadin Tsokanarta Hararansa Tayi kafin ta Ture kansa Dake kan Cinyarta da Sauri ya Mike Zaune yana Fadin"Anty Sunaima me yayi Zafi..?
Kai tsaye tace"Shafa kaji..!
Lokaci Daya Tana Murgudamai baki Da Sauri ya Rumgumeta ta baya yana Fadin"Kin ma isa..?ai Tunda kikace na Shafa naji..Yasin sai na Shafa din kuma naji..!
Kokarin Turesa take yafara mata Chakulkuli,ta Gefen Hamnatanta ta Fara Dariya tana Zillewa fadi take"Saraki ka bari Cikina..!
Da Sauri yace"To ki barni na Shafa na gani..!
Dole ta barsa ya fara Hidimansa Itama Tana Tayasa,Ahakan tana da Tsohon Cikin ta tallafesa da komai ya kamallah ya Matseta acikin Jikinsa yana Shafa Cikinta Lokaci Daya yana Fadin"yarinya kima godemin....!
Ture hannunsa Tayi tana Tura mai baki yar Dariya yayi yana Fadin"Daga Taimako..?ko bakisan Yawan yin nan da nake yi ba zai sa ranar Labour Kina Barci sai dai na tashe ki nace kin Haihu baki sani ba..!
Ya fada yana Dariya tana Tayashi,Cikin Dariyan yace"Allah..Wajen Santsi yake yi..Shine nake so na wasa wajen sosai yadda in kikazo Haihuwa wajen zai Wage Sai Sulum kan Yaro ya fito..!
Yafada yana Dariya bakinsa ta matse tana Fadin"Wagewa..hala kofar gari ce..?
Yana Matse hannunta Dake kam bakinsa yace"Zai zama dai..Bakin ki bari na wage wajen ba..My Urborn baby zai min aiki aie..!
Dariya take yi tana Girgiza kai Lokaci Daya take fadin"Saraki Allah ya shiryaka wanda bai Zauna dakai ba yasha Haushinka..!
Yana mata Rada yace"kamar yadda Abaya bamu Fahimci juna ba..Nayi ta jin Haushinki nace kin cika son girma da Girman kai..!
Sunaima tace"Ni kuma nace ka cika Daga kai da Dagawa ga Wulakanci..!
Yana Shafa cikinta yace"Allah..?yanzu fa me zaki ce..?
Sunaima tace"Saraki Very Friendly..Sai wanda ya zauna Dakai yasan ka..Sai ayanzu nake kara ganin Wasu Hallayarka..Kai din ka bambamta da Sauran maza..Ina Alhafari Dakai Saraki..!
Yana jin Dadin kalamanta ya Sumbaci Saman kanta yana Fadin"Nima haka Sunaimata sai da na zauna Dake nasan kedin ta musamman ce..Na kara Godema Inna ta iya Haihuwan ya"yan baiwa..!
Haka sukayi ta gayama juna kalaman Soyayya da yarda Cikin Irin Lokutan da suke samu na juna.
Sunaima ta koma tafiya Dakyar tashi Dakyar,Ciki ya yi kasa ta zama sai a lallaba Hajiya tazo kargi ta Biyo ta ganta Ganin yadda ta koma yasa tama Sulaiman mganar Sunaima ta koma gaban Inna ta Haihu nan da nan ya Hade rai yace bai yarda ba sai dai Asamo wacce Zata zauna da Sunaimar ammh a Tsarinsa babu wankan gida Tunda yana da inda kowama zai zo ya Zauna awadace Sunaima ma bata saka Rai ba Domin tasan Sulaiman bazai bari ba Hajiya kuma Daman Bata matsa ba Duk inda Sunaina Zata tayi jego barin Gidan Mijinta ne sai ta Saki.
Ammh da kanta taje ta samu Inna sukayi mganar wacce zata zauna da Sunaimar Inna tace sai taje Zuntu tayi mgana akwai Kanwarta Tani zataje tayi mgana da Mijinta in ya amince sai tazo ta zauna da ita,Haka kuwa akayi Inna Taje Zuntu ta samu Tani sukayi mgana Mijinta bai Hana ba Tunda yana da Wata Matar tace da Zarar Sunaima ta Haihu zata zo ta Zauna mata Har sai tayi arba"in.
Cikin Sunaima bai Cika EDD dinsa ba Wataranar Jumma"a ta fara Naguda Sulaiman baya nan yana Office Tunda taji alamu ta Hada kayan Haihuwa Ita da Magajiya suka tafi asibiti,Sani ta Kira yakaisu Daman yana gidan Asibitin Datake aiki ne Tunda nan tayi awo tana zuwa aka shiga Labour Room da ita Tun Safe take abu Daya kuma taki yarda afadama kowa.
Magajiya ce taga rashin kyautar haka wayar Sunaimar na Hannunta da Inna ta Kira ta Fadamata Inna batace Zatazo ba sai dai Tana gida Tana mata addu"am Allah yasa asamu kai Lafiya.
Sulaiman bai sani ba Sai Da ya Kira Sani Zasu Fita akacr Sani baya Kamfani sai ya Kirasa a waya yana Dauka yafaramai Fadan yana ina nan yake Fadamai yana asibiti ya kawo Sunaima ita da Magajiya.
Sulaiman ya fara Fada da Masifan meyasa bai Fadamai ba Hankali Tashe shida Saifullahi dake kusa dashi suka Nufi asibitin Kamar Jiransu ake yi suna Shiga asibitin Sunaima ta Haifi Santalelen yaronta mai kama Da Sulaiman kamar yayi kaki
Suna zuwa Magajiya suka iske bakin Labour room Alokacin Sister Aneesa ta Fito tana Sanar dasu Haihuwan Sulaiman Hannu ya Daga sama yana ma Allah Godiya sai da ya Tabbatar da Lafiyar Sunaima Dake Ciki suna gyarata ita da yaron sannan ya Fara Kiran waya yana Fadama Jama"a Daga Abuja sai Inna ya Kira ya Fadamata Tayi Hamdala sannan ya Kira Baba Shima yayi addu"a da Fatam Allah ya Raya..!
Duk wanda ya kamata yaji Haihuwar nan Sai da Sulaiman ya kira ya Fadamai su Sadiya suna Tsallen Kaduna tayi kira,Sulaiman ya Kira Maimartaba ya Fadamai Cikin Farinciki yace"Alhandulillah..Me aka Samu ne Saraki..?
Saraki yace"An samu Takwaran Maimartaba Kuma Takwaran Saraki Ranka ya Dade..!
Maimartaba baki yaki Rufuwa Cikin Jin Dadi yace"Masha Allahu..An kara Samun gwarzon SULAIMAN din Ne..!To wannan sai dai yaci Sunan SADAUKIN KARGI Allah ya raya Sadauki ya ingantasa ya bama Mahaifiyarsa Lafiya mai Dorewa a isar min da gaisuwata wajen Diyata ta iya Haihuwa sannan da Albishiri Din Maimartaba da kansa zai zo yayi ma Takwaransa Huduba..!
Bakin Saraki yaki Rufuwa jin Abunda Maimartaba yace haka yabama su Fulani sukayi mai barka.
Saifullahi Khadija ya kira ya Fadamawa da mama,Suma suna ta Barka da Fatan Alheri.
Basu samu ganin Sunaima ba sai Dare da aka kaita Aminity Daki na Musamman likita yace sai Gobe zasu Sallameta Allah yasa ko kari Sunaima bata samu ba.
Magajiya na nan Tare dasu Samira ce tazo Daga baya da Ruwan zafi da kayan Tea da Ferfesun kayan Ciki Sai Ahmad da Baba inna taki zuwa Daman bazata zo ba Tana da kawaici da Alkunya tadai kira Zuntu ta Sanar dasu Har Tani tace gobe insha Allahu Tana tafe
Sulaimam bai samu kebewa da Sunaima ba sai bayan tafiyar su Baba Sani ya tafi kaisu gida Dagachan zai kai Samira gida shi kuma Sulaiman Saifullahi zai maidasa sun Fita Waje shi da magajiya su bama Baban Yaro Daman ganawa da matarsa.
Sai da ya Dauki yaron ya Kuramai ido yana kallonsa Allahu akbar wannan Rabon ne Silar Faruwar duk abunda ya Faru Ciki harda Rasuwar Sunaira Allah ya jikanta da gafara sai da ya share kwallah Jikinsa yayi sanyi ganin kamar yayi kaki.
Sunaima na Zaune an saka mata Filo abayanta ta kallesa Cikin Mirmishi kafin tace"Saraki..Ya haifi Saraki yau..!
Kallonta yayi kafin ya isa Gefen gadon ya Zauna dora mata yaron akan Cinyarta yana Fadin"Ya kika gansa.?me zaki ce ma Allah ayau Sunaima Daya bamu wannan kyautar..!
Kan yaron ta shafa Dake Cikin kayan Sanyi masu kyau da Tsada tace"Allah ya rayasa Cikin addinin Islama..Godiyata kuma ga Allah Daya azurtamu da wannwn kyautar..Sannan ina kara godemai Bisa Kaddaran data Ratso ni Cikin Rayuwarka Sannan ina Fatan Allah ya Haskaka kabarin yar"uwata ya Sadamu agidan Aljanna Firdausi..!
Sai kuka shima kamar yayi kukan ya Hadasu Dukkansu ya basu wani Rumguma mai karfi yana Fadin"Ameen Ameen..Allah ya raya SULAIMAN..MAimartaba yamai Lakabi da Sadauki sannan yace yana Miki Sannu da albishirin din Da kansa Zai zo yayi ma Takwaransa Huduba..!
Sunaima ta Dago kanta Cikin Hawaye tace"Au Saraki ya Haifi Sadauki zan ce..!
Yana Share mata kwallah yace"Acikin Satin da Sunaira zata bar Duniya Tayi Fatan ta samu Ciki ta Haifi me Sunana Sunaima..Ni kuma ban manta wannan Burin nata ba Shiyasa na Cika mata shi..!
Hannayensa ta Damke tana Fadin"ni kuma da mace na Haifa ni kadai araina nace zan Rokeka ka Sanya mata Suna SUNAIRA domin itace Silan Kaddaran data Hadamu waje Daya Saraki..!
Da Sauri yace"Insha Allahu Zaki Haifa mana Sunaira..Da izinin Lahi zamu Hada Sulaiman da Sunaira aduniyarmu Sunaima..!
Dukkansu Hawaye suke suka Rumgume juna Sulaiman na Fadin"Tanque Sunainma..Allah yayi miki albarka..!
Kamar kada ya barsu haka yakeji ammh Dole ya tafi gida Saifullahi nata Kira Sallama yayi mata Magajiya Zata kwana Dasu zuwa gobe
Tun da garin Allah ya waye Sunaima ke amsa wayoyin Mutane masu barka Hajiya da ya"yanta Kaf sun kirata har da Abba su Sadiya kuwa sun ce suna nqn tafe in suka Biyo Hajiya sai bayan Suna zasu koma.
Karfe 9:00am na Safe aka Sallamesu suka koma gida Sulaiman da kansa yazo ya Daukesu Suka koma Gida.
Suna komawa Gida ba Dadewa sai ga Inna Tani ta iso ita da Habiba Diyarta Gidan Inna suka fara Biyawa kafin su yada Zango Gidan Sunaima Tazo da kayan wanka ma masu jego kuma Daman Daga asibiti Sunaima Direct Sabon Shashenta Sulaiman yace ta Zauna.
Inna Tani tayi ma Sunaima wanka Ta gyara Jariri tas kamar ba ita ba Gida ya Kaure da Kamshin Masu jego da Turaran wuta tasaka akayi mata Ferfesun kan Rago ta tasata ta Cinye ga Kunu da Tea mai kauri Tana Fadin sha Haihuwa kikayi Sunaima na Tura baki Habiba na mata Dariya.
Sulaiman kuwa kamar Wannan ne Haihuwarsa na Farko yadda yake Rawan Jiki Inna bata zo ba ammh Ahmad ya kawo su Wasim sun zo haka suke Murna Wafiyya Harda Rigiman sai an goyamata Shi Sai da Inna Tani ta Lallasheta Saboda Darajan Haihuwa da kuma Hutun da yaran suka samu tace don Allah abar mata su Saraki yace ai shi yanzu komai tace ba Gaddama.
Habiba ba yanzu zata koma ba sai an yi Suna Sunaima na kwana Uku da Haihuwa sai ga Hajiya karama da Su Sadiya da Saddiqa da Safiya da Fatima dasu Radiya kaf dinsu harda su Sadiq sunxo barka da kayan Arziki akwatuna Biyu Cike da kayan sawa na Sunaima da na Jariri.
Haka suke Daukan yaron bakinsu yaki Rufuwa suna ta ma Sunaima Sannu da godiya sai dai tayi Mirmishi batacewa komai.
Basu kwana ba Aranar suka koma sai dai Sadiya da Saddiqa suna nan sai an yi suna Washegari sai ga Tawagan yan kargi su Hajiya uwa suma da kayan arziki sai wanda ya gani.
Suma basu kwanan ba sun yi barka suka koma Gida ya cika sosai Samira da magajiya ba zama suna ta Fama da Hidima.
Kwana Biyar da Haihuwa Hajiya tazo ita da Aminiyarta Hajiya Salame Allah Sarki,Amana batace haka ba Hajiya tace kafarta kafar kawarta ita ta kirata Tun jiya tazo Abujan yau suka Zo Barka suma Kayan arziki kamar Sunaima zata Bude shago in ji Tani Turman Atamfa uku Super wax hajiya Salame ta kawo mata da Kayan Bby harda 20k ta Dora mata abun sai wanda ya gani suma basu jima ba suka Wuce kargi Chan zasu kwana sai Gobe zasu koma.
Ana gobe suna Baki suka Cika Gida Khadijar Saifullahi tazo ita da Mama da tayi barka ita ta koma Jidda ta Fara Zama harda koyon Tafiya itama da nata kayan arzikin,Dangin Inna ma sunzo yan Zunti Sunaima ta rasa ina Zata kanta don Farimcikin ganin yadda aka Taru duk Saboda ita.
Ga kawayenta Yan wajen aikinsu Tare da ita su Aneesa da Fatima ga Matar Habib Salaha itama tazo.
Da yammah sai ga Maimartaba yazo da kansa Lalle wani Kaya sai Amale Sunaima tasha Lallunbi ta Sauko Falon kasa ta Zube gaban Maimartaba Sulaiman ya karbi Jaririn ya mika masa ya karba yayi mai Huduba bayan ya Bashi Dabino da Ruwan Zam zam ya mikama Sunaima yana Fadin"Allah ya raya Sulaiman Sadaukin kargi!
Gabadaya aka amsa da Ameen Fadawa nata Kirari maimartaba mai Dade ba ya fita bayan sun zo da Shanaye da Ragunan da Gobe za"a yankama Takwaransa Sunaina ta Zama yar gata ta ko"ina da Daddare sai ga Ahmad da Sakon Baba da Inna Kaya sukayi mata nagani na Fada ita da Sadauki Sunaima sai kuka Domin adaran Sulaiman ya Damkamata key din sabuwar Motarta 4matic baka Tana Haraban gidan sannan da Sakom Abba na 100k Cash da ban Hakuri yana nan zuwa ganin Mai Sunan Maimartaba.
Washegari aka tashi da Hidiman suna daman Tun jiya Matar Habib ta mata Kitso da kunshi Dayake ta iya Sosai mejego ta fito ras da ita Sai walwali Take Cikin kayanta ita da Jariri batasan asadin kyautan data samu da wannan Haihuwan ba sai godiya ga Allah kawai duk inda tabi kallonta kawai ake yi ana yabama wannan kyau da Zatin da tayi.
Anyaka Raguna Biyar Shanaye uku,Dole aka Dauko Hadimai Daga Fada su marliya saboda aikin nama da Abinci ga Matan Sani Direba dama Iyalan Auwal megadi suma sun zo sunan nan suna ta Taimakawa.
Anyi abinci kala kala sai wanda ka Zaba Nama ko har da gashi akayi ga Madara da Fura nan sai Badali akeyi Sulaiman kuma sun Shirya Walima a Kamfani suma an ci an sa"a an yanki Gashin nama da Fatan Allah ya Raya Sulaimam Sadauki.
Sai yamma suka zo Gidan akayi ta Hotuna da Baban,Sadauki da Uwar Sadauki sun sha kyau kamar ka Sacesu ka gudu abun sai wanda ya gani.
Kwana akayi ana ta Hidima sai Washegari sannan aka Fara Raguwa bakin Zuntu suka koma Da Kayan arziki sai wanda ya gani Haka ma yan Kargi suma Duk sun zo sunan Harda da Su Safiya dukkansu kannensa sun so sunan suma sai Washegari suka koma da Naman sunan da aka bama kowa,Kawayen ma su Aneesa suma sun tafi da irin Arzikin da Sunaima ta Samu,Khadija dai sai ta takara kwana Tatafi ita da Matar Habib sunaima ta Gode musu sosai ta kuma saka aranta Sune kawayenta Daga yanzu.
Habiba ma aranar ta koma Zuntu da kayan arziki aka bar Inna Tani Tana kara kula da mejego.
Gida ya Rage Daga mejego sai ya"yanta sai su Magajiya da Samira sai Sadiya da Saddiq sunce sai sun koma makaranta zasu tafi.
Dole Sulaiman ya bar musu Shashen Sunaima shi kuma yana Shashensa sai dai su Sadiya su kai mai Sadauki ya gansa in ya Dawo.
Haka suka Cigaba da Jegonsu Inna Tani na kansu tana Kulasu koda wani Lokaci Hajiya na kira tana jin Lafiyarsu,Sannan Abba ma yazo yayi barka yaga Sadauki Hajiya ta dawo ita da Hajiya karama.
Inna dai batazo ba sai da Sunaima tayi arba"in ta kai mata Sadauki da kanta Zuntu kuwa su suka maida Inna Tani gida da abun arziki kamar zata Bude shago har sai da tayi hawaye Godiya kuwa kamar bakinta zai Cire haka ta Dinga yi musu.
Su Sadiya sun koma Gida Shiyasa bayan sun dawo daga Zuntu ta tafi Abuja wajen Sati Daya tayi Duk da Saraki yaso ya hana tacemai yayi Hakuri Ta zaga Duka Gidajen Kannensa sai da taje ita da yaran su Wasim.
Bayan ta dawo Kargi taje ta kara kaima Maimartaba Saraki dasu Fulani kwana Uku tayi ta dawo bayan taje ta gaidasu su Hajiya uwa nan suka Hadu da Hajja Bilki tazo suka gaisa taga Sadauki.
Taje Karaye Wajen Khadija ta kwana Daya itama suna ta Shirin Dawowa nan kaduna Mama ta amince,Sannan taje tayima Salahar Habib Wuni da ita dasu Aneensa da Fatima Domin sun mata Hallaci Sosai bazata yada su ba
Sai da tagama yawon Dangin da Gaisuwan ban gajiya kana ta Samu Zama agida su Wasim sun koma Gidan Inna Daga ita sai Sadauki sai su Magajiya bata da mtsalan Reno Matar Sani sun dawo Nan tare dasu matar mai Kirki Karime ita ke Shigowa tana Tayata Kula da Sadauki.
Inna Tani bata koma Zuntu ba sai da ta gyara Yarta sosai kana ta koma Ranar da suka Hade da Saraki Kamar
Ya Haukace mata tasha Sambatu da Surutu kamar me sai da tagaji ta Danne mai Baki sannan yayi Shuru.
Wata Biyu da Haihuwarta ta koma aikinta,ba ason ran Sulaiman ba sai da Hajiya ta Saka baki ya barta ta koma in tana da aikin kwana Kamar kada ya barta Haka yakeji wai Zata kwaso ma Sadauki sanyi da Cizon Sauro ita dai nata Shuru bazatayi mgana ba yace ta bar aikin gabadaya..Duk da babu abunda ta rasa ammh aikinta na Fannin lafiya ne ba Domin Dukiya ko wani abu ba Saboda Taimakom mata ne.
******
*MURFI...*
*Bayan Shekaru uku..*
Bayan shudewar Shekaru uku abubuwa Dadama sun Faru na Samu dana rashi,Na rashin Shine Rasuwar Fulani hakika an yi rashi Sosai,Sannan an samu Cigaba sosai ta Fanni Rayuwa da arziki Sunaima ta kara Haihuwan Mace taci sunan Sunaira suna Kiranta Bibi sai kuma yanzu Datake Dauke da Wani Cikin dan wata Biyar ajikinta..
Arzikin Sulaiman ya kara Hauhawa Kamfaninsa na Madara ya Zarce sa"a da Tsara yakai Inna da Baba Hajji Domin yace har abada bazai iya Biyansu ba,Sannan yaje shi da Sunaima da yaran kafin ta Haifi Bibi Sunje har Kasheshen Duniya irin su India,America,China Da Sauransu a wani Karshen Shekara da sunaima ta Samu Hutun Annual leave.
Sannan yakai iyayansa Abba da Hajiya da Hajiya karama Maimartaba dai Tsufa ya zo sai Fatan gamawa da Duniya Lafiya ya Nada Saraki Saurata Wato Sarakin Kargin gabadaya Sannan yana kokarin yin Murabus ya Dora Daya cikin ya"yansa Tunda shi dai yanzu an kwana Biyi aduniya.
Sunaima ta siya ma su Inna Sabon Gida da kudin aikinta ta kuma kai Ahmad Makarantar Sojoji,Har zuwa Lokacin su Wasim suna wajen Inna Sai dai Hutu ke Kawo su gidansu.
Ayanzu da Wasim keda Shekaru goma sha Daya aduniya yana Primary 6 sai Wafiyya Dake da Shekaru Takwas tana Primary2 Sadauki ma an sakashi a makaranta yana Nursry 1 shi.
Khadijan Saifullahi sun dawo nan anguwan Mu"azu da Saifullahi ya mallaki gida suna kwancensu su uku gwanin sha"awa da Matar Habib Salaha.
Kannen Sulaiman sunyi aure Sadiya da Saddiq rana Daya Sadiya tana nan kaduna Saddiq ne tayi aure anan Abuja Sadiq ya gama makaranta yana Service Kamfanin A.S kargi ya kai wani matakin Kololuwa Riba kan Riban da Abba bai Taba Tsammani ba Har Taron karramawa ya shirya musu Shi da Saifullahi abun sai wanda ya gani Da kyauttukan kudade Makudai da Gidaje da Motocin hawa Cikin su ba wacce bata Hawa Mota mai Tsada Sunaima ta iya Driving ita take Tuka kanta zuwa wajen aiki ko zata Fita ko kai yara makaranta bata da mtsalan komai agida su magajiya na taimakawa Duk da Ita ke shiga tayi ma Saraki girki da kanta.
Sannan ga karime matar sani na Taimaka mata da Dawainiyar yaran sai abubuwa suka Ragun mata.
Sulaiman ya gaji da korafin aiki ya Daina mgana Domin yaga aikin Taimako ne shiyasa ya kyaleta Tanayi ba Domin ta rasa komai Tunda Duk wani jin Dadi sai dai Ta samma wani Cikin jin Dadinta.
Laila ta sake aure da wani Abokin Babanta A lagos yake matansa uku itace ta Hudu chan Lagos din take da Zama Amarya Hajiya Salame ta Haihuwa,yan Biyu na Farko Hassan da Hussaini suna nan Dole ta Zauna tayi Hakuri daman ance in bakayi Sharan masallaci ba kayi na kasuwa.
Hajiya Zabba"u bata Ja baya da Salaha ba suna aminci sosai sai dai wani abu ne da Hajiya take kiyeyewa yima Allah Shishshigi.
Sunaima ta zama Tauraruwa wajen Mijinta da yan"uwansa Hajiya ko ya"yanta yanzu ta Daina Shawara dasu sai da Sunaima Domin itace komai ayanzu agidan haka Hajiya karama ta Dauketa Abba ma kamar Sulaimam haka suka Dauketa Kullun inna Hamdala suke yi da ita Baba suna kara Godema Allah Daya Daidaita Duka al"muran.
*****
*9:00am*
Jiya jumma"a aikin Dare tayi Shiyasa yau da Safe tana Dawowa gidan ta Ke adaki tana Barci Rufe Bedroom dinta tayi bataso Biba ko Sadauki wani yazo ya Dameta ta gaji ga aiki ga Nauyin Jiki Dakyar ta iya bari tayi wanka ko kaya bata saka ba Daga ita sai Towel ta Fada kan gado tana Barci.
Sulaiman yana Shashensa Shima yana Hutun karshen mako,baima san Sunaima ta shigo gidan ba sai da su Sadauki suka zo suna Rigimansu shi da Bibi ya taso daga Cikin Daki Sanye da Jallabiya Sadauki ya kara Kiba da Fari kamar bashi ba Jikinsa Likwai likwai alamun yana samun Hutu da jin Dadi.
Biba ya Dauka ya saba yana kama Hannun Sadauki suka fito Falo yana Fadin"Ina Anty Sadauki..?
Haka su wasin ke kiranta ya kama bakin kowa har su Sadauki sun kama kowa anty.
Sadauki da muryansa ta yara yace"Cha kulle kofa Daddy..muna kiranta bata jo ba..!
Sulaiman yayi Dariya bai ce komai ba ammh aransa yana so yayi mganin Sunaima tasan fa Jiya haka tata fi ta barshi Shikadai ammh tana Dawowa taje ta kwanta ko ta nemesa.
Kasa suka Sauka shi da yaran Samira Dake gyaran Falon ta Duka ta gaisheshi ya amsa yana Fadin"Samira yaran nan sun yi breakfast kuwa..!?
Kanta na kasa tace"Tun Safe suka sha Tea ranka ya Dade..Kuma yanzu suka gama cin Dambun naman da Anty tayi Shekaran jiya..!
Biba na ganin Samira ta Fara Zillo ya Saketa ta isa gareta tana Nuna mata baya Samira na Dariya tace"Bambu ko Biba..?
Kai ta gyada mata itama kuma ta Dauketa ta goya Sulaiman na kallonsu Cikin Shagwaba da Rigima Sadauki yace"Daddy ni ma Bambu..!
Sulaiman yace"To Sadauki ai bayan ta Daya kuma ta goya Biba..kana gani Anty kuma kasan bazata iya goyo ba yanzu sai dai in ni kake so na goyaka..?
Da Sauri yace"Eh Daddy..!
Sulaiman ya batarai kafin yace"Sadauki ka zama Lukuti zaka karyama Daddy baya..!
Yadda yafada yasa Dole ya Kyalkyale Da Dariya sai ga Magajiya ta Fito suka gaisa da Sulaiman tana Fadin"Taho na Giyaka Sadaukin kyale Samira muma ai muma da baya..!
Da gudu ya Nufeta yana Fadin"Mama..bumbun..
Daman haka Sunaima tace su rika Kiran Magajiya bayan ta ya Dane yana Dagama Sulaiman hannu ya Dagamai yana Fadin"Bayan Daddy ya Huta..!
Sulaiman ya kalli Samira yana Fadin"Sani ya same da mganar kun Daidaita da gaske ne..?nasan Sani da Shiririta nake sai naji ta bakin ki..?
Kai ta sunkuyar cikin jin kunya ta kasa mgana Magajiya tace"Ai soyayyar bata yanzu bane yallabai ta Dade..!
Sulaiman yace"Shikenan zan yi mgana da Maimartaba..In sun Daidaita kansu ni zan zame musu uba Sunaima uwa ayi komai agama Tunda Daga Sanin Har Samira Duka suna Cikin Ahalina ne..!
Nan da nan magajiya ta Fara godiya Itama Samira nan ya barsu da yaran ya Koma sama Direct Dakin Sunaima ya shiga yaji Bedroom din a kulle Dakinsa ya koma ya Binciko key yazo ya Bude kwance ya ganta da Towel Mirmishin mugunta yayi yana Fadin "Yes Saraki mai Sa"a..!
Jallabiyansa ya Cire Dagashi sai karamin wando ya Haye gadon ya Zare Towel din ya Jawota Jikinsa ya Rungume da karfi Cikin magagin barci taji an riketa tace"Waye..?
Da Sauri yace'MIJIN KANWARKI NE..!
Cikin rada ya fada yasa tana jin muryansa ta Bude ido sai akan Gwarzonta Saraki Baban Sadauki da Biba.
Mirmishi ta saki kafin tace"Kace MIJIN KANWATA...Kaddarata..!
Matseta yayi yana Fadin"Uhmm
Kimsan ni kaddaran ki ne kika barni Jiya Baki Bude yauma haka ko..?
Tana gyara kwanciya kan jikinsa tace"na gaji ne Saraki..!
Yana Shafa Cikinta yace"Ni na gajiyar dake..?malama bana son wannan mugutar taki gwalemin kayana na Shige..!
Kirjinsa ta Daka tana Fadi"innalillhi Saraki..Saraki..!
Yana Dariya yake fadin"Yo karya nayi..?ba gwalemin kike yi ba Hajiyata..?
Bakinsa ta rufe da nata suka Tallafi juna na wani Lokaci kafin ta Sakeshi Tana Fadin"Wannan bakin naka sai na Konasa da wuta kafin yayi Linzami..!
Tafada tana jan bakin Dariya yayi yana Tura mata bakin yana Fadin"Nidai kafin ki koma shi da Wuta Fara konashi da bakin ki..Bayan kin gwal..!
Bata bari ya karisa ba ta Dinga Dukan Kirjinsa tana Fadin"Saraki Saraki..!
Dariya yake yi yana kare kansa Lokaci Daya yana Fadin"Sunaima..Sunaima..Gwaleee min....!
*Tammata Bihamdillahi...godiyata ta tabbata ga Allah Subuhanahu wata"ala Daya bani ikon Fara Rubutu Labarin nan cikin ikonsa gashi yau ma acikin ikonsa na kamallah Godiyata ta tabbata ga Annabinmu muhammad sallallahu alaihi wasallam tare da iyalansa da Sahabansa gabadaya*
*Janafty*
*29/06/2022*