MARTANI BY RUKAYYA YUSUF IBRAHIM (A. Y. M Creatives)

MARTANI Episode 0ne

by @aymcreatives


MARTANI

A Story of Retribution

Rukayya Yusuf Ibrahim 
(A. Y. M Creatives)



Arewapen!@https://www.arewapen.com/u/aymcreatives


GMJ/26/49

GODIYA
Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhamdulillahi Rabbil 'Alamin.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (Subhanahu wa Ta'ala), Mai kowa da komai, wanda Ya ba ni lafiya, lokaci da ikon fara wannan aiki. Ina roƙonSa da Ya ba ni damar kammala shi cikin alheri, Ya sanya abin da ke cikinsa ya zama haske, nasiha da darasi ga al'umma. Allah Ya sa duk wanda ya karanta wannan littafi ya amfana da saƙon da ke cikinsa. Amin Ya Rabbal 'Alamin.
Ina miƙa godiya ga dukkan iyaye, malamai, 'yan uwa, abokai da masu ƙarfafa mini guiwa da addu'o'insu. Allah Ya saka musu da alheri.

SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafin ga duk wanda ya taɓa yin kuskure ya yi nadama, ga duk wanda aka zalunta yake jiran adalci, da kuma masu imani da ƙaddarar Allah, masu yafiya, da masu haƙuri a lokacin jarabawa."
Allah Ya sanya wannan aiki ya zama sanadin ƙara mana kusanci da gaskiya da adalci. Amin.

SHIMFIƊA
Rayuwa cike take da ƙaddara, Ruɗani da sakamakon laifikanmu. Wasu kurakurai kan zama ƙanana a idanun masu aikata su, amma zunubinsu kan shafi rayuwar mutane da dama.
MARTANI labari ne da ya ginu a kan soyayya, zalunci, yaudara, nadama, tarbiyya da sakamakon abin da mutum ya aikata. Yana ɗauke da darussa da za su tunatar da mai karatu muhimmancin tarbiyyar yara, adalci, gaskiya, yafiya da kiyaye haƙƙin mutane.
Ina fatan wannan littafi zai nishaɗantar da ku tare da ilmantarwa, ya kuma zama abin tunani ga duk mai karantawa.
GARGAƊI
MARTANI ƙirƙirarren labari ne. An rubuta shi ne domin nishaɗantarwa tare da isar da saƙo da darasi ga al'umma. Duk wani kamanceceniya da sunaye, wurare ko abubuwan da suka faru da rayuwar wani ko wata, kamanceceniya ce kawai ba da gangan ba.
Haƙƙin mallakar wannan littafi na marubuciya ne.
Ba a yarda a kwafa, a sake wallafawa ko a juya shi zuwa kowace siga ta (audio, fim, ko wani tsari), ko a rarraba shi ta kowace hanya ba tare da izinin marubuciya ba. Yin hakan ya saɓa wa dokokin haƙƙin mallaka kuma za a ɗauki matakin da ya dace.

 

بسم اله راحمن ارحىم


"A'isha...A'isha.. A'isha.." Umma ta kira sunan A'isha da karfi cikin daga murya.
Fitowa tayi cikin natsuwa tana cewa "na'am Ummana gani nan zuwa ".
Jugum wacca aka kira da Umma tayi , tana jiran zuwan A'isha.
A'isha ta nufi gurin da take tana duban Umman ta ce " gani Umma me ya faru ne ?" . 
Ajiyar zuciya Umma ta sauke ta dan yi shiru kamar me nazari sai kuma ta ce" kawunki ya zo ɗazu bayan kin fita makaranta".
Dafe ƙirji tayi idonta sun ƙwalalo waje alamar firgici tana duban Umman cikin rawar baki ta ce" ba dai maganar fitar da mijin yayi miki ba?".
Sauke zazzafan numfashi tayi hannunta kan sandar da take gefenta ta fara cewa " hakuri zakiyi A'isha domin wannan karon ba ma zancan ki fitar da mijin ba ne .
Ya riga da ya aura miki aure dazun nan bayan sallar Jumma'a".
Tunkan ta ƙarasa A'isha ta miƙe cikin tashin hankali, idonta na zubar da wani zazzafan hawaye , ta ma kasa magana sai girgiza kanta kawai take tana kallon Umma.
Umma jin shirum da tayi ga kuma sheheƙar kuka da take ji yasa ta miƙa sandarta tana cewa " kina ina A'isha? Kar kiyi kuka kinji. 
Kar kiyi kuka Aishatu, ina ji a jikina wannan auran alkhairi ne ba sharri ba a gareki.
Bana so ki tayar da hankali don Allah, a yanzu bani kowa sai Allah sai ke da ɗan uwanki.
Muddin kika bijire to tabbas baza su ƙyalle mu ba".
Umma ta share hawaye ta cigaba da cewa " ki tuna abunda ya faru a baya da ƴar uwar ki A'ishatu . Idan kika nutsu; kika yi tunani sai kiga suna da gaskiya, auran shi ne rufin asirinmu baki daya".
Cikin kuka ta fara cewa "Umma don Allah karki dinga tuna baya , duk da ban san me ya faru ba amma ina da tabbacin kaddara ce ta faɗawa Yaya Halima.
Umma kun bamu tarbiya iyaka ƙoƙarin ku , babu wani ko wata da zai canza mana tarbiyyar banda ƙaddara.
Babban burina shine nayi ƙaratun nan , na samu madafar da zan dinga kulawa da ku Umma.
Ki duba Adnan har yanzu yaro ne, bai da tsayayyar sana'a gashi karatun ma saboda kudi yana neman gagararsa.
Yayan mu kuma tun bayan da su Kawu suka kore shi ko duriyarsa ba a sake ji ba.
San nan yanzu Umma ga larurar rashin ganinki, a haka suke so na tafi na barki? Bayan basu san cin mu ko shan mu ba.
Umma kina da haƙƙi akan mu fa, ya kamata ki magantu a wannan lokacin don Allah . Cewar A'isha tana shasheƙar kuka".
Shiru Umma tayi kamar mai nazarin maganganun A'isha sai kuma ta ɗago kamar ganin fuskar A'ishatu ta fara cewa"A'ishatu kenan " .
Kafin ta nisa ta ce" danginku ne su , kuma dangin ma na mahaifi. 
Wadanda suke da iko sosai a kanku, don haka kuyi hakuri da komai ya faru da ku Allah na tare da ku.
Duk wani abu da kika ga yana faruwa da bawa, to ba Allah yana yi masa haka ba ne don cutarwa. Hasalima wanda yafi jarbata sai kiga Allah ƙaunarsa yake.
Ni bani da bakin maidawa danginku MARTANI akan duk abinda suka ga ya dace daku. Nasani in har cutar da ku suke to Allah bazai barsu ba domin shi baya zalunci, kuma ya sanya zalunci ya zama haramun acikin bayinsa.
Kunga kuwa muddin suna zaluntarku da kansa zai maida musu da MARTANI".
A'isha kukanta ne ya ƙaru ,yaƙi tsayawa sai kallon mahaifiyarta take cike da zallar mamakin waccan irin zuciyace a kirjinta.
Shin da gaske ne dole dangin ubanka suna da iko da kai ko a Muslunci, ko kuma al'adar Malam bahaushe ce?.
Umma shiru tayi tana jin sautin kukan yarinyarta, domin babu idon ganinta.
Ita kaɗai tasan me take ji a ranta, babu yadda zata yi ne , don ance fadan da yafi ƙarfinka sai ka maida shi wasa .
Amma tabbas mutane da yawa sun dasa mata baƙin ciki a zuciyarta , ciki kuwa har da dangin mijinta. 
Bakin cikin da har ta mutu baza ta manta da shi a rayuwarta ba.
Amma ta riga tayi imani da cewa "duk abunda ya faru da ita ƙaddara ce. Kuma idan bata da haƙƙi ko mai daran dadewa Allah zai maita sakayya.
" Umma wa suka aura min?" Muryar A'isha ta tsaida tunanin da Umma take.
Gyara zamanta tayi ta ce" ban sani ba A'isha amma ya ce Mahaifin yaron abokin Baffan Birni ne.
Dan Allah A'isha kiyi hakuri ki karbi hakan a matsayin ƙaddararki. Ina so kisa a ranki mijin so kika aura .
Dan Allah kiyi masa biyayya sau da ƙafa, nasan baki da damuwa zaki iya zama da kowa a lafiya a duk inda kika shiga wannan zan shaide ki.
Amma ki sani ,babban burin makiyanka suga gazawarka. Ina so ki nuna tamkar da son ranki akayi auran nan don Allah".
Kallon Umman tayi zuciyar na mata zafi-zafi san nan ta ce" Umma ai tunda sun daura min aure dole ne nayi biyayya ko dan kaucewa sabawa Allah.
Allah ya taimake ni ban sa son kowa a raina ba , balle zuciyata ta kasa karbar mijin da suka aura min.
Zanyi biyayya Umma in sha Allahu san nan bazan hakura da karatuna ba , zan fadawa Kawu da kuma aikin koyarwar nan.
Tunda in na barsu da me zaku dinga cin abinci".
Girgiza kai Umma tare da cewa "kar kiyi sabo mana A'isha, bakin da Allah ya tsaga ai ba ya hana shi abinci.
Yanzu ki shirya muje gidan Rahana don ya ce wani satin zaki tare".
Bata ce komai ba ta mike hawaye na sake zuba akan kuncinta, ta shiga ta ɗako hijabinta da ta ajiye.
San nan ta dawo ta taimakawa Umma ta saka nata suka fita .
______
"Abinda bazai taɓa yiwuwa ba ma ke nan Yaya" .
Cewar wani matashin saurayi tsayeye kuma ingarmar namiji. Domin kana kallon sa zaka san ya cika da kamala da zati,yana tsaye a tsadaddan falonsu mai kyau.
Cikin shigar manya kaya farara wanda akayi musu plan dikin, wanda yayi daidai da jikinsa. 
Hannunsa ɗauke silver watch mai dankaran kyau.
Kan kujerar dake fuskantar sa wata matashiyar mace cikin shigar marron color Abaya. A kallon farko zaka gane bazata wuce shekara Arba'in da biyu ba ko zuwa da uku ba .
Yayin da gefan hangunsa shima matashi ne kyakkyawa domin har yaso yafi su duk kyau wanda zai yi shekaru 38 ko 39 yana wheelchair da alamun ba shi da lafiyar ƙafa. Duk sun zuba masa ido suna kallonsa .
Babu wanda ya yi masa magana a cikinsu don kansa ya zauna yana hucci.
Cikin ƙarfin hali wacca ya kira da Yaya ta ce" Muna buƙatar hankalinka Ashraf . Wannan auran fa ba muyi shi ba sai da amincewarka don haka baka isa ka kawo mana zancan banza ba".
"Amma Yaya me yasa zaku ce wancan bahagon ta bangaransa za a samu matar da zan aura? Har yanzu bai daina shaye-shayensa ba fa.
Ƴar dan iska abokinsa zai kawo min na aura kenan ko me? Gaskiya a duba lamarin nan.
Ai in haka ne gwara da kaina na nemo wacca zan aura".
"Ashraf...! Ya isa mana, ba abunda kake tunani bane , kuɗi na dauka na bawa Uncle Khasim akan ya nemo mana wacca zaka aura.
Kuma sai da nayi masa gar-gaɗi akan cewa sai ta ciki waddan nan dokokin.
Na farko mai hankali , na biyo wacca tasan ilimin addini sosai kuma mai ilimi zamani ko ya-ya ne. Na uku kuma mai tsafta da hakuri domin zuri'a zamu haɗa da ita.
Kuma naji dadi domin Kawu Malan ya tabbatar min da cewa ƴar gidan mutunci ce".
Wani shu'umin murmushi Ashraf ya saki kafin ya ce" ƴar manyan mutane baza a siye ta da kudi ba , don haka kawai a janye maganar nan Yaya".
Ajiyar zuciyar tayi haɗi da gyaran muryatare da gyara zamanta tana fuskantar sa ta ce " Allah Ashraf zan hukuntaka da tsatsauran hukunci . Ya ina faɗa maka abu kana kaucewa, a'a?".
" Sorry second Mom amma.." ya faɗa yana sunkuyar da kansa.
Tayi saurin dakatar da ta hanyar cewa" ya isa Malam yarinyar nan zamu gwada ta kafin mu saki jikin mu da ita fa, duk yadda ya faɗa dole sai munga shaida da idanun mu".
Sauke numfashi yayi da kyau kafin ya ce" ta ya-ya kenan?".
Ta buɗe baki zata yi magana kenan wata matashiyar mace ta shigo cikin shigar atamfa Dinkin T bubu ta kafa ɗauri tana taunar cigum.
Wuce su tazo tayi ba tare da tayi musu sallama ba.
Ajiyar zuciya duk suka sauke suma ba tare sun bi ta kanta ba .

"Yaya labib kayi shiru baka cewa komai" cewar Ashraf da ya katse musu shirin da ya ratsa.
Murmushi yayi ya ce" plan din mu da muka shirya akan matarka shine.
Zeenah ce mata ta ita kuma Yaya Rumana mai aikin mu".
Don muna so muga ta yaya zata mu'amalance mu".
Cikin ɓacin rai ya ce" haba!haba Yaya Labib ta ya zaka zauna ka dinga amfani da shawarar mata. Yanzu ita waccan banzar me zata iya yi banda rashin kunya , da zubar mana da mutunci a gaban bare..".
"Ayi hir din ka Malam Ashraf, ina raga maka ne saboda bani da matsala da kai da kuma wasiyyar iyayenmu.
Kayiwa bakin ka linzami akan faɗin mummunan kalma a kaina" faɗin Zeenah da tayi saurin fitowa kamar an jeho ta .
Ta cigaba da cewa" da kake iƙrarin zan zubar da kima da mutuncinku a gaban bare, wallahi ka ji kunya.
Ina mutuncin?, Ina ƙimar da za a zubar? Na rantse da Allah tausayin yarinyar da za auro nake ma. 
Domin za a cutar da ita ne a sa ta haɗa iri da mu . Ni da zaku ji shawarata ku hakura mu zauna a yadda muke domin kar mu ɗorawa kan mu wani zunubin, ba mu gama wanke wanda ya gabata ba da wanda aka mutu a kabar mana saurans...".
Zazzafan marin da taji ne ya sanya tsaigaitawa da maganar ta bata shirya ba.
"Mari? Mari ! Yaya Rumana? Me nayi Miki?" Cewar Zeenah tana kallon babbar Yayarta su hannunta riƙe da kumatunta.
Cikin hucci Yaya Rumana ta fara cewa " an mareki din , kiyi abinda zakiyi.
Ki sani zan jure duk wani wulakancinki amma banda tabo iyayyan mu da suke kwance cikin ƙasa.
Ki ƙyalle su huta mana, wannan waca irin masifa ce Zeenah!" Ta karasa maganar cikin daga murya.
Mutmushi Zeenah tayi hadi da tafa hannu kafin ta ce" ai babu su babu hutu Yaya Rumana tunda ba su shuka iri me kyau a duniya ba .
 Don Allah kada ku wahalar da kanku da bakinku. 
Binta da kuma Saude sai da su shiga Rahamar Allah tunda shi Allah Mai Rahama ne amma basu yi abinda Allah zai dube su ba".
"Ze..Zeenah ! Baki da hankali ne wai ? Iyayyan mu kike fadawa wannan maganar?".
Juyawa tayi tana kallon Labib dake kan wheelchair ta saki murmushi mai sauti ta ce " Alhaji Labib har kana da bakin magana kenan. Kai da Allah ya fara yanke ma hukunci tun a nan kana nan ƙafufuwa a naɗe.
To shawara zan baka a matsayina na matar dole a gurinka, domin mummunan ƙaddarar ce zama da kai a matsayin miji wanda bai da amfani.
Don na riga da nasa a raina kai ne abunda aka jarfce ni da shi . To ina mai baka shawara ka koma ga Allah ka dage da istigifari kafin lokacin cikawa.
Ka fita sabgar hada auran nan da za a yiwa Ashraf domin ko an samu zuri'ar dole sai dai ace ƴanƴan ƙaninka ne ba na ka ba.
Kuma baku da tabbas din cewa shi din me haihuwa ne , domin bazai yiyu shima ya ci bulus ba , tunda haƙƙinku zai bibiyeshi ".
A fusace Ashraf ya matso kusa da Zeenah yana hucci ya dunƙule hannunsa zai dake ta, Yayarsu ta riƙe shi.
Cikin kunar rai ya fara magana amma taƙi fita, domin basa jin me yake cewa.
Kawai sai ya fice daga gidan idonsa ya kaɗa yayi ja sosai.