KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA GOMA

by @maidambu41

KARFE DUKKA KARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah}
BABI NA GOMA
   
Page din na Group din MIJIN Mariah ne da fıtıklar Hikayar Mai_Dambu🥰

Gatari langawa

Yadda zaku fahimci Ya Man yayi fushi da lamarina, haka aka muka tafi garin babu tsinken da Ya Man  ya bari na dauka kuma ya hana kowa bina domin ya riga da zare ni cikin Yaransa, haka muka isa garin wanda tunda aka haife ni ban taba shiga gari irin wannan ba, haka muka shiga gida me cike da mata sama da talatin, kuma su bakiɗaya zuri'a daya ne. nice bare a cikinsu haka yasa ban samu karɓuwa a cikinsu ba, dakin da aka bani asali na kiwon dabbobi ne, kusan dakin ban san yadda zan gaya muku yaƙe ba, amma idan kuna tunanin samun wani jin dadi a dakin to babu a wannan dakin, ga kwarin dabbobi, kai to babu sai azaba da kuncin rayuwa, haka ya kira kartin mazan kannenshi suka fitar da kome aka gyara mun dakin aka wanke sannan aka kawo irin katifar mutanen kauye aka jefa a cikin dakin sai wani zanin gado da aka shimfida min, nasan dai ba baiwa bace amma daga ranar albarkan Ya Man ya fara aiki a kaina domin kuwa duk girman gidan ni ce me share shi na daura abincin karyawa Alhaji me mata uku ni ce ta hudu kuma me karancin shekaru ni ce me kula da gidan domin kuwa shine babba su mazan gidan rai bakwai ban da yaran Salisu uku suma da matansu Uwargidansa me suna Suwaiba suna kiranta Suwai, sai abinda ta ce ake yi a gidan domin kuwa idan tana sonka ka gama idan bata sonka kwanan ka ya kare don kare kuma duk da haka haihuwa take sauran matan tsoronta suke domin bata da mutunci ko kadan. Shi kansa sai yadda ta ce mishi yake yi, zuwana gidan matar danta Ummita ta fara nakuda, tun safe ake abu daya kasancewar degree ne da ni yasa nayi kokarin tsaya musu amma suka hanani wai zan mus shirme gashi yarinyar ta fara bleeding. Gashi itama unguwarzomar ta sare haka yasa na shiga na dauki kasadar kula da yarinyar da ikon Allah aka samu Uwar da babyn da ta wahala, gashi takaru sosai don haka na shiga dakina na zauna kuka ne ya kwace min domin bani da kome na aiki, mijin Ummita me suna Ayuba shi ya min magana na fita ina goge fuskana ya ce min ''hajiya ya zamu yi kin ce zaa yi mata aikin gaggawa.'' cikin shashekar kuka na ce mishi. '' Ba ni da kayanki zaka iya samo mana kafin awa daya?'' kura min ido yayi ya ga ina share kwalla murmushi yayi min ya ce min. ''To meye na kuka? idan shine ba sai naje na nimo ba ki daina kuka haka bari naje na dawo.''   tunda nazo gidan babu wanda ya muamalance ni ta hanyar arziki saboda Suwai ta hana kowa kula hatta mijin bai isa kallona ba, kuma ga gori abu daya zasu fara cewa matar chushe bata da wata daraja
Inda Allah ya so mu bai gaya musu kome kaina ba sai dai yace sadakata aka bashi ni.

     Kamar yadda na karanta a matsayina na unguwarzoma haka ma rubuta mishi duk abinda zai buƙata, kuwa kafin wani lokaci sai gashi  ya kawo min, baka sanin jarumtar mace sai an zo mata dinki, Ummita sai da ta roke ni da na rufa mata asiri kada na faɗa tayi kuka ko wani abu, amma a wurin dinkin duk da alluran da na mata haka tayi ta kuka, na gama gyara dakin na barta da Uwar Mijinta da take aika mata da harara wai bata kishinta, bayan na dawo daki domin wanka nayi na dawo dakina kayan da nazo dashi na maimaita sai wata jallabiyarshi da ya bani har guda biyu, su nake sauyawa a sati daya da nazo Yar damaturu suke kirana, amma amsar haihuwar nan yasa na koma Yadiko Amarya. Wanke wanke da aka jibga min da aikin gidan duk aka sauke min, sai dai Suwai ta haramta min Mijinta, ni kuma haka bai dame ni ba, saboda ba shi bane damuwata, tunda iyayena suka iya watsar da ni waye ba zai yi haka da ni ba.  Abinda ban sani ba shi ne Ummita wannan shine haihuwata na uku duk haihuwar mutuwa suke kafin suna, bayan na fito wanka Matar Nazimu kanin Ayuba ta shigo dakin muka gaisa tace min. "Yadiko Amarya, dama ina son na gaya miki Ummita fa yaranta Basu kaiwa suna saboda wabi take idan ba Sa'a na nan da sati daya Yaron zai koma, da sauri na ce mata. "Me yasa basu zuwa asibiti?" Shiru tayi tana faɗin, "Wallahi ban sani ba amma Bama zuwa asibiti gaskiya:". "muje dakin?" 
        Ta biyo ni zuwa dakin na mata tambayoyi kafin ta bani amsa, na zata jundis ne sai na fahimci kamar jininta da na uban akwai matsalaa"ina baki bashi nono ba?" "Eh Yadiko Amarya." "Ina babanshi?" "Yana waje" "don Allah ku kira shi muje asibiti." "Babu inda zaku je wabi ne idan tayi hakuri zata kuma haifa wani ai." "Maman Gambo." sunan karamin danta kenan na kirata da shi na ce mata. "Idan muka je akwai wani gwajin da za'a mata su bata alluran da zai taimaka mata in sha Allah ki yi hakuri a je can." Na faɗa ina rike babyn ban san me ta tuna ba, amma ma ga ta kalli Ummita ɗin sai ta ce mata. "Kina ganin idan kuka je zasu iya hana shi mutuwa ne?" Kallon yarinyar nayi wacce akala zan bata shekara uku zuwa hudu,  jikina yayi sanyi sosai domin kuwa ban zaci haka ba shirin da tayi yasa na fahimci ta hakura na juya zan mika mata Yaron ta ce min. "Muje zan gwada ya rayu ko ya mutu duk na Allah ne Suwai gara mu gwada can." 

       "Amma kin san baa zuwa asibiti a gidan nan? Ayuba da yake ubansa ma sai da na kusan mutuwa sannan na haife shi."  Idan Uwa ta sare kaf duniya babu wanda ba zai sare ba, amma ta nuna min ita uwa ce ta gaske ta gyaɗa kai haka na rungume Babyn muka wuce waje, mashi muka hau ni da ita ga babyn muka nufi bakin hanya tafiyar minti arba'in ya kai mu, yadda take takawa na tausaya mata haka muka samu mota zuwa babban asibitin fataskum,   muna zuwa abinda na fara shine fara ganin likita wanda muka sha wahala kafin na ga likitan Dr Mansur Gaidam, sake baki yayi yana faɗin. Ayshatou Mustapha Liman." "Doctor muna bukatar a gajin gaggawa ne!" "Kin san Nafiu ya saka nimanki?"
              "Doctor Ka taimaka mana Please." Na faɗa ina me barin office din, biyo ni yayi ai kuwa muna zuwa waje jini ne ya ɓalle mata, wata nurse ta fara ihu tare da masu gyara asibitn, haka dai aka shiga bamu kulawa saboda ganin doctor Gaidam, koda na mishi bayani shima hasashena ya ɗauka haka muka yi ta zirga-zirga har zuwa dare, duk wannan abin da yake faruwa ba kudinmu ko sisi, kudin Dr Mansur Gaidam ne, wurin karfe biyar na yammacin ranar sai ga Ya Nafiu, ina ganinsa na kura mishi ido, da guda na nufe shi, bai rungume ni ba, sai dai ya janyo ni gefen kafadarshi, na fashe da kuka, "I'm sorry Daddy" murmushi yayi, Ayuba yazo ya gaishe shi sannan muka nufi office din doctor Gaidam, muka zauna. Mika min wayata yayi ya ce min. "Kin ɓace a cikin sati ɗaya, no call no show up sai yau." 

    "Ya Man ya ce baya son." Shiru nayi ina jin kuka yana zuwa min. Don ya kauda kukan ya ce min. "Shine mijikinki na wajen!" Girgiza mishi kai nayi tare da cewa. "Danshi na biyu." Gyaɗa kai nayi ina wasa da hannuna na ce mishi. "Nice ta hudu a gidan, mace ta Talatin da ɗaya..." "Lilly wannan auren bai dace da ke ba, kalli yadda kika koma?" Murmushi nayi, na mike tsaye ina faɗin. "Zan tafi niman abinda zanci." Kallona yake a hankali kafin ya ce min, "Na taɓa barinku da yunwa ne?" Yadda yayi maganar a dake ya sani komawa na zauna,shi kuma ya fita waje can sai gashi da abinci, da ruwa ya Nafi'u ya tsallake duk wani abinda yake ya biyo ni, a daren zuwa wayewar washe gari, har an gama kome, wurin karfe biyu na rana na kunna wayata sai ga sakon mutane kashewa nayi ban kuma dubawa ba,  da aka sallame mu sai da na jira kayana aka kawo sannan Aunty zuhrah, murmushi nayi tare da rungume ta ina kuka. "Auta" yadda nake kuka ta kara rungume ni sosai. "Ya isa haka." Matsowa Ayuba yayi ya ce min. "Yadiko Amarya, iyayeki ne?" "Yayu ne.." gaida Aunty zuhrah yayi ta amsa mishi sannan muka wuce a motar da tazo da shi, gaskiya mun sha hanya daya motar kayana ne sai ya Nafi'u,. Sai wannan na Aunty Zuhrah da nake ciki Ayuba da ya Nafi'u,  turanci ta juya min cikin faɗa take cewa. "Zaki zo shine ba zaki gaya mana ba sai shi wanda ya fi mu ko?" Idanuna ne ya cika da kwalla,  na ce mata. "Kiyi hakuri nima ba nice na Kira shi ba" shiru tayi har muka shiga cikin garin Gatarin langawa, ai kuwa sai ga mutann garin na ta fitowa, suna kallonmu saboda labarin ya bazu an kai matar Ayuba asibiti, na san an gaya mishi halin da matar da shi kansa suke ciki for the sake of yara masu zuwa dole sai tana karban alluran rogh, domin kuwa yaransu ba zasu rayu, kosisi basu kashe ba, Alhaji Salisu yana can gindin durumi aka gaya mishi, sai gashi nan a guje, lokacin da yazo yadda ya mikawa ya Nafi'u hannu kin amsa yayi, tare da nunawa kamar yana waya. Ummita ce ta bani kofi me kyau da ruwa aka kai mishi, Aunty Zuhrah kuwa kallon dakin take cike da tsoro, take kallona na zauna, dama a tsarin gidan bamu abincin rana, dankalin hausa ake dafawa a raba part part kuma idan baka gida baka da kaso, wannan yasa bamu samu abinci ba daga gidansu aka kawo riqon dawa miyar kuka danya aka zubo min harda yajin daddawa aka kawo min.

                 Lokacin da Aunty Zuhrah ta ta abincin hawaye ne ya shiga zubo mata, tana kallon yadda na fara ci, ita kan bata ci ba. Har sai da Salisu ya kawo musu fura da nono, shine ta sha, aka shigo min da kayana kusan akwati biyar, da manya ghana mostgo guda biyu kayana dukka,   har waje na rako su na kuwa basu sakon gaida Hajja Mama, haka muka rabu cike da kewar juna, bayan tafiyarsu ne Salisu ya zo zai raba ni da abinda suka bani na ce mishi. "To bari na kira Yayana da Aunty na tambaye su domin na sun baka ai har yaran gidan nan."

      "Haba baki san wasa bane" da haka kudina ya tsira, bayan dawowarmu aka yi ta zuba ido Yaron ya mutu, amma ina sai gashi ranar suna yaro yaci sunan Ya Man Mustapha, nayi kuka kamar idanuna zasu fita, ana cikin hidimar Mustapha sai ga kaya daga gida da yayuna mata, aka zo aka gyara min tass, ba sai ga Ango na rawar kafa, yan uwana jin irin abinda nayiwa Ummita shine Ayuba ya saka sunan Ya Man, har dakin me jego suka shiga suka bata kuɗi da alkhairi kafin suka bar garin cike da tausayina, tunda Salisu yaga gara da abubuwan da aka kawo min ya fara rawar kafa da na jiki, zai shigo dakina tuni Suwai ta taka mishi burki a tsakar gida, yana ji yana gani ya barni ko dakina bai taɓa takawa kamar sauran matan ba. Abincin da aka kawo min ya tattara ya kai dakin Suwai, ashe ban san yanzu zaa fara zaman gaske domin kuwa Suwai da team ɗita sai da suka hana Ni fitowa waje, sai biyu suna yunkurin dukana Ayuba na amsa na a hannunsu, ganin haka suka koma haɗa ni da mijinmu, GA haushin Suwai ta shiga tsakaninmu, haka zai rufe ni da dukka........