GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 33

by @nusybee143

Page 33





Maman Ahmad da umman faruku ma ba su yi sanya ba suka rufawa maman jidda baya zuwa ɗakin da Shaheeda take, Shaheeda kuwa wadda take jin duk abin da suke cewa tuni ta tashi zaune tana jiran shigowarsu,ko ma me za su yi mata su yi mata,ita yanzu ta daina tayar da hankalinta akan ko menene ma zai same ta rayuwa,gwara ta koyawa zuciyarta dakewa da juriya 

Ko sallama maman jidda bata yi ba ta bankaɗa labule ta shigo tana aikawa Shaheeda wani mugun kallo, Shaheeda ta dai ko motsawa daga inda take zaune bata yi ba,sai idanu da take ta bin ta da shi,babu jumawa Kuma sai ga umman faruku d maman Ahmad su ma sun shigo ɗakin 

Da wani mugun kallo maman jidda take kallonta, kafin ta ce"wacece ke?

Daga ina kike?

Ina kika samu cikin jikinki?ina buƙatar ki gaya min gaskiya, sannan kuma ki rantse min da Allah cewa gaskiya kika faɗa idan har kina son ki cigaba da zaman gidan nan"

Ita dai Shaheeda ko motsi bata yi ba, asalima bata da niyyar motsin,maman jidda da ta fi su fusata ta ƙaraso inda Shaheeda take ta ɗauke ta da wani mari,sai da ta tintsira 

Gigicewa ta yi,don marin ya shige ta,amma saboda taurin kai bata yi magana ba sai hawayen da ta fara zubarwa

Maman Ahmad ta kalle su tana faɗin "maman jidda rabu da ita,amma mu fincike ta mu jefar a bakin titi idan bata tashi ta bar mana gida ba 

Matsiyaciyar yarinya tun kina ƴar mitsitsiyarki amma kin san makirci?kuma kin san ki kwanta da namiji?"

Har yanzu kuka Shaheeda take yi, kuma babu niyyar tashi,a fusace maman faruku ta fincike ta,ta ƙanƙame jikinta tana runtse idanu,amma hakan bai hana su fincikarta ba,a fusace maman faruku take faɗin "yau ko gidan ubanki ne nan ɗin sai kin bar shi wallahi,shegiya munafuka"ganin za su illata ta ya sa ta miƙe tana kuka ta gyara zaman hijabinta,ta kalle su ta ce"Allah ya ba ku haƙuri"sannan ta goge hawayenta ta nufi hanyar waje

Maman Ahmad ta watsa mata mugun kallo ta ce "Ameen!sai a bi wani sarkin kuma, shegiyar yarinya kalle ta kamar ta Allah"maman jidda tana huci ta ce"haka suke ai,su yi maka lumbu-lumbu su shiga jikinka su cuce ka su bar ka da wayyo Allah, irin wannan kyasa-kyasan da ake samu akan irin waɗannan mutanen ai suna da yawa,shine ba za muyi hankali ba?kuma sai abin ashsha ya faru mu ɗorawa ƙaddara?"

Maman Ahmad ta gyara tsayuwa ta ce"an taɓa samun makamancin haka fa da ƴar babbar yayarmu,wai mijin ya taimakawa wata yarinya ya kai ta gidanta, shegiya ashe tana biye-biye, ƙarshe ta aure mijin ta kori waccan matar,daga baya ma ta yi mata asiri ta kusa haukacewa, Allah ya taimaka aka shawo kan abin"

Maman jidda ta riƙe haɓa ta ce"oh Allah!

Ki ce mutanen nan matsiyata ne,ki taimaka musu ki janyo su daga rana zuwa inuwa,daga sun ji sanyi sai su tura ki wuta, a'a wallahi,su yi zamansu a rana, Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani"ta fice daga ɗakin tana jinjina abin,su ma sauran matan suka fito suna kakabin lamarin Shaheeda, musamman yadda ta kafe ta ƙi magana,hakan ya tabbatar musu bata da gaskiya 

Shaheeda kuwa tana fita ta goge hawayenta,kai tsaye ta nufi titi ta samu abin hawa,ta ce a kai ta kasuwar gwal,babu musu ya ɗauke ta suka tafi

A hanya sai sauke ajiyar zuciya take yi, saboda ta ji daɗin abin da ya faru ma zata ce kai tsaye,jiya da ta rasa yadda zata yi,ga yunwa ga rashin matsuguni,kuma babu ko sisi a hannunta,sai Allah ya kawo mata baban faruku,a gidansa ta kwana kuma ta ci abinci,kuma a ƙarshe ya ba ta kuɗin da zata kashe, wanda ya zamar mata kuɗin mota 

Yana sauke ta ta nemi inda zata siyar, kasancewar babu receipt ya sa ba'a siya da daraja sosai ba,don zoben ƙimarsa zata kai 600k saboda diamond stone da yake jikinsa,amma a 400k ya tashi,hakan bai dame ta ba,ta karɓi kuɗinta ta wuce kasuwa ta siya kayan jarirai, sannan ta samu laptop wadda bata gama shan jiki ba,da waya ƴar madaidaiciya ta siya, sannan ta wuce inda zata kama hotel 

Mai sauƙin kuɗi ta kama na kwana uku,don ta san zai iya janta waɗannan kwanakin kafin ta sami gidan da zata zauna 

Ai kuwa da ƙyar ta samu,don bata san kowa ba,sai da ta je gidan mai unguwar yankin,ta shirya ƙarya kamar yadda ta shiryawa baban faruku,mai unguwa ya tausaya mata,har ya ba ta dubu biyar,ta yi ta godiya 

Gida ne madaidaici aka samar mata,sai dai ba ita kaɗai ba ce,gaba ɗaya gidan ɗakuna uku ne,wasu sun kama biyu ita kuma ta kama ɗaya,a ranar ta siya madaidaiciyar katifa da yan abubuwan buƙatu bayan ta siyar da ɗan kunnenta,duk da nauyin cikin jikinta ta miƙe zata fara gyaran ɗakin 

Sallama aka yi mata,ta juyo tana kallon matar wadda ba zata wuce ta ba a shekaru,amma saboda talauci da babu gaba ɗaya ta lalace, ƙuruciyarta ma tana neman ta ɓuya, Shaheeda ta yi wa matar murmushi itama tana kallonta,matar ta ce"bari na taya ki ko?"

Shaheeda ta ce"na gode"daga nan suka mayar da hankali sosai ga gyaran ɗakin,amma matar ita ce ƙarfin aikin 

Bayan sun gama Shaheeda ta yi ta yi wa matar godiya,matar tana murmushi ta ce"kar ki damu,ba komai,bari na zubo mana abinci"bata jira amsar Shaheeda ba ta yi waje "

Faten tsaki da yakuwa ne,ya burge Shaheeda,duk yadda ta so ta yi kara kasawa ta yi, saboda yadda faten ya rinƙa tsinka mata yawu,ai kuwa ta ci shi sosai,ta yi ta yiwa matar godiya, matar tana murmushi ta ce"ai ke ƴar'uwata ce,ya sunanki?

Ni sunana AZEEMA,ni da mijina daga wani ƙauye muke a can Ghana,bamu da kowa a nan"Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma sunana Fatima,mijina ya rasu babu jumawa,gashi bani da kowa"Azeema cikin jimami ta girgiza kai ta ce"Allah sarki! Allah ya ji ƙanshi ya yi masa rahama "Shaheeda ta lumshe idanu kawai bata ce komai ba

Wat guda da tariyar Shaheeda,gaba ɗaya damuwarta a yanzu ta kau, saboda Azeema da mijinta RABI'U sun ɗauke ta tamkar ƴar'uwarsu, musamman da ya kasance mijinta ya rasu,kuma bata da kowa,su ma kuma ba su da kowa sai kansu,sai kuma ita da Allah ya kawo ta rayuwarsu 

Shaheeda ta kula da yadda talauci ya ci jikinsu sosai,wani lokacin ma abin da za su ci sai sun yi da gaske suke samu,amma duk da haka in dai sun yi girki ko yaya ne sai sun ɗibar mata

Karamcin mutanen yana matuƙar burge ta,har ta ji a ranta ya kamata ta zama wata itama don ta taimake su watarana 

Tun daren jiya take ta fama da matsanancin ciwon mara,amma kasancewar bata taɓa haihuwa ba sam bata kawo naƙuda take yi ba,sai da abin ya tsananta,tana durƙushe tana fama da kanta Azeema ta shiga da sallama 

Ɗagowa ta yi idanunta suna chanja kamanni tana kallon ta, Azeema ta ƙaraso da sauri tana faɗin "me ya faru?

Ba ki da lafiya ne?"

Murya ƙasa-ƙasa ta fara faɗin "bayana!marata!!ji nake yi kamar zan mutu"gaban Azeema ya faɗi,a tsorace ta ce "ko dai haihuwa ce?"gaban Shaheeda ya faɗi,a tsorace ta ce"ina ga ita ce"Azeema ta miƙe a tsorace tana safa da marwa,bata san yadda zata yi mata ba,itama Shaheedan bata san yadda za'a yi mata ba,gashi ba su da kuɗin motar da za su tafi asibiti,gashi Rabi'u baya nan,yana wajen aikinsa na gini da yake yi idan ya samu 

Haka Shaheeda ta wuni ta malelekuwar azaba,tun tana kuka Azeema tana taya ta,har bakin ya mutu 

Sai daf da magriba Allah ya yankewa Shaheeda ta haifi ɗanta,sai dai kallo ɗaya Shaheeda ta yi masa,duk bata san yanayin jariri sabuwar haihuwa sosai ba, kasancewar Ummeey bata haihuwa,kuma matan gidansu ko sun haihu sai ta ga dama take shiga,kuma ba sa ba ta ɗan,amma a haka ta gane nata jaririn ba shi da ƙoshin lafiya, musamman yadda numfashinsa yake fita da yadda yake kuka a wahale

Azeema ce ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa ta goge masa jiki, ta yi masa wanka,don dama ita ta iya kula da jariri kasancewar ta taɓa haihuwa ɗan ya rasu bayan ta gama shirya shi sannan ta fita maƙobtansu,akwai wata tsohuwa,ita ce ta taimakawa Shaheeda ta yi wanka ta gyara jikinta 

Sai da suka nutsu, Shaheeda tana cin abinci sai ga Rabi'u,ya yi murnar ganin Shaheeda ta haihu lafiya,amma ya yi ta yiwa Azeema fadan meyasa ko maƙobta bata shiga ta aro waya ta kira shi ba, Azeema ta ce ta sha'afa ne, saboda yadda suka gigice a lokacin 

Ya ce"ki dai rinƙa kulawa, yanzu dai alhamdulillah,amma duk da haka sai mun je asibiti an sake duba ta,ga wannan kuɗin ki adana"ya miƙa mata dubu biyu,ya ce"wannan kuma"ya nuna mata kuɗin da za su iya kai wa biyar zuwa sama ya ce "sai a duba ta da yaron ko?"

Azeema ta ce"tabbas ka kawo dabara,don wallahi yaron magana ne kawai ban yi ba,amma kamar bashi da lafiya,ni kaina a tsorace nake wallahi, daɗinta ma uwar bata san yadda jariri yake ba da alamu,amma yaron nan ba shi da lafiya"

Da haka suka yiwa Shaheeda magana,bata yi musu ba ta bi su suka nufi asibiti

A can aka duba ta,ita dai babu wata matsala sosai, amma jaririn nata likitoci sun bayar da tabbacin cewa yana ɗauke da larurar asthma, wadda alamu ya tabbatar da gadonta ya yi

Hankalin Rabi'u ya tashi sosai,ya koma ya same ta yana tambayarta da yi mata bayani, bata damu ba sosai,kuma bata yi mamaki ba,ta dube shi ta ce"tabbas haka ne, mahaifinsa ya tabbatar min da cewa nashi mahaifin an ce ciwon asthma ne ya kashe shi,babu mamaki don ya samu shima"Rabi'u ya jinjina kai cike da jimami ya ce"Allah ya ji ƙansu baki ɗaya 

Kin tanadar wa yaron suna?"

Girgiza kai Shaheeda ta yi, Rabi'u ya ce"ya sunan babansa?"

Shiru Shaheeda ta yi, kafin ta yi shahada ta ce"Mubarak!"

Rabi'u ya ce"to ai kuwa za'a mayar masa da sunan babansa, Allah ya raya shi ya albarkaci rayuwarsa, Allah ya raya mana MUBARAK"

Kallonsa ta yi tana ɗan murmushin yaƙe, don bata so hakan ba,amma gudun kar asirin da ta binne ya tonu ya sa bata yi magana ba, Rabi'u bai kula ba ya ce"me za'a rinƙa kiransa?"

Shaheeda kanta a ƙasa ta ce"a kira shi da Mubarak ɗin sa,ya fi daɗi ma"

Ba su juma ba aka sallame su,bayan an ɗora Mubarak akan magani da ganin likita, sannan ga dokokin da aka kafawa Shaheedan akanshi 

Ranar suna Rabi'u ya yi ƙoƙari, don hakika ya yankawa Mubarak banda kayan jarirai da suka yi ƙoƙarin shigowa masu sauƙin kuɗi duk da cewa itama Shaheedan ta siya,ya yiwa Shaheeda ɗinki mai kyau,aka yi taron suna daidai misali, wanda ya saka Shaheeda tsananin farin cikin da ta juma bata yi shi ba

Dukkansu daga Rabi'u har Azeema ba su ɗauke ta komai ba sai ƴar'uwa,sun riƙe ta da zuciya ɗaya,sun cike mata gurbin da ya yi mata saura, to ita kuwa me zata yiwa bayin Allan nan ta biya su?ko ta faranta musu?

Hakan ya sa bayan ta yi arba'in ta fara tunanin ta bi kamfanoni don neman aiki,amma kafin ta fara wannan yunƙurin sai da ta gayawa su Rabi'u 

Dukansu sun goya mata baya tare da fatan Alkhairi, Azeema tana murmushi ta ce"ki ce mun kusa zama cele a garin nan,don masu aikin kwamfutan nan Allah kuɗi suke samu sosai,su ne fa za ki ga suna hawa jirgi suna barin ƙasar nan"

Ƴar dariya Shaheeda ta yi, Azeema ta ce"Allah da gaske,ko don ke ma watarana ko ba mu hau jirgi ba ai za mu gani, Allah ya kai damo ga harawa kawai"Shaheeda ta yi murmushi tana girgiza kai,da Azeema ta santa ai ba ma zata fara faɗar hakan ba

Cikin lokaci ƙanƙani ta fara neman aiki,da wani kamfanin software ta fara,bayan ta gama ganawa da Manager ɗin kamfanin ta sanar masa da abin da ta karanta, kai tsaye ya buƙaci ganin takardu 

Idanunta suka yi ƙwal-ƙwal,a sanyaye ta ce"ban ƙarasa karatun ba ai, saboda matsalolin rayuwa da suka sha min kai,amma....."mutumin ya katse ta faɗin"ba ki da takardu kuma kike tunani za mu ɗauke ki aiki?"

Shiru ta yi jikinta a sanyaye, kafin ta ce"na iya aikin fa,ku gwada ni ku gani,ban damu ba ko da ace rabin kuɗi za ku bani ba,ni dai ina roƙonku don Allah ku ba ni aiki, ko yaya za ku biya ni zan yi"mutumin ya ƙare mata kallo, ganinta matashiyar yarinya mai jini a jika,kuma kyakykyawa sai ya gyara zama ya ce"to zan ba ki aiki a companyn nan,babban matsayi ma, amma da sharaɗi"

Cikin ɗoki tana murmushi ta ce"menene sharadi?"kai tsaye ya ce"za mu kwana tare,kuma duk sanda na neme ki za ki biya min buƙata,idan kika yi haka I'm ready"






#Nusy_bee