ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

16

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


#THE TRIO OF TALES 

(THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY)


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.


NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k.


*SHAFI NA SHA SHIDDA*


Cikin tashin hankali suka isa asibitin da aka ce musu Diva tana chan tun cikin daren jiya. Kai tsaye Reception suka tsaya suna tambayar wacce aka kawo emergency.


Nurse din ta kallesu tace

"'yan uwan Suhan?”


Shaly ce ta amsa 

“Eh, tana ina?”


Gaba ta shige suka bita har ɗakin da take kwance, sai da Obafiya ya rike jagaban ya zaunar don jiri ne ya kwashe shi ganinta, likitan dake kanta ne ya kallesu yace 


“Kai ne Babanta?”

“Likita me ya sameta? Su wa suka kawota? Garin yaya hakan ya faru?”

Pascal ya shiga jerowa likitan tambayoyi.


“Ni ma ba zan ce ba amma wani ne ya kawota emergency, hasali ma da asuba ya bar nan don sai da aka yi mata aiki aka iya cire wukar da yake hakarkarinta”

Likitan ya amsa yana sanya hannayensa a aljihu.


Ya kara da cewa


“Ku kwantar da hankalinku she’s out of danger dukda dai sai mun yi hoto mun tabbatar da wukar bai ta’ba kodarta ba tukun za mu tabbatar amma duk wani physical ciwo mun magance shi har ta farka ma ta ba ni layinku na kira kan ta sake komawa saboda alluran da nayi mata”


Idanunsu duka zube kanta tana sanye da wasu fararen kayan asibiti riga da wando, goshinta bandage ne da ya rufe rabin gashin kanta, a wuyanta akawai ciwuka haka hannayenta, a hankali Shaly ta karasa ta dan d’aga rigarta sai ta runtse idanu bruises ne sossai a shafaffen cikin nata bayan katon bandage da aka rufe inda aka yi mata dinki.


Zubash da zee idanunsu suka cika da kwallah, bacin rai da tashin hankali duk sun bayyana a fuskokin mazan, duk wanda zai iya yiwa Diva haka sun san ba karamin dan daba ba ne kuma babu ta yadda mutum daya zai iya hakan, duk sun tafi tunanin waye ne? Sai dai sun san suna da makiya ko ta wani bangare sun taba yara dayawa, sun gagari duk ‘yan dabar zagayen kano.


Har likitan zai fita jagaban yace 

“Likita babu wani hint daga wanda ya kawota? Wanene shi? Ta ya kuka karbeta babu hukuma?”


“Shi karan kanshi hukuma ne, kuma gaskiya ya yi kokari don da bai yi gaggawar kawota ba komai ma zai iya faruwa da ita, shi ya tsaya ya biya kudin komai hatta jini da aka kara mata shi ya bayar saboda babu jinin da zai hau da nata a blood bank….”


Ya ɗan dakata yace 

"Yauwa abu d’aya akwai rubutu da aka yi a bayanta da kaman wuka JJ”


Wani irin mikewa tsaye Jagaban yayi, ya tafi gabas ya dawo yamma da sauri ya nufeta, likitan ya ba shaly umurnin yadda zata dan karkatata, ya bude kafadarta daga sama ga JJ din a zane guda biyu su ma sai da aka dinka don ya shiga sossai.


Gasping Air jagaban yayi ya koma da baya baya ya zauna hannunshi kan bakinshi.


Likitan ya juya ya fita.


Pabloo ne yace 

“Jagaban ka dauki wani haske ne kan waenda suka aikata mata hakan”


Shiru yayi na seconds kan ya girgiza kai sai kuma ya mike zuruf ya nufi fita daga dakin sai kuma ya dakata ya waigo ya kalle su.


“Ku tabbatar duk runtsi baku bar dakin nan ba, ku tabbatar baku dauke idanunku akanta ba, ku kuma tabbatar da duk wani likita ko ma’iakacin asibiti da zai shigo dakin nan kan ya ta’ba ta… ku kula”

Yana kai nan ya fice daga dakin, duk da kallo suka bi shi.


Skipo yace

“Anya jagaban bai da masaniyar abin da ya faru fa diva?”


Pabloo yace 

“Ba wannan ba Skipo, ban taɓa ganin tsoro ko shakka akan idanun Jagaban ba sai yau dole akwai abin da ke faruwa da mu bamu sani ba”


Shaly tace

“Idan harkarshi ne to me ya sako Diva? Idan fa da karar kwana da sai dai mu ji labarin mutuwarta”

Duk jikinsu ya yi sanyi kowa ya nemi wuri ya zauna suka zuba mata idanu.


****


"Tun yana ƙarami na fahimci cewa zai iya zama barazana a gareni, na tsani ganin yana numfashi…”


Ya faɗa cikin ɓacin rai jin mummunan labarin cewa Irshad zai shiga company ranar monday bisa tilastawar mahaifinshi ko da awanni kadan ne ya dinga leƙawa yana yi.


Daga ɗaya ɓangaren aka ce 

"Toh yanzu ya za’a yi da shi?”


“Zan yi tunani a kai amma na rantse ko da zan tafi tsirara sai na tabbatar Irshad bai yi min shamaki da cikon burina ba. Za ka ji ni!”


Yana kai nan ya katse wayar tare da jefarwa kan kujera cikin nazari da zurfafa tunani.


*****


Fusgota yayi ya dora kan wuyanshi tana ihu tana wurge wurgen kafafu da kai mishi duka bai direta ko ina ba sai wani karamin daki.


“Natsu!”

Ya daka mata tsawa 


“Duk rashin kunyarki idan na ga dama zan turmusheki ne kamar cinnaka wallahi, kina cin sa’a J ya hana a aikata miki komai ne da yanzu sai wata ba ke ba!”


Dukunkunewa tayi wuri guda tana hawaye, wani tv ya kunna sai ga Ma’u nan an saka mata bindiga marar kara a goshinta.


Ihu tayi tana kuma rufe baki lokaci guda idanunta duk a waje


“Me…me za ku mata? Don Allah kar ku kasheta kar ku kashe min ‘yar uwa!”

Kuka take yi tana rokonsu. Shadow yayi murmushi


“Ba za mu kasheta ba ne kawai idan kin yi abin da muke so”


“Ko menene kuke so wallahi zan yi, zan yi ko menene amma don Allah kar ku kasheta….”


“Ashe kina da wayo”


Wasu uniform ya watso mata kaman na islamiyya

“Tashi ki saka!”

Ta tattara, ya juya ya fita cikin lokaci kankani ta shirya kamar ‘yar makaranta.


Ya dawo ya bata school bag


“Ki goya wannan jaka a bayanki kamar ‘yar makaranta, ki tabbatar kin natsu ko me zai faru sako ne kawai za ki kai ki dawo karki yiwa kowa magana kuma kar ki bari a yi miki, kika kuskura aka samu akasi haka za ki dawo ki kwashi kwakwalwar yayarki a kasa wallahi”


Kai take gyadawa har ya gama ta goya jakar ta sauke hijabin da ya kai mata gwiwa a kai, ya mata jagora zuwa harabar akwai mota guda daya da wani da yayi shigar bahaushe amma talaka alamun dai acting yake as driver ta shiga baya shadow ya sake ja mata kunne kan suka fice daga gidan.


Duk karfin halinta zuciyarta rawa yake, idanunta cike suke da wani irin tsoro haka matukin ke tafiya cikin garin da ba zata ce ga sunanshi ba kalle kalle take ko zata ga wani signboard tayi kokarin karantawa ko zata fahimci ina suke, ta ya za su kubuta? Ta ina za ta fara neman taimako a yadda suke ta tabbatar tsaff za su iya kashe Ma’u hakan ya sa bata ko motsin kirki cikin motar a hankali suka tsaya inda ake ba da hannu, kasancewar farar glass ce da motar idanunta na ta kalle kalle kaman an ce ta waiga hannun damanta idanunta suka faɗa cikin nashi da a lokacin ya ɗago.


Yanayinta bai mishi kama da wacce take cikin natsuwa ba hakan ya sa ya dan tsawaita kallon sai ya ga ta yi sauri ta dukar da kai kuma ya ga sadda bakin driver din ya motsa, idanun ya kawar yana mayarwa kasa a daidai lokacin da wutar ta ba da kalar green suka wuce ta hanyoyi daban daban.


“Tsaya….”

Ya tsinci kanshi da furtawa haka kawai yan jin zuciyarsa bata natsu ba.