11
11
***Duk bayanin da yaya faruk ke yi masa baya fahimtar su dan gaba ɗaya hankalinsa da tunaninsa da kuma nutsuwarsa basa tare dashi he was out of his sense, baƙin ciki da wani irin radadi sune suka lullube zuciyarsa suka hana shi tuna komai a wannan hali wani abu mai nauyi ya sauka ya dirar masa akan ƙirjinsa even his breath was heavy, wai shi Afeef ya dubi tsabar idonsa yace zai tare da Mimi acikin gidansa, lallai ta tabbata wannan yaron bai shiryawa zaman lafiya ba sannan bai so a rabu lafiya ba he don't want peace,
Ganin babu abinda zai fahimta ko kuma zai gane kawai yasa ya yiwa Yaya Faruk sallama ya figi motar sa ya fita, ganin ya fita yasa yaya faruk shiga ɓangaren hajiya wadda duk gidajensu guda uku babu wanda yasan abinda yake faruwa, kitso ya tarar ana yiwa hajiyan bai zauna ba ya nufi bedroom din anty Mimi dake can upstairs, tana kwance tana sharar hawaye kamar koda yaushe cikin yan kwanaki nan,
"Mimi..... Tashi..." taji yaya faruk ya fada bayan ya shigo har cikin bedroom din nata, tashi zaune tayi tana sharar hawaye,
"Mimi me yasa zaki rinka shiga motar Faruk da sunan lift? Yes na san dan uwa ki ne ko babu aure, amma tunda mijin ki ya nuna baya so to ina baki shawarar ki hakura da hakan, kibi umarnin mijinki....."
Wasu hawaye masu ƙuna da raɗaɗi taji sun fara tsere kan kumatunta, wannan kuma wacce irin masifa ce?
" Dan Allah ki kiyaye kar na sake jin wani abu ya faru makamancin haka please..... "
Zubawa faruk ido kawai tayi tana hawaye bakin ciki ya hana ta magana koda yake bata da abinda zata fada daidai wannan lokaci, shiyasa har ya ƙaraci fadansa cikin nasiha ya gama ya fita bata ce uffan ba, wani tashin hankali take ji irin wanda bata taɓa jinsa ba, Afeef ya cuci rayuwar su sannan ya yaudare su, bayan fitar yaya faruk kwanciya ta koma ta sake yi tana zubar da hawaye.
Baƙin cikin maganar da Afeef ya faɗawa yaya Aliyu itace ta tsaye masa a rai ya kasa zaune ya kasa tsaye kuma ya kasa ci ya kasa sha sannan bacci ya kauracewa idanuwansa, wai har shi wannan dan tatsitsin yaron zai saka a gaba yana fadawa magana any how? Ƙudurcewa yayi a ransa duk ranar da Allah ya sake hada shi da Afeef sai anyi ɓacacciya sai yayi masa mugun duka irin duka na mutuwa.
Afeef gida ya koma ransa a ɓace kuma a jagwalgwale, yana shiga Irfan ya kirashi a waya kamar ba zai dauka ba amma ya daure ya dauka yana kokarin saisaita kansa,
"Naje family house ban same ka ba, gashi har na dawo gida ma...."
"ok shine ba zaka jirani ba?"
"zan sake dawowa an jima...."
Daga haka ya katse wayar yana nazari, dole ya dauki mataki akan anty Mimi da yaya Aliyu, ba zai zuba musu ido suna wulakantashi ba sun mayar dashi kamar wani soko ko kuma dolo, baya jin ƙarfin jikinsa dan kamar ciwon sa na kokarin tashi shiyasa ya wuce part din mommy ya hada coffee mai zafi tafasasshe ya sha amma duk da haka bai ji shi daidai ba, part dinshi ya koma ya hada ruwan zafi sosai sannan ya shiga cikin bahon wankan ya kwanta yana jin zafin ruwan yana ratsa kowacce kafa ta jikinsa yana gasuwa, ya jima ciki yana juyi daga bisani ya fito ya saka kaya ya zauna saboda ya dan ji dama dama, a duk lokacin da yake irin wannan ciwon nashi anty Mimi ke kulawa dashi dan wani lokacin ma can family house din yake tattarawa ya koma har sai yaji sauki sannan ya dawo gida. Bai sake fita ba sai bayan magriba lokacin ne ya tafi family house dan yana son ya samu iyayen su maza gaba ɗaya kamar yadda ya tsara cikin ransa,
Yaga motar yaya faruk da ta yaya Aliyu wannan ya bashi tabbacin suna cikin gidan gaba ɗayansu, kamar koda yaushe suna zagaye da hajiya kaka yayanta da jikokinta anata hira ana raha,
Da sallama a bakinsa ya shiga cikin falon nan gaba daya hankalin kowa ya dawo kansa aka fara yi masa sannu da zuwa dan da yawa basu ganshi ba tun dawowarsa sai yanzu, ya gaida kowa ya amsa banda yaya Aliyu da ko kallonsa bai yiba in banda harara da yake aika masa, kusa da Afeef yaje ya zauna suka fara gaisawa, zuwa can ya matsa kusa da kaka yace,
"Hajiya ina son Magana dasu Abba...."
"ya isa.... Sha lele yana son magana da iyayensa.... Lele na me ya faru?" hajiya ta fada cikin kulawa,
"Hajiya akan maganar auren mu da anty Mimi ne...... So nake ayi mana tsakani da yaya Aliyu daga yau babu shi babu ita....." ai tun kafin ya rufe bakinsa Aliyu yayi kukan kura ya cakumo shi ya fara kifa masa mari nan wani fadan ya kaure a tsakanin su Irfan da yaya Faruk suka tashi suna kokarin raba su yayin da su kuma iyayen su maza kowa ya fara daka tsawa,
" Kai har ka isa...... Dan kutumar ubanka nawa kake....."
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun....... Wai me yake faruwa haka? Kai Aliyu me ya hadaka dashi?" hajiya ta fada cikin tashin hankali, shi dai Daddy wato mahaifin Afeef bai ce komai ba saboda ganin yayyensa na nan wato Abba fari da Abba baƙi, wata tsawa Abba fari ya dakawa Aliyu,
"Aliyu you must be very stupid, Idan na sake jin bakinka Haidar sai naci mutuncinka..... Ashe dama baka da mutunci? Kai Irfan kira min Mimi...." cikin sauri Irfan ya tashi ya haura upstairs bedroom din anty Mimi inda take kwance tun bayan da ta idar da sallar magrib,
"Anty Mimi Abba yana kiran ki..... Kiyi sauri ki zo dan a fusace yake he's upset" daga haka ya juya ya fita dan yasan halin Abba idan ransa ya baci bai da sauki,
"Abba gata nan zuwa...."
Tun daga nesa gabanta ke faduwa tana kallonsu daya bayan daya, idonta ne ya sauka kan Afeef da ke zaune cikin fushi hancinsa duk jini wanda gashi nan har ya zuba a gaban rigar sa ya ɓata,
Tsugunnawa tayi ta durkusa daga nesa dasu kadan,
" Abba ina yininku?"
Bai amsa gaisuwar ta ba ya juya ya kalli Afeef yace,
"Afeef me kace akan mimi da Aliyu?"
"Abba so nake ayi mana tsakani da yaya Aliyu daga yau babu shi babu ita, ban yarda ya sake daukar ta ko acikin motar sa ba ko ya kirata a waya, gaisuwa kadai na yarda ta hada su...."
"saboda Kaine wa? Kai ka isa ka raba ni da ita? Who do you think you are?" ya Aliyu ya fada yana kokarin sake tashi faruk yana rike shi,
"Aliyu baka da mutunci ko? Bance kar ka sake magana ba? To duka ku bude kunnen ku gaba daya ku jini da kyau, daga yau daga yanzu ban sake yarda irin wannan ta sake faruwa ba, kuna yan uwa ciki daya kuna fada har da dambe, ke mimi kar na sake ji ko gani ko da wasa kin shiga motar Aliyu tunda mijin ki baya so sannan ban yarda ki sake wata magana dashi ba a waya..... Idan kika sake kuma ban yafe miki ba...... Kai kuma Aliyu daga yau babu kai babu ita ban yarda in sake jin wani abu ba makamancin wannan... Afeef shine mijinta a yanzu kuma duk dokar da ya kafa dole ta bita........ "
Kuka kawai anty Mimi ta fashe dashi ta tashi ta koma upstairs yayin da shi kuma yaya haidar ya cika fam ya kawo har wuya, mintuna kadan da zartar da wannan hukuncin da Abba yayi Aliyun ya tashi ya fita yana yiwa Afeef kallon zamu gamu ne, a fusace ya figi motar sa yabar gidan wanda har su Abba na jiyo kugin motar tasa, gudu kawai yake shararawa zuciyarsa na tafarfasa sai zancen zuci yake, yazo kan wani junction suka yi taho mu gama da wata babbar mota tirela,
Su Abba na kokarin shiga sallar ishah aka kira wayar yaya faruk, bai fada musu abinda yake faruwa ba kawai ya shiga mota ya fita da sauri, motar haidar din tayi kwatsa kwatsa haka shima yaji raunuka sosai har an wuce dashi asibiti mafi kusa, sai bayan da suka fito daga masallaci sannan yaya faruk ya kira Abba ya sanar dashi, gaba daya gidan suka dunguma suka tafi asibiti domin duba shi inda yake emergency, duk da abinda ya faru hakan bai hana Afeef bin Irfan ba suka tafi tare, yana kwance yana ta bacci lokacin da suka je duk jikinsa raunuka amma anyi sa'a babu karaya, misalin karfe 11 na dare duk aka tattafi sai iya umma mahaifiyarsa da Janan sune zasu zauna a wurinsa.
Anty Mimi tamkar zata yi hauka saboda hukuncin da taji Abba ya yanke a kanta ita da Aliyu, yanzu shikenan Afeef ya samu nasarar raba su da haidar? Wannan wacce irin mugunta ce da cuta mai girma? Kuka take kamar ranta zai fita haka ta kwana bayan gari ya waye kuma Suhana ta shigo bedroom din nata dauke da breakfast dan babu kowa agidan duk suna asibiti hatta hajiya ma ta tafi, tana kwance cikin bargo kamar marar lafiya,
"Anty Mimi ina kwana? Ga breakfast dinki inji Ammi...."
"Abba ya fita?" shine kawai tambayar da ta yiwa Suhana,
"ehh duk sun tafi asibiti wurin yaya Aliyu...."
"me ya samu yaya Aliyun?" ta fada bakinta na rawa sannan wuf ta tashi zaune tana son jin amsar da suhana zata bata,
"baki san yayi accident ba jiya da daddare?"
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun......" ta fada tare da dafe kanta, cikin zuciyar ta kuma cewa take "Allah ya isa tsakanina dakai Afeef.... Allah ya isa"
"nima zanje in shirya.... Ga breakfast din nan"
Da kallo tabi suhana har ta wuce ta fita daga cikin bedroom din, yanzu shikenan ko duba shi ta san ba zata samu damar zuwa ba tunda ga sharadin da Abba ya gindaya mata shima kuma ta san wannan bakin cikin hukuncin na Abba ne yasa har yayi accident dinnan,wayarta ta dauka ta fara kiran number Afeef, bacci yake yi abinsa hankalinsa kwance amma yana son idan ya tashi zaije hospital ya dubo yaya Aliyun, ɗaukar wayar yayi yaga Mimi ce ke kiran sa, bai dauki kiran ba ya mayar da wayar ya ajiye yaci gaba da baccinsa har tayi kiran ta gaji, cikin bakin ciki ta ajiye wayar kafin daga bisani ta sake dauka ta kira hajiya tana dauka ta fara tambayar ta ya jikin Aliyu hajiya tace da sauki yana bacci har yanzu bai farka ba, katse wayar tayi ranta na yi mata wani irin suya.
Bayan Afeef ya tashi daga bacci ya yi breakfast yayi wanka asibiti ya tafi dan kusan kowa yana can in banda su Abba da suka tafi aiki bayan sun duba shi, shima bai jima sosai ba yacewa Irfan bari yaje gida yaga anty Mimi ta kirashi dazu ta yuyu ko tana neman sa ne, tare suka tafi da suhana ya sauketa itama a gida zata ɗora girki, part din hajiya ya shiga inda anan ne anty mimin take, tana zaune bakin gado daure da jan towel ta fito daga wanka idanuwan ta jajur saboda kukan da ta sha, knocking yayi tace "come in..." saboda duk tunanin ta hajjo ce ko kuma ɗaya daga cikin hadiman gidan, har ya shiga cikin dakin bata san shi ne ba dan gaba daya tunani ya cika kwakwalwarta, tsaye yayi yana kallonta wanda ita sai da taji shurun yayi yawa sannan ta kai dubanta hanyar ƙofa nan taga ya zuba mata ido ko ƙiftawa baya yi......