YARIMA BAHJAT

Shafi na uku

by @uwarbatoorl96

YARIMA BAHJAT 🌏

        Na

Harira Salihu Isah

   (Uwar Batoorl)

Wannan shafi naki ne Dr Seeeyert

SHAFI NA UKU

⭐️

Zancen zucin Fulani Samira ne ya katse sanadin ƙiran sunanta da Gimbiya  Hadiza tayi.

Wani nauyayyan ajiyar zuciya Fulani Samira ta saki, tana mai share hawaye a fakaice.

"Gimbiya kun shigo ne?"

Fulani Samira ta tambaya da murya mai cike da damuwa.

"Eh!"

Gimbiya Hadiza ta amsa a taƙaice tana mai aikawa Fulani Samira wani irin kallo.

Fulani Samira yi tayi kamar bata lura da kallon ba, ta cigaba da sharar ƙwallarta tana bai wa Fulani Hajara baki cike da jimami.

⭐️

MASARAUTAR BAHJA

"Ciki yana nan daram"

Boka dodongaji ya faɗa ba tare da ya ba wa Sarki Gamboji damar amsa tambayar da ya masa da farko ba.

"Hnnn!"

Sarki Gamboji ya sauƙe wani ƙaƙƙarfan numfashi, wanda yake riƙe da shi tun sanda Jakadiya ta kawo masa labarin zubar jini ga Baiwa Kubura.

Wani busashshen murmushi mara kyan gani boka dodongaji ya saki, saboda sautin sauƙar numfashin Sarki Gamboji, da yayi daidai da hayagagar wutar da ke hure a gabansa saman iska.

"Fiye da yadda wannan wutan yayi amo, haka ka sake zuzuta lamura, ka sake caɓa komai, wanda ke nufin komai na iya faruwa a masarautarka, idan na ce komai ina nufin komai, fiye da abu na ƙarshe mafi muni da zuciyarka za ta iya haƙaito maka."

"Indai ciki na nan daram lafiya to komai ma ya faru, domin kuwa mai tsoron ta kife shi ne gawan farko, a haife mini jika shi ne babban buri na, na samu shaƙiƙin magaji, Yarima Bahjat ya zo duniya, a kuma ranar da aka haife shi, a ranar zan damƙa masa karagar shi."

"Duk gaggawan asara dole ta jirayi samu, Sarki Gamboji ba zai yiwu ka bawa jariri mulki ba, dole sai ya kai shekarun riƙe karagar shi, idan damuwarka kan abinda zai iya zuwa ya dawo ne, kana da dodongaji, ka kuma yi imani da dodongaji, ka yarda da dodongaji, wannan ciki duk iya ƙulli da surƙullen masu bacci da ido guda, dole sai an haife shi, kuma namiji za ta haifa, sai ya kuma mulki wannan daula, Sarki Gamboji kar ka bari imaninka ga dodongaji yayi rauni, domin hakan na nufin lalacewan duk lamarunka, za ka taɓe, za ka ɗaiɗaice."

"Hakan ba zai taɓa yiwuwa ba dodongaji, ba abinda zai raɓi imaninmu da ku, kuyi komai yadda kuka saba, wuta ta ba ku sa'a."

  Sarki Gamboji ya faɗa ya na kai hannunsa ya dafa goshinsa gami da rusunar da kai.

"Ka koma ka sha zamanka, ka cigaba da tafiyar da sha'anin mulki yadda ka so, dodongaji ya tsaya maka, duk rintsi wannan cikin sai an haife shi tunda aka same shi, daga yanzu badakiren Aljani ƙunƙur da tawagarsa za su ke bai wa abun cikin tsaro na musamman, har zuwa lokacin da za ta haife shi, ka kwantar da hankalinka Sarki Gamboji, kamar yadda na faɗa maka ne tun a ranar farko, za'a haifi Yarima, kuma shi zai mulki masarautar nan bayan kai."

"Sanin haka ya sa na feɗe biri har wutsiya a idon maƙiya, tunda ba yadda aka iya da magajin Bahja, dole sai ya zo duniya kuma sai ya mulki Bahja."

  Sarki Gamboji ya faɗa yana mai jin salama a zuciyarsa, domin sai lokacin ya nitsa, har wani basaraken murmushi ya saki.

"Amma.."

Maganar Sarki Gamboji ya katse saboda ɗaga masa hannu da boka dodongaji yayi.

"Sarki Gamboji, idan lokaci yayi da ya kamata ku san komai to zan sanar muku, amma ba yanzu ba."

Guntun numfashi Sarki Gamboji ya ja ya sauƙe, domin ya so a yau dodongaji ya sanar da shi, abinda ke tafiya a gidan Abdi, wanda dalilin ɓoyayyen abinda ke tafiya, ya sa suka yanke wannan hukunci na bai wa abun cikin baiwa Kubura sarautar Bahja.

***

Cikin ikon Allah aka bai wa baiwa Kubura duk wani taimako da ya kamata a gargajiyance, kuma jini ya tsaya a take.

  Sai bayan da ta huta zuwa wasu ƴan awanni, Magajiya ta sa amintattun bayinta suka taimaka mata, ta sake gyara jikinta, ta shirya cikin kayaki na alfarma, domin kasancewarta mai ɗauke da cikin Sarki na gobe, to matsayinta ya wuce na ƙasƙantacciyar baiwa, uwa take ga Yarima Bahjat.

Abinci na alfarma aka wadata ta da shi, wanda ke ƙara sinadaran da ake buƙata ga mai juna biyu.

  Bayi mata na sashin Magajiya suka ta ɗawainiya da ita da hidimta mata, har sai da ta kwanta sannan suka fice domin barinta tayi bacci cikin nitsuwa.

***

"To Mama Argiji me amfanin sunayenmu na matsayin da aka bamu? Idan an san wani can banza ake jira a haifa ya zama Sarki, to me amfanin bani matsayin Yarima da aka yi? Akan me za'a lasa mini zuma a baki kuma a hana ni shanyewa? Wallahi wannan ba adalci bane, sam-sam tsohon nan ba ya abu da lissafi, bai da imani bai da adal...."

"Yarima!!"

Mahaifiyarsa wacce ta kasance mace ta farko ga Abdi, Jaruma Argiji ta Bahja, ta ƙira sunansa da kaurin murya.

"Ki yi haƙuri Mama Argiji"

  Yarima wanda ya kasance ɗan farko ga Abdi ya faɗa, yana mai yin ƙasa da idanuwansa cikin girmamawa.

"Babu ruwanka da wannan faɗan, kar ka kuskura ka lalata mini aiki, ba zai yiwu ina saƙa kana warwara ba, ka kwana da sanin idan hankali ya ɓace to hankali ake aiki da shi domin nemo shi, to dan haka wannan yaƙin nawa ne, kai dai ka kasance a kame yadda ya kamata, ta yadda za ka haye karagar Bahja cikin aminci."

Jaruma Argiji tayi maganar cikin yanayi na jan kunne, da tuna masa me kalamansa za su iya janyowa.

"Zan kiyaye gaba da yardar Allah, Allah ya huci zuciyarku, Uwa Argiji, Jarumar Abdi, Jarumar Bahja, Uwa ga Yarima...."

"Kuma Uwa ga Sarkin gobe"

Faɗin Jaruma Argiji tana mai katse Yarima, fiskarta ɗauke da wani irin murmushin da ita kaɗai ta san manufarsa.

Yarima ba jimawa ya fice cikin taku na izza da ji da kai.

Da kallo Jaruma Argiji tabi Yarima har ya fice, sannan ta ja wani numfashi ta sauƙe, a fili ta ce, "Tsoho Gamboji da ni kake zancen, ai iya masu nufin amsan kujerarka ne ba su isa yin fito na fito da kai ba, amma mu tsaf za mu ƙalubalanceka ko da kuwa ta bayan gida ne, domin abinda kake shirin aikatawa, abu ne wanda ba zai taɓa faruwa ba, a baya bai faru da wasu ba, dan haka a yanzu ba zai fara faruwa a kanmu ba, kai har ma a gaba hakan ba zai taɓa faruwa ba, a tsallake yaran Abdi har goma sha ɗaya a ce ɗan da baiwa za ta haifa ne zai mulki Bahja, zancen banza ma kenan."

"Barkanki da hutawa dai uwargijiyata, Uwa Argiji Jarumar Abdi...."

"Jakadiya!"

Jaruma Argiji ta katseta ta hanyar ƙirar sunanta.

"Rankishidaɗe gwanata, kin ƙira na amsa, ko baki ƙira ba dole na zo."

"Ki shirya mana tafiya zuwa wajan bokan da kika mini magana, lallai-lallai ban amince ba kuma ban lamunce da maganar tsoho Gamboji ba, dan haka tsugunne bata ƙare ba, tunda dama ta ƙiya sai a koma hagu."

"Wannan haka yake Uwar ɗakina, Jarumar Abdi gwanata, lallai kuwa a wannan karon za kiga aiki da cikawa, domin wannan hatsabibin boka, Yautai yake mugun tsuntsu, kowa ya sha miyarsa to yayi dare, akwai tsantsar hatsabibanci da wahala a aikinsa, sai dai akwai biyan buƙata."

  Jakadiya ta ƙarisa maganar cikin tsantsar zuzutawa, da bayar da tabbaci na cin aikin hatsabibi Yautai.

"Duk wahalar aikinsa mai sauƙi ne a wajena ko da kuwa menene, dan haka ki shirya mana tafiya a daren yau, sannan ina kwaɓarki, domin sarai motsinki a kaf gidan nan a tafin hannuna yake, Jakadiya duk ranar da na kama ki da laifin cin amanata sai na tsireki da ranki, Jakadiya duk ranar da na kama ki da fallasa wani sirri nawa, wallahi sai na lahira ya fi ki jin daɗi, ni Jaruma Argiji sai na gana miki kalar azabar da ba'a taɓa ganawa wani mahaluƙi ba a masarautar nan."

"Ban isa ba uwargijiyata, wane ni, ina mai tabbatar miki ko a cikin mafarki na saɓa miki, to ni da kaina ba zan ƙyale kai na ba, biyayya gare ki dole, dan haka bakina ƙanin ƙafata Jarumar Bahja, Jarumar Abdi, Giwar Abdi, Sarauniyar Abdi."

"Kowa yayi da kyau zai ga da kyau, domin kin fi kowa sanin duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, dan haka za ki iya ficewa ki bani waje, zuwa dare za mu tafi kar ki kawo mini wani tangarɗa."

Jaruma Argiji ta ƙarishe maganar cikin shan ƙamshi, tana taɓe baki.

Jiki na rawa Jakadiya ta miƙe ta fice, ko da ta bar sashin Jaruma Argiji, numfashi ta tsaya tana mayarwa, a zuciyarta take faɗin Allah ya raba ta da kaidin Jaruma Argiji, domin sanin kanta ne hatsabibanci da kaidin Jaruma Argiji ya wuce duk lissafin mai lissafi.

   Shiyasa a kullum take addu'ar kafun zuwan ranar da Jaruma Argiji za ta san, tana tare da Jaruma maitakalmi a bayan fage, to Allah ya ɗauki numfashinta kafun zuwan ranar.

"Kaska raɓi mai jini!"

Maganar da ya katsewa Jakadiya zancen zucinta kenan, wanda tun kafun ta kai ga kallon wacce tayi maganar, tuni zuciyarta ta shaida mata ko wacece, tunda ta kwana da sanin wacce take takun saƙa da ita a gidan, ita kaɗai ke iya yaɓa mata magana a ko ina cikin ruwan sanyi.

"Uwar Bayi!"

Jakadiya ta ƙira sunanta da murya mai ɗauke da tsana da kashedi.

"Na'am, Jakadiya jakar tsegumi, Jakadiya jakar munafunci, Jakadiya kaska raɓi mai jini ki bar shi da gashi, Jakadiya ganga bugi can bugi nan, Jakadiya abokiyar mutum biyu munafukar mutum ɗaya, Jakadiya....."

"Uwar bayi!"

Jakadiya ta ƙira sunanta a hasale.

"Ina tausaya miki ranar da labulen asirinki zai bankaɗu gaban iyayen gidanki, na san kin kwana da sanin duk cikinsu ba mai imani balle mutunci, a ranar da ɗaya ta san kina wa ɗaya aiki bayan ita to kashinki ya bushe Jakadiya, Jaruma maitakalmi ba ta da Imani ba ta da tausayi, domin duk hatsabibancin Jaruma Argiji ina jin gwanda ita, ki dai bi a sannu, tun kan ruwa ya ƙarewa ɗan kada."

  Uwar bayi ta ƙarishe maganar cikin gatsali.

"Munafuki dai bai ji daɗin rayuwarsa ba, ƴan hassada masu bacci da ido ɗaya, idan kin gama soki-burutsun kya iya kauce mini a hanya na wuce, ni kinga ina da abin yi, ba sakawa rayuwar wasu ido bane a gabana"

  Jakadiya ta faɗa ta na aikawa Uwar bayi mugun kallo.

"Gyara kayanka dai bai zamo sauƙe mu raba ba, amma duk wanda ya ji ya gani zai haɗiye gatari, sakar masa ƙota ake, dan haka mu dai sai mu ce Allah kiyaye ɓacin rana."

"Yauwa, na mance abinda ya sa na iyo ta nan nemanki, Uwar ɗakinki Jaruma maitakalmi na nemanki"

  Uwar bayi na gama magana tayi gaba abinta ta na ƴan waƙe-waƙenta, wanda sarai na habaici ne ga Jakadiya.

Ƙwafa Jakadiya ta saki, a ranta tana ayyana dole tayi maganin Uwar bayi, dole ma ta taka mata birki tun kafun abun yayi nisa, domin ta ga alamar idan ta ƙyaleta to za ta zama barazana ne ga rayuwarta.

"Duk kanwar ja ce."

Faɗin Jakadiya tana hararar inda uwar bayi tabi da kallo, tunda dai ita ɗin ma munafukar kanta ce, kuma makira annamimiya.

Sai da Jakadiya ta ja wani kakkauran numfashi ta sauƙe, sannan ta juya ta nufi sashin Jaruma maitakalmi, wacce ta kasance mata ta biyu ga Abdi, mace mara mutunci mara kirki, mace mai matuƙar ji da kanta, macen da ba ta shayin yi wa kowa rashin daraja, domin ba ta kallon kowa da gashin ido.

Zuciyar Jakadiya na bugawa da sauri-sauri, ta kai hannunta ta tura ƙofar da zai sada ta da sashin Jaruma maitakalmi, tana shiga hadiman da ke sashin suka fara miƙo mata gaisuwa, ta amsa gami da dakatawa sai da aka mata iso, sannan ta ƙarisa har ɗakin Jaruma maitakalmi, inda ta same ta zaune cikin shigarta ta alfarma, ta hakimce ta ɗaura ɗaya a kan ɗaya, kallo guda za ka mata ka san idan ma da abinda ya dameta, to tana daf da maganinsa.

"Barka da hutawa farar jakada, kuturwar uwa zama dake dole, mai takalmi kike kowa ya so lafiyar ƙafarsa dole ya so ki, fara mai farar aniya, yaɗin mage kowa ya ci ki sai yayi amai, nan a ganki nan a barki farar tumfafiya, rigafi kin fi magani, rumbun kasa a tashi a barki dole, ƙarfe duka ƙarfe ne, amma ko a cikin ƙarafan akwai Zirnari akwai azurfa, don haka ko a cikin Jaruman ma ke ce ta gaba kin shallake kowa, ta gaban goshin Abdi, Jarumar Jarumai."

"Jakadiya."

Jaruma maitakalmi ta ƙira sunanta da sassauƙar murya, tana gyaɗa kai uwa ƙadangariya.

"Na'am bangon sikari, maitakalmin Bahja, farar jakada, Uwa ga Sadauki, Uwa ga Tafida, Uwa ga matawalle, Uwa ga Sarkin gobe, Sardauna Sarkin gobe ko a so ko a ƙi, kai maƙi gani ya kau da ido."

"Jakadiya ba na yarda da mutum cikin sauƙi, amma ke na yarda dake cikin aminci, Jakadiya ƴan amin su amshi ta bakinki, ina mai tabbatar miki da idan Sardauna ya zama Sarkin Bahja, to za'a kwashi romon mulki da ke."

"Da yardar Allah sai Sardauna ya mulki Bahja, Allah ya kai damo ga harawa."

"Ko bai ci ba sai yayi ɓarna Jakadiya."

Jaruma maitakalmi ta faɗa tana gyaɗa kai hankali kwance, domin ita ko kaɗan kalaman Sarki Gamboji ba su wani ɗaɗata da ƙasa ba, mulkin Bahja na ɗanta Sardauna ne, bokaye da hatsabiban matsafa marassa adadi sun faɗa mata hakan, kuma ta yarda ta aminta tayi imani da hakan.

"Jaruma Argiji ta umurceni da na shirya mana tafiya zuwa wajan hatsabibi Yautai a daren yau, Rankishidaɗe fatan ba damuwar komai a hakan?"

  Jakadiya ta tambaya.

"Ba komai Jakadiya, ki rakata ku je lafiya ku dawo lafiya, ina kuma yi mata fatan alkairi da sa'a, duk da dai da zan bata shawara taji da na ce ta bar wahalar da kanta, domin Sardauna ne mai mulkar Bahja ba ɗaya daga cikin yaranta, ko kuwa yaran Jaruma Ƴarbaraya ba, jininane zai yi mulki, jinina ni Kanden maitakalmi, dan haka iska na wahalar da mai karayan kara ne kawai."

"Aiki ne ya ganta farar jakada, za kuma mu zuba mata ido ta tayi, kowa ya ci zomo ai ya ci gudu, kowa yayi ya gama Mulki dai ta Sardauna ne, Sardaunan Bahja, Jarumin Bahja, badakiren Bahja, ingarman basaraken Bahja."

"Ya batun ita Kubura kuma Uwar ɗakina?"

Jakadiya ta tambaya.

"Labari ya iskeni na zuwan Ungozomar fada sashin Magajiyar gari, na san dole wani abu ne ya samu cikin, sai dai ban zargi Jaruma Argiji ba, tunda nasan ita hankalinta haɗa shi take da tuwo ta cinye, kafun zaman ba za ta aikata komai ba, sai dai bayan zaman, amma wannan makirar Ƴarbaraya za ta aikata yin komai tun kafun zaman, dan haka ita nake zargi, sai dai ba abinda ya dameni, duk sharar hanya suke mini, idan suka kashe baiwar da cikin jikinta sun rage mini aiki, idan kuma suka bar ta da cikin, aikina zai biyo ta kanta lokacin da buƙatar hakan ta tashi."

  Jaruma maitakalmi ta ƙarishe maganar tana sakin wani hamshaƙin murmushi mai wuyar fassara, ita fa yadda tayi imani da ƙulle-ƙullenta, ta kuma yarda da kanta, to ba ta jin akwai wanda ya isa ya kawo mata wani tangarɗa a lamuranta, ba wannan mahaluƙin.

"Sarki Gamboji fa Rankishidaɗe?"

Jakadiya ta sake tambaya.

"Wannan gawa ne ka ƙi rami, duk sumbatu yake yi, duk fa wanda ya ja da hawan Sardauna karagar Bahja, to ajalinsa ya runguma, za ki iya tafiya Jakadiya, ki kuma cigaba da yin komai a sace, domin ba yanzu nake son yin fito na fito da Argiji ba, da saura, sai ta iso wajan da ya kamata, sannan za ta fahimci ta jima tana aikin banza, tayi ba tayi ba tunda ta rufe ƙofa da ɓatawo, dan hakaki cigabada shiga jikinra da kyau."

Godiya da kuma ƙirari Jakadiya ta dinga zubawa Jaruma maitakalmi, sannan ta tashi ta fice kamar ba komai.

***

Zuwa dare kamar yadda Jaruma Argiji ta buƙata, tuni Jakadiya ta shirya musu komai na tafiya, cikin ɓadda kama suka fice a masarautar, tafiya suka yi sosai cikin wani ƙasurgumin daji, duk da Jakadiya ba yau ne ranar ta na farko a tafiyar ba, amma ta wahala sosai, sai dai ita Jaruma Argiji ko gizau wai an tsikari kakkausa, cikin karsashi cike da mayen nemar cikar muradi take tafiya.

Kafun su isa Jakadiya tayi wujiga-wujiga, ko da suka isa daidai wani jibgegen bishiyar kuka, Jakadiya ce ta nuna wa Jaruma Argiji abubuwan da ake yi kafun isa ga hatsabibi Yautai.

Abu suka samu a wajan suka yanki jikinsu, sannan suka shafa jininsu a jikin bishiyar kukan, ko kafun kiftawar ido wani guguwa ya tarnaƙe wajan.

"Uwargijiyata ki kama hannuna, wannan guguwan shi zai kai mu ga hatsabibi Yautai."

  Faɗin Jakadiya da ke ƙoƙarin miƙa hannu domin ta riƙo Jaruma Argiji.

"Iya nan nake buƙatar rakiyarki, ki jira dawowana."

Jaruma Argiji ta faɗa gami da ɗaga hannuwanta sama ta kulle idanuwanta, a zuciyarta sai ambata kirarin hatsabibi Yautai take yi, kafun can taji kamar guguwar na yin sama da ita tana tafiya da ita, zuwa wasu mintuna kuma a sannu a hankali gurguwar ta fara tsagaitawa, can komai ya tsaya cak kamar ba wani abu mai numfashi a wajan.

"Maraba da zuwa fadar Yautai, ni Yautai hatsabibi, ni Yautai mugun tsuntsu kowa ya sha miyana yayi dare, Argijin Bahja mun san me ke tafe da ke tun kafun ki zo nan, ɗan ki Yarima kike so ya gaji mulkin Bahja, a wajan mu duka wannan shi yafi komai sauƙi, sai dai a wajanki zai zama mafi wahala, duk da haka kuma ki sani, kowa ya zo fadar Yautai kuwa dole sai ya aikata abinda Yautai ya ce, ki na da zaɓi biyu zuwa uku, duk wanda kika yi a ciki to ki ɗauka kawai aikinki ya gama ci, za ki iya buɗe idanuwanki yanzu."

  Wani tsattsaman baƙin guntun dattijo yayi maganar, tsayin gashin gemunsa har kan cinyarsa, irin wari da ɗoyin da ke tashi a wajan zai iya haukata mutum.

Amma a ɓangaren Jaruma Argiji ko kaɗan bata damu ba, buɗe idanuwanta tayi kamar yadda ya ce, sannan ta sauƙe hannayenta, da muryarta mai nuni da ta aminta da komai ta ce, "Ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba, ko wani irin sharaɗi ne, na shirya ni zan cika shi muddin jinina zai zama Sarkin Bahja."

"Hahahaha!"

   Hatsabibi Yautai ya saki wata jahilar dariya, jajayen haƙoransa suka bayyana,  bakinsa na wani irin wari da ɗoyi mai kisa.

"Ina son mutane irinki, ga sharruɗan ki sauraresu da kyau, ɗanki da kikeso ya hau karagar mulki zai tara da ke, ko kuma za ki sadaukar wa aljanu jinin ɗan kishiyarki ta uku, ɗanta Jarma, ko kuma aljanun da za su yi aikinki za su ke tarawa da ke na tsawon wata guda, duk wanda kika zaɓa a ciki za'a sanar da ke sharaɗin yin sa, ammafa ki sani dole sai kin yi ɗaya a ciki, idan kika nemi kaucewa aikata ko ɗaya a ciki, to aljanu za su aikata hakan da ke ta ƙarfin yaji."

"Hahahaha!"

Ya kuma sakin wata dariya mara kan gado, da bakinsa mai shegen ɗoyi.

"Ga wannan, duk yadda za kiyi, ki tabbatar baiwar da Sarki yayi magana a kanta ta ci wannan maganin, cikin ba zai zube ba saboda wanda ya tsayawa Sarki ba ƙaramin hatsabibi bane, amma cikin zai kwanta kwanciya na har abada, wanda hakan ke nufin cikar muradinki cikin ruwan sanyi, ki tabbatar ta ci maganin nan, hatsarin da ke bayan amsar maganinmu kuma ba ta ci ba, ya fi hatsarin da ke cikin baiwa abun cikinta mulkin Bahja, ni Yautai hatsabibin boka, kowa ya zo wajena ya kawo kansa, bin sharaɗina dole, aiki da abinda na bayar dole, kafun ka zo gareni ne sai ka ga dama, amma bayan ka zo na zamo maka wajibabbe, saɓanin haka kuma abinda zai biyo baya mara daɗi ne, hahahahahahaha!"

Hatsabibi Yautai ya ƙarishe maganar da wata mahaukaciyar dariya, wacce sautinta ya karaɗe rijiyar da fadarsa take, sauti mara daɗin saurara mai kuma tsoratarwa.

"Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, karagar kawai, ita ce abu mafi muhimmanci, komai mai sauƙi ne"

  Jaruma Argiji ta amsa cikin dakiyar zuciya da zallar rashin imani.

"Ladan aikinki, uwargijiyar aljanu za ta tara da uban ɗanki Yarima."

  Faɗin Yautai.

Wani irin tsinkewa zuciyar Jaruma Argiji tayi, hakan ya sa cikin sauri ta kai dubanta ga hatsabibi Yautai, cike da fatan ya dakata da abinda yake shirin faɗa take kallonsa, wannan wani abu ne da hatta a tsakanin ita da zuciyarta ba ta maganar, ba iya mutanene ba ta yarda da su ba, har zuciyarta ba ta yarda da ita ba, shiyasa ko a wasa ba ta zancen zuci a kan rufaffen sirrinta, sirrin da ƙarewar numfashinta ya fi mata sauƙi, fiye da fallasuwan sirrin.

"Hahahaha!"

Hatsabibi Yautai ya sake fashewa da wani irin dariya.